Jump to content

Daƙiƙa:Injila

Daga wikishia

Injila, Bible ko a ce littafi mai tsarki (Larabci: الإنجيل) bisa koyarwar Muslunci suna ne na littafin annabi Isah (A.S), wanda ake jinginashi da cewa littafi ne da Allah ya saukar daga sama zuwa ga annabi Isah (A.S) ƙur'ani ya yi magana daban-danban kan Injila. A wasu gurare yana tabbatar da cewa Injila littafi ne na wahayi daga Allah, kuma yana tabbatar da annabtar Isah Bin Maryam (A.S), yana ambaton wasu busharori a da za su tabbata a gaba kan aiko da Manzon Allah (S.A.W), a wani gurin kuma yana kawo wasu aƙidu da suke rushe haka, kamar aƙidar Trinity (Trinity na nufin Allah ɗaya neamma yana cikin mutane uku: Allah uba, Allah Ɗa, da ruhi mai tsarki) da allantar da Isa ɗan Maryam.

Malam Nasir Makarim Shirazi ɗaya daga cikin maraji'an taƙalidi na Shi'a yana cewa, Injilar asali an ɓatar da ita, babu abin da ya yi saura a cikin sai ɗan wani abu da bai taka kara ya karya ba daga koyarwar annabi Isah wanda aka cuɗanya shi da shirme a cikin Injila da take hannun mutane a yanzu. Wasu daga cikin masana cikin Musulmi, irin su Muhammad Hadi Ma'arifat suna ganin cewa Injili ba littafin da Allah ya saukar ba ne daga sama kan annabi Isah (A.S) wanda wanda aka rubuta shi, a a abin da ya sauka kan Isah (A.S) wata koyarwa ce da wasu busharori na baki waɗanda aka yaɗa su ta hanyar Hawariyyun (Mabiya Annabi Isah) zuwa ga waɗanda suka biyo bayansu da haka har aka rubuta abin da yake cikin waɗannan Linjilolin guda huɗu da ake dasu a yau.

A mahangar Kiristoci Yusu'u bai bar wani abu rubutacce ba, kawai abin da ya bari shi ne koyarwar na baki da tarihin na rayuwa, Kiristoci na da suna ganin maganganunshi da ayyukanshi mun same su ne ta hanyar ɗalibanshi waɗanda suka kasance tare da shi a rayuwarshi ta kira zuwa ga addini wace ta kasance gajeriya. Ya yin da ya mutu mafi yawancin waɗanda suka kasance tare da shi suna ɗauke da abubuwan da suka gani a gare shi kai tsaye, sai suka ga akwai buƙata mai tsanani a rubuta tarihin rayuwarshi da koyarwarshi, to da haka ne dukkan Injila guda huɗu suka bayyana da sunan wasu mutane waɗanda suka yi zamani da manzo kamar Marƙus da Luka, ko kuma zuwa ga ɗalibai masu yaɗa bushara ga Yasu'u misalin Matta da Yohanna, kuma dukkan Injiloli an rubuta su ne da tsohon harshan Yunan wanda shi ne ake amfani da shi a wancan zamani. Kiristoci suna la'akari da waɗanan Injiloli guda huɗu (Matta da Marƙus da Luka da Yohanna) a matsayin litattafai halastattu karɓaɓɓu waɗanda ake dogara kansu daga cikin sauran Injiloli da ake dasu. Su wannan Injiloli guda huɗu ana kiransu da Anajilu Aza'iyya, saboda kamanceceniyarsu wajan jero ko zayyanu abin da ya faru da kuma yadda aka rubutasu.

Injilar Barnaba ko Barnabe ɗaya ce daga cikin Injilolin da ba a yarda da su ba a aƙidar Kiristoci, wanda wannan shi littafin da yake zuwa cikin ƙwaƙwalan Musulmi, saboda shi Barnaba yana ƙarfafar cewa Yeso Almasihu bawan Allah ne kuma manzonshi, ya ce yana tsoron Allah zai ƙasƙantar da kai gabanshi a ranar alƙiyama, saboda ya rubuta shedar Almasihu kan Annabi Muhammad (S.A.W) da cewa shi ne Masihu da ya yi sheda ga Muslunci da Musulmi.

Malaman Muslunci sun yi ƙoƙari wajan tabbatar da sanadi, wato hanyar da aka rawaito waɗannan Injiloli guda huɗu, inda suka bayyana cewa shin sanadin wannan Injiloli ya kai ga annabi Isah ko kuma bai kai zuwa gareshi ba? Shin ya inganta a jingina wannan littafin ga annabi Isah ko a a? Ko kuma al'amarin saɓanin haka ne? Malamai sun yi ittifaƙi kan cewa annabi Isah (A.S) bai bar wannan littafi ba a rubuce a tarihi mai suna Injila, saboda haka abin da aka rubuta an rubuta shi ne da yawunshi amma ta hanyar ɗalibanshi waɗanda ake kira da Hawariyyun, abin yake a bayyane cewa su waɗannan ɗaliban na shi za su iya kuskure.

A Faɗin shugabannin majami'u na farko Yuhanna ya kasance bishara ta ƙarshe da aka rubuta

Littafin Da Aka Saukarwa Da Isah (A.S) Daga Sama

Bisa abin da ya zo a ƙur'ani[1] da ruwayoyi[2] Injila littafi ne da aka saukarwa annabi Isah (A.S)[3] daga sama. Wasu masana sun yi imani cewa yawan ruwayoyi da maganganu kan wannan littafi na Injila yana hana yin shakka kan cewa akwai wani littafi da ake kiranshi da Injila.[4] Bisa abin da malam Nasir makarim Shirazi mai tafsirin ƙur'ani cikin malaman Shi'a yake cewa, wannan littafi na linjila an ɓatar da duk abin da ya ƙunsa, abin da yake cikin Injilar yau, wasu abubuwa ne wanda aka rubuta ta hanyar mabiyan annabi Isah (A.S) wanda aka gwamashi da shirme da tatsuniyoyi[5]

وَ قَفَّيْنا عَلى‏ آثارِهِمْ بِعيسَى ابْنِ مَرْيَمَ مُصَدِّقاً لِما بَيْنَ يَدَيْهِ مِنَ التَّوْراةِ وَ آتَيْناهُ الْإِنْجيلَ فيهِ هُدىً وَ نُورٌ وَ مُصَدِّقاً لِما بَيْنَ يَدَيْهِ مِنَ التَّوْراةِ وَ هُدىً وَ مَوْعِظَةً لِلْمُتَّقين‏َ
Kuma muka bi sawun su da Isa ɗan Maryam, mai gaskata abin da yake gabansa daga cikin Attaura. Kuma muka ba shi Injila, a cikinta akwai shiriya da haske, kuma mai gaskata abin da yake gabansa daga cikin Attaura, da shiriya da wa’azi ga masu tsoron Allah.



