As'habul Sabti
As'habul Sabti, (Larabci: أصحاب السبت) wasu gungun jama'a ne daga Bani Isra'il waɗanda bisa bayanin da ya zo cikin ayoyin Alkur'ani sakamakon saɓawa umarnin Ubangiji da ya hana su ɗebo kifi daga kogi a ranar asabar sun faɗa cikin azabar Allah, kamar yanda Alkur'ani ya ba da labari As'habul Sabti halittarsu ta jirkita sun koma Birrai, bisa ba'arin wasu riwayoyi an yi masak ɗin wannan gungun Jama'a sannan bayan kwana uku aka halaka su, aksarin riwayoyi sun bada rahoto kan cewa wannan abu ya faru a zamanin Annabi Dauda (A.S) a garin Ileh wanda yanzu yake matsayin Palasɗinu da aka mamaye. Allama Ɗabaɗaba'i cikin tafsirul almizan ya ce: kaɗai dai mutanen da suka tsira daga As'habul Sabti sun kasance masu umarni da kyakkyawa da hani da mummuna, sannan waɗanda suka aikata lefi, haka kuma waɗanda suka yi shiru daga wancan lefi ba su kwaɓe su ba sun faɗa cikin azabar Allah.
Sanin Mafhumi
As'habul Sabti, wasu gungun jama'a ne daga Bani Isra'il da suka faɗa cikin azabar Allah sakamakon saɓawa umarninsa cikin hana su yin su da ɗebo Kifi ranar asabar,[1] waɗannan mutane sun rayu ne a zamanin Annabi Dauda (A.S) adadinsu ya kai mutane dubu goma sha biyu ko dubu saba'in,[2] jumlar As'habul Sabti sau ɗaya ta zo cikin Alkur'ani ƙarara a fili a cikin aya ta 47 suratul nisa'i, amma cikin sauran ayoyin Alkur'ani mai girma [Tsokaci 1] an yi bayanin ƙissar waɗannan mutane.[3] Sabti yana nufin yankewa ko yanke aiki,[4] a harshen Abriyanci suna karanta ta da Shabat,[5] suna ne na ranar asabar tsakankanin Yahudawa,[6] a harshen Abriyanci yana bada ma'anar hutu,[7] kan asasin Al'adar Yahudawa mutanen Yahud, ranar asabar wajibi mutum ya ajiye dukkanin ayyukansa a gefe ya huta,[8] kiyaye alfarmar ranar asabar da rashin yin aiki cikin wannan rana ya kasance ɗaya daga cikin umarni guda goma na Annabi Musa.[9]
Waƙi'a
Bisa Alkur'ani Mai girma, As'habul sabti sakamakon saɓa umarni da ketare dokoki da iyakokin Allah a ranar asabar, da su ɗin kifi tare da ɗebo shi daga ruwa a wannan rana wanda haka ƙarara saɓawa umarnin da aka hane su ne,[10] sai Allah ya yi masak ya jirkita halittarsu matsayin uƙuba kan abin da suka aikata da kuma zama darasi ga masu tsoran Allah.[11] Kan asasin wata riwaya daga Imam Sajjad (A.S), As'habul Sabti wasu mutane ne da suka kasance suna rayuwa a gefen kogi sai Allah ya hana su yin su ɗin Kifi ranar Asabar,[12] sakamakon kifaye masu tarin yawa suna gangarowa gaɓar kogi a ranar asabar, sai suka shirya wata dabara domin yin su ɗin kifi a wannan rana, suka haƙa ramuka kusa da gaɓar kogin ta yanda kifaye za su dinga shiga wannan ramuka su taru da yawa kuma ba zasu iya fita daga wannan ramuka ba,[13] As'habul Sabti duk da cewa a zahiri ba su yi su ɗin kifi ba ranar asabar amma washegari lahadi sai suka je suka ɗebe kifaye da suka haƙawa tarko suka shiga waɗannan ramuka,[14] As'habul Sabti da wannan dabara ce suka tara dukiya mai yawa gaske tare da samun ni'imomi masu yawan gaske,[15] kan asasin wannan riwaya adadinsu ya kai mutane dubu tamanin, dubu saba'in daga cikinsu suka saɓawa umarnin Allah kan abin da ya hana su na su ɗin kifi a ranar asabar.[16]
Masak As'habul Sabti
- Asalin Maƙala: Masak
As'habus Sabti a ƙarshe al'amari dai azabar Allah ta sauka kansu an jirkita halittarsu. Kamar yanda bayani ya zo daga Alkur'ani mai girma bisa umarni Ubangiji sun jirkita sun koma Birrai,[17] bisa ba'arin rahotan da ya zo daga riwayoyi waɗannan gungun jama'a an jirkita halittarsu sannan kuma bayan kwanaki uku aka halaka su.[18] Sayyid Muhammad Husaini Ɗabaɗaba'i cikin tafsirul almizan ya rubuta cewa: kan asasin aya ta 165 suratul A'araf, waɗanda daga cikinsu suka kasance suna umarni da kyakkyawa da hani daga mummuna sun tsira, amma sauran jama'a biyu daga cikinsu ma'ana waɗanda suka aikata lefi da waɗanda suka kame bakinsu ba su tsawatar musu ba dukkaninsu azabar Allaha ta sauka kansu.[19] Wasu ba'ari daga jumlarsu akwai Mujahid Bn Jabar, Malamin tafsirin Shi'a wanda ya rasu a shekarar 104 h ƙamari, da kuma Muhammad Abduhu Malamin tafsiri na Ahlus-sunna sun yi Imani kan cewa Masak a kan gangar jiki bai faru da As'habul Sabti ba, sannan abin da ya zo a aya ta 65 suratul Baƙara misali ne kawai da hikaya kan jirkitar zuciyoyin As'habul Sabti.[20]
Wuri Da Lokaci Kamar yadda ayoyin Kur'ani suka nuna cewaAs'habul Sabti suna rayuwa ne a bakin teku [21] A cikin ruwayar Imam Bakir (A.S) an bayyana birnin Ileh matsayin inda suka rayu[22] Fakhr Razi shima yana ganin sun zauna a birnin Ileh [23] akwai tsammanin birnin Ileh shi ne dai birnin Eilat na yanzu, wanda ke kusa da tekun Bahar Maliya kuma a cikin Palastinu da Isra'ila ta mamaye.[24] A cewar Allama Ɗabaɗabai, garuruwan Madyana da Tiberias kuma an ambaci su a matsayin wuraren da Ash'habul Sabti suka rayu.[25]
Mafi yawan hadisai sun yi la'akari da kissar As'habul Sabti ta kasance a zamanin Annabi Dauda.[26]
Bayanin kula
- ↑ Rouhi, "As'habul Sabti", shafi na 232.
