Jump to content

Tattakin Mutanen Da Ba Su Je Tattakin Arba'in Ba

Daga wikishia
Tattakin Mutanen Da Ba Su Je Tattakin Arba'in Ba
Tattakin mutanen da ba su je Arba'in ba a 2020 da aka yi a garin Tabriz[1]
Tattakin mutanen da ba su je Arba'in ba a 2020 da aka yi a garin Tabriz[1]
Lokacin da aka shiryaArba'in na Husaini
Faɗin ƙasaIran, Iraƙi, Fakistan, Afganinstan da Najeriya
Abubuwa da AlamomiTutoci da masu tattaki


Tattakin waɗanda ba su rabauta da zuwa Arba’in ba (Larabci: مسيرة المتأخرين عن الأربعين) Wani takawa da ƙafafu ne ko ace gangami da ake yi a ƙasashan Muslumi da ma waɗanda ba na Musulmi ba a dai-dai lokacin da ake tattakin arba’i na Imam Husaini (A.S) a ƙasar Iraƙi, a wannan tattaki ko taro duk wanda bai sami zuwa tattakin Arba’in ba, to zai kasance ya yi tarayya a wannan tattakin a garin su.[2] Kuma a wannan tattaki ko taro ana kafa runfuna kamar waɗanda ake kafawa a lokacin taron Arba’in, kuma ana bada taimako ga waɗanda suke halartar wannan tattaki.[3]

Wannan taro, taro ne da ya kasance ana aiwatar da shi tun kafin yaɗuwar Korona (Annobar cutar shaƙe numfashi) a garuruwan Iran, bisa wata majiya ta wata kafar watsa labarai an fara aiwatar da wannan taro tin daga shekarar 2016 a garin Tehran,[4] amma bayan yaɗuwar Korona a shekara ta 2019 Miladiyya bayan da gwamnatin Iraƙi ta sa dokar killace mutane maziyarta waɗanda suka zo daga ƙasashen duniya domin ziyara, sai ake aiwatar da wannan taro a cikin garuruwa daban-daban na Iran, masamman abin ya fi yaɗuwa a shekara ta 2020 da 2021 Miladiyya.[5] Shugaban mu’assasar Tabligin Muslinci a Iran ya ce a shekara ta 2023 an sami damar aiwatar da wannan taro a garuruwa guda 600 da kuma ƙauyuka guda 6300 a Iran, kuma mahalarta wannan taro sun kai mutum miliyan 14.[6]

Har ila yau an aiwatar da irin wannan taro a ƙasashe daban-daban kamar Iraƙi,[7]Fakistan,[8] Afganistan,[9] da Najeriya,[10] kai harda wasu ƙasashan da ba na Musulmi ba, inda masoya iyalan gidan Manzo (A.S)kamar ƙasar Suwidin,[11] Japan[12] da Astiraliya.[13]

Bayanin kula

  1. «پیاده‌روی جاماندگان اربعین در تبریز»، خبرگزاری مهر.
  2. نگاه کنید به: «مسیرهای راهپیمایی جاماندگان اربعین در شهرستان‌های استان تهران اعلام شد»، Kamfanin dillancin labarai na IRNA.
  3. نگاه کنید به «صفر تا صد پیاده‌روی جاماندگان اربعین + عکس و فیلم»، Kamfanin dillancin labarai na ISNA
  4. Duba: "Rahefaimayi Arba'in, Rasaneh Jahani", Jaridar Hamdali, shafi. 4.
  5. «در مورد پیاده‌روی اربعین در ویکی تابناک بیشتر بخوانید»، Tabnak.
  6. Duba: «تلخی کرونا بر دل عاشقان جامانده از قافله عشاق اربعین»، Kamfanin dillancin labarai na IRNA.
  7. «حضور ۱۴میلیون نفری در آئین جاماندگان اربعین»، Kamfanin dillancin labarai na IRNA.
  8. «تجلی اربعین حسینی در پاکستان؛ ندای وحدت و برائت از تفرقه طنین‌انداز شد»، Kamfanin dillancin labarai na IRNA.
  9. «پیاده‌روی جا ماندگان اربعین در افغانستان به روایت تصویر»، Kamfanin dillancin labarai na IRNA..
  10. «اجتماع عظیم اربعین بی‌نظیر است/ شبیه‌سازی پیاده‌روی جاماندگان اربعین در نیجریه»، Kamfanin dillancin labarai na IRNA..
  11. تقرير مصور/ مشاركة واسعة بمسيرة الأربعين في العاصمة السويدية، Shafin yanar gizo na Abna.
  12. تقرير مصور/ مسيرة أربعينية الإمام الحسين(ع) في بلد يعتنق غالبية شعبه "الديانة الشنتوية"،Shafin yanar gizo na Abna.
  13. تقرير مصور/ مشاية الأربعين الحسيني في مدينة أديليد الاسترالية، Shafin yanar gizo na Abna

Nassoshi