Mu'ijizozin Annabi (S.A.W)

Daga wikishia

Mu'ujizozin Annabi, (Larabci: مُعجزات النّبي (ص)) abubuwa ne da suka saɓa da yadda ɗan Adam ya saba rayuwa, Allah yake gudanar da su ta hanyar Manzonsa (S.A.W), domin tabbatar da annabtar shi, kuma akwai mu'ujizozi da yawa a tarihi waɗanda suka faro ga annabi fiyayyan halitta Muhammad (S.A.W), su mu'ujizozin sun kasu gida biyu, mu'ujizozi na Ma'anawi da kuma mu'ujizozi na zahiri ma'ana waɗanda za a iya gani ko taɓawa ko ji da sauransu. girma ɗaya ne daga cikin mu'ujiza mai muhimmmanci wanda ya wanzu ga Annabi Muhammad (S.A.W) saɓanin sauran annabawa, kamar yadda dawo da rana bayan faɗuwa da tsaga wata gida biyu duka su na daga cikin mu'ujizozi da aka gani na Annabi Muhammad (S.A.W), kuma ya zo a cikin wasu litattafai cewa, halayya ta gari tana daga cikin mu'ujizozin Annabi waɗanda ba a ganin su da ido ko taɓawa da dai sauransu....

Mu'ujiza

Tushen Kasida:Mu'ujiza

mu'ujiza ita ce yin wani abu wanda ya saɓa al'adar yadda mutane suke rayuwa kuma ita mu'ujiza ta fi karfin mutane su zo da irinta, kuma Allah ne yake aiwatar da ita ta hanyar Annabawa saɓanin al'ada domin tabbatar da annabtarsu a yayin da aka ƙalubalance su.[1]

Adadin Mu'ujiza

Haƙiƙa an kawo mu'ujizozi da yawa na annabi Musulinci Muhammad (S.A.W), inda Ibnil Jauzi ya ce wasu litattafai sun kawo mu'ajizi dubu ga Annabi.[2] kamar yadda Ibni Kasir ya kawo mu'ujizozi da yawa a cikin littafinshi mai suna mu'ujizar Annabi, kuma shima ya raba mu'ujizozi zuwa gida biyu ta Ma'anawiyya da Hissiyya (wato mu'ujizar da ba'a ganinta da kuma wacca za a iya gani) daga cikin mu'ujizozin shi na Ma'anawiyya akwai saukar da Alƙur'ani da kuma kyawawan halaye da tarihin annabtarshi, amma mu'ujizozinshi na Hissiyya sun rabu zuwa waɗanda suke da alaƙa da abin da ya faru a sama da kuma waɗanda suke da alaƙa da ƙasa, amma mu'ujizozi na hissiyya waɗanda suke da alaƙa da ƙasa, daga cikinsu akwai waɗanda suke da alaƙa da daskaraun abubuwa da kuma waɗanda suke da alaƙa da dabbobi.[3]

Alƙur'ani Mai girma

Tushen Kasida: I'ijazin Kur'ani

Alƙur'ani mai girma mu'ujiza ce matabbaciya ta Annabi Musulinci Muhammad (S.A.W), mu'ujizar alƙur'ani tana nufin cewa shi ƙur'ani littafi ne na masamman wanda ya sha banban da duk wata magana da shi ba, ta fuskacin kalmomi da ma'ana da tarkibinshi da sauransu,tabbas ɗan adam ba zai iya ƙirƙirar irinshi ba, shi ƙur'ani ba maganar mutum bane, maganar ubangijin talikai ce.[4] domin tabbatar da mu'ujizar ƙur'ani Allah ya ƙalubalanci ɗan adam a cikin ayoyi da yawa cewa su zo da irinshi idan sun isa. ƙalubalanta da Alƙur'ani ya na nufin, Allah buƙata daga waɗanda basu yarda da ƙur'ani ba waɗanda suke da fasaha ta Larabci da su zo da irinshi idan sun isa,[5] idan har suka kasa kawo irinshi, to hakan zai zamo dalili na cewa ƙur'ani mu'ujiza ne kuma annabtar annabi musulinci Muhammad gaskiya ce.[6] mu'ujizozi na Hissiyya (waɗanda za a iya gani ko taɓawa)

