Ali Bn Muhammad Samari
Ali Bin Muhammad Samari (Larabci: علي بن محمد السمري) ko Samuri wanda ya mutu shekara ta 329 hijiri kamari shi ne na hudu cikin jerin Na'ibai guda hudu na Imam Zaman (A.F) an ayyana shi a Mukamin Na'ibanci daga shekara 326-329 bayan mutuwar Husaini Bin Ruhu Naubekti, a zamanin Na'ibanci ya kasance matsayin `dan tsakani tsakanin Hazrat Mahadi (A.F) da `Yan Shi'a, mutanen suna kawo masa hakkokin shari'a, kuma ya kasance daga Sahabban Imam Asakari (A.S) akwai rahotan musayan wasiku tsakaninsu, hakika daurar na'ibancinsa ta kasance gajeriya bata da tsayi idan aka yi la'akari da kebantattun Na'ibai uku da suka gabace shi, tsananin gwamnati ana ganin ya hana shi gudanar da ayyuka da dama a hukumar wakilai, hakika tauki'i na Imam Zaman zuwa ga Ali Bin Muhammad Samari yana ba shi labarin wafatinsa da kuma karshen daurar Na'ibancinsa yana daga muhimman abubuwa da suka fara a zamaninsa, bayan mutuwarsa alakar Jakadu kai da Imam Zaman ta yanke sannan an shiga daurar Gaiba Kubra
Tarihin Rayuwarsa
Ba a ambaci shekarar da aka haifi Ali Bin Muhammad samari cikin Masadir din Tarih ba, amma ane masa Alkunya da Abu Hassan[1] ana masa Lakabi da Samari ko Saimuri da Saimari amma da Samari ya fi shahara[2] tare da haka a wasu ba'arin Masadir na Shi'a an bayyana Lakabinsa da Samuri ko Sammara da Summara,[3]Saimari suna ne na wani kauye da yake a garin Basara a kasar Iraki wanda a can ne Danginsa suka rayu[4]
Dangi
Ali Bin Muhammad ya fito daga Dangi `Yan Shi'a masu riko da addini wadanda suka kasance Hadiman Imaman Shi'a, sun shahara matuka, wannan Asali na wannan Dangi shi ya zama sababin samu sassauci daga Hukuma bayan tare da Na'iban Imamin Shi'a[5] Yakubi ya tafi kan cewa da yawa yawan dangin Naubekti sun yi wakafi Kadarori da sunan Imami na sha daya (A.S) a garin Basara kuma kowacce shekara yana karbar ribar da aka samu daga Kadarorin ya kuma ana sanar da Imam (A.S)[6]daga cikin wasu dangin samari na daban akwai Ali Bin Muhammad Zayad ya kasance daya daga cikin Wakilan Imamai biyu Askariyaini (A.S) ya kuma rubuta wani littafi da ake kira Al-Ausiya'u ya rubuta shi ne yunkurin tabbatar da Imamancin Imami na goma sha biyu (A.S)[7]
Alakarsa da Imam Askari (A.S)
Shaik Tusi ya kira shi da Ali Bin Muhammad Saimari kuma ya kidaya shi cikin Sahabban Imam Hassan Askari (A.S)[8] sun yi musayen wasiku da juna, Ali Bin Muhammad Samari yana cewa: Abu Muhammad (Imam Askari) ya rubuto min: (akwai wata fitina da za ta faru za ta karkatar da kai saboda haka ka kasance cikin taka tsantsan) bayan kwanaki uku sai waki'ar Banu Hashim ta afku wacce haifar musu da tsanani da yanayi mara dadi, sai na rubuta tawa Hazrat wasika na aika masa (dama wanann maganar ce kake fada?) sai ya bada amsa (a'a ba wannan bace, kai dai ka kiyaye kanka) bayan wasu kwanaki bayan sai kwatsam ga waki'ar kashe Mu'utazzu ta afku[9]
Mutuwa
Kan asasin abinda Shaik Tusi ya nakalto hakika Ali Bin Muhammad Samari yayi bankwana da wannan duniya a shekara ta 329 hijiri kamari an binne shi a garin Bagdad a kan Titin Khalanji kusa da Koramar Abi Itab[10] kusa da Makabartar Kulaini[11] Mawallafin Littafin A'ayanush Ashshi'a ya mutu a 15 ga watan Sha'aban[12]Shaik Saduk da Ɗabarasi sun tafi kan cewa ya mutu a shekara ta 328 kamari[13],[14]
Na'ibancin Imam Mahadi (A.F)
Tauki'n Imam Mahadi (A.J)
“Allah Ya sakawa ‘yan’uwanku da lada a cikin mutuwarku. Za ku mutu nan da kwana shida. Don haka ku ƙoƙarin gama aikinku kada ku maye gurbinku da kowa; Domin a yanzu fakuwa (Gaiba) ta biyu ta fara, kuma ba za a daɗe ba, matukar Allah Ya yarda, har sai zukata sun cika (mutane) da duniya sun cika da zalunci, mutane su zo wurin magoya bayana ('yan Shi'a). kuma suna da'awar cewa sun gan ni. Amma ku sani, duk wanda ya ce ya ganni tun kafin Miƙewar Sufyani da Karajin Sama, to wannan kazafi ne kuma makaryaci.