(Quran: Ma'ida: Aya ta 46)


Wasu masu bincike a cikinsu akwai Muhammad Hadi Ma'arifat mai bincike kan abin da ya shafi Ulumul ƙur'an, suna ganin cewa saɓanin abin da ya yaɗu tsakanin musulmi na cewa Injila littafi ne da aka saukarwa annabi Isah (A.S), a haƙiƙa littafin Injila ba littafi bane rubutacce wanda aka saukarwa annabi Isah (A.S)[6] a mahangar Muhamad Hadi Ma'arifat abin da ya sauka ga Almasihu, shi ne wata koyarwa ce da busharori na baka waɗanda aka yaɗa su ta hanyar mabiyan annabi Isah (A.S) zuwa waɗanda suka biyo bayansu, to daga nan ne aka rubuta waɗannan abubuwa cikin Injiloli guda huɗu[7] Waɗannan masu bincike sun yi imani cewa abin da ya sauka kan annabi Isah ɗan Maryam shi ne wahayi da hukunce-hukunce na Shari'a da hujjar cewa shi ƙur'ani bai san Injila ba koda a guri guda ɗaya kowa a matsayin littafin annabi Isah (A.S), sai dai ya sanshi a mastayin wani littafi wanda ya ƙunshi wahayi wanda annabi Isah (A.S) ya samu daga ubangijin talikai.[8] amma kiran wannan littafi da Injila ya samu asali ne saboda kalmomi da Isɗilahohi da suka yaɗu a wancan lokacin a gurin Kiristoci domin kafa tattaunawa cikin yanayi mai kyau da wanda ake tattaunawa da shi.[9] Bisa abin wata ruwaya daga Imam Sadiƙ (A.S) cewa Injila an saukar da ita ne kan annabi Isah (A.S) a 12 da 13 cikin wata Ramadan.[10] An ce an saukar da shi ne lokaci guda kuma a dunƙule. Bisa abin da ya zo daga ruwayoyin Injila da wasu littafan da aka saukar daga sama an tara su da haɗe su a gurin imaman Shi'a[11]

Siffofin Injila A Kur'ani Da Ruwayoyi

Kur'ani ya yi amfani da kalmar Injila sau goma sha biyu[12] cikin sigar kalma guda ɗaya tilo cikin ayoyinshi masu tsarki[13] wannan yana nuna maka cewa ƙur'ani bai yarda da inganci injiloli da yawa ba[14] a cikin ayoyin da ƙur'ani ya yi magana da yawun Injila, ya jingina wannan littafi zuwa ga Allah, ya nuna cewa wannan littafin gaskiya ne, kuma ya ambaci bushaouri aiko da annabi Isah (A.S) da faɗin risalarshi[15] cikin aya ta 46 a sauratul Ma'ida, wannan littafi na Injila ya ƙunshi shiriya da haske da wa'azi ga masu tsoran Allah.[16] a cikin aya ta 171 cikin suratul Nisa'i ya yi busharar zuwan annabi Isah (A.S) ya kuma nuna rashin yarda da Trinity da kuma jikkanta Allah.[17]

Ra'ayin Malaman Muslunci Kan Injila

Malaman Musulmi sun ambaci abubuwa guda biyu kan Injila, abu na farko shi ne, an goge abubuwa da yawa da wannan littafi ya ƙunsa ta hanyar waɗanda suka rubuta ta daga baya, kuma abin bai taƙaita da haka ba kawai, an shigar da shirme cikinta. Abu na biyu shi ne cewa an jingine da barin Injilar asali da mantawa da ita, amma abin da yake hannun Kiristoci yanzu wasu litattafai ne da aka rubuta daga baya[18] wasu daga cikin masu bincike sunyi imani cewa akwai dacewa tsakanin sifofin da aka yi magana kansu cikin ruwayoyin da suka zo a litattafan ƴanshi'a da Injilolin da ake dasu guda huɗu (Matta, Marƙus, Luƙa, da Yuhan) abin da yake nuna cewa akwai wannan abu gamagari a tsakanin Injilar da take a yanzu da kuma Injilar da Imamai (A.S) da sahabbansu suke yi magana kanta, ga abubuwa kamar haka; Hana aibata mutane da zargin munafiki, da nisantar maƙaryata, da fifita haƙƙin mutane a kan haƙƙin Allah, da amsa ranar alƙiyama da yin wasicci kan yin afwa da ɗaga-ƙafa.[19]

Injīl al-Rusul (Injila na Manzanni) shi ne tsohon rubutun da aka fi samu daga cikin injiloli, an rubuta shi da harshen Syriac (Ashuri) a kan fatar kifi, kuma yana ajiye a Babban Maktabar Tabriz.[20]

Injila A Wurin Almasihu

Ana kiran kowana ɗaya daga cikin littafi guda huɗu da Injila a matsayin sabon alƙawari a tsakanin kiristoci, ga su kamar haka; Matta, Marƙus, Luƙa da Yohanna[21] ana kiran Injila a cikin litattafan tarihin addinai ga litattafan da aka rubuta a ƙarni na ɗaya na Miladiyya, wanda hadafin wannan litattafai shi ne, adana duk abin da ya shafi aƙida da halayya ta annabi Isah (A.S)[22] mabiya addini Kiristanci sun yi imani cewa annabi Isah (A.S) bai zo da wani littafi ba wanda ake kira da Injila ba kwatakwata, kuma a gurinsu ba a fassara wahayi ba kamar yadda aka fassara shi a gurin Musulmi ba, a mahangar mabiyanshi shi Yesu shi ne jikin Allah da wahayi kuma shi ba manzo ba ne kuma ba mai isar da saƙo bane.[23]

Kiristoci suna la'akari da dukkan Injiloli guda huɗu Matta, Marƙus, Luka da Yohanna a matsayin ingantattu kuma sune litattafai na addini a gunsu, saboda Kiristoci na farko suna ganin waɗannan litattafai daga Allah ne.[24] bisa abin da Tomas Mashal ya ce, malamin coci da aƙida Kiristanci wanda aka haifa a shekara ta 1941 Miladiyya, ya ce Kiristoci ba sa ganin karo tsakanin waɗannan Injiloli guda huɗu, suna ganinsu a mastayin ɗaya wajan inganci da girmamawa a gurinsu.[25] a mahangarsu ƙin yarda da ɗaya daga cikin waɗannan litattafan guda huɗu, hakan yana zama tawayar imanin mutum.[26] a sharar fage na littafin sabon alƙawari, ance Kiristoci sun kasance suna karanta waɗannan litattafai guda huɗu a ranar Lahadi a zaman ibada da suke yi duk sati a Coci, a cikin ƙasa da shekara 150 ta Miladiyya suka fara lissafin wannan litattafai a matsayin wahayi kuma suna lissafa su a matsayin littafi mai tsarki.[27]

