Jump to content

wikishia:Featured articles/2024

Daga wikishia

Falalolin Imam Ali (A.S) (Larabci: فضائل الإمام علي (ع)) wasu halaye ne da siffofi na Amirul muminin Ali (A.S), Imamin na farko a wurin ƴan shi'a, waɗannan falaloli ne na sa an yi ishara kan su cikin kur'ani da riwayoyi da abubuwan da suka faru a tarihi. An naƙalto daga Annabin muslunci (S.A.W) cewa ba za a iya ƙidaya dukkanin falalolin Imam Ali (A.S) ba, bisa wata riwaya daban an yi bayani game da shi cewa rubuta falalolinsa, saurarensu, da kallonsu wani nau'i ne daga ibada, kuma yana sanya a gafarta zunubai.

Falalolin Imam Ali (A.S) sun kasu rukuni biyu: keɓantattun falaloli da kuma falaloli da ya yi tarayya da Ahlul-baiti (A.S) cikinsu: ayar wilaya, ayar shira'u (ayar lailatul mabit), ayar infaƙ, hadisul ghadir, hadisul ɗairil mashwiyyi, hadisul manzilat da kyautar zobe suna daga cikin keɓantattun falaloli da Imam Ali (A.S) da ya keɓantu da su, ayar taɗhir, ayar zikri, ayar mawadda da hadis saƙlaini su kuma sun kasance daga falaloli da ya yi tarayya cikinsu da Ahlul-baiti (A.S) cikinsu.

Lokacin mulkin bani umayya sun hana faɗar falalolin Imam Ali (A.S) da yaɗa su. A lokacin wannnan gwamnati ana kashe masu naƙalto duk wata falala ta Imam Ali (A.S) ko kuma mafi ƙarancin abin da za yi musu shi ne jefa su a kurkuku. Haka nan bisa umarnin Mu'awiya ana ƙarfafa masu ƙirƙirar falalolin halifofi uku don kishiyantar falalolin Imam Ali (A.S), ba'arin malaman ahlus-sunna misalin Ibn Taimiyya shugaban ƴan salafiyya da almajiransa Ibn Kasir da Ibn ƙayyim Jauzi sun raunana ma'anonin ayoyi da hadisai da suke magana kan falalolin Imam Ali (A.S) ko kuma dai suna ma ganin cewa wannan magana ce kawai ta ƙarya. Tare da dukkanin da maƙiya suka yi cikin hana yaɗuwar falalolin Imam Ali (A.S), cikin litattafan hadisi na shi'a da ahlus-sunna an naƙalto falalolin Imam Ali (A.S) masu tarin yawa, malaman mazhabobi biyu, sun wallafa litattafai masu cin gashin kansu game da falalolin Ali ɗan Abi ɗalibi (A.S). Fada'ilul Amirul Al-muminin na Ahmad ɗan Hanbal, Khasa'isu Amirul Al-muminin na Nasa'i da Umdatul Uyuni Sihahil Al-Akhbar Fi Manaƙib Imamil Al-abrar na Ibn Biɗriƙ suna daga cikin jumlar litattafan da aka rubuta kan falalolin Imam Ali (A.S

Full article ...