Mamaye Ofishin Jakadancin Amurka A Tehran
| Sauran sunaye | Mamaye sheƙar leƙen asiri. juyin juya hali na biyu |
|---|---|
| Bayanin Abin da ya faru | Mamaye ofishin jakadancin Amurka a Tehran ta hannun ɗaliban jami'a mabiya hanyar Imam |
| Lokaci | 4 Nuwamba 1979 miladiyya |
| Zamanin | Jamhuriyar Muslunci Ta Iran |
| Wuri | Ofishin jakadancin Amurka a Tehran |
| Dalili | Baiwa Sarki Shah mafaka a Amurka |
| Manufa | Dawo da Sarki Shah ƙasar Iran. takawa Amurka birki daga yunƙurinta na shirya juyin mulki |
| Mutanen da suka kai harin | ɗalibai mabiya hanyar Imam |
| Sakamako | Katse hulɗoɗin diflomasiyya tsakanin Amurka da Iran. katse fitar da man fetur daga Iran zuwa Amurka |
| Asara | Babu |
| Martani | Murabus na gayyar ƙusoshin tsohuwar gwamnatin Shah. toshe asusun kuɗin Iran a bankunan Amurka |
Mamaye ofishin jakadancin Amurka a Tehran, (Larabci: احتلال السفارة الأمريكية في طهران) wanda aka fi sani da mamaye sheƙar leƙen asiri, magana ce game da karɓe iko kan ofishin jakadancin Amurka a Tehran da ɗaliban jami'a mabiya hanyar Imam Khomaini a ranar 4 Nuwamba 1979m, suka yi, hakan ta faru ne a ƙoƙarin nuna rashin amincewarsu da karɓar Sarki Muhammad Rida Pahlawi da Amurka ta yi. Imam Khomaini, jagoran Iran a wancan lokaci, ya bayyana wannaد mataki matsayin juyin juya hali na biyu, ya kuma kira Amurka da laƙabin babbar shaiɗaniya, kuma ofishin jakadancinta a Tehran ya kasance sheƙar leƙen asiri.
Wannan muhimmi lamari ya kasance tare da saƙonni; daga jumlarsu an samu gungun ƙusoshin gwamnatin wucin gadi sun yi murabus, yankewar hulɗar diflomasiyya tsakanin Amurka da Iran da kuma dagatar da kadarorin Iran da suke ƙasar Amurka.
Bayan wargajewar shirin harin soja na Amurka a garin Ɗabas a shekarar 1980m, daga ƙarshe bayan kwanaki 444 an saki ma'aikatan Amurka da aka kama matsayin garkuwa, baya ga shiga tsakanin da ƙasar Aljeriya ta yi da kuma amincewar majalisar shura ta Muslunci.
Wannan rana ta 4 Nuwamba 1979m, a Iran ana tunawa da ita a matsayin ranar ƙasa ta yaƙi da girman kai na Duniya.
Muhimmanci Da Matsayi
Mamaye ofishin jakadancin Amurka a Tehran a ranar 4 Nuwamba 1979m, wanda aka fi sani da mamaye sheƙar leƙen asiri,[1] A cewar wasu yana cikin muhimman lokuta na tarihin juyin juya halin Muslunci na Iran.[2] Wasu sun yi imani da cewa wannan lamari sakamakon tasiri da yake da shi cikin katse ƙarfin ikon manyan ƙasashe kan Iran(Imperialism),[Tsokaci 1] yana da muhimmin matsayi a tarihin juyin juya halin Muslunci.[3]
Imam Khomaini ya kira wannan mataki da ɗalibai suka ɗauka da sunan juyin juya hali na biyu, tare da bayyana shi a matsayin wani mataki da yake sama da juyin juya halin.[4] Wannan lamari a cewar jagororin Iran ya kasance sababin kunyata Amurka[5] da rusa makirce-makircen da maƙiya suka shirya a kan Iran[6] Haka nan wannan mataki ya kasance tare da wasu saƙonni na daban, da suka haɗa da katse hulɗoɗin diflomasiyya da dagatar da dukiyoyin Iran a Amurka.
