Sailul Arim

Daga wikishia

Sailul Arim (Larabci: سیل العَرِم ) babbar anbaliya ce wace Allah ya turowa mutanan Saba'i a ƙasar Yaman a matsayin azaba, kuma an anbaci wannan azaba a aya ta 16 cikin suratul Saba'i, sabo da Allah ya turo musu annabawa da yawa amma ba su yi imani da su ba kuma ba su shiriya ba, sai anbaliyar ruwa ta faro saka makon fashewar madatsar ruwa ta Ma'arib ko kuma dama na Al'arim wanda mutane suka kasance suna anfani da shi wajen ban ruwa ga shuka a gonakinsu, sai ruwa ya shanye garin da duk gonakinsu su ka zama ba bu komai a ciki kuma suka zama hamada bushashshiya, wasu masu tafsiri sun fassara cewa dalilin da yasa dam ɗin ya balle shi ne, Allah ne ya turo da bera wanda ya bula katangar dam ɗin sai ya ruguje.

Malaman tarihi sun ce anbaliya ta Sailil Arim ta faru ne a arewa maso gabas a garin San'a'a a ƙasar Yaman a yau, kuma wannan anbaliya ta faru shekara ta 532 miladiyya.

Ƙissar Sailul Arim

Sailil Arim anbaliya ce babba kuma mai ƙarfi wacce ba za a iya daure mata ba, wanda ya sami garin Ma'arib a ƙasar Yaman, sabo da lalacewar dam ɗin garin wanda mutanan wannan yanki suke anfani da shi wajan ban ruwa ga lambunsu da kuma gonakinsu.[1] Addinuri da Masa'udi waɗan da suke malaman tarihi ne su na ƙarni na uku sun yi imani da cewa mutanan Saba'a su ne suka kasance mazauna garin Ma'arib.[2] kuma malaman tarihi sun ce ƙasar Saba'i ƙasa ce mafi kyan numa a ƙasar Yaman kuma mafi dukiya da yawan yabanya da kuma gina-gine masu kyau da bushiyu jerarru kuma duk mutanan yanki sun kasance suna anfani da dam na garin Ma'ari ne.[3]

Kuma wasu daga cikin bincike sun nuna cewa wannan anbaliya ta Sailil Arimi ta faru ne a shekara ta 447 zuwa 450 kuma shekara ɗari huɗu kafin zuwa musulinci kuma ya faru ne a ƙarni na shida a miladiya,[4] sabo da haka ne ya zo a tarihi cewa mutanan da suka kasance suna rayuwa a wancan lokacin kafin faruwar wannan anbaliya sun yi ƙaura zuwa wasu yankuna kamar Iraƙi, Sham da kuma Yasriba [Madina].[5]

Masa'udi ya faɗa a cikin littafin shi cewa shi dam ɗin Al'arim yana da faɗin kilo mita ashirin da biyu na murabba'i,[6] kuma ya shahara da sunan dam na Ma'arib,[7] ya kuma ƙara da cewa Luƙuman ɗan Ad shi ne wanda ya gina wannan dam ɗin,[8] amma shi Abul Futuh Arrazi ya tafi kan cewa Bilkisu sarauniyar Saba'a ita ce ta gina wannan dam ɗin.[9]

An anbaci fuskoki masu yawa kan ma'anar kalmar Arim, daga ciki akwai, suna ne na anbaliya da ta faru wace ta kai ga lalata duk gari,[10] kuma ruwan sama ne wanda ya kai ga faruwar anbaliya,[11] kuma suna ne na dam wanda mutanan Saba'a suka gina,[12] sunan beran da ya lalata katangar dam ɗin Ma'arib wanda daga ƙarshe ya kai ga anbaliya babba,[13] sun anbaci cewa sunan wannan ruwa ne mai jar kala wanda ya zo a matsayin azaba ga mutanan Saba'a.[14]

Anbatan Wannan Anbaliya A Cikin Kur'ani

Aya ta 16 suratul Saba'i ta ambaci sailul arim, malaman tafsiri sun yi bayani abin da ya faru da mutanen saba'i yayin da Allah ya aiko musu da anbaliya.[15] Abu al-Futuh al-Razi, malamin tafsirin Shi'a a karni na shida bayan hijira, ya ambaci cewa Allah Ta'ala ya aiko da (annabawa|annabawa) 13 domin su shiryar da mutanen Saba'a, amma sun karyata annabawa, kuma sun gaskata cewa duk wata ni'ima da suke da ita. ya zo daga gare su, ba daga wurin Allah ba,[16]

