Abdullahi ɗan Budail

Daga wikishia
(an turo daga Abdullahi Bin Budail)

Abdullahi ɗan Budail Al-Khuza'i(Larabci:عبد الله بن بُدَيل الخُزاعي) ɗaya ne daga cikin sahabban Manzon Allah (S.A.W) da Imam Ali (a.s), kuma ɗaya daga cikin shedun Hadisin Al-Ghadir. Ya musulunta tare da mahaifinsa fatahu makka, ya halarci yakin tabuka da Hunain, kuma manzon Allah (s.a.w) ya aika shi a matsayin wakilinsa a kasar Yaman. ya rawaito Hadisi daga Manzon (s.a.w) da wasida. Ya kasance a cikin yakokin da aka yi a zamanin halifofi, kuma an ci Isfahan, Kerman, da Hamadan a hannunsa. a lokacin da aka yi wa Usman bn Affan kawanya da kashe shi. Yana daga cikin wadanda suka fara yi wa Imam Ali (a.s) mubaya'a, kuma ya halarci yaƙin Jamal da Siffin, kuma ya yi shahada a yaƙin Siffin. An yi tattaunawa tsakaninsa da Aisha a yaƙin Jamal, domin tabbatar da hakkin Imam Ali (a.s) kuma yana daya daga cikin jagororin sojojin Imam Ali (a.s) a yaƙin Siffin.

Sanin Wanene Abdullahi ɗan Budail

Abdullahi ɗan Budail ɗan Warƙa Al-Khuza'i ɗaya ne daga cikin sahabban Annabi (s.a.w)[1] kuma ɗaya daga cikin muhajirun,[2] kuma Muhammad ɗan Umar Al-Kashi ya dauke shi ɗaya daga cikin Tabi'ai[3] Ya kasance cikin manyan mutane,[4] kuma yana daga cikin fitattun sahabban Imam Ali (a.s).[5] Ana ɗaukar Abdullahi ɗan Budail ɗaya daga cikin mazaje masu hankali guda biyar,[6] ko shida[7] kuma ɗaya daga cikin fitattun masu iya hudubar larabawa,[8] kuma mutum ne mai kima[9] da mai daraja.[10] An ruwaito nasabar Abdullahi zuwa Adi ɗan Amru ɗan Rabi'ah[11] babu ingantaccen bayani game da shekarar da aka haife shi. [tsokaci 1] Ya yi shahada a yaƙin Siffin a shekara ta 37 bayan hijira.[12] Akwai fitattun mutane daga zuriyar Abdullah, kamar su Abdurrahaman Naishaburi,[13] Di'ibil Al-Khuza'i,[14] da Abu Al-Futuh al-Razi,[15] al-Budaili Lakabi ne ga wadanda nasabarsu ta koma ga Budail ɗan Warƙa' baban Abdullah.[16] A bisa bukatar Amirul Muminin Abdullah ya ba da shaida hadisin Al-Ghadir tare da Khuzaimah ɗan Sabit da ƙaisu ɗan Sa'ad ɗan Ubada da sauransu.[17] wanda aka fi sani da ranar Rukban.[18] A lokacin Annabi yana raye Abdullahi ɗan Budail ya kasance ɗaya daga cikin shehunan kabilar Khuza'a,[19] Shi da mahaifinsa Budail ɗan Warƙa' sun je wurin Manzon Allah (S.A.W) a lokacin fatahu makka.[20] ko gabaninsa, kuma suka yi bushara da musulunta,[21] gidan mahaifinsa ya zama mafaka ga Kuraishawa a ranar da aka ci Makka da yaƙi (fatahu nmakka).[22] kuma ya kasance halifan babanshi wajan kiyaye wasikun manzon Allah (s.a.w).[23] da sahabbansa,[24] wanda a cikinsa ya yabi kabilar Khuza'a.[25] Wasu sun ce Abdullahi ya halarci Bai'atul Ridwan,[26] Ya jeyaƙin ɗa'if, Tabuka, da Hunain tare da Manzon Allah (s.a.w).[27] Haka nan an aiko Abdullahi tare da dan'uwansa Muhammad,[28] ko Abdur-rahman ko kuma duk ukun gabaɗaya.[29] zuwa Yaman a matsayin `yan aiken Manzon Allah (S.A.W).[30] ya ruwaito hadisi daga manzon Allah (s.a.w) bakai tsaye ba.