Tattakin Arba'in (Najeriya)
| Lokacin da aka shirya | 20 Safar |
|---|---|
| Wurin da aka shirya | Najeriya |
| Faɗin ƙasa | Najeriya |
| Wuridai da Take | Labbaika Ya Husain (A.S) da Labbaika Ya Mahdi (A.F) |
| Mu'assasa da ƙarƙashinta | Harkar Muslunci Najeriya |
Tattakin arba'in a Najeriya, (Larabci: المسيرة الأربعينية في نيجيريا) yana cikin ayyukan addini a wurin Shi'a a Najeriya da suke yi kwanakin ƙarshe na arba'in na Husaini (20 Safar) wannan tattaki yana kasancewa a yankuna daban-daban n Arewacin Najeriya zuwa garin Zariya. Wannan tattaki yana daga cikin mafi girman manya-manyan tarurruka na duniyar Muslunci bayan tattaki da ake yi zuwa Karbala, Ana cewa dubunnan ɗaruruwan ƴanshi'ar Najeriya ne suke shiga wannan tattaki. A lokuta da dama gwamnatin Najeriya ta afkawa masu yin tattaki lamarin da ya jawo asarar rayuka da jikkata wasu adadi.
Waɗanda Suka Kasa Zuwa Arba'in Na Karbala
Tattakin arba'in a Najeriya yana daga cikin manyan taron jama'a a duniyar Muslunci, bayan taron tattakin arba'in a Iraƙ.[1] Bisa rahotanni, dubunnan ɗaruruwan mutane ne suke halartar wannan taro[2] na makokin Imam Husaini (A.S) daga yankuna daban-daban na Najeriya, inda suke doguwar tafiya tsakanin kilomita 80-160 suna tattaki da ƙafafunsu[3] zuwa Husainiyyar Baƙiyatullahi Zariya[4] An ce wannan tattaki yana da tasiri matuƙa cikin janyo mutane zuwa shi'anci.[5] Najeriya ita ce ƙasa mafi yawan adadin jama'a a Afrika, kuma ita ce ta uku a yawan jama'a a cikin ƙasashen Musulmi a duniya.[6] An bada rahota cewa Ahlus-Sunna[7] da Kiristoci su ma suna shiga wannan tattaki a Najeriya.[8]
Labbaika Ya Imam Mahadi (A.F) Labbaika Ya Husaini (A.S) suna daga cikin taken da ƴanshi'ar Najeriya suke rerawa a lokacin wannan tattaki.[9]
Kashe-kashen Masu Tattakin Arba'in A Najeriya
Bisa rahotanni, gwamnatin Najeriya duk shekara tana afkawa masu makokin ranar arba'in na lumana tare da amfani da harsashi mai rai a kansu.[10]
A shekarar 2015 gwamnatin Najeriya bayan kashe ɗaruruwan ƴanshi'a a Najeriya ta ruguje Husainiyyar Baƙiyyatullahi a garin Zariya ta kuma kama Shaikh Zakzaky shugaban ƴan shi'ar Najeriya[11] tare kuma da kashe masa ƴaƴa.[12]
A shekarar 2016m, sakamakon buɗewa wuta da sojojin Najeriya suka yi ka ƴanshi'a masu tattaki a garin Kano, an kashe kusan mutane 100 da suka haɗa da mata da ƙananan yara..[13]
A lokacin tattakin arba'in na shekarar 2018m, wasu jama'a daga ƴanshi'a a Najeriya cikin nuna fushinsu kan ci gaba da tsare Shaik Zakzaky, sun shirya jerin gwano tare da neman gaggauta sakin Shaikh Zakzaky. Sojojin Najeriya sun kai hari kan masu muzahara, bisa madogaran labarai an ce an shahadantar mutum 40 daga masu muzahara.[14]
A ranar 10 Satumba 2024m, a garin Abuja babban birnin tarayyar Najeriya ƴansandan sun kai hari kan masu tattaki tare da shahadantar wasu adadi da jikkata wasu adadi da kama wasu adadi.[15]
kamfanin dillancin labarai na Abna, a taron arba'in na 2024 jami'an tsaron Najeriya sun tilastawa mata na Shi'a cire hijabi, wand ahaka ya fusata `yanshi'a suka yi jerin gwano a titunan garuruwa daban-daban don nuna rashin amincewa da wannan mataki.[16]
Haka nan a shekarar 2013m, Boko Haram sun ɗana bom cikin masu tattaki, bayan fashewa kusan mutane 30 suka yi shahada tare da jikkata gomomi.[17]
Ku Duba
Bayanin kula
- ↑ Kurdi, Shi'ayane Nijriye (Fursatha, Tahdidha, Babarha)," shafi. 123.
- ↑ Hosseini,Qatle Am Bi Saro Sida Shi'ayane Nijeriya Arbaeen 97,” shafi. 64; Kurdi, Shi'ayane Nijriye (Fursatha, Tahdidha, Babarha)," shafi. 123.
- ↑ «برگزاری باشکوهترین مراسم اربعین»، Hukumar Labarai ta Jamhuriyar Musulunci.
- ↑ «پیاده روی اربعین در نیجریه»، "Hukumar Labarai ta Ƙasa da Ƙasa mai Hotuna – Iran Press".