Malaman tafsiri sun yi imanin cewa, dalilin da ya sa wannan ambaliya ya faru ne sakamakon rashin godiyar da mutanen Sheba suka yi da kuma musun wannan ni'imar.[17] Allah ya aiko da bera ya huda dam din kogin don ya halaka mutane da ambaliya[18] Ambaliyar Al-Aram ta kai ga rugujewar gonakin noman da ke bangarorin biyu na birnin,[19] kuma filayensa sun koma kasa mai gishiri da ba za a iya amfani da su ba Al-Kafi da Mirat Al-Uƙul da cewa shi ne azabar Ubangiji ga mutanen Saba.[20]

Binciken Malaman Tarihi

Kamar yadda wani bincike da wasu masana gabas da binciken tarihi suka gudanar a karni na sha tara miladiyya, kogin Al-Aram ya afku a birnin Ma'rib, dake arewa maso gabashin birnin Sana'a na yanzu.[21] Wasu masu bincike sun bayyana cewa, an gina madatsar ruwa ta Al-Aram a tsayin mita 1160 sama da matakin teku, ta hanyar amfani da fasahohin injiniya mafi inganci a wancan lokaci, amma daga shekara ta 447 zuwa 450 Miladiyya an samu wani kogi wanda ya kai ga hijirar mutane. kuma a shekara ta 532 miladiyya dam din ya ruguje.[22] An samu wani rukuni na rubuce-rubuce da kayan ado a kusa da wurin dam din da suka yi magana kan tarihin mutanen Sheba da ambaliyar Al-Aram.[23] kasancewar masana gabas da masana tarihi a wurin da ruwan Al-Aram ya yi.[24]

Bayanin kula

  1. Al-Dinuri, Al-Akhbar al-Tawwal, shafi na 17; Al-Masoodi, Moruj al-Dahahab, juzu'i na 2, shafi na 161.
  2. Al-Dinuri, Al-Akhbar al-Tawwal, shafi na 17; Al-Masoodi, Moruj al-Dahahab, juzu'i na 2, shafi na 161.
  3. Al-Masoudi, Moruj al-Dahahab, juzu'i na 2, shafi na 162
  4. Jafarian,Nufuzul Islami dar Yathrib, shafi na 95.
  5. Minhaj Siraj, Tabaqat Nasiri, juzu'i na 1, shafi na 183.
  6. Al-Masoudi, Murooj al-Dhahab, juzu'i na 2, shafi na 161.
  7. Abu al-Futuh al-Razi, Rawd al-Jinan, juzu'i na 16, shafi na 60; Al-Tabarsi, Majma’ al-Bayan, juzu’i na 8, shafi na 606.
  8. Al-Masoudi, Murooj al-Dhahab, juzu'i na 2, shafi na 161.
  9. Abu al-Futuh al-Razi, Rawd al-jinan, juzu'i na 16, shafi na 60
  10. Abu al-Futuh al-Razi, Rawd al-jinan, juzu'i na 16, shafi na 60.
  11. Abu al-Futuh al-Razi, Rawd al-jinan, juzu'i na 16, shafi na 60.
  12. Abu al-Futuh al-Razi, Rawd al-jinan, juzu'i na 16, shafi na 60.
  13. Abu al-Futuh al-Razi, Rawd al-jinan, juzu'i na 16, shafi na 60.
  14. Al-Balaghi, Hujjat al-Tafsir, juzu'i na 1, shafi na 146.
  15. Al-Tabari, Jami’ al-Bayan, juzu’i na 2, shafi na 53-59; Al-Suyuti, Al-Durr Al-Manthur, juzu'i na 5, shafi na 331-333; Al-Tabatabai, Al-Mizan, juzu'i na 16, shafi na 362-368.
  16. Abu al-Futuh al-Razi, Rawd al-jinan, juzu'i na 16, shafi na 60.
  17. Al-Tabatabai, Al-Mizan, juzu'i na 16, shafi na 362-368; Abu al-Futuh al-Razi, Rawd al-jinan, juzu'i na 16, shafi na 60.
  18. Abu al-Futuh al-Razi, Rawd al-Jinan, juzu'i na 16, shafi na 60; Makarem Al-Shirazi, Al-Athmal, juzu'i na 18, shafi na 68.
  19. Makarem Al-Shirazi, Al-Amsal, juzu'i na 18, shafi na 68
  20. Al-Kulayni, Al-Kafi, juzu'i na 2, shafi na 274; Al-Majlisi,Mir'atul Al-uqul, juzu'i na 9, shafi na 422-424.
  21. Makarem Al-Shirazi, Al-Amsal, juzu'i na 18, shafi na 69; Al-Balaghi, Kisas Kur’ani, shafi na 379.
  22. Biazar Shirazi, Bastane shinasi wa Geograph Taikhi qasas Kur'ani, shafi na 331-333.
  23. Makarem Al-Shirazi, Al-amsal, juzu'i na 18, shafi na 69.
  24. Al-Balaghi, Qases al-Qur'an, shafi na 379.