[31] Lokacin halifofi Abdullahi ɗan Budail ya kasance a cikin yaƙe-yaƙe da suka jagoranta, kuma shi ne shugaban dakarun Abdullahi ɗan Amir a yaƙin Isfahan a shekara ta 29 bayan hijira.[32] Wasu na ganin an yi wannan nasara cikin lumana.[33] Al-Balazri ya yi imanin cewa halifa na biyu ne ya aika Abdullahi zuwa Isfahan are da samun nasarar kwace wannan birni a shekara ta 23 bayan hijira,[34] shi ma Al-Yaƙubi ya tafi kan cin nasarar Isfahan da Hamadan a hannun ɗan Budail a shekara ta 23 bayan hijira[35] da kuma cin Karman shi ma an danganta shi da shi[36] Tabbas ana masa ana danganta masa kofar Kurasan.[37] tare da kula da wannan kasa, amma halifa ya sabawa hakan.[38] Al-Balazri, ɗaya daga cikin malaman tarihi na Ahlus-Sunna ya ambaci cewa, Abdullahi yana daga cikin waɗanda suka halarta a lokacin da aka kewaye gidan halifa na uku, kuma ya dauke shi ɗaya daga cikin waɗanda suke da hannun cikin kashe shi.[39] kuma shi ne ya datse jijiyar halifa na uku.[40] A loƙacin Amirul mu'uminina Ali (a.s) Abdullahi ɗan Budail ya kasance daya daga cikin muhajirun na farko da suka yi mubaya'a ga Imam Ali (a.s),[41] Ana yi masa kallon ɗaya daga cikin fitattun mutane a zamanin Amirul Muminin (a.s) - waɗanda suka halarci yaƙinn Jamal. da Siffin,[42] ɗansa ya yi shahada a yaƙi Jamal,[43] A cikin wannan yaƙin ne ya yi ya tattauna da A'isha, ya gaya mata cewa ta nakalto hadisi daga Manzon Allah (s.a.w) dangane da hakkin Imam Ali (a.s)[44] An ruwaito cewa ɗan Budail da ɗan uwansa Abdur-rahman sun yi magana da Imam don kwadaitar da shi ya yaƙi Mu'awiya,[45] kafin a fara yaƙin Siffin, Amirul Muminin ya aika shi zuwa birnin Anbar. Imam ya bukace shi a cikin wasika da ya sa ido kan motsin maƙiya ka da ya yi motsi sai da izininsa.[46] A yaƙin Siffin, Abdullahi shi ne kwamandan rundunar mayaka masu tattaki,[47] ko wadanda suka kan Dawakai,[48] ko kuma shugaban wasu ƙabilun Kufa,[49] ko masu karatunsu,[50] kuma an ce shi ne ya kasance kula da na hannun daman sojojin Imam Ali (a.s).[51] ya gabatar da jawabai, don kwadaitar da sahabban Imam Ali zuwa yaƙin.[52] ya fallasa karyar Mu'awiya da rundunarsa,[53] Wasu masu bincike sun amfana da fadar Abdullahi cewa yana da masaniya kan yanayin zamaninsa,[54] ya shahara da jarumtaka da yaƙi da takubba biyu da garkuwa biyu a yaƙin Siffin.[55]

Shahadar shi

A rana ta bakwai.[56] ko ta tara na yaƙin Siffin.[57] Abdullah ɗan Budail ya kai wa sojojin makiya hari bayan shahada da raunata abokansa, duk da cewa Malik al-Ashtar ya bukaci da kada ya ci gaba.[58] wanda ya kuduri aniyar kashe Mu'awiya,[59] sai ya matso kusa da sansaninsa ya kashe sojojin makiya guda 9,[60] bayan da suka gagara su kashe shi sai suka jefe shi da duwatsu ya faɗi kasa, sai suka kashe shi da takubbansu.[61] ɗan A'asam al-Kufi ya bayar da karin bayani kan jarumtakarsa da jajircewarsa a fagaen yaƙi.