Tarikh Bagani, Sadouq, Kamal al-Din da Tammam Al-Naimah, 1395 AH, juzu'i na 2, shafi na 516.
Na uku a Na'iban Imam Zaman (A.F) ya yi wasiyya da cewa Ali Bin Muhammad Samari ya gaje shi ya zauna a mazauninsa cikin am'amuran Na'ibanci[15] zabarsa ta kasance karkashin umarnin Imam zaman (A.F) babu riwaya da ta zo kan haka sai dai kuma Ɗabarasi cikin Littafin Al-Ihtijaj ya rubuta cewa babu wani cikin Na'ibai hudu ya kai ga wannan Mukami sai bayan da Sahibul Amri ya bada Umarni da wanda ya gabace wanda zai zo ya ayyana shi wanda zai gaje shi[16]
Lokacin Na'ibanci
Daga ayyukan Samari a lokacin Na'ibancin Na'ibai uku da suka gabace shi babu wata Magana da ta zo dangane da hakan babu wani cikakken rahoto kan ayyukansa a lokacin Na'ibanci[17] amma ance imamin `Yan Shi'a kan girmamarsa da yarda da shi daidai da sauran Na'ibai da suka gabace ya samu dukkanin karbuwa[18] Kan asasin Riwayar Shaik Saduk, Hakika Wakilansa sun kabe shi a matsayin Jakadan Imam Na gaskiya kuma suna kawo masa hakkokin Shari'a[19] Lokacin Na'ibancin Samari lokaci da yake cike da zaluncin Hukuma da zuabar da jinni wannan shi ne ma sababin buyan ayyukansa[20] ba'arin wasu Masu zurfafa bincike sun bayyana illa ta asali kan gajertuwar daurar Na'ibanci kai hatta ma yankewarta da da karshen daurar Gaiba Sugra shi ne tsanantawa da Fadar Abbasiyawa ta yi a zamanin.[21]
Tauki'in Imam Zaman
Kwanaki shida kafin mutuwar Samari wani tauki'i daga Imami na sha biyu ya fito, cikin wannan tauki'i Imam ya bayyana wafatin Samari da kuma farkon shiga Gaiba Kubra ya kuma umarce shi yayi kokari kammala ayyukan da bai kammala su ba sannan ka da ya nada wani mutum matsayin Magajinsa.[22] kwanaki shida bayan fitowar wannan tauki'i sai wakilansa suka hallara a shimfidar da yake jinya wacce a itane ya yi bankwana da su, sai suka tambayae shi wane ne Magajinka? Sai ya basu amsa, wannnan al'amari ne da yake hannun Allah, kuma shi ne da kansa zai kula da shi, wannan itace maganarsa ta karshe kafin mutuwarsa[23] bayan ya rasu sai ya zamana Alaka ta kai tsaye tsakanin `Yan Shi'a da Na'ibai da Imami na goma sha biyu ta yanke kuma Daurar Gaiba Sugra ta zo karshe[24]
Karamomi
A cikin Masadir na Riwaya daga Ali Bin Muhammad Samari an nakalto wata Karama domin kawar da kokwanto ga Shi'a an aike da labarin mutuwar Ibn Babawaihi Mahaifin Shaik Saduk zuwa ga wasu Mutane a garin Qum daga cikin mutanen akwai Salihu Bin Shu'aibu Talikani ya nakalto daga Ahmad Bin Muklid cewa na kasance a Bagdad cikin hallarar Shehunai a wannan taro Ali Bin Muhammad Samari ya halarta, sai ya fara Magana ya ce: Allah ya jikan Ali Bin Babawaihi Mahaifin Shai Saduk[25]Shehunnan da suke zaune a wannan Majalisi sai suka rubuta kwanan wata na ranar ai kuwa daga lokacin da labari ya je kunnen Ali Bin Babawaihi sai Allah ya karbi ransa a wannan Rana[26]
Bayanin kula
- ↑ Mamqani, Tangih al-Maqal, 1352 AH, juzu'i na 2, shafi na 305.
- ↑ Sadr, Tarikh al-Ghaibah, 1412 AH, juzu'i na 1, shafi na 413.