Wasu mu'ujizozin Annabi musulinci (S.A.W) sun haɗa da aiyuka ko abubuwa waɗanda suka saɓa al'adar mutane waɗanda zai yi wu a gan su ko a ji su ko a taɓa su ga wasu masu muhimmanci daga cikinsu:

Tsaga Wata Zuwa Gida Biyu

Rabuwar wata gida biyu ɗaya ce daga cikin mu'ujizozi da musulmi suka yi imani da cewa,annabi ya yita ne domin buƙatar da Mushirikai sukayi daga gareshi, kuma wannan mu'ujiza ta faro ne a shekarar farko ta annabtarshi, a wannan mu'ujiza ne annabi ya nuna wata da ɗan yatsansa, sai wata ya rabu gida biyu, kuma akwai riwayoyi da yawa da suka kawo wannan mu'ijiza,[7] malaman tafsiri da dama sun yi imani da cewa, ayoyin farko na surar ƙamar suna nuni ne kan wannan mu'ujiza.[8] Allah maɗaukaci ya na cewa,

﴿اقْتَرَبَتِ السَّاعَةُ وَانْشَقَّ الْقَمَرُ * وَإِنْ يَرَوْا آيَةً يُعْرِضُوا وَيَقُولُوا سِحْرٌ مُسْتَمِرٌّ * وَكَذَّبُوا وَاتَّبَعُوا أَهْوَاءَهُمْ وَكُلُّ أَمْرٍ مُسْتَقِرٌّ

﴾.[9]

Dawo Da Rana

Tushen Kasida: Dawo Da Rana

ɗaya daga cikin abubuwan al'ajabi da aka ambata a ruwayoyi da littattafan tarihi, shine batun dawo da rana. A cikin wannan waki'ar ne rana da ta faɗi ta dawo wa Imam Ali (A.S) domin ya yi sallar la'asar a lokacinta. Ya zo a wasu litattafai cewa rana ma an dawo da ita ne saboda Yusha'u bin Nun wanda yake shi ne ya kasance magajin Annabi Musa (A.S), sau biyu,[10] aka dawowa da Imam Ali (A.S) rana sau ɗaya a zamanin Manzon Allah (S.A.W) da kuma bayan wafatinshi.[11]

Wasu Mu'ujizozi Daban

Ruwa ya gudana daga tsakanin yatsun Manzo (S.A.W), Bukhari ya ruwaito daga Anas ɗan Malik cewa, wata rana mutane sun so yin sallar la'asar a bayan Manzon Allah (S.A.W) ba su sami ruwan alwala ba. sai Manzon Allah (S.A.W) ya sanya hannunsa a cikin kwarya, ya umurci mutane da su yi alwala daga gare ta, sai ruwa ya fara fitowa daga tsakanin ‘yan yatsunshi tsira da aminci su tabbata a gareshi, sai suka yi alwala dukkansu.[12]

Tafiyar bishiya zuwa ga Manzo (S.A.W) An ruwaito daga Imam Ali (A.S) a cikin hudubar ƙasi'a cewa wasu shehunan kuraishawa sun zo wurin Manzon Allah (S.A.W) wata rana suka ce ya kira bishiya ta zo wurinshi, kuma ta tsaya a gabanshi, domin su yi imani da annabtarshi, sai Manzon Allah (S.A.W) ya yi umarni cewa bishyar ta tumɓuko daga tushanta da yardar Allah, kuma ta zo ta tsaya a gabanshi,sai bishiyar ta tunɓuko daga gurinta,ta zo gaban annabi amincin Allah ya tabbata a gareshi ta tsaya, amma duk da haka ba su yi imani da Annabi ba,sai suka siffanta shi da cewa shi mai sihiri.[13]

