Ainun Najasati
- Wannan wata ƙasida ce mai bayyanawa game da mafhumi na fikihu kuma ba za ta iya zama ma'auni na ayyukan addini ba. ku koma zuwa wasu tushe don ayyukan addini.
Ainun Najasati (Larabci: عين النجاسة) shi ne abin da a zatinsa shi Najasa ne, a mahangar muslunci wannan abu ba za a iya tsarkake shi, a ra'ayin Malaman fiƙihu na Shi'a idan Ainun Najasati ya taɓa wani abu da ya kasance tsarkakakke kuma yayin haɗuwarsu ɗaya cikinsu jikinsa akwai danshi, to shi ma wannan tsarkakakken abu ya zama najasa, a mahangar Muslunci jini, fitsari, kashi, maniyyi, mushe, Kare, Alade, Kafiri, giya da Fuƙƙa'u (giyar ruwan sha'ir) dukkanin ainun Ainun najasati ne.
Sanin Mafhumi
A ra'ayin mashhur ɗin Malaman fiƙihu Ainun Najasati yana da najasa ta zati a mahangar Muslunci, ba ya tsarkakuwa.[1] A fiƙihun Shi'a abubuwa guda goma ana lissafa su cikin Ainun Najasati, su ne kamar haka: jini, fitsari, kashi, mushe, Kare, Alade, maniyyi, Kafiri, giya, Fuƙƙa'u (giyar ruwan sha'ir)[2] tare da haka Sayyid Murtada ɗaya daga cikin manyan Malaman fiƙihun Shi'a a ƙarni na biyar ya tafi kan cewa sassan jikin Kare da Alade da babu rai tare da su bisa la'akari da rashin rai tare da su da kuma wasu alfanu ana lissafa su tsarkakakku.[3] wasu adadin Maraji'an taƙlidi sun sanya gumin jikin Raƙumi mai cin najasa cikin layin najasa.[4]
Hukunce- hukunce
Cikin fiƙihun Shi'a an ambaci hukunce-hukunce dangane da najasa. su ne kamar yanda bayaninsu zai zo a ƙasa: Idan Ainun najasati ya taɓa jikin wani abu da ya kasance tsakakakke shi ma wannan abun zai zama najasa,[5] ana kiran wannan abu da sunan Mutanajjisu (wanda ya najastu), na'am ciratuwa najasa tana da sharuɗɗa tsakanin abubuwan guda biyu Ainun najasati da abin da yake tsarkake dole ɗaya daga cikinsu ya zamana yana da danshi,[6] an jingina zuwa ga Faizul Kashani cewa bayan kawar da najasa daga Mutanajjisu ba tare da amfani da ruwa cikin kawar da ita da misalin amfani da Toilet paper najasar jikinsa ba zata ciratu ta tsallaka zuwa wani abu da yake tsarkakakke ba.[7] Shigar da Ainun najasati cikin Masallaci idan ya kasance domin wulaƙanta Masallacin to haramun ne.[8] Haramun ne cin Ainun najasati.[9] Ruwan da ya haɗu da Ainun najasati, idan ɗanɗano da kalarsa da warinsa ya canja ko da kuwa wannan ruwa ya kasance daga ruwa Jari ruwa mai gangara da gudana to zai zama najasa.[10] Wajibi ne a kawar da Ainun najasati daga baƙiɗayan gaɓɓan Alwala da na wanka na wajibi,[11] cikin alwala za a iya kawar da Ainun Najasati kafin a fara alwala da kuma lokacin da ake yin alwalar ta hanyar wanketa ko shafeta,[12] amma a cikin wanka dole kafin fara wankan a kawar da Ainun najasati.[13] Idan jiki ko tufafi suka taɓu da najasa da wani miƙdari da ya kasance ƙasa da girman dirhami (gwargwadon fadin babban ɗan yatsan hannu) daga jini da yake daga Ainun Najasati, babu matsala ayi sallah tare da wannan jini kuma sallar ta inganta.[14]
Bayanin kula
- ↑ Ghadiri, Al-ƙamos Al-Jame LilMustalahat Al-fikhiyya, 1418 AH, shafi na 576; Mughniyeh, Fiƙhu Al-Imam Al-Sadiƙ, 1414 AH, juzu'i na 1, shafi na 41.