- ↑ Nahavandi, َl-Obqari َl-Hثsan, 2006, juzu'i na 5, shafi na 116.
- ↑ Jabari, Sazemaneh Wekalat 2013, juzu'i na 2, shafi 479.
- ↑ Jassim, Tarikh siyasi Gaibat Imam Dawazdahom, 2005, shafi na 210.
- ↑ Jafarian, hayate Fikri wa Siyasi Imaman Shi'eh, 2001, shafi na 583, an nakalto daga Hujjar Al-Wasiyya, 1426H, shafi na 255.
- ↑ Jabari,Sazemane Wekalat, 2013, juzu'i na 2, shafi 479.
- ↑ Tusi, Rizal al-Tusi, 1415 AH, shafi na 400.
- ↑ Sadr, Tarikh al-Ghaibah, 1412 AH, juzu'i na 1, shafi na 199
- ↑ Tusi, Al-Ghaiba, 1411H, shafi na 396.
- ↑ Re Toshe Atbat Aaliyat, shafi na 394.
- ↑ Amin, Ayan al-Shia, 1403 AH, juzu'i na 2, shafi na 48.
- ↑ Sadouq, Kamaluddin, 1359, juzu'i na 2, shafi 503.
- ↑ Tabarsi,Elamul Alwara, 1417 AH, juzu'i na 2, shafi na 260.
- ↑ Tusi, Al-Ghaibah, 1411 AH, shafi na 395.
- ↑ Tabarsi, al-Ihtjaj, 1403 AH, juzu'i na 2, shafi na 478.
- ↑ Jabari, Sazeamneh Wekalat, 2013, juzu'i na 2, shafi 480.
- ↑ Sadr, Tarikh al-Ghaibah, 1412 AH, juzu'i na 1, shafi na 413.
- ↑ Sadouq, Kamaluddin, 1359, juzu'i na 2, shafi na 517.
- ↑ Ghafarzadeh, Zindagi Nawab Khas Imam Zaman, 1375, shafi na 304.
- ↑ Sadr, Tarikh al-Ghaibah, 1412 AH, juzu'i na 1, shafi na 414.
- ↑ Sadouq, Kamaluddin, 1395 AH, juzu'i na 2, shafi na 516.
- ↑ Tusi, Al-Ghaibah, 1411 AH, shafi na 395.
- ↑ Sadr, Tarikh al-Ghaibah, 1412 AH, juzu'i na 1, shafi na 414.
- ↑ Tusi, Al-Ghaiba, 1411H, shafi na 396.
- ↑ Sadouq, Kamaluddin, 1395 AH, juzu'i na 2, shafi na 503.
Nassoshi
- Amin Ameli, Seyyed Mohsen, Ayan al-Shia, Beirut, Dar al-Taarif, 1403 AH.
- Jassim, Hossein, Tarikh Siyasi Gaibat Imam Dawazdahom (AS), Muhammad Taqi Ayatollahi, Amir Kabir, Tehran, 2005, ya fassara.
- Jabari, Mohammadreza, Sazeman Wekalat shari'a da rawar da ta taka a zamanin Imamai (amincin Allah ya tabbata a gare su), Qum, Cibiyar Nazarin Ilimin Imam Khumaini, 1382.
- Jafar, Rasulu, Ilimi da Siyasa na Imaman Shi'a, Qum, Ansari, 1381.
- Kungiyar marubuta, Rahtoshe Atbat Aliayat, Tehran, Mashaar, 2008.
- Sadr, Sayyid Muhammad, Tarikh al-Ghaibah, Beirut, Dar al-Taarif, 1412H.
- Sadouq, Muhammad bin Ali, Kamal al-Din da Tammam Al-Naimah, Tehran, Islamia, 1395H.
- Tabarsi, Ahmed bin Ali, Al-Ihtjaj, Ibrahim Bahadri ya yi bincike, Qom, Aswa, 2003.
- Tabarsi, Fazl bin Hasan, shelar al-Wori na Alam al-Hadi, Kum, Al-Bait, 1417H.
- Tousi, Muhammad bin Hassan, Rizal al-Tousi, bincike na Javad Qayyumi Isfahani, Qom, Jamia Modaresin, 1373.
- Tusi, Muhammad bin Hassan, Al-Ghaibah, Qum, Al-Maarif Islamic Foundation, 1411H.
- Mamqani, Abdullah, bitar Al-Maqal fi ilm al-Rajal, Najaf, al-Muttaba al-Mortazawiyya, 1352H.
- Nahavandi, Ali Akbar, al-Ubqari al-Hasan fi ahval na Maulana Sahib al-Zaman, Qom, Jamkaran Mosque, 1386.