- ↑ Rouhi, "As'habul Sabti", shafi na 232.
- ↑ Rouhi, "As'habul Sabti", shafi na 232.
- ↑ ƙureshi Bonabi, ƙamus ƙur'an, 1372, juzu'i na 3, shafi na 207.
- ↑ Rouhi, "As'habul Sabti", shafi na 232.
- ↑ ƙureshi Bonabi, ƙamus ƙur'an, 1372, juzu'i na 3, shafi na 207
- ↑ ƙureshi Bonabi, ƙamus ƙur'an, 1372, juzu'i na 3, shafi na 207
- ↑ ƙureshi Bonabi, ƙamus ƙur'an, 1372, juzu'i na 3, shafi na 207
- ↑ ƙureshi Bonabi, ƙamus ƙur'an, 1372, juzu'i na 3, shafi na 207
- ↑ Suratul Baƙarah, aya ta 65; Duba kuma: Majlesi, Hayatul Al-ƙulob, 2004, juzu'i na 2, shafi.947.
- ↑ Suratul Baƙarah, aya ta 66; Duba kuma: Majlesi, Hayatul Al-ƙulob, 2004, juzu'i na 2, shafi.948.
- ↑ Majlisi, Hayatul Al-ƙulob, 2004, juzu'i na 2, shafi na 948.
- ↑ Majlisi, Hayatul Al-ƙulob, 2004, juzu'i na 2, shafi na 948.
- ↑ Majlisi, Hayatul Al-ƙulob, 2004, juzu'i na 2, shafi na 948.
- ↑ Majlisi, Hayatul Al-ƙulob, 2004, juzu'i na 2, shafi na 948.
- ↑ Majlisi, Hayatul Al-ƙulob, 2004, juzu'i na 2, shafi na 948.
- ↑ Suratul Baƙarah aya ta 65.
- ↑ Tafsirin Imam Hasan Askari, 1409H, shafi na 279.
- ↑ Tabatabai, Al-Mizan, 1417 AH, Mujalladi na 8, shafi na 268-269.
- ↑ Mughniyeh, Tafsir Al-Kashif, 1424 AH, juzu'i na 1, shafi na 121.
- ↑ Suratul A'araf, aya ta 163.
- ↑ Ɗabarasi, Majma Al-Bayan, 1372, juzu'i na 1, shafi na 266.
- ↑ Fakhr Razi, Mufatih Al-Ghaib, juzu'i na 12, shafi na 412.
- ↑ Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 2013, juzu'i na 6, shafi.418.
- ↑ Tabatabaei, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 8, shafi na 303.
- ↑ Fakhr Razi, Mufatih al-Ghaib, 1420 AH, juzu'i na 12, shafi na 412.
Tsokaci
- ↑ Aya ta 65 suratul bakara, aya ta 154 suratul nisa, aya ta 163 suratul a'araf, aya ta 124 suratul nahli
Nassoshi
- Alkur'an Al-Kareem.
- Tafsirin Imam Hasan Askari, ƙum, Madrasah Al-Imam al-Mahdi, 1409H.
- Ruhi, Abulfazl, "Sahabbai", a cikin shelar Al-ƙur'ani: Daga Encyclopedia of the Holy ƙur'an, juzu'i na 2, ƙum, Bostan Kitab Institute, 2005.
- Tabatabaei, Seyyed Mohammad Hossein, Al-Mizan fi Tafsirin Al-ƙur'an, ƙum, Islamic Publications Office, 1417H.
- Ɗabarasi, Fazl bin Hassan, Majma Al-Bayan fi Tafsir al-ƙur'an, Tehran, Nasser Khosrow, 1372.
- Fakhr Razi, Muhammad bin Omar, Mufatih Al-Ghaib, Beirut, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, 1420H.
- ƙureshi Banabi, Ali Akbar, ƙamus ƙuran , Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya, 1371.
- Majlesi, Mohammad Baƙer, Hayatul Al-ƙulob, ƙom, Sarwar, 2004.
- Mughniyeh, Mohammad Javad, Tafsir Al-Kashif, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya, 1424H.
- Makarem Shirazi, Nasser, et al., Tafsir Namuneh,Tehran, Dar al-Katb al-Islamiyya, 1380.