Tasbihi da tsakuwa ta yi a hannun Manzon Allah (S.A.W) hadisin da aka rawaito daga Anas annabi ya cika hannunshi da tsakuwa, sai suka yi tasbihi a cikin hannunshi, san nan ya zuba su a hannun Ali, suka yi tasbihi a hannunshi shi ma, har sai da muka ji tasbihinsu a hannunsu, sai ya zuba su a hannunmu, sai ya zuba su a hannunmu amma ba su yi tasbihi ba.[14]

An ruwaito wasu mu'ujizozi daga Manzon Allah (S.A.W) da suka haɗa da: yin magana da namun daji da dabbobi da tsuntsaye da ba su labarin abin da suke ci da abin da suke ajiyewa a cikin gidajensu...[15]

Mu'ujizar Kyawawan Halaye

Ya zo a cikin wasu litattafai cewa, ɗaya daga cikin mu'ujizozin Manzon Allah (S.A.W) ita ce kyawawan dabi'unshi,[16] kuma akwai wata sabuwar fahimta da masu binciken Musulunci na wannan zamani suka tafi a kai,ita ce kasa mu'ujizar Manzon Allah (S.A.W) zuwa gida uku: Alkur'ani, halaye, da sauran mu'ujizozi. Dabi'un Manzon Allah (S.A.W) ana ganinsu ƙasa da Alkur'ani, kuma sun fi sauran suna sama da sauran mu'ujizozin na annabi; domin kuwa Alkur'ani magana ce da aiki na Allah, alhali kuwa halayya aikin Annabi (S.A.W), duk da cewa shima aikin annabi daga Allah ne. Haka nan akwai kamanceceniya tsakanin wahayi da dabi'un annabi, kasancewar sun kebanta da matsayin annabin da yake cikwamakin annabawa, kuma wannan ba abu ne mai sauki ga waɗanda suka gabata ba,ko kuma ga waɗanda za su zo daga baya ba, kuma haka ne zai sa akalaƙ da halayyar annabi ya yiwa mutane wahala, saboda haka halayyarshi abin girmamawa ce sosai, kuma saboda haka ne yasa ɗabi'ushi suke da tasiri a tarihin Musulunci.[17]

Bayanin kula

  1. Al-Mufid, Al-Nukat Al-Itiqadiyya, shafi na 35; Misbah Al-Yazdi, Dorus fi akida Islamiyya, shafi na 253.
  2. Ibn al-Jawzi, Al-Mutazim, juzu'i na 15, shafi na 129.
  3. Ibn Kathir, Mu’ujizat Annabiyi, shafi na 7-57.
  4. Ibn Kathir, Mu’ujizat Annabiyi, shafi na 7-8; Al-Subhani,Muhazarat fi ilahiyyat, shafi na 289-290.
  5. Al-Sabzwari, Asrar Al-Hikam, juzu'i na 1, shafi na 472.
  6. Al-Sabzwari, Asrar Al-Hikam, juzu'i na 1, shafi na 473; Al-Baqalani, Ihjaz Kur’ani, shafi na 161-162; Ibn Kathir, Mu'ujizat Annabi, shafi na 7-8.
  7. Al-Majlisi, Bihar Al-Anwar, juzu'i na 17, shafi na 355.
  8. Al-Tabarsi, Majma’ al-Bayan, juzu’i na 9, shafi na 282; Al-Fakhr Al-Razi, Mafatih Al-Ghayb, juzu'i na 29, shafi na 337.
  9. القمر: 1 ــ 3.
  10. Al-Saduq, Min La Yahdrahu Al-Faqih, juzu'i na 1, shafi na 203; Al-Mufid, Al-Irshad, juzu'i na 2, shafi na 385.
  11. Al-Dailami, Irshad al-Qulub, juzu'i na 1, shafi na 346; Al-Mufid, Al-Irshad, juzu'i na 1, shafi na 346; Al-Rawandi, Kisasul Anbiya, shafi na 291-292; Al-Saduq, Min La Yahdrahu Al-Faqih, juzu'i na 1, shafi na 203.
  12. Bukhari, Sahihul Bukhari, juzu'i na 3, shafi na 310.
  13. Nahj al-Balagha, hadisi na 194.
  14. Al-Rawandi, Al-Kharayj wal-Jawarih, juzu'i na 1, shafi na 47; Al-Majlisi, Bihar Al-Anwar, juzu'i na 41, shafi na 252.
  15. Al-Masoudi, Isbatul Wasiyya, shafi na 119.
  16. Ibn Kathir, Mu’ujizat Annabi, shafi na 17.
  17. Faramarz Qaramalki, Aklak Hirfeyi, 157.

