Jump to content

Yaumul Husaini (Ayyukan Ibada)

Daga wikishia
Yaumul Husaini
Bikin Ranar Imam Husaini (A.S) a garin Isfahan
Bikin Ranar Imam Husaini (A.S) a garin Isfahan
Lokacin da aka shiryaKwanakin Muharram da Safar
Wurin da aka shiryaMasallatai. Takaya, Jami'o'i
Faɗin ƙasaIran. Indiya. Fakistan, Ingila. Amurka
Tushe na tarihiShahadar Imam Husaini (A.S) a lokacin Waƙi'ar Karbala
Abubuwa da AlamomiSanya Baƙaƙen Kaya. Jar fulawa


Yaumul Husaini (Larabci: يوم الحُسَين ) Ranar Husaini (A.S) suna ne na wani taro na ƴanShi'a a duniya, wanda ake yin shi domin tinawa da shahadar Imam Husaini(A.S) shi wannan taro ana yin shi a garuruwa daban-daban, za ka samu ana gabatar da ƙasidu da laccoci kan Imam Husain (A.S) da shahidan Karbala da kuma mene ne ma'anar shahada[1] Wasu hadisai sun yi bayanin abin da ya faru a Karbala da ranar Imam Husain (A.S).[2] Ana shirya wasu taruka a lokacin Ashura a wasu garuruwan Iran kamar misalin Isfahan da Burujurdi da sunan ranar Imam Husaini (A.S)[3] kazalika a garin Bingalur a ƙasar Indiya ana yin irin wannan taro da sunan ranar Imam Husain (A.S) a duk shekara a ranakon zaman makokin watan Muharram da Safar, kuma a wannan taro mutane ma'abota addinai da mazhabobi daban-daban da kuma mabambantan harsuna daga Larabci, Urdu da Turanci suna gabatar da laccoci kan Imam Husaini (A.S)[4] Masu shirya wannan taro suna sanar da manifarsu ta shirya wannan taro ita ce, samar da dai-daito a tsakanin mutane da yin Allah wadai da ayyukan ta'addanci ko amfani da ƙarfi kan Musulmi dama sauran addinai,[5] kuma yayin wannan taro ana raba tutoci ga mu'assasosi a ƙasar Indiya da ɗaga tutar nuna baƙin ciki a wasu garuruwan Indiya.[6]

Ƙungiyar ɗalibai mabiya mazhabin Imamiyya na ƙasar Pakistan suna gudanar da taro mai sunan Ranar Imam Husaini a ranar sha uku ga wata Muharram a ko wace shekara a cikin jami'o'i a ƙasar Pakistan[7] Wasu kafofin labarai suna nuna cewa shugabannin yanki suna nuna adawarsu kan aiwatar da wannan taro[8]bisa labaran da ake samu a ƙasar Pakistan ana amfani da Ranar imam Husaini (A.S) kan wasu taruka da ake yi a lokacin tinawa da ranar haihuwar imam Husaini(A.S)[9]

Kazalika ana aiwatar taruka da suna Imam Husaini (A.S)a garin New York na ƙasar Amurka, `yanshi'a a Amurka suna tarayya a wani tattaki a ranar Lahadi kafin ranar Ashura, suna raba kyautar jar filawa da takardu da suke ɗauki da bayani abin da ya faru a ranar Ashura,[10] Wata majiyar labarai ta nuna cewa ana irin wannan taro a ƙasar Ingila, a shekara ta 2023 ƙungiyar Waskas ta `yanshi'a a ƙasar Ingila ta gudanar da taro mai suna ranar Imam Husaini (A.S) inda Kiristoci da Yahudawa da mutane daga mazhabobi daban-daban suka sami halartar wannan taro[11] ita ma ƙungiyar Jama'atu Ahlul-Baiti ta Sikotiland tana shirya laccoci mai ɗauke da sunan Imam Husaini (A.S) a ranar 12 ga wata Oktoba a ko wace shekara, kuma dukkan laccocin za a yi su ne kan shahada da ma'anarta da kuma Imam Husain (A.S) da neman tabbatar da adalci.[12]

Bayanin kula

  1. «Hussain Day International Convention», International Media Center (IMC); Call for social equality at Hussain Day event; deccanherald.com; اقامة مؤتمر يوم الحسين بمشاركة العتبة الحسينية»، مركز الاعلام الدولي.
  2. Sadouq, Amali, 1376, shafi. 128
  3. «اجتماع یوم الحسین در بروجرد برگزار شد»؛ وكالة اعتلای ایران؛ «اجتماع یوم الحسین در اصفهان»Kamfanin dillancin labaai na Mizan.
  4. «Hussain Day International Convention», International Media Center (IMC); Call for social equality at Hussain Day event; deccanherald.com; اقامة مؤتمر يوم الحسين بمشاركة العتبة الحسينية»، مركز الاعلام الدولي.
  5. «اقامة مؤتمر يوم الحسين بمشاركة العتبة الحسينية»،Cibiyar Yada Labarai ta Duniya،
  6. «اقامة مؤتمر يوم الحسين بمشاركة العتبة الحسينية»، Cibiyar Labari ta duniya،
  7. «هدف از برگزاری «یوم الحسین/» در پاکستان تبیین اهداف عاشورا است»؛ Kamfanin dillancin labarai na Hauza؛ ملتان-میں-سالانه-یوم-حسین-کا-انعقاد، Rasa News؛ «آئی ایس او کی جانب سے جامعہ کراچی میں سالانہ یوم حسین کا انعقاد»، Kamfanin dillancin labarai na Hauza؛ «پشاور، امامیہ اسٹوڈنٹس آرگنائزیشن کے زیر اہتمام سالانہ یوم حسینؑ»؛Islam TimesYOUM-E-HUSSAIN; Institute of Business Administration.
  8. «برگزاری همایش «یوم الحسین» باوجود اعلام ممنوعیت دولت ایالتی پاکستان»،Kamfanin dillancin labarai na Tasneem.
  9. Youm-e-Hussain; thenews.com
  10. «روز حسین در آمریکا به کنگره می‌رفتیم»Mashriq News؛ Mourning rituals held in New York on Hussain Day; iranpress.
  11. Husayn Day at Wessex Jamaat | 8th December 2013; Al Mahdi Center.
  12. The launch event of ‘Imam Hussain Day’ in Scotland; scottish ahlulbayt society.

Nassoshi