Farancis Antony Boyle, manazarci kuma malamin ilimin siyasa a jami'ar Illinois Amurka, ya bayyana cewa bisa dogara da doka mai lamba 51 cikin dokokin majalisar ɗinkin duniya wannan mataki yana matsayin halattacen haƙƙin kare kai na Iran gaban barazanar Amurka. Ya kuma siffanta wannan mataki da ɗaliban jami'ar Iran suka ɗauka matsayin matakin takawa Amurka birki daga ƙoƙarin keta alfarmar Iran da kuma yunƙurin juyin mulki da take son yi a Iran.[7]
A yau ana la'akari da wannan rana a cikin kalandar Iran matsayin ranar yaƙi da girman kai na duniya, kuma duk shekara ana shirya jerin gwano domin girmama wannan rana.[8]
Jawabain Imam Khomaini game da mamaye ofishin jakadancin Amurka da ya yi a ranar 5 Nuwamba 1979m, yau ba rana ce da za mu zauna muna zuba idanu ba a gaban makirci da cin amana da ake yi a ofisoshin jakadanci, musamman na Amurka. Yana kiran Amurka da “Babban Shaidan”, yana nuna cewa ita ce tushen makirci da barazana ga Iran. Yana ƙarfafa al'umma su tashi tsaye, su hana Amurka aiwatar da manufofinta ba tare da martani ba. Yana kiran wannan mataki da "juyin juya hali na biyu", wanda zai fi na farko tasiri da girma.
Muhimman Dalilai Kan Mamaye Wannan Wuri
Baiwa Muhammad Rida Pahlawi mafakar gudun hijira a Amurka a ranar 22 Oktoba 1979m, yana daga cikin dalilan mamaye ofishin jakadancin Amurka a Tehran da ɗalibai suka yi.[10] Imam Khomaini a ranar 31 Oktoba da 3 Nuwamba 1979m, cikin nuna rashin amincewa da baiwa Muhammad Rida Pahlawi mafaka da Amurka ta yi, ya buƙaci ɗaliban jami'a da na Sakandire da kuma ɗaliban makarantun addini su fito su ƙalubalanci Amurka kan wannan mataki da ta ɗauka.[11] A cewar Hamid Ansari mataimakin shugaban cibiyar kula da tsare-tsare da yaɗa ayyukan Imam Khomaini, haƙiƙa jawaban Imam Khomaini sun sanya ƙungiyoyin Muslunci jin cewa wajibi ne su ɗauki wani mataki, domin ƙasar Iran da juyin juya halin Muslunci da zai kuɓutar Iran da juyin juya hali daga halin rikice-rikice da kuma masu yunƙurin raba haɗin kan ƙasa.[12]
Mayar da ofishin jakadancin Amurka zuwa cibiyar leƙen asiri[13] Hulɗa da ƙungiyoyin masu adawa da juyin juya halin Muslunci da kuma taimaka musu, da kare masu neman kifar da gwamnati da kuma ƴanta'adda,[14] ƙoƙarin ofishin jakadancin Amurka na jawo hankalin shugabannin gwamnatin Iran,[15] Rattaba hannu kan ƙudurin doka a majalisar dattijai ta Amurka kan ƙalubalantar zartar da hukunce-hukunce kisa da aka yi a farkon juyin juya hali a Iran,[16] goyan bayan saƙon Imam Khomaini a ranar 29 Oktoba 1979m, da nuna rashin amincewa da yarjejeniyar mulkin mallaka tsakanin Iran da Amurka[17] da kuma ramuwa kan juyin mulki na Agusta 1953m da aka yi a Iran[18] suna daga cikin dalilai da aka ambata na mamaye ofishin jakadancin Amurka a Tehran.