- ↑ Bani Hashemi Khomeini, Risaleh Tauzihul Masa'il Maraji'u, 1385, juzu’i na 1, shafi na 64.
- ↑ Sayyid Morteza, Al-Masa'il Al-Nasiriyat, 1417 AH, shafi na 100.
- ↑ Bani Hashemi Khomeini, Risalahe Tauzihul Masa'il Maraji'u, 1385, juzu’i na 1, shafi
- ↑ Mousavi Khalkhali, Fiƙh Al-Shi’a, juzu’i na 3, shafi na 354.
- ↑ Bani Hashemi Khomeini, Tauzihul Masa'il Maraji, 1385, shafi na 85; Najafi, Jawahirul Al-Kalam, 1362, juzu'i na 6, shafi na 202.
- ↑ Al-Tabatabaei Al-Hakim, Mustamsak Al-urwa Al-Wuthgha 1384 A.H., juzu'i na 1, shafi.479; Mousavi Khalkhali, Fiƙh al-Shi’a, juzu’i na 3, shafi na 354.
- ↑ Najafi, Jawahirul Al-Kalam, 1362, juzu'i na 14, shafi na 97.
- ↑ Bani Hashemi Khomeini, Tauzihul al-Masa'il Al-Maraji, 1385, shafi na 91.
- ↑ Bahrani, Al-Hada'eƙ al-Nadrah, juzu'i na 1, shafi na 197 da 202.
- ↑ Najafi, Jawahirul Al-Kalam, 1362, juzu'i na 3, shafi na 101; Tabataba'i Yazdi, Al-Urwa Al-Wuthgha, Al-Maktab Al-Alamiya al-Islami, Mujalladi na 1, shafi na 169.
- ↑ Tabataba'i Yazdi, Al-Urwa Al-Wuthgha, Al-Maktab Al-Alamiya al-Islami, Mujalladi na 1, shafi na 169.
- ↑ Najafi, Jawahirul Al-Kalam, 1362, juzu'i na 3, shafi na 101-102.
- ↑ Shahid Sani, Al-Rawda al-Bahiyya, 1410 AH, juzu'i na 1, shafi na 289.
Nassoshi
- Bani Hashemi Khomeini, Mohammad Tauzihul masa'il Maraji: mutabik fatawa sizda nafar az maraji taklid, ƙum, ofishin wallafe-wallafen Musulunci (Kungiyar Malaman Makarantar Sakandare ta Kum), 2005.
- Sayyid Morteza, Ali bin Hossein, Al-Masa'il al-Nasiriyat, Tehran, dangantakar al'adu da alakar Musulunci, bugu na farko, 1417H.
- Shahidi Thani, ZainulDin bin Nur al-Din Ali, Al-Rawda' Al-Bahiyya fi Sharh al-Luma'a Al-Damashƙiyya, ƙum, al-Dawari School, 1410 AH.
- Tabatabai Elizdi, Sayyed Mohammad Kazem, Al-urwa Al-Wuthgha, School of Ayatullah Azami Al-Sayed Al-Sistani, B.T.
- Al-Tabatabaei Al-Hakim, Seyyed Mohsen, Mustamsak Al-Urwa Al-Wuthgha, Beirut, Dar Ihya Al-Trath Al-Arabi, 1384H.
- Ghadiri, Abdullah Isa Ibrahim, al-ƙamos al-JamaeLil-Mustalahat Alifiƙhiyya, Beirut, Darul Hijjah al-Bayda, 1418 AH.
- Mughniyeh, Mohammad Javad, Fiƙh Al-Imam Al-Sadiƙ, ƙom, Cibiyar Ansari, 1414 AH.
- Najafi, Mohammad Hassan, Jawaher Al-Kalam, Beirut, Dar Ihya Al-Trath Al-Arabi, bugu na 7, 1362.