[62] Alkali Numan ya ce Abdullahi tare da sahabbansa dubu uku; Sun kashe mutanen sham kusan 20,000[63] A cikin ruwayar ɗan Abi Al-Hadid, ɗaya daga cikin Sahabban Imam ya wuce Abdullahi ɗan Budail a karshen rayuwarsa, sai ya buƙace da ya yi masa nasiha, ya yi masa nasiha da ya ji tsoron Allah, ya taimaki Imam, da isar da gaisuwarsa. ga Imam, da maganarsa ta je wurin Imam, sai ya ce: Allah Ya yi masa rahama: “Ka yi gwagwarmaya da makiyinmu a rayuwa. kuma Ya yi mana nasiha game da mutuwa.[64] Al-Yaƙubi ya yi imani da cewa gawar Abdullahi dan uwansa ne ya dauketa zuwa sansanin Imam, kuma Imam Ali (a.s) ya ce: “Ya Allah ka shaida.”[65] Shi ma dan'uwansa Abdurrahman yana daga cikin shahidai. na yaƙin Siffin,[66] kuma a wata mahanga da yaɗa cewa ya yi shahada a yaƙin Jamal.[67] Bayan shahadar Abdullahi ɗan Budail, Muawiya ya yi niyyar yin wasa da gaƙarshi, amma Abdullahi ɗan Amir ya hana shi.[68] An ce Mu'awiya ya yabi Abdullahi, ya ce:[69] Soyayyar kabilar Khuza'a ga Ali ya kai ga da za a umarci matan kabilar Khuza'a da suka kashe da sun kashe ni ballantana mazajensu.[70] bayan Muawiya bai gafala daga yabon ɗan Budail.[71] ɗan Abi Al-Hadid ya ambata a cikin littafinsa Sharhu Nahj Al-Balagha cewa, Amirul Muminin (A.S) bayan yaƙin Siffin, ya ambaci Abdullahi da sauran waɗanda suka yi shahada a matsayin shahidan yaƙin Siffin, kuma ya yi takaici da bakin ciki kan rabuwarsu.[72]

Bayanin kula

  1. Ibn Abi Al-Hadid, Sharhin Nahj al-Balaghah, 1404 AH, juzu'i na 9, shafi na 111.
  2. Tabari, Tarikh Tabari, 1387 AH, juzu'i na 5, shafi na 164; Ibn Hajar, Ḥaṭṭa, 1415 AH, juzu'i na 4, shafi na 19.
  3. Kashi, Rizal Al-Kashshi, 1409 AH, shafi na 69.
  4. Dinouri, Al-Akhbar Al-Tawal, 1368, shafi na 175.
  5. Ibn Athir, Usdul Ghabah, 1409H, juzu'i na 3, shafi na 80.
  6. Ibn Hajar, Al-Isaba, 1415 AH, juzu'i na 4, shafi na 19; Ibn Kathir, Al-Bidaya wa Al-Nihaya, 1407H, juzu'i na 5, shafi na 338.
  7. Ibn Habib, Al-Mohbar, Beirut, shafi na 184.
  8. Zarkali, Al Alam, 1989, juzu'i na 4, shafi na 73.
  9. Ibn Abd Al-Barr, Al-Istiy'ab, 1412H, juzu'i na 3, shafi na 872.
  10. Dhahabi, Tarikh Al-Islam 1413 Hijira, juzu'i na 3, shafi na 567.
  11. Tabari, Tarikh Tabari, 1387 AH, juzu'i na 11, shafi na 511 da dan bambanci: Ibn Hazm, Jamhara Ansab al-Arab, 1403 AH, shafi na 239.
  12. Zarkali, Al Alam, 1989, juzu'i na 4, shafi na 221.
  13. Dhahabi, Tarikhul Islam, 1413 Hijira, juzu'i na 33, shafi na 151.
  14. Tusi, Amali, 1414 AH, shafi 361; Najashi, Rijal al-Najashi, 1365, shafi na 161.
  15. Nouri, Mostadrak Al-Wasail, Al-Khatama, 1408 AH, juzu'i na 3, shafi na 72.
  16. Samani, Al-Ansab, 1382 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 116.
  17. Kashi, Rijal al-Kashi, 1409 AH, shafi na 45.
  18. Bahrani Esfahani, Awalim Uloom, 2013, shafi na 489.
  19. Ibn Abd al-Barr, al-Istiy'ab, 1412 AH, juzu'i na 3, shafi na 872; Ibn Athir, usdul Ghabah, 1409H, juzu'i na 3, shafi na 80.
  20. Ibn Abd al-Barr, al-Istiy'ab, 1412H, juzu'i na 1, shafi na 150.
  21. Ibn Athir, Usdul Ghabah, 1409 AH, juzu'i na 3, shafi na 80; Ibn Abd al-Barr, al-Istiyab, 1412H, juzu'i na 3, shafi na 872.