Nassoshi

Kor'an.

  • Nahj Al-Balagha.
  • Ibn al-Jawzi, Abd al-Rahman bin Ali, Al-Muntazim fi Tarikh al-Muluk wa'l-umam, gyara: Muhammad Abd al-Qadir Atta, Mustafa Abd al-Qadir Atta, Beirut, Dar al-Kutub al-Ilmiyyah, 1st edition, 1412 AH/1992 AD.
  • Ibn Kathir, Ismail bin Amr, Mujizat Annabiyi, maigyara: Ibrahim Amin Muhammad, Cairo, Endowment Library, D.T.
  • Al-Baqilani, Abu Bakr, Ijazul Kur'an', commentator: Abu Abdul Rahman Awaida, Beirut, Dar Al-Kutub Al-Ilmiyyah, 1421 AH.
  • Al-Bukhari, Muhammad bin Ismail, Sahih al-Bukhari, Beirut, Dar Ibn Kathir, 3rd edition, 1407 AH.
  • Al-Dailami, Hassan bin Muhammad, Irshadul kulub, Qom, Al-Sharif Al-Radi, 1st edition, 1412 AH.
  • Al-Rawandi, Qutb al-Din, Alkhara'iz wal jawari, edita by: Sayyed Muhammad Baqir al-Muwahid al-Abtahi, Qom, Imam al-Mahdi Foundation peace be upon him, 1st edition, 1409 AH.
  • Al-Rawandi, Qutb al-Din, 'Kisas Anbiya, Mashhad, Mu'assasa Bincike na Musulunci, 1409H.
  • Al-Subhani, Jaafar, Muhazarat Ilahiyyat', takaitaccen bayani:Mai bincike Ali Al-Rabbani, Qum, Mu'assasa Imam Al-Sadiq {{A.S}, bugu na 19, 1435H.
  • Al-Sabzwari, Muhammad Baqir, 'Asrarul hikam, , bugun: Karim Al-Faydi, Qum, Publications na Addini, 1383H.
  • Al-Saduq, Muhammad bn Ali bn Al-Hussein, Wanda ba ya halartan malamin fikihu Qum, Mu'assasa Madaba'ar Musulunci, bugu na 2, 1413 Hijira.
  • Al-Tabarsi, Al-Fadl bin Al-Hasan, Al-Bayan Complex, Beirut, Al-Alami Publications Foundation, bugu na daya, 1415 AH/1995 miladiyya.
  • Al-Fakhr Al-Razi, Muhammad bin Omar, Tafsirul kabir', Beirut, Gidan Rayar da Al'adun Larabawa, bugu na uku, 1420H.
  • Al-Majlisi, Muhammad Baqir, Bihar Al-Anwar, Beirut, Dar Ihya Al-Arabi Heritage, bugu na uku, 1403H/1983 miladiyya.
  • Al-Masoudi, Ali bin Hussein, ' Isbatul wasiyyar Imam Ali bin Abi Talib Template:A.S, Qom, Ansar, 1423 Hijira.
  • Al-Mufid, Muhammad bn Muhammad bn al-Nu`man, 'Irshad fi marifati hujajillahi alal ibad Qum, Taron Duniya na Millennium na Sheikh Al-Mufid, bugu na 1, 1413 AH.
  • Al-Mufid, Muhammad bin Muhammad bin Al-Numan, Nukat Itikadiyya Qum, taron duniya na Sheikh Al-Mufid, 1413H.
  • Framarz Karamliki, Ahad, "'Da'a na Sana'a (Kwararrun Da'a)'", D.M., D.N., D.T.
  • Misbah Al-Yazdi, Muhammad Taqi, Durus fi akida islamiyya, D.M., Mu'assasa Al-Huda, bugu na 4, 1424H.