Nassoshi

  • "Al-Qur'ani Mai Girma".
  • Abu al-Futuh al-Razi, Hussein, 'Rawd al-jinan wa Ruh al-jinan a cikin Tafsirin Alqur'ani, Mashhad - Iran, mawallafi: Ataba al-Radawiyya, bugu na 1, 1408 AH.
  • Al-Balaghi, Abd al-Hajjah, Hujjat al-Tafsir wa Balagh al-Ixir, Qom - Iran, mawallafi: Hikmat, bugu na 1, 1386H.
  • Al-Balaghi, Sadr al-Din, 'Qasas Al-Qur'ani, Tehran - Iran, mawallafi: Amir Kabir, 1381H.
  • Al-Dinuri, Abu Hanifa, The Long News, Qom - Iran, publisher: Al-Radi Publications, 1368 A.H.
  • Al-Kulayni, Muhammad bin Yaqoub, Al-Kafi, Tehran - Iran, mawallafi: Dar Al-Kutub Al-Islamiyyah, 1407H.
  • Al-Majlisi, Muhammad Baqir, Mir'atrul Al-uqool', Tehran - Iran, mawallafi: Dar Al-Kutub Al-Islamiyyah, 1404H.
  • Al-Masoudi, Ali, Murujil Zahab, Qom - Iran, mawallafi: Darul Hijra, bugu na biyu, 1409H.
  • Al-Shirazi, Abdul Karim, Bastan Shenasi jiyogirafi Tarikhi qur'an, Tehran - Iran, Mawallafi: Littafin Rubutu na Farhang Islami, bugu na 3, 1380 AH.
  • Al-Suyuti, Abd al-Rahman, 'Al-Durr al-Manthur fi al-Tafsir bi al-Ma'thur, Qom - Iran, mawallafi: Kitabkhana Marashi Najafi, 1404 AH.
  • Al-Tabarsi, Al-Fadl bin Al-Hasan, Majma' Al-Bayan fi Tafsir Al-Qur'an, editors: Hashim Al-Rasuli and Fadlallah Al-Yazdi, Beirut - Lebanon, publisher: Darul Ma’rifa, 1406 Hijira/1986 Miladiyya.
  • Al-Tabatabai, Muhammad Hussein, 'Al-Mizan fi Tafsirin Alqur'ani, Beirut - Lebanon, mawallafi: Al-Alami Publications Foundation, bugu na biyu, 1390H.
  • Jafarian, Rasul, Nafouth Islam in Yathrib, Magazine Miqat Hajj, mawallafi: Namayandaki Wali Fakih Dur Amār Hajj wa Ziyarat, 1372 AH.
  • Makarem Al-Shirazi, Nasser, Al-amsal fi Tafsiril Kitabillahi AL-munazzal, Qom - Iran, Mawallafi: Mazhabar Imam Ali bin Abi Talib {{A.S}, bugu na daya, 1421H.
  • Minhaj al-Sarraj, Abu Omar, Tabaqat Nasiri, edited by: Abd al-Hay al-Habibi, Tehran - Iran, mawallafi: Dunyaei Kuttab, 1363 AH.

Al-Tabari, Muhammad bin Jarir, Jami' al-Bayan fi Tafsir al-Qur'an, Beirut - Lebanon, mawallafi: Dar Al-Fikr, 1412 AH.