  22. Ibn Athir, Usdul Ghabah, 1409 AH, juzu'i na 3, shafi na 80; Ibn Abd al-Barr, al-Istiyab, 1412H, juzu'i na 3, shafi na 872.
  23. Ibn Hajar, Al'isaba 1415 Hijira, Mujalladi na 1, shafi na 409
  24. Ahmadi Mianji, Makatib Rasul (s.a.w), juzu’i na 3, shafi na 127.
  25. Waqidi, Al-Magazi, 1409 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 749.
  26. Ibn Hayyun, Sharh al-Akhbar, 1409 AH, juzu'i na 2, shafi na 32.
  27. Ibn Abd al-Barr, Al-Istiy'ab, 1412 AH, juzu'i na 1, shafi na 150, juzu'i na 3, shafi na 872; Ibn Athir, Usdul Ghabah, 1409 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 203.
  28. Ibn Hajar, Al-Isaba, 1415 AH, juzu'i na 6, shafi na 5; Tusi, Rijal Al-Tosi, 1373, shafi na 49.
  29. Ibn Hajar, Al-Isaba, 1415 AH, juzu'i na 4, shafi na 18; Salehi al-Shami, Sabl Al-Huda, 1414 AH, juzu'i na 11, shafi na 363.
  30. Tousi, Rijal Al-Tousi, 1373, shafi na 70; Ibn Dawud, Al-Rijal, 1342, shafi na 199; Hali, Rijal Allama Al-Hilli, 1411H, shafi na 103.
  31. Ibn Hajar, Al-Isaba, 1415 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 409, juzu'i na 5, shafi na 438; Ibn Athir, Usdul Ghabah, 1409 AH, juzu'i na 4, shafi na 168; Majlesi, Bihar al-Anwar, 1403 AH, juzu'i na 96, shafi na 308.
  32. Ibn Khayyat, Tarikh Khalifa, 1415 AH, shafi na 93; Dhahabi, Tarikh Al-islm 1413 AH, juzu'i na 3, shafi na 326; Ibn Abd al-Barr, al-Istiy'ab, 1412H, juzu'i na 3, shafi na 872.
  33. Ibn Atham Al-Kufi, al-Futuh, 1411 AH, juzu'i na 2, shafi na 314; Ibn al-Abri, Tarikh Mukhtasar Al-Duwal, 1992, shafi na 102.
  34. Balazri, Fatuh Al-Baldan, 1988, shafi na 304.
  35. Yaqoubi, Tarikh Elyaqoubi, Beirut, juzu'i na 2, shafi na 157.
  36. Ibn Khaldun, Tarikh Ibn Khaldun, 1408H, juzu'i na 2, shafi na 566; Ibn Kathir, Al-Bidaya wa Al-Nihaiya, 1407H, juzu'i na 7, shafi na 132.
  37. Balazri, Fatuh al-Baldan, 1988, shafi na 390; Ibnul Faqih, al-Baldan, 1416H, shafi na 611.
  38. Tabari, Tarikh Tabari, 1387 AH, juzu'i na 4, shafi 180; Ibn Khaldun, Tarikh Ibn Khaldun, 1408H, juzu'i na 2, shafi na 566.
  39. Balazri, Ansab al-Ashraf, 1417 AH, juzu'i na 8, shafi na 120.
  40. Dhahabi, Tariklh Al-Islam 1413 Hijira, juzu'i na 3, shafi na 567.
  41. Mufid, Al-Jamal wa Nusra, 1413H, shafi na 103.
  42. Mufid, Al-Jamal wa Nusra, 1413H, shafi na 481.
  43. Mufid, Al-Jamal wa Nusra, 1413H, shafi na 342.
  44. Ibn Hayyun, Sharh al-Akhbar, 1409 AH, juzu'i na 2, shafi na 525; Mofid, Al-Kafa’a, 1372, shafi na 35; Mufid, Al-Jamal wa Nusra, 1413H, shafi na 433.
  45. Balazri, Ansab al-Ashraf, 1417 AH, juzu'i na 2, shafi na 331.
  46. Ahmadi Mianji, Makatib Al'a'imma (a.s), 1426 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 358.
  47. Ibn Khayat, Tarikh Khalifa, 1415 AH, shafi na 117; Manqari, Waqqa Safin, 1382 AH, shafi na 205; Dhahabi, Tarikh Islam, 1413 Hijira, juzu'i na 3, shafi na 541.
