Alullah
Ahlullah, (Larabci: آل الله) kalma ce da ake nufi Ahlul-Baiti, kamar yadda ya zo a cikin ruwayoyi, kuma masu wa'azi da mawaƙa na Ahlul-Baiti (A.S) an yi amfani da ita don nuni Ahlul-baiti (A.S). wannann kuwa saboda girman matsayin da suke da shi a wurin Allah ta'ala, ba kamar yadda ake zaton su mutanen Allah ne a zahirin ma'anar kalmar ba. Kuma ana kiran ƙuraishawa da Alullah, dangin Allah. Saboda alaƙarsu da ɗakin Allah mai alfarma.
Abin da Ake Nufi Da Alullah
Abin da ake nufi da ahlullah sune iyalan gidan manzo (s.a.w),،[1] kalmar Alu a yaran larabci an ciro ta daga kalmar al-ahlu kuma tana nufin mutanan gida, amma a asali tana nufin kusanci, kuma ana kiran mabiya da wannan,[2] kuma ita wannan kalma ta zo a cikin alƙur'ani mai girma, misali Alu Imran,[3] iyalan Imrana ya ƙunshi Maryam (A.S) da kuma Isa (A.S)[4] abin nufi daga Alu Luɗ[5] su ne iyalan Annabi Luɗ[6] da Alu Fira'auna[7] su ne mabiyan shi da sujojinsa,[8] amma a Luga idan aka jingina Alu zuwa ga Allah, to nuni ne na girma da ɗaukaka da matsayi babba. ba ana nufin cewa su `ƴa`yan Allah ne da matan shi ba, Allah bai haifa ba kuma ba a haife shi ba.
Su Wanene Alullah
Bisa abin da ya zo daga ruwayoyi, imamai suna da ilimi na masamma saboda su ne sirrin Allah kuma Alullah wato makusantan Allah kuma su ne magadan annabawa,[9] saboda haka ne masu wa'azi da mawaƙa suka yi amfani da kalmar Alulallah akan Ahlil-baiti domin nuni akan matsayinsu ya zo a cikin waƙa kamar;
Wasu dangi sun zubar da jinin muhammad da `ya`yansa daga wannan dangi ne Yazidu da ziyad suka fito Sun cika hannayansu da dukiyar Allah. Amma nauyin jini Alullah na nan a wuyansu.
Dalilin da yasa ake cewa Imamai Alullah saboda tsananin kusancinsu da Allah da ɗaukakarsu da falalar su da ɗaukakar matsayinsu a gun Allah maɗaukaki. kuma saboda hakane ake ce musu waliyan Allah da hujjojinsa a doran ƙasa.[11] Kamar yadda aka yi anfani da kalmar alullah akan ƙuraishawa saboda su ne masu kula da Ka'aba (ɗakin Allah) kamar yadda aka kira su da makwabtan Allah da mazauna ɗakin Allah.[12] kamar yadda wani malamin Shi'a Mansur ɗan Husain Al'abi a ƙarni na biyar yace: Abin da ya faru na As'habil fil ya sanya ƙabilar ƙuraishawa ta zama babba a idan larabawa ta kai ga har ana kiransu da Alullah.[13]
Bayanin kula
- ↑ ما معنى أنّ أهل البيت (عليهم السلام) هم آل الله؟
- ↑ Al-Misbah Al-Munir: 28
- ↑ Suratul Al-Imran, aya ta 33.
- ↑ Makarem Al-Shirazi, Tafsir al-amsal, juzu'i na 2, shafi na 472.
- ↑ Suratul Naml, aya ta 56; Suratul Hajr, aya ta 61.
- ↑ Tabatabai, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 15, shafi na 376.
- ↑ Suratul Baqarah, aya ta 50; Suratul Anfal, aya ta:54.
- ↑ Makarem Al-Shirazi, Tafsir Al-amsal, juzu'i na 1, shafi na 224; Qurashi, Tafsiri Ahsan al-Hadith, 1391, juzu'i na 1, shafi na 120.
- ↑ Al-Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 592, shafi na 184
- ↑ الأميني، الغدير، ج 4، ص 216.
- ↑ ما معنى أنّ أهل البيت (عليهم السلام) هم آل الله؟
- ↑ Ibn Abd Rabbah, al-Iqdul al-Farid, Dar al-Kutub Al-Elamiya, juzu'i na 3, shafi na 226; Al-Majlisi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 15, shafi 258; Sheikh al-Sadooq, Amali, 1417 AH, shafi na 317.
- ↑ Al-Abi, Nasr Al-Durri, 1424H, shafi na 273.
Nassoshi
- Al-Abi, Mansour bin Hossein, Nasr al-Adr fi al-Mahaderat, bincike: Mahfouz Khaled Abdul Ghani, Beirut, Dar al-Kitab Al-Alamiya, 1424 AH/2004 AD.
- Al-Amini, Abdul Hussein, Al-Ghadir fi Al-kitab, wa Sunnah wa Adab, Beirut, Dar Al-Kutub Al-Arabiyya, 1397 - 1977 Miladiyya.
- Makarim Shirazi, Nasser, Al-Amsal fi Tafsir Al-Qur’an Al-Manzil, Kum, Mazhabar Imam Ali bin Abi Talib (a
- Al-Majlisi, Muhammad Baqir, Bihar Al-Anwar, Beirut, bugun Mu'assasar Al-Wafa, 1403H.
- Al-Tabatabai, Muhammad Hussein, Al-Mizan fi Tafsir al-Qur’an, Islamic Publications Notebook, 1417 AH.
- Ibn Abd Rabbihi, Ahmed bin Muhammad, Al-Iqdul Al-farid, edited by: Abdel Majeed Tarhini, Beirut, Dar Al-Kutub Al-Ilmiyyah.
- Qurashi, Ali Akbar, Tafsir Ahsan al-Hadith, Navid Islam Publication Notebook, 1391 AH..s), 1379H.
- ما معنى أنّ أهل البيت (عليهم السلام) هم آل الله؟ مركز الأبحاث العقائدية، آخر مراجعة 16 ديسمبر/كانون الأول 2020 م.