Wannan litattafai guda huɗu suna ɗauke da mu'ujizozi na annabi Isah (A.S) da koyarwashi da tarihinshi da laccocin da ya yi da maganganunshi.[28]

Ma'ana

Kada ku yi tunanin cewa na zo domin rushe wata alfarma taku ko annabawa. Ban zo domin rushewa ba, sai dai domin cika ta

Injila Matta babi na 5, aya ta 17

Al'injil kalma ce tilo ya harshan Igriƙ, wacca take nufi bushara[29] bushara ne na zuwa Malakuti na sama, da wata ma'anar hakan yana nufin bushara da zuwan sabon alƙawari[30] ana kiransu da Anajili saboda sun ƙunshi busharorin Malakut da zuwan sabon alƙawari[31] ana cewa wannan busharori a farko suna nufin bushara da gafara da hasken malakut, amma a lokacin Hawariyyun sai aka yi amfani da ita wannan kalma a Injilolin da aka rubuta a matsayin busharar bayyanar ɗan Allah da kuma miƙewarsa da gwagwarmayarshi.[32]

Yadda Aka Haɗa Wannan Injiloli Guda Huɗu Da Mayar Da Su Littafin Addini Karɓaɓɓe

An fara rubuta Linjila a shekara hamsi da biyar a ƙarnin farko na Miladiyya, kuma an fara ne da Linjila ta Marƙus bayan nan sai ta Matta da Lukas da ta Yohanna a ƙarsha ƙarnin na ɗaya[33] Kiristoci sun yi imani cewa maganar Almasihu (A.S) da tarihinshi da duk abin da ya ta'allaƙa da shi ya yaɗu ne da baka a farko[34] har sanda tinanin rubuta wannan abubuwa ya zo musu a ƙarni na ɗaya na Miladiyya, sai wasu suka fara rubuta tarihin annabi Isah (A.S) da maganganunshi[35] lokacin rubuta Injila ya dace da rawar da Bulus ya taka ta kira zuwa ga addini Kiristanci da gina Majami'ai. Inda wasu mutane suka fara wannan rubutu da farawa da tarihin annabi Isah (A.S) da wasu abubuwa da suka faro dangane da shi, kuma an gama wannan rubutu cikin yanayi mabambanci, rubutun ya wakana ne bisa ra'ayin marubutan kuma wannan shi ne ya kai ga samun mabambanta Inajila[36] bisa abin da Tomas mashal ya faɗa, Kiristoci da taimakon Ruhi mai tsarki sun iya zaɓar ɗaya daga cikin Injiloli guda huɗu da aka rubuta, kuma sun yarda da littafi 23 a matsayin Nusus masu tsarki daga Allah[37] amma akwai ra'ayi mabambanci kan lokacin da aka yarda da wannan Injiloli guda huɗu; akwai ra'ayin da yake cewa, an ajiye dukkanin injiloli a gefe guda a Majma'a ƙarɗaja,in banda guda huɗu kawai, hakan ya faro ne a shekara ta 397 Miladiyya, sai aka yarda da cewa waɗanan linjiloli guda huɗu sune litattafai karɓaɓɓu, wannan ya faro ne a ƙarni na biyar[38] Wasu sun yi imani cewa wannan linjiloli sun kasance ana la'akari da su a matsayin wani gadon annabawa da cewa su hujja ce hakan ya faro cikin shekara 150 ta Miladiyya, an soke wannan la'akari ne a shekara ta 170 Miladiyya, duk da wannan imani amma fa ba'ayi magana kansu ba.[39]

Sifofin Wannan Injiloli Guda Huɗu

Akwai shaku kan marubuta wannan Injiloli guda huɗu da jingina su zuwa ga marubutan ba abu ne da yake da tabbbas[40] Husaini Taufiƙi yana faɗa a litttafinshi mai suna "Ashina ba Adyan Buzurg", Kiristoci sun yi imani cewa an rubuta wannan linjiloli ne gudu huɗu ta hanyar Hawariyyun kuma ta hannun ɗalibanshi bayan shekaru masu yawa[41] bisa ra'ayin da Tomas Mashal ya fi karkata gare shi, yana cewa Kiristoci ba sa ganin cewa annabi ne ya rubuta littafin Ahdul Jadid (Sabon alƙawari), sai dai cewa sun yi imani sun rubuta wannan Nassosi ne da Ilhama daga Allah.[42] ya ƙara da cewa harshan da aka rubuta wannan Injiloli a farko shi ne harshen girka.[43]

Al'anajilul Iza'iyya

Kiristoci suna la'akarin linjiloli gudu huɗu (Matta da Marƙus da Luka da Yohanna) a matsayin litattafai na addini da doka waɗanda suke dogara kansu a tsakanin sauran linjiloli da ake da su, guda uku farko ana kiransu da Al'iza'iyya, hakan saboda kamaceceniyar da suke da ita wajan zayyanu abubuwa a dunƙule.[44] Amma ga wasu abubuwa da suka sa Injila ɗin Yohanna ta sha bamban daga sauran ga su kamar haka; a cikin wannan littafi an ambaci mu'ujizozi da ba a ambace su ba a sauran litattafan, kamar canzawar ruwa zuwa giya a ƙana ko kuma raya wani mutum da ake kira La'azar, shigar da laccoci masu tsayi cikin wannan Injilar da kuma nuna hoton Almasihu domin tabbatar cewa annabi Isah (A.S) Allah ne.[45] su wannan Injiloli na Iza'iyya sun fi karkata ga adabi na Yahudanci, amma Injilar Yuhan ana kallonta a matsayin wadda ta tasirantu da Falsafar Yunan.[46]