  48. Ibn Atham al-Kufi, al-Futuh 1411 AH, juzu'i na 3, shafi na 25; Ibn Shahr Ashub, Manaqib Al Abi Talib (AS), 1379 Hijira, Mujalladi na 3, shafi na 169.
  49. Dinouri, Al-Akhbar Al-Tawal, 1368, shafi na 172; Tabari, Tarikh Tabari, 1387 Hijira, juzu'i na 5, shafi na 11.
  50. Ibn Moskawieh, Tajarub Al-umam, 1379, juzu’i na 1, shafi na 522.
  51. Manqari, Waqqa Safin, 1382 AH, shafi 208, 232; Tabari, Tarikh Tabari, 1387 AH, juzu’i na 5, shafi na 15; Ibn Kathir, al-Bidaya wa al-Nihaya, 1407H, juzu'i na 7, shafi na 262, 271, 310.
  52. Ibn Moskawieh, Tajarub Al-umam , 1379, juzu'i na 1, shafi na 522; Ibn Kathir, Al-Bidaya wa al-Nihaya, 1407H, juzu'i na 7, shafi na 262.
  53. Manqari, Waqqa Safin, 1382 AH, shafi 102, 234; Ibn Abi al-Hadid, Sharh Nahj al-Balaghah, 1404 AH, juzu'i na 3, shafi na 874-180; Balazri, Ansab al-Ashraf, 1417 AH, juzu'i na 2, shafi na 294.
  54. Ahmadi Mianji, Makatib Al-A'imma(a.s), 1426 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 358.
  55. Manqari, Waqqa Siffin, 1382 AH, shafi na 245; Dhahabi, Tarikh Al-Islam 1413 Hijira, juzu'i na 3, shafi na 541.
  56. Ibn Abi al-Hadid, Sharhin Nahj al-Balaghah, 1404 AH, juzu'i na 5, shafi na 186; Ahmadi Mianji, Makarantun Imamai (a.s), 1426 Hijira, Mujalladi na 1, shafi na 535.a.s
  57. Hashemi Khoi, Minhaj al-Baraa', 1400H, juzu'i na 15, shafi na 258.
  58. Tabari, Tarikh Tabari, 1387 AH, juzu'i na 5, shafi na 23; Ibn Kathir, Al-Bidaya wa al-Nihaya, 1407 AH, juzu'i na 7, shafi na 264.
  59. Ibn Abi al-Hadid, Sharh Nahj al-Balaghah, 1404 AH, juzu'i na 5, shafi na 197.
  60. Ibn Moskawieh,Tajarub Al-umam, 1379, juzu'i na 1, shafi na 528.
  61. Manqari, Waqqa Siffin, 1382 AH, shafi na 246; Dinouri, Al-Akhbar al-Tawal, 1368, shafi na 176.
  62. Ibn Atham Al-Kufi, al-Futuh, 1411 AH, juzu'i na 3, shafi na 25.
  63. Ibn Hayyun, Sharh al-Akhbar, 1409 A.H., juzu'i na 2, shafi na 32.A.
  64. Ibn Abi al-Hadid, Sharh Nahj al-Balaghah, 1404 AH, juzu'i na 8, shafi na 92-93.
  65. Ibn Abi al-Hadid, Sharh Nahj al-Balaghah, 1404 AH, juzu'i na 8, shafi na 92-93.
  66. Ibn Abd al-Barr, al-Istiyab, 1412 AH, juzu'i na 3, shafi na 872; Ibn Athir, Usdul Ghabah, 1409 AH, juzu'i na 3, shafi na 80; Masoudi, Moruj al-Dahahab, 1409 AH, juzu'i na 2, shafi na 384U
  67. Ibn Hajar, Al-Isaba 1415 AH, juzu'i na 4, shafi na 19; Ibn Abi al-Hadid, Sharh Nahj al-Balaghah, 1404 AH, juzu'i na 9, shafi na 111.
  68. Manqari, Waqqa Siffin, 1382 AH, shafi na 246; Masoudi, Moruj al-Dahahab, 1409 AH, juzu'i na 2, shafi.388; Ibn Abd al-Barr, al-Istiyab, 1412 Hijira, juzu'i na 3, shafi na 873.
  69. Ibn Athir, Usdul Ghabah, 1409 AH, juzu'i na 3, shafi na 81; Dinouri, Al-Akhbar al-Tawal, 1368, shafi na 176; Tabari, Tarikh Tabari, 1387 Hijira, juzu'i na 5, shafi na 24.