- ↑ Shojaei Fard,Negahi beh Zindagi Sheikh Ibrahim Zakzaky, Rahbare Shi’ayane a Nijeriye, Ibrahimi Ba Qudrat Yek Ummat, shafi. 40
- ↑ Ghaibi Hajipour da Namdar, "Tasirat Wa Baztab Inqilabe Islami Iran Dar Nijeriye," shafi na. 72
- ↑ «اربعین در نیجریه»، Kamfanin Dillancin Labarai na Mizan.
- ↑ Ghaibi Hajipour da Namdar, "Tasirat Wa Baztab Inqilabe Islami Iran Dar Nijeriye," shafi na. 81
- ↑ Kurdi, Shi'ayane Nijriye (Fursatha, Tahdidha, Babarha)," shafi. 123.
- ↑ «اربعین خونین ابوجا»، روزنامه خراسان.
- ↑ «توطئه سعودیها و صیهونیستها برای سرکوب شعیان نیجریه»، Kamfanin Dillancin Labarai na Mizan؛ «افشاگری شیخ زکزاکی از نقش انگلیس در کشتار شیعیان نیجریه» Shafin Kihan
- ↑ «اربعین خونین ابوجا»، Jaridar Khorasan; Pishvaei, "Maganar Watan: Launin Parisian, Beiruti, da Jinin Najeriya," shafi. 7;«افشاگری شیخ زکزاکی از نقش انگلیس در کشتار شیعیان نیجریه» Shafin Kihan
- ↑ «شیعیان نیجریه»، Shafin Diflomasiya ta Iran.
- ↑ «شیعیان نیجریه»، Shafin Diflomasiya ta Iran.
- ↑ «شیعیان نیجریه»، Shafin Diflomasiya ta Iran
- ↑ «تظاهرات شیعیان نیجریه علیه سرکوب عزاداران اربعین حسینی»، Kamfanin dillancin labarai na Abna.
- ↑ «شیعیان نیجریه»، Shafin Diflomasiya ta Iran.
Nassoshi
- "Arbaeen dar Nijeriye", Kamfanin Dillancin Labarai na Mizan, kwanan wata: 13 Azar 1394, kwanan wata ziyara: 14 Shahrivar 1403.
- "Barguzari Ba Shukuhutarin Marasim Arbaeen", Kamfanin Dillancin Labaran Jamhuriyar Musulunci, kwanan wata: 14 Azar 1394.
- "Piyade Arbaeen Dar Nijeriye", Iran Press International Video Agency, kwanan wata: 17 Sharif 1401, kwanan wata ziyara: 8 Sharif 1403.
- Tautiye Saudiyeha Wa Sahayunistiha Baraye Sarkube Shi'ayane Nijeriye, Kamfanin Dillancin Labarai na Mizan, kwanan wata: 9 Aban 1397, ranar ziyara: 14 Sharif 1403.
- "Didare Shaikh Zakzaky Ba Jam'i Az Daste Andekaran Arba'in, Kamfanin Dillancin Labarai na Hawza, Ranar Shiga: 13 ga Agusta, 1403, Ranar Ziyara: 7 ga Satumba 1403.
- Nijeriye: Sewomin Kishware Islami: Shiayane Nijeriye, a cikin mujallar Darsahayee iz Maktab al-Islam, No. 661, Yuni 1395.
- Pishvaei, Mehdi, "Sukhane Mahe: Watan: Range Khun Parisian, Beiruti dar Najeriye", a cikin mujallar Darsahayee iz Maktab al-Islam, No. 657, Fabrairu 1394.
- Hosseini, Mehdi, "Qatle Amme Bi Saro Sida Shiayane Nijerye dar Arbaeen 97", a cikin Mujallar Pasdar al-Islam, mai lamba 441-442, Nuwamba da Disamba 1398.
- Shojaifard, Mohammad Hassan, Negahi Beh Zindagi Sheikh Ibrahim Zakzaky, Rahbare Shi’ayane Nijeriya, Ibrahimi Ba Qudrate Yek Ummat,” a cikin Mujallar Pasdaran Islam, mai lamba 455 da 456, Janairu da Fabrairu 2019.
- Ghaibi Hajipour, Nazanin da Mahdieh Namdar, “Tasirat Wa Baztabhaye Inqilabe Islami Iran Dar Nijeriye” a cikin Mujallar Nazarin Alqur’ani ta Nameh-e-Jame’a, No. 119, Fall 2016.
- Kurdi, Hamid Reza, Shi’ayane Nijeriye (Fursatha, Tahdidha, Babarha),” a cikin Mujallar Payam, No. 116, Winter 2015.
- Tazahurat Shiayane Nijeriye Alaihi Sarkub Azadaran Arba'in Husaini, Kamfanin Dillancin Labarai na ABNA, Ranar Buga: 1 ga Satumba, 1403, Ranar Ziyara: 11 ga Satumba, 1403.
- Ifshageri Sheikh Zakzaky Az Naqshe Ingilis Dar Kushtare Nijeriye", Shafin Kayhan, Ranar Buga: 1 ga Oktoba, 1401, Ranar Ziyara: 16 ga Satumba, 1403.