Linjilar Matta

Injilar Matta ita ce farkon litattafan sabon alƙawari.[47] bisa rahoton Tomas Mashal, ya yi imani da cewa malaman littafi mai tsarki sun yi imani cewa Injilar Matta litattafai ne domin tattaunawa tare da wasu malaman Yahudawa.[48] akwai kace-nace kan lokaci da gurin rubuta wannan littafi, amma ra'ayukan da suka fi lokacin sune kamar haka; shekara 38 Miladiyya, cikin shekara 50 zuwa 60 Miladiyya ko shekara ta 70[49] amma abin da ya shafi guri yana kai-kawo ne tsakanin ƙasar Falasɗinu da kuma garin Anɗakiya a Siriya.[50] wannan littafi yana bayyana Isah (A.S) a matsayin wanda ya zo domin cikasa addinin Yahudanci kuma shi ne babban malami, Annabi Musa (A.S) shi ne mai shari'a sabuwa.[51] ga abin da wannan littafi ya ƙunsa; nasabar annabi Isah (A.S) da yadda aka haife shi, jarrabawar da Shaiɗan ya yi mishi, umarni na kyawawan halaye da aklaƙ ga mutane da ɗalibanshi, mu'ujizozin annabi Isah (A.S) da zaɓin ƴan'aiki guda goma sha biyu, da bayyanar Musa (A.S) da Iliyas (A.S) da kitsa kasheshi da tayar dashi daga kabarinshi.[52] wanda ya rubuta wannan Injila shi ne ɗaya daga cikin ɗaliban annabi Isah (A.S),[53]mutuman da aka ce ya kasance mai tattara haraji kafin ya yi imani da annabi Isah(A.S), Linjilar Matta shi ne littafi mafi daɗewa a cikin litattafan sabon alƙawari, amma masu bincike a yau suna ganin Injilar Marƙus shi ne littafi mafi daɗewa cikin Injilolin da ake da su.[54]

Injilar Marƙus

Littafin Injilar Marƙus ana la'akari da shi a matsayin littafi taƙaitacce kuma mafi daɗewa[55] wanda ya rubuta wannan Injila shi ne Marƙus kuma shi bai kasancce daga ƴan aike ba, ya kasance mabiyi na manzo Biɗrus da ɗalibanshi,[Tsokaci 1][56] ya rubuta wannan Injila a shekara ta 60[57] ko 61[58] ko 70,[59] cikin Italiya ko Rum[60] cikin wannan littafi an ƙarfafi ɓangaren ƴan'adamtaka da wahalhalun annabi Isah (A.S)[61] Linjilar Marƙus ta rabu zuwa gida biyu; a juzi'i na farko yana bayyana wane ne annabi Isah (A.S) da malakutinshi, amma a juzi'i na biyu ya yi magana kan mutuwarshi[62] Marƙus ya tattauna ayyukan annabi Isah (A.S) da gwagwarmayarshi tare da Shaiɗanu da fitar da su da ya yi daga ciwan hauka da yafiyarshi ga masu kuskure da laifi da mu'ujizozinshi.[63] wannan littafi yana bayani kan rayuwar annabi Isah (A.S) tiin lokacin da annabi Yahaya (A.S) ya ce ya yi kuskure da farkon annabtarshi amma bai ambaci nasabarshi da haihuwarshi ba,[64] jumla ta farko a Injilar Marƙus gata kamar haka; farawa da bushara ta Yesu Almasihu ɗan Allah.

Yusu'a ya ce alƙiyama ita ce yin imani da ni kuma koda mutum ya mutu, to za'a tasheshi, amma wanda yake a raye kuma ya yi imani dani, to har abada bazai mutu ba, shin kun yi imani da hakan? Sai ya ce mishi, eh ya ubangijin talikai, nayi imani cewa lalle kai ne Masihu ɗan'allah, kuma kai ne wannan lokacin da zai bayyana a duniya.

Injilar Yohanna Matta babi na 115, aya ta 25-27

Injilar Luka

Amma Injilar Luka ita ce mafi tsayi cikin Injiloli[65] an rubuta ta a tsakanin shekata 70 zuwa ta 90 Miladiyya, da niyar magana da Mushirikan[66] Ruma[67] ana la'akarin wannan Injila ta Luƙa a matsayin littafin da ya keɓanta da bayyana siffofin annabi Isah (A.S) da yarintarshi a matsayin ɗaya daga cikin abin da ya keɓanta da shi.[68] haihuwar annabi Yahaya (A.S) da mu'ujizozin Isa (A.S) masu yawa da aka ambata, da baiwa annabawa (A.S) ƙarfin da ya wuce wanda aka saba da shi da zaɓan mutum 70 domin yin aikin bushara ga mutane, da magana kan rataye mutum da tayar da su daga kabari, wannan duk suna cikin abin da littafin ya ƙunsa[69] kuma a cikin wannan Injila annabawa (A.S) sun yi magana da annabi Isa (A.S) a matsayinshi na ubangiji.[70] cikin wannan Injila dai an gabatar da shi matsayin kammalallen mutum.[71]

Injilar Yuhanna

Sanan nan abu ne cewa Injilar Yohanna shi ne littafi mafi sabunta kan ruyuwar annabi isah (A.S) da maganganunshi, yana ƙarfafa cewa shi Yasu'u yana sama da mutum.[72] kuma shi Yohanna ɗaya daga cikin mutum 12 ne[73] mabiya annabi Isah (A.S) akwai saɓani kan shekarar da aka rubuta wannan littafi,[74] saɓanin ya rabu gida biyu; ra'ayi na farko shi ne ra'ayin gargajiya wanda yake cewa an rubuta wannan littafi ne a ƙarshan ƙarni na ɗaya Miladiyya daga shekara ta 85 zuwa abin da ya yi sama[75] ra'ayi na biyu kuma yana la'akarin tarihin rubuta wannan littafi ya faru ne a shekara ta 50 ko 70 Miladiyya, amma wasu sun karkata zuwa ga shekara 65[76]. A wannan Injila an bawa maganar annabi Isah (A.S) muhimmanci fiye da rayuwarshi, ana kawo maganar annabi Isah (A.S) a matsayin wa'azi, faɗakarwa mai tsayi cikin tinani mai wahalar ganewa.[77] amma wannan marubuci ya bayyana hadafin yin wannan rubutu kamar haka; wannan abubuwa ana rubuta su ne domin mutane su yi imani cewa shi Yesu ɗan Allah ne, idan kuka yi imani zaku yi rayuwa da sunanshi.[78]

Ya zo cikin Injila ta Yahana cewa annabi Isah (A.S) ɗan Allah ne[79] kuma maganar shi ce[80] ya kasance yana nan tin azal[81] kuma a cikin wannan littafi[82] ana kiran annabi Isah (A.S) da cewa shi Allah ne,[83] an faɗi cewa cikin wannan ne aka ambaci Farƙaliɗ ( Abin nufi mai yin gaisuwa ko mai taimako), an ce shi wannan mai taimako zai zo ne bayan annabi Isah (A.S) wanda zai san komai kuma zai mulki duniya.[84]

Ya zo cikin gabatarwar Linjila ta Yohanna a sabon alƙawari, cewa akwai shakku kan wanda ya rubuta wannan Linjila, saboda karo da juna da abubuwa suke yi da rashin futowar abubuwa a fili. An ce wasu abubuwan ɗaliban Yuhanna ne suka ƙara bayan rasuwarshi. An kuma yi imani da cewa wannan littafin an rubuta shi da haɗa shi ne bayan a matakai daban-daban. Bisa ra'ayin marubucin muƙadaddama, mutuman da ya rubuta wannan littafi mai girma a ƙarshe ba a sanshi ba.[85]