  70. Ibn Abd al-Barr, al-Istiyab, 1412 Hijira, juzu'i na 3, shafi na 873.
  71. Ibn Atham al-Kufi, al-Futuh, 1411, juzu'i na 3, shafi na 162.
  72. Ibn Abi Al-Hadid, Sharh Nahj al-Balaghah, 1404 AH, juzu'i na 10, shafi na 110.

Nassoshi

  • Ibn Abi al-Hadid, Abdul Hamid bn Haballah, Sharh Nahj al-Balagha, Kum, Mazhabar Aya Allah al-Marashi al-Najafi, 1404H.
  • Ibn Athir, Ali bn Muhammad al-Jazri, Usudul al-Ghaba a cikin ilimin Sahabbai, Beirut, Darul Fakr, 1409 q.
  • Ibn 'Atham al-Kufi, Abu Muhammad Ahmad, Kitab al-Futuh, Tahqiq Ali Shiri, Beirut, Darul Adwa', 1411H.
  • Ibn al-Faqih, Ahmad bn Muhammad bn Ishaq al-Hamzani, Kitab al-Baladan, Tahqiq Yusuf Al-Hadi, Beirut, Alam al-Kitb, 1416H.
  • Ibn Habib, Muhammad bn Habib bn Umiyah al-Hashimi al-Baghdadi, Kitab al-Muhabbar, Tahqiq al-Ilza Likhtan Shtiter, Beirut, Dar al-Afaq al-Jaded, B. Ta.
  • Ibn Hajar al-Asqalani, Ahmad bn Ali, Al-Isabah fi Tamiyiz al-Sahabah, Tahqiq Adel Ahmad Abdul Majud da Ali Muhammad Ma'waz, Beirut, Dar al-Kitb al-Ilamiyah, 1415H.
  • Ibn Hazm, Ali bn Ahmad bn Saeed, Jumrah al-Ansab al-Arab, kwamitin malamai Tahqiq, Beirut, Darul Kitb al-Ulamiyah, 1403H.
  • Ibn Hayun, Nu'man bn Muhammad, Sharh al-Akhbar fi Fada'il al-A'ima al-Atahar (AS), Qom, Jami'a al-Mudarsin, 1409H.
  • Ibn Khaldun, Abdul Rahman ibn Muhammad, Diwan al-Mubtada'a wa al-Khabar fi Tarikh al-Arab wa al-Barbar, da sauransu, Tahqiq Khalil Shahada, Beirut, Darul Fikr, bugu na biyu, 1408H.
  • Ibn Khayat, Khalifa bn Khayat bn Abi Habira al-Laithi, Tarikh Khalifa bn Khayat, Tahqiq Fawaz, Beirut, Darul Kitb al-Ulamiyah, 1415H.
  • Ibn Dawud, Hassan bn Ali bn Dawud, Al-Rajal, Tehran, Tehran University,
  • Ibn Shahr Ashub Mazandarani, Muhammad bn Ali, Manaqab al-Abi Talib (AS), Qum, Alamah Publishing House, 1990H.
  • Ibn 'Abd al-Barr, Yusuf bn Abdullahi bn Muhammad, Al-Isti'ab fi Ilimin Sahabbai, Bincike akan Muhammad al-Bajawi, Beirut, Dar al-Jil, 1412 q.
  • Ibn al-Ibri, Grigorius al-Multi, Tarikh Mukhtar al-Dul, Tahqiq Anton Salehani al-Yisu'i, Beirut, Dar al-Sharq, bugu na biyu,
  • Ibn Katheer, Ismail bn Umar, Al-Bidayah da Al-Nihayah, Beirut, Darul Fakr, 1407H.
  • Ibn Maskuyeh, Abu Ali Maskuyeh al-Razi, Tajarub Al-Umam Abul Qasim Imami, Tehran, Sarush, 1990.
  • Ahmadi Mianji, Ali, Makatib A'imma (AS), Qum, Darul-Hadith, 1426H.
  • Ahmadi Mianji, Ali, Makatib Al-Rasool (a.s), Kum, Dar al-Hadith, 1419 q.
  • Bahrani Isfahani, Abdullah ibn Nuur Allah, Duniyar Kimiyya, Ilimi da Sharuɗɗa daga Ayoyi, Labarai da Magana - Imam Ali bn Abi Talib (AS), Qum, Imamul Mahdi Foundation (AS), 2003, Bugu na Biyu Sh.