Bayanin Abin da Ya Faru

A ranar 4 Nuwamba 1979m, wasu jama'a daga ɗaliban jami'o'in Tehran sun shirya gangami a titin Ayatullahi Ɗaliƙani, inda suka yi jerin gwano zuwa jami'ar Tehran, sa'ad da suka isa gaban ofishin jakadancin Amurka, sai wasu daga cikinsu suka kwance sarƙar da aka kulle ƙofar shiga ofishin, wasu kuma suka haura katangar ginin suka kutsa cikin ginin[19] Bayan ɗauki ba daɗi na tsawon awanni uku a farfajiyar ofishin jakadancin Amurka tare da jami'an tsaron Amurka ɗauke da bindigu da kuma fesa gas mai sanya hawaye kan waɗanda suka kutso cikin wannan gini[20]
Daga ƙarshe dai waɗannan ɗalibai sun sanar da cewa sun samu nasarar karɓe iko da mamaye wannan wuri.[21]] Kafin samun nasarar mamaye wannan wuri, ma'aikatan Amurka sun lalata muhimman takardu da shaidu.[22] A Lokacin faruwar wannan lamari, an cafke Amurkawa 72 a matsayin garkuwa, mutane uku da suka je ma'aikatar harkokin waje domin tattaunawa su ma an cafke su.[23] Waɗannan ɗalibai sun kira kansu da sunan ɗaliban jami'a da suke bin hanyar Imam Khomaini, sun kuma bayyana borensu da nuna rashin amincewa kan siyasoshin Amurka tare kuma da goyan bayan matakan Imam Khomaini.[24]
Bayan mamayewa, da farko ofishin jakadancin ya kasance ƙarƙashin ikon dakarun kare juyin juya halin Muslunci, daga baya sai aka miƙa shi ga gidauniyar kur'ani da Itra. A yanzu wannan wuri yana hannun cibiyar al'adu ta ɗalibai 4 Nuwamba..[25]
Riwayar Ibrahim Asgar Zadeh game da ɗalibai mabiya hanyar Imam dangane da tattaunawa ta talafon ta Musawi Khu'iniha tare da Sayyid Ahmad Khomaini da tambaya game da ra'ayin Imam Khomaini game da mamaye ofishin jkadancin Amurka a ranar 4 Nuwamba 1979m, da ɗalibai da ƙungiyoyin Muslunci na jami'o'i: sai Sayyida Ahmad ya je ya tambayi ra'ayin Imam ya dawo ya ce: Imam ya ce: Yara sun yi daidai ka da su saki wannan wuri da suka kame
Martanoni
Murabus ɗin Daular Wucin Gadi Bayan mamaye ofishin jakadanci, gungun shuwagabannin daular wucin gadi sun yi murabus tare da miƙa gwamnati hannun Mahadi Bazargan a 5 Nuwamba[27] a wani naƙalin kuma 6 Nuwamba 1979m,[28] majalisar shura ta juyin juya hali ta ɗauki alhakin gudanarwar ƙasa a wannan lokaci, a mataki na farko-farko da suka ɗauka sun katse fitar da man fetur zuwa Amurka.[29]
Yanke Hulɗoɗin Diflomasiyya Tsakanin Iran Da Amurka
Amurka ita ma a ɓangarenta ta cafke ɗaliban jami'a Iraniyawa guda 150[30] da korar Iraniyawa dubu casa'in da suke zaune a Amurka.[31]Bayan nan kuma ta toshe kuɗaɗen Iran da suke ajiye a bankuna na duniya[32]> a ta katse hulɗar Diflomasiyya da Iran.[33] Amurka ta kai ƙarar Iran a gaban kotun Duniya ta Lahai, da kuma kwamitin tsaro na majalisar ɗinkin Duniya kai hatta ƙungiyar taron ƙasashen Musulmi..[34]
Fatali Da Buƙatar Amurka Da Imam Khomaini Ya Yi
Bayan mamaye ofishin jakadancin Amurka da ɗaliban jami'ai suka yi, Imam Khomaini ya kira Amurka da babbar shaiɗaniya kuma ofishin jadakadancinta da sheƙar leƙen asiri.[35] Haka ƙusoshin gwamnatin Amurka guda biyu da suka zo Iran domin tattaunawa, Imam Khomaini bai karɓe su ba.[36]
Har ila yau, manya-manyan jami'ai misalin Kurt Waldheim, babban sakataren majalisar ɗinkin duniya na lokacin, sun yi ta zuwa Tehran[37] haka zalika Paparoma na biyu shugaban kiristocin mabiya ɗariƙar katolika na Duniya ya shiga Tsakani domin ganin an saki Amurkawa da ake garkuwa da su, sai dai kuma Imam Khomaini ya yi watsi da buƙatar ganawa da shi da babban sakataren majalisar ɗinkin duniya ya yi, haka zalika buƙatar Paparoma ta neman sakin Amurkawa ba tare da ƙaidi ko sharaɗi ba..[38]
A watan Afrilu 1980m, Amurka a ƙoƙarinta na kwato Amurkawa da aka yi garkuwa da su a Tehran, ta shirya wani hari na soja ta hanyar sauke sojojinta a saharar ɗabas , sai dai kuma shi ma wannan yunƙuri na ta bai kai ga nasara ba.[39]
Sakin Amurkawa Da Aka Yi Garkuwa Da Su
Bayan kwanaki 444, shuwagabannin gwamnatin wucin gadi tare da izinin Imam Khomaini kuma bayan amincewar majalisar shura ta Muslunci, tare kuma da shiga tsakanin daular Aljeriya tsakanin Amurka da Iran, tare da yarjejeniya da aka cimma, Iran ta saki Amurkawa da take garkuwa da su, cikin yarjejeniya da aka cimma, Iran ta bayyanar da buƙatu guda biyar ciki kuwa har da dawo mata da Sarki Shah ƙasar Iran, sai dai cewa bayan mutuwarsa wannan buƙata ta kau, na biyu a dawo mata da dukkanin dukiyar Iran, na uku a soke baki ɗayan ƙararrakin da Amurka ta kai kan Iran, na huɗu a tabbatar mata da rashin tsoma bakin Amurka cikin harkokin siyasa da soja na Iran, na biyar dawo da kuɗaɗen Iran da Sarki Shah ya sace ya kai Amurka.[40]
Jawabin Imam Khomaini washegarin mamaye ofishin jakadancin Amurka, ranar 17 Nuwamba 1979m: Cibiyar makirci da leƙen asiri da ake kira ofishin Jakadancin Amurka' da mutanen da ke ciki suna ƙoƙarin yin makirci kan ƙungiyarmu ta addini, ba su da wani girmamawa na siyasa a duniya... Al'ummar Iran sun tashi tsaye don hana waɗannan gidajen leƙen asiri ci gaba da aikata ayyukan banƙyama a Iran
[41]Duba: Khumaini, Sahifeh Imam Khumaini, 2010, juzu'i. 11, shafi na. 54.
Taƙaitaccen Nazari
An rubuta adadin litattafai game da batun mamaye ofishin jakadancin Amurka, daga jumlarsu akwai:
- Inƙilabe Dubom, na Ahmad Rida Shah Ali, cikin fasalai huɗu da ya ƙunshi bayani game da tarihin juyin juya halin Muslunci a Iran, dalilai kan mamaye ofishin jakadanci da taƙaitaccen tarihinsa da bincike kan kufaifayi da saƙonninsa a shekarar 1979m, cibiyar markaz asnad Inƙilabe Islami ta buga wannan littafi..[42]
- Rawabiɗ Iran Wa Amrika Az Firuzi Inƙilabe Islami Ta Taskhir laneh Jasusi, na Hassan Khodawardi, markaz asnad Inƙilabe Islami ta buga wannan littafi cikin shafi 260, wannan littafi ya ƙunshi bayan ikan halayen daular lokacin, ayyukan ofishin jakadancin Amurka a Tehran, da kuma yadda ɗalibai mabiya hanyar Imam Khomaini suka mamaye wannan wuri.[43]
- Mururi Bra Iƙdame Inƙilabi Juryane Daneshjuyi Dar Taskhir Lane Jasusi, na Wahid Husaini Zade da Ali Jafari Harastan, wannan littafi yana bayani game da sasanni daban-daban na wannan lamari, dalilin faruwa da kuma kufaifayin na cikin gida da na majalisar ɗinkin duniya, ƙungiyar ɗaliban jami'ar Imam Sadiƙ (A.S) suka buga wannan littafi a shekarar 1980m, cikin shafi 126..[44]
Bayanin kula
- ↑ Hashempour Yazdanparast, Taskhir Laneh Jasusi Amurka; Ilal Wa Zamineha shafi. 413.
- ↑ روحانی مقدم، «بازخوانی ۶ روایت کمتر شنیده شده از تسخیر لانه جاسوسی»،Yanar Gizo na Kamfanin Dillancin Labarai na Shabestan.
- ↑ Shah Ali, "Inqilabe Dubom Barsi Waqieh Taskhir Laneh Jasusi, shafi na 72
- ↑ «چرا حضرت امام خمینی(ره) قاطعانه از تسخیر لانه جاسوسی آمریکا حمایت کردند؟»، Gidan yanar gizon Cibiyar Takardun Juyin Juya Halin Musulunci.
- ↑ Shah Ali, "Inqilabe Dubom Barsi Waqieh Taskhir Laneh Jasusi, shafi na 76
- ↑ «بیانات در دیدار دانشآموزان و دانشجویان»،Yanar Gizo na ofishin kiyayewa da buga ayyukan Ayatollah Khamenei.
- ↑ Shiroodi, Taskhir Laneh Jasusi Amrika: Ilal Wa Payamadha, shafi 127-128.
- ↑ برای نمونه نگاه کنید به: «حضور معنادار مردم ایران در راهپیمایی ۱۳ آبان/ خط و نشان راهپیمایان برای "آمریکا و اغتشاشگران" + فیلم»، Yanar Gizo na Kamfanin Dillancin Labarai na Tasnim.
- ↑ Duba: Khumaini, Sahifeh Imam Khumaini, 2010, juzu'i. 10, shafi na 493.
- ↑ امینآبادی، «اسناد لانه جاسوسی فتنهگران را رسوا میکند: بیپرده با تاریخ/ شهریور و مهر ۱۳۵۸»، ص۶۳؛ «به مناسبت بزرگداشت سالروز اشغال لانه جاسوسی (تحلیلی کوتاه بر وقایع سیزدهم آبان ماه)»، در مجله تربیت، ص۲۰؛ جمعی از محققین، «اشغال لانه جاسوسی امریکا زمینهها و پیامدها»، Portal IMam Khomaini.
- ↑ "A mataki tare da babban nasara; 13 ga Nuwamba - kama gidan leken asirin Amurka", a cikin Mujallar Pasdar Islam, p. 11; Hashempour Yazdanparast, Taskhir Laneh Jasusi, Amrika; Ilal wa Zamineha", shafi. 416; Shiroodi, Taskhir Laneh Jasusi, Amrika: dalilai, tIlal wa Payamadha", shafi 125-127
- ↑ Shah Ali, Inqilabe Dubom Barsi Waqieh Taskhir Laneh Jausi: shafi na 72.
- ↑ Shiroodi, askhir Laneh Jasusi, Amrika: dalilai, tIlal wa Payamadha", shafi 123
- ↑ Samadifard, Majaraye Lanaeh Jasusi Namunehaye Ashkar Doshmani Istikbar. shafi na 92; Fawzi Tuyserkani, Jamhuri Islami Iran Wa Janbeshaye Islami, 1400, shafi. 169; Nawazani, Bahaye Shararat: Zamineaha Wa Payamadha Eshkqale Sifarate Amrika Dar Tehran,shafi na 30-31.
- ↑ Fawzi Tuyserkani, Jamhuri Islami Iran Wa Janbesh'haye Islamgera, 1400, shafi. 169; Nawazani, "Bahaye Shararat: Zamineha Wa Payamadha Eshqale Sefarat Amrika Dar Tehran," shafi. 29; Shiroudi, Taskhir Laneh Jasusi Amrika: Ilal Wa Payamadha, shafi. 124.
- ↑ Shiroudi, Taskhir Laneh Jasusi Amrika: Ilal Wa Payamadha, shafi 125. Nawazani, "Bahaye Shararat: Zamineha Wa Payamadha Eshqale Sefarat Amrika Dar Tehran," shafi. 31
- ↑ "A mataki tare da babban nasara; 13 ga Nuwamba - Taskhir Laneh Jasusi Amrika", a cikin Mujallar Pasdar-e-Islam, shafi. 11; Shiroodi, "Taskhir Laneh Jasusi Amrika: Ilal Wa Payamadha", p. 125; Shah-Ali, " Tasir Waqieh Taskhir Laneh Jasusi Amrika akan Bar Juryane Siyasi Dakhili", shafi. 146
- ↑ Nawazani, "Bahaye Shararat: Zamineha Wa Payamadha Eshqale Sefarat Amrika Dar Tehran," shafi. 33
- ↑ Nawazani, "Bahaye Shararat: Zamineha Wa Payamadha Eshqale Sefarat Amrika Dar Tehran," shafi. 33
- ↑ Shiroodi, Taskhir Laneh Jasusi, Amrika: dalilai, tIlal wa Payamadha", shafi 125-128
- ↑ Nawazani, "Bahaye Shararat: Zamineha Wa Payamadha Eshqale Sefarat Amrika Dar Tehran," shafi. 33
- ↑ Heydari, Taskhir Laneh Jasusi Amrika Wa Safre Komisiyone Tahqiq Sazimane Melal Beh Iran," shafi na 352.
- ↑ Shiroudi, Morteza, Tahlil Jaieh Shenakti Az Janbashe Daneshjuyi Iran," shafi. 158; Shiroudi, " Taskhir Laneh Jasusi Amrika: Ilal, Rawande Wa Payamadha, shafi na 129
- ↑ Shiroudi, Morteza, Tahlil Jaieh Shenakti Az Janbashe Daneshjuyi Iran," shafi. 158; Shiroudi, " Taskhir Laneh Jasusi Amrika: Ilal, Rawande Wa Payamadha, shafi na 130
- ↑ «چرا آمریکا تختجمشید را برای سفارتخانه خود انتخاب کرد؟»،Yanar Gizo na Kamfanin Dillancin Labarai na Jamhuriyar Musulunci ta Iran (IRNA).
- ↑ Dubi: Beheshtipour, Hossein, Naqshe Imam Khomeini dar Mudiriyate Buhrane Girogangiri Dar Laneh Jasusi Amirka, a cikin Jarida na Nazarin Tarihi, No. 30, Fall 2010, shafi na 30. 17..
- ↑ Shah Ali, "Inqilabe Dubom Barsi Waqieh Taskhir Laneh Jasusi," shafi na 72; Shah Ali, "Tasir Waiqeh Taskhir Laneh Jasusi Amrika Bar Juryanehehaye Siyasi Dakhili Kishwar," shafi na 146-147.
- ↑ جمعی از محققین، «اشغال لانه جاسوسی امریکا زمینهها و پیامدها»،Portal Imam Khomaini
- ↑ Aminabadi, "Asnade Laneh Jasusi Fitnehgeran Ra Roswa Mi konad, bi farde ba trikh/Satumba da Oktoba 1979", shafi. 63
- ↑ "A mataki tare da babban nasara; 13 ga Nuwamba - Taskhir Laneh Jasusi Amrika," a cikin Mujallar Pasdar Islam, p. 11.
- ↑ جمعی از محققین، «اشغال لانه جاسوسی امریکا زمینهها و پیامدها»،Portal Imam Khomaini
- ↑ Aminabadi, "Asnade Laneh Jasusi Fitnehgeran Ra Roswa Mi konad, bi farde ba trikh/Satumba da Oktoba 1979", shafi. 63."A lokacin tunawa da ranar tunawa da mamayar 'yan leƙen asiri (wani taƙaitaccen nazarin abubuwan da suka faru na Nuwamba 13)," a cikin Mujallar Tarbiat, shafi. 20.
- ↑ Samadifard,Majaraye Laneh Jasusi Wa Namunehaye Ashkar Doshmani Istikbar, shafi. 92
- ↑ «اقدامات سیاسی آمریکا بعد از تسخیر سفارت آمریکا»، Gidan yanar gizon Cibiyar Takardun Juyin Juya Halin Musulunci.
- ↑ Shah Ali, "Tasir Waiqeh Taskhir Laneh Jasusi Amrika Bar Juryanehehaye Siyasi Dakhili Kishwar," shafi na 145
- ↑ "A mataki tare da babban nasara; 13 ga Nuwamba - Taskhir Laneh Jasusi Amrika," a cikin Mujallar Pasdar Islam, shafi 11.
- ↑ Wasu manazarta «اشغال لانه جاسوسی امریکا زمینهها و پیامدها»، Portal Imam Khomaini
- ↑ Wasu nmasana، «اشغال لانه جاسوسی امریکا زمینهها و پیامدها»