A wani ƙaulin Yohanna shine bisharar ƙarshe da aka rubuta. Duk da haka, ya bambanta gaba daya da sauran a cikin gabaɗayan gabatarwa da abubuwan da ke ciki[86]

Injiloli Da Ba A Yarda Da Su Ba

Ƙari kan Linjiloli guda huɗu da ake da su, akwai wasu Linjiloli da ba a yarda da su ba, waɗanda aka sani da "Abukarifa" ko ana kiransu litattafan sabon alƙawari, a coci ba a la'akari da waɗannan Linjiloli[87] daga cikin linjilolin da ba karɓaɓɓu bane akwai, Linjila ta Al'ibraniyin da Masar da ta Biɗrus da Tuma data Filibis da ta Ɗufula.

Lallai Annabawa dukkansu sun zo sai Manzon Allah nan kusa shima zai zo a bayana, saboda Allah yana nufi daga gare ni in share masa hanya..

Injilar Barnaba babi na 36, aya ta 6

Injila ta Barnaba

Ana la'akari da Littafin mai tsarki daga litattafai masu tsarki da basu samu karɓuwa a hukumance ba, waɗanda ya ja hankalin Musulmi, amma a gun Kiristoci suna ganinshi a matsayin wani littafi daba na gaskiya ba,[88] ana cewa shi wannan littafi da irinshi su ɗari uku ba a yarda da su ba kuma an lalata su a wani guri da ake kira da Majma'a Naƙiyya (Shi ne matattarar majami'u na farko a duniya) a shekara ta 325 Miladiyya[89] bayan haka sai Fada-fada (Pastors) suka yi sanarwar cewa waɗannan litattafai suna cikin littafan da aka haramta,[90] amma abin da ya sa aka ƙi yarda da wannan littafi mai tsarki shi ne, rashi dacewar abin da yake cikinshi da abin da su suka yi imani da shi a coci. Kuma a cikin wannan littafi akwai ƙorafi kan manzo Bulus da aƙidarshi.[91]

Injilar Barnaba tasha bamban da sauran injiloli guda huɗu ta fuskoki da yawa:

  • A cikinta akwai rashin yarda da cewa Isah (A.S) Allah ne da cewa shi baɗan Allah ba ne.[92]
  • Cikin wannan Injila ta Barnaba Yesu ya bayyana sau da yawa cewa annabi Muhammad shi ne Almasihu.[93]
  • Bisa abin da ya zo a wannan littafi mai tsarki, tabbas an rataye ɗaya daga cikin manzannin Yesu mai suna Yahuza Al'iskar Buɗi a madadinshi, wanda shi wannan manzo fuskarshi ta jirkita ta zama irin ta Yesu (A.S).[94]

Tabbas Injilar Barnabas tana karo da ƙur'ani da abin da Musulmi sukayi imani da shi. Daga cikin abubuwan da suke karo akwai, cewa mutane ƴa'ƴan Allah ne da cewa su a ɗabi'arsu masu saɓo ne, duk annabawa (A.S) banda Isah (A.S) kamar Ibrahim, Haruna, Ayyub, sun kasance masu saɓo da son Shirka.[95] amma masu binciken Kiristoci suna ganin wannan Linjila an rubuta ta ne a wani zamani wanda bana Almasihu ba ne kuma a gurin daba Falasɗinu ba,[96] Kirista Tum Mashal yana cewa, bisa dalili a tarihi da abin da aka ji a baki, cewa wannan littafi mai tsarki an rubuta shi ne a ƙarshan ƙarni na 16..[97] ta wata fuskar kuma wasu daga cikin Musulmi sun yi imanin cewa wannan Injila tana da inganci.[98]

Sannan akwai saɓani kan wanda ya rubuta wannan littafin. Wasu suna ganin cewa Barnabas laƙabi ne na ɗaya daga cikin masu bisharan Kiristanci mai suna Yusuf, ɗan'ƙasar ƙabarus (Cyprus) wanda ya fito daga gidan Yahudawa, asalinshi yana komawa zuwa ga Lawi ɗa ga annabi Yaƙub (A.S)[99] saboda ƙoƙarin da ya yi wajan yaɗa Yahudanci sai ake kiranshi da sunan Barnabas. Ita kalmar Barnabas tana nufin ɗan'aike mai ƙoƙari,[100] ya kasance amini ga Almasihu (A.S)[101] bisa abin da ya zo a saɓon alƙawari Barnabas wani mutum ne mai biyayya da amana. A ɓangare guda kuma, wasu malamain Kiristoci suna ganin cewa wanda ya rubuta Injila wani Kirista ne ɗan'ƙasar Isfaniya wanda a cikin ƙarni 16 ya karɓi Musulinci.[102]

Matsaloli Da Ƙorafi Kan Injiloli

Tabbas masu suka sun yi suka kan dukkan Injiloli guda huɗu da Saɓon Alƙawari a dunƙule, ga wasu daga ciki:

  • "Rashin cancatar waɗanda suka rubuta wannan linjololi":Kiristoci da kansu sun ce waɗanda suka rubuta wannan linjiloli ba annabawa ba ne ba, saboda haka wasu mutane ne waɗanda basu kuɓuta da yin saɓo ne suka rubuta su, wasu mutane ne gamagari da suka yi imani da Yesu suka rubuta su. An jingina kafurci da rashin yin imani da annabi Isah (A.S) da ƙin yarda da maganarshi a cikin wannan Injiloli ga ƴan'aiken annabi Isah (A.S) da ɗalibanshi a bayyane, da samun saɓani a tsakaninsu, saboda haka ba zai yiwu ba mutum ya sami kwanciyar hankali kan cewa wannan koyarwa ce ta Yesu (A.S).[103]

Tomas Mashal malami Kirista ya ce da yawa daga cikin Kiristoci ba su yarda rashin kuskuren Littafi mai tsarki ba. Kiristoci sun yi imani da cewa sakon da Yesu ya zo da shi daga Allah ne, amma shakalinsa da yadda aka gina wannan littafi, to daga mutum ne, tana kan magangarar kuskure, saboda haka wannan litattafai kamar sauran abubuwan da ɗan'adam ya yake yi ne, wanda akwai dai cikinsu kuma akwai kuskure ciki, saboda haka zai yiwu marubuta wannan litattafai sun yi kuskure cikinsu da sanya tinaninsu irin na ɗan'adam a cikinsu.[104]

  • "Karo da juna da Injiloli suke yi a junansu", wasu matsaloli da karo da juna da yake farowa a tsakanin Injiloli dalili ne kan rashin ingancinsu. Misali akwai bambanci kan nasabar Isah (A.S) a tsakanin Injilar Matta da Luka da Marƙus, a cikin Injilar Matta da Luka an tabbatar da cewa Almasihu ya fito daga zuiyar Dawdu (A.S), amma a cikin Linjila ta Marƙus an ambaci cewa Dawud (A.S) ɗan'reno ne, amma shi Yesu shi ne Allah gare shi, to tambaya anan ta ya ya Yesu (A.S) zai zama ɗa ga annabi Dawud (A.S)? daga cikin karo da ake samu akwai yadda aka kama Yesu (A.S) zuwa da alamar ɗalibinshi maha'inci (Mmai suna Yahuza Al'iskarayuɗi) da ƙissar sake raya shi da taso shi daga kabari.[105]
  • "Kurakurai da shirme da yake cikin wannan Injiloli" kamar aƙidar Tasalis (trinity) da ƙissar sadaukar da kai da annabi Isah (A.S) ya yi domin ceton mutane da nema musu gafara ta hannun wannan malamin coci, duk wannan ƙarairayi ne cikin Injiloli[106] kazalika an jingina kurakurai ga waɗannan Injiloli.[107]

Maƙaloli Masu Alaƙa

Bayanin kula

  1. Suratul Al-Imran, aya ta 3 da ta 4; Suratul Maidah, aya ta 46 da ta 47; Suratul Maryam, aya ta 30; Suratul Hadid, aya ta:27.
  2. Duba: Al-Kulayni, Al-Kafi, 1407H, Mujalladi. 4, shafi. 157; Shaykh Saduq, Man La Yahduruhu Al-Faqih, 1413 AH, juzu'i. 2, shafi. 159.
  3. Makarem Shirazi, Al-Amthal fi Tafsir al-Kitab al-Munazzal, juzu'i. 2, shafi. 389; Zibai Nejad, Masihit-Shenasi-Maqayisah, 1389 SH, shafi 155 da 156; Razavi, “Injil”, shafi na 77 da 83.
  4. Zibayinghad, Messiyat Şhināsi Muqaysa I, 1389 AH, shafi na 156 da 157.
  5. Makarem Shirazi, Al-Amthal fi Tafsir al-Kitab al-Munazzal, juzu'i. 2, shafi. 389.
  6. Duba, Siyanat Alƙur'an Minat Tahrifi, 1428 AH, shafi na 129; Naqavi, "Tadwini Attaura Wa Linjil Az Didgahe Ayate Qur'an", shafi na 19-23; Mu'addab Wa Khabbazian, "Barrasi Farhangi Wa tarikhi Karburde Linjila Dar Qur'an", shafi na 110.
  7. Marifat, Siyanatul Alƙur'an Minatat Tahrifi, 1428 AH, shafi na 129.
  8. Mu'addab Wa Khabbazian, "Barrasi Farhangi Wa tarikhi Karburde Linjila Dar Qur'an", shafi na 112.
  9. Mu'addab Wa Khabbazian, "Barrasi Farhangi Wa tarikhi Karburde Linjila Dar Qur'an", shafi na 110.
  10. Al-Kulayni, Al-Kafi, 1407 AH, juzu'i. 2, shafi. 629.
  11. Duba: Al-Kulayni, Al-Kafi, 1407H, Mujalladi. 1, shafi 225, 227; Safar, Basair Al-Darajat, 1404H, shafi na 132-141.
  12. Duba: Suratul Al Imran, aya ta 3, 48 da 65; Suratul Ma’idah, aya ta 46 da ta 47, 66, 68 da 110; Suratul A’araf, aya ta 157.
  13. Makarem Shirazi, Al-Amthal fi Tafsir Kitabillahil al-Munazzil, 1421 AH, juzu'i. 4, shafi na 221-224.
  14. Asadi, “Injil ƙur’an,” shafi na 31.
  15. Rizvi, “Injil,” shafi. 83; Asadi, "Injil Kur'an," shafi na 31-37.
  16. Makarem Shirazi, Al-Amthal fi Tafsir Kitabillahil al-Munazzil, 1421 AH, juzu'i. 4, shafi. 396.
  17. Makarem Shirazi, Al-Amthal fi Tafsir Kitabillahil al-Munazzil, 1421 AH, juzu'i. 4, shafi. 221-224.
  18. Radawi, “Linjil”, shafi na 84 da 85.
  19. Duba: Haidari da Khosravi, “Linjila Dronmayh Dar ruwayate Shi’i,” shafi na 108-116.
  20. «قديمي‌ترين انجيل جهان در تبريز»Markaze Dayiratel Ma'arif Bozorg Islami.
  21. Michel, Kalame Masihi, 1381 AD, shafi na 43.
  22. Radawi, "Linjil", shafi na 77.
  23. Michel, Kalame Masihi, 1381 AH, shafi na 49 da 50.
  24. Tawfiqi, Ashnayi Ba Adyan Buzorg, 1389 AH, shafi. 176.
  25. Michel, Kalame Masihi, 1381 AD, shafi na 44.
  26. Tawfiqi, Ashnayi Ba Adyan Buzorg, 1389 AH, shafi. 176.
  27. Ahade Jadid, 1394 A.M., Duramdi Barr Ahade Jadid, shafi na 58.
  28. Michel, Kalame Masihi, 1381 AH, shafi na 43; Asadi, “Injil ƙur’an”, shafi na 27.
  29. Rk: Ahade Jadid, 1394 AH, shafi na 85; Michel, Kalame Masihi, 1381 AH, shafi na 43.
  30. Tawfiqi, Ashnayi Ba Adyan Buzorg, 1389 AH, shafi. 169.
  31. Zibaei Nejad, Messiyat Shenasi Maqaysa A, 1389 AH, shafi. 139.
  32. Lajordi, “Linjil,” shafi na 318.
  33. Soleimani Ardestani, Sairi dar Adyan Zinda Jahan, 1387 AH, shafi. 217.
  34. Michel, Kalame Masihi, 1381 AD, shafi na 43, 44 da 50.
  35. Radawi, "Injil", shafi na 78.
  36. Radawi, "Injil", shafi na 78.
  37. Michel, Kalame Masihi, 1381 AD, shafi na 51.
  38. Radawi, “Linjil”, shafi na 79 da 80.
  39. Ahade Jadid, 1394 A.M., Duramdi Barr Ahade Jadid, shafi na 60.
  40. Soleimani Ardestani, Sairi dar Adyan Zinde Jahan, 1387 AH, shafi na 218 da 219.
  41. Tawfiqi, Ashnayi Ba Adyan Buzorg, 1389 AH, shafi. 174.
  42. Michel, Kalame Masihi, 1381 AD, shafi na 43.
  43. Ahade Jadid, 1394 A.M., Duramdi Barr Ahade Jadid, shafi na 64; Michel, Kalamen Masihi, 1381 AH, shafi na 42.
  44. Duba: Ahade Jadid, 1394 A.H., Mukaddime Injilhaye Nazir Nazir, shafi na 85; Muhammadian, Dayrat al-Ma'arif, Kitabe Muƙaddas, 1381 AH, shafi na 259; Tawfiqi, Ashnayi Ba Adyan Buzorg, 1389 AH, shafi. 170.
  45. Ahade Jadid, 1394 AH, Muƙaddime Injil Wa Risalahaye Yohanna, shafi na 451.
  46. Zibayinjad, Masihiyat Shinasi Meqayise'i, 1389 AH, shafi. 146; Soleimani Ardestani, Sairi dar Adyan Zinde Jahan, 1387 AH, shafi na 214 da 215.
  47. Lajordi, “Injil,” shafi na 318.
  48. Michel, Kalame Masihi, 1381 AD, shafi na 45.
  49. Nikzad, Naqze Wa Barrasi Kitabe Muƙaddas, 1380 AH, shafi na 42.
  50. Nikzad, Naqze Wa Barrasi Kitabe Muƙaddas, 1380 AH, shafi na 42.
  51. Michel, Kalame Masihi, 1381 AH, shafi na 4; Razavi, “Injil”, shafi na 80.
  52. Zibaei Nejad, Messiyat Shenasi Maqaysa A, 1389 AH, shafi. 139.
  53. Zibaei Nejad, Messiyat Shenasi Maqaysa A, 1389 AH, shafi. 139.
  54. Nikzad, Naqze Wa Barrasi Kitabe Muƙaddas, 1380 AH, shafi na 42.
  55. Michel, Kalame Masihi, 1381 AH, shafi. 46; Tawfiqi, Ashnayi Ba Adyan Buzorg, 1389 AH, shafi. 171; Zibayinjad, Masihita ShinasiMeqeyse'i, 1389 AH, shafi. 146.
  56. Nikzad, Naqze Wa Barrasi Kitabe Muƙaddas, 1380 AH, shafi na 43.
  57. Michel, Kalame Masihi, 1381 AH, shafi na 44; Nikzad, Naqze Wa Barrasi Kitabe Muƙadda, 1380 AH, shafi na 102
  58. Nikzad, Naqze Wa Barrasi Kitabe Muƙadda, 1380 AH, shafi na44.
  59. Soleimani Ardestani, Sairi dar Adyan Zinde Jahan, 1387 AH, shafi. 217; Rizvi, “Injil,” shafi. 80.
  60. Muhammadian, Da'iratul Ma'arif Kitab Muƙaddas, 1381 AH, shafi na 264.
  61. Michel, Kalame Masihi, 1381 AD, shafi na 46.
  62. Ahade Jadid, 1394 A.M., Muƙaddime Injilhaye Nazir, shafi na 103 da 104.
  63. Michel, Kalame Masihi, 1381 AD, shafi na 46.
  64. Zibaei Nejad, Messiyat Shenasi Maqaysa A, 1389 AH, shafi. 140.
  65. Zibaei Nejad, Messiyat Shenasi Maqaysa A, 1389 AH, shafi. 140.
  66. Zibaei Nejad, Messiyat Shenasi Maqaysa A, 1389 AH, shafi. 148.Radawi, “Injil”, shafi na 80-81.
  67. Muhammadian, Dayiratul Alma'aif Ikatabe Muƙaddas, 1381 AH, shafi na 268.
  68. Zibaei Nejad, Messiyat Shenasi Maqaysa A, 1389 AH, shafi. 140
  69. Zibaei Nejad, Messiyat Shenasi Maqaysa A, 1389 AH, shafi. 140
  70. Duba: Injil Luka, Babi na 11, Aya ta 1.
  71. Zibaei Nejad, Messiyat Shenasi Maqaysa A, 1389 AH, shafi. 141
  72. Tawfiqi, Ashnayi Ba Adyan Buzorg, 1389 AH, shafi. 171.
  73. Zibayi Nejad, Messiyat Shenasi Maqaysayi, 1389 AH, shafi. 141; Nikzad, Naqze Wa Barrasi Kitabe Muƙaddas, 1380 AH, shafi. 45.
  74. Ahade Jadid, 1394, Muƙaddime Injil Wa Risalehaye Yohanna, shafi na 463-465.
  75. Muhammadian, Da'iratul Ma'arif Kitabae Muƙaddas, 1381 AH, shafi na 270 da 271.
  76. Michel, Kalame Masihi, 1381 AD, shafi na 48.
  77. Michel, Kalame Masihi, 1381 AD, shafi na 48.
  78. Injil Yohanna, Babi na 29, Aya ta 31.
  79. Duba: Injil Yohanna, Babi na 1, Aya ta 49 da Babi na 5, Aya ta 19-27.
  80. Duba: Injil Yohanna, Babi na 1, Aya ta 1-3.
  81. Zibayi Nejad, Messiyat Shenasi Maqaysayi, 1389 AH, shafi. 141
  82. Injil Yohanna, Babi na 1, Aya ta 1 da Babi na 20, Aya ta 28.
  83. Ahade Jadid, 1394 AH, Muƙaddime Injil Wa Risalahaye Yohanna, shafi na 460
  84. Zibayi Nejad, Messiyat Shenasi Maqaysayi, 1389 AH, shafi. 141
  85. Duba: Ahade Jadid, 1394 AH, Muƙaddime Wa Risalahaye Yohanna, shafi na 459-462.
  86. Life.liegeman:https://life.liegeman.org/ha/whats-it-all-about/christn/historymaker/ntdocs/ntdocs6/
  87. Michel, Kalame Masihi, 1381 AD, shafi na 51.
  88. Tawfiqi, Ashnayi Ba Adyan Buzorg, 1389 AH, shafi. 170.
  89. Elhami da Naderi, “Barnaba”, shafi na 213.
  90. Zibayinghad, Messiyat Shenasi Muqaysa I, 1389 AH, shafi na 162 da 163.
  91. Zibayinghad, Messiyat Shenasi Muqaysa I, 1389 AH, shafi na 164.
  92. Linjilar Barnaba, Babi na 52, ayoyi 12-15 da Babi na 53, aya ta 35.
  93. Duba: Injil Barnaba, Babi na 43, Aya ta 30 da Babi na 82, Aya ta 9-19.
  94. Motamadi, “Barnaba,”shafi, 19; Al-Hami da Naderi, “Barnaba,” shafi. 214.
  95. Duba: Haidar da Degrain, “Injil Barnaba Dar Ta'aruz Ba Kur'an Kareem,” shafi na 7-28.
  96. Motamadi, “Barnaba,” shafi. 19.
  97. Michel, Kalame Masiha, 1381, shafi na 53.
  98. Duba: Injil Barnaba, Muƙaddime Sardar Kabli, shafi na 297-313.
  99. Motamadi, “Barnaba,” shafi. 17.
  100. Zibaei Nejad, Messiyat Shenasi Maqaysa A, 1389 AH, shafi. 161.
  101. Zibaei Nejad, Messiyat Shenasi Maqaysa A, 1389 AH, shafi. 161.
  102. Michel, Kalame Masihi, 1381, shafi na 53.
  103. Nikzad, Naqze Wa Barrasi Kitabe Muƙaddas, 1380 AH, shafi na 103-109.
  104. Michel, Kalame Masihi, 1381 AD, shafi na 27.
  105. Nikzad, Naqze Wa Barrasi Kitabe Muƙaddas, 1380 AH, shafi na 119-140
  106. Nikzad, Naqze Wa Barrasi Kitabe Muƙaddas, 1380 AH, shafi na 140-149.
  107. Nikzad, Naqze Wa Barrasi Kitabe Muƙaddas, 1380 AH, shafi na 149-160.

Tsokaci

  1. Ana ɗaukar Biɗrus a matsayin mafi girma daga cikin manzannin Almasihu. Sunansa na asali Shi ne Sham'un, kuma Isa (A.S) ya sanya masa suna Bitrus (ma’ana Dutse), ya kuma zartar da shi a matsayin dutse na asali wajen gina coci da al’umma ta Kirista.” (Ɗauke daga: Taufiqi, Ashna’i ba Adiyan Bozorg, 1389 SH, shafi na 148.)

Nassoshi

  • Ali Asadi«انجيلِ قرآن», Nashreya Marafat, Shamarah 120, Azar 1386 A.M.
  • Heydari, Hossein dan Rezvan Khosravi,«درون مايه انجيل در روايات شيعي»، Dofsalnameh Hadith Pajohi, Lamba ta 17, Bazara da Lokacin Rana 1396 SH.
  • Muaddib, Sayed Reza Da Meysam Khabbazian,«بررسي فرهنگي تاريخي كاربرد انجيل در قرآن», Karatun Alqur'ani na Faslnama da Farhang na Musulunci, lamba 3, Al-Kharif 1396 A.H.
  • Rasol Rezawi«انجيل»، Dar Faslnama Islamic Kalam, Shamara 49, Bahar 1383 Sh.
  • Al-Kulaini, Muhammad bin Ya‘qub, Al-Kafi, Tehran, Dar al-Kutub al-Islamiyya, bugu na huɗu, 1407 H.
  • Al-‘Ahd al-Jadid, fassarar Piroz Sayyar, Tehran, Nashr Ni, 1394 SH.
  • Haidar, Hossein da sauran marubuta,«انجيل برنابا در تعارض با قرآن كريم»، Sanin Addinai, Fitowa ta 21, Lokacin hunturu 1393 AH.
  • Husain Naqawi«تدوين تورات وانجيل از ديدگاه آيات قرآن»، Mujallar bayan watanni uku-uku, Marafat Adyan, Ginin 9, Zamistan 1390 A.M.
  • Ibn Shu’bah Harani, Hasan bin Ali, Tuhaf al-‘Uqul, Qum, Jami’ar Malamai, 1404 H.
  • Ilhami, Dawud wa Nigar Nadari, “Barnaba”, a cikin Danishnama Jahan Islam (juz’i na 3), ƙarƙashin kulawar Ghulam Ali Haddad Adel, Tehran, Bunyad Da’irat al-Ma’arif Islami, bugu na biyu, 1378 SH.
  • Injil Barnaba, fassarar Haydar Quli Sardar Kabuli, Tehran, Nashr Niyayish, 1380 SH.
  • Lajurdi, Fatima, …«انجيل» Dar Da’irat al-Ma’arif-e Bozorg-e Islami, Vol. 10, Tehran, Markaz Da’irat al-Ma’arif-e Bozorg-e Islami, 1380H.
  • Life.liegeman[1]
  • Makarim Shirazi, Nasir, Al-Amthal fi Tafsir Kitab al-Munzal, 1421 H., Tehran, Dar al-Kutub al-Islamiyya, bugu na goma, 1371 SH.
  • Ma‘rifat, Muhammad Hadi, Siyanat al-Qur’an min al-Tahrif, Qum, al-Tamhid, bugu na farko, 1428 H.
  • Michel, Thomas, Kalam Masihi, fassarar Husayn Tawfiqi, Qum, Markaz Mutala‘at wa Tahqiqat Adiyan wa Madhahib, 1381 SH.
  • Muhammadiyan, Bahram, Da’irat al-Ma’arif Kitab Muqaddas, Tehran, Sarkhdar, 1381 SH.
  • Mu‘tamidi, Mansur, “Barnaba” a cikin Da’irat al-Ma’arif Bozorg Islami, juz’i na 12, Tehran, Markaz Da’irat al-Ma’arif Bozorg Islami, 1383 SH.
  • Nikzad, Abbas, Naqd wa Barrasi Kitab Muqaddas, Qum, Markaz Pajuhesh-hayi Islami Sada wa Sima, 1380 SH.
  • Saffar, Muhammad bin Hasan, Basair al-Darajat fi Fadail Aal Muhammad, Qum, Maktabat Ayatullah al-Mar’ashi al-Najafi, bugu na biyu, 1404 H.
  • Shaykh Saduq, Muhammad bin Ali bin Babawayh, Man la Yahduruhu al-Faqih, Qum, Dar al-Nashr al-Islami ta Jami’ar Malamai a Huzar Ilmiyya Qum, bugu na biyu, 1413 H.
  • Sulaymani Ardistani, Abdulrahim, Siri dar Addinan Rayayyun Duniya (banda Musulunci), Qum, Ayat al-‘Ishq, bugu na biyu, 1387 SH.
  • Tawfiqi, Husayn, Ashna’i ba Adiyan Bozorg.
  • Zibayi Nejad, Muhammad Rida, Masihiyya-shenasi Muqayisayi, Tehran, Soroush, bugu na uku, 1389 SH.
  • قديمي‌ترين انجيل جهان در تبريز»،Cibiyar Kundin Tarihi na Musulunci, Ranar Bugawa: 10 Esfand 1394 SH, Ranar da aka Yi Bita: 20 Esfand 1401 SH.