  • Bladhari, Abu al-Hassan Ahmad ibn Yahya, Fatuh al-Baladan, Beirut, Dar da Al-Hilal School.
  • Balazri, Ahmad bn Yahya bn Jabir, Ansab Al-Ashraf, Tahqiq Sahil Zakar da Riyadh Zarkali, Beirut, Darul Fakr, 1417H.
  • Hilli, Hassan bn Yusuf, Mazajen Alamar Hali, Najaf, Darul Dhakhair, bugu na biyu, 1411q.
  • Dinuri, Abu Hanifah Ahmad ibn Dawud, Al-Akhbar al-Tawal, Tahqiq Abdul Mun'im Amer, Kum, Manshurat al-Razi, 1989.
  • Dhahabi, Shams al-Din Muhammad ibn Ahmad, Tarikh Al-Islam wa Fiyat al-Mashahir wa al-Alam, Tahqiq Omar Abdul Salam Tadmri, Beirut, Dar al-Kitab al-Araby, bugu na biyu, 1413 q.
  • Zarkali, Khairuddin, Al-Alam, Beirut, Dar al-Alam al-Mulayin, bugu na takwas, 1989m.
  • Sam'ani, Abdul Karim bn Muhammad bn Mansoor al-Tamimi, Ansab, Tahqiq Abdul Rahman ibn Yahya al-Mualmi, Hyderabad, Majalisar Sashen Wayar da Kan Ottoman, 2003.
  • Saleh al-Shamsi, Muhammad bn Yusuf, Sabl al-Hadi da al-Rishad a cikin Sirah na Khair al-Abbad, Tahqiq Adel Ahmad Abdul Majud da Ali Muhammad Ma'waz, Beirut, Dar al-Kitb al-Ulamiyah, 1414 ku.
  • Tabari, Abu Ja'afar Muhammad bn Jarir, Tarikh al-Umm wa al-Maluk, Tahqiq Muhammad Abu al-Fadl Ibrahim, Beirut, Darul-Tarath, 2008H.
  • Tusi, Muhammad bn al-Hassan, al-Amali, Kum, Darul Thaqafa, 1414H.
  • Tusi, Mohammad ibn Hassan, Rajal al-Tusi, Qum, Islamic Publishing House, Sum Printing House, 1994.
  • Kashi, Muhammad bn Omar, Mazajen Kashi - Zabin Ilimin Maza, Mashhad, Mawallafin Jami'ar Mashhad, 1409Q.
  • Majlisi, Muhammad Baqir bn Muhammad Taqi, Bahar al-Anwar al-Jami'a don labaran Imaman Tahar, Beirut, Darul Tarath al-Arabi, bugu na biyu, 1403H.
  • Massoudi, Ali bn al-Hussein, Maruj al-Dhahab da Minerals of Jawhar, Tahqiq Asad Dagher, Qum, Dar al-Hijrah, bugu na biyu, 1409 q.
  • Mufid, Muhammad ibn Muhammad, Al-Jamal wa Nusra li Sayyid al-Atra fi Harbi Basara, 1413q.
  • Mofid, Mohammad ibn Mohammad, Al-Kafi'a fi Ibtal Tawbah al-Khati'a, Qom, Sheikh Mofid Congress, 1993.
  • Manqari, Nasr ibn Mazaham, Waq'a Safeen, Tahqiq Abdul Salam Mohammed Harun, Alkahira, Arab Haditha Foundation, bugu na biyu, 2003.
  • Najashi, Ahmad bn Ali, Mazan Najashi, Qum, Buga Na Shida, 1986.
  • Nuri, Hussein bn Muhammad Taqi, Mustdark al-Wasa'il wa Mustanbat al-Masa'il, Qum, Al-Bait Foundation (AS), 1408H.
  • Hashemi Khoyi, Mirza Habibullah, Minhaj al-Bara'a fi Sharh Nahj al-Balagha wa takmila Minhaj al-Bara'a, Tehran, Islamic School, Bugu na Hudu, 1400H.
  • Waqdi, Muhammad ibn Omar, Kitab al-Maghazi, Marsden Jones Research, Beirut, Scientific Foundation, bugu na biyu, 1409 AH.
  • Yaqubi, Ahmed ibn Abi Yaqub, Tarikh Yaqubi, Beirut, Dar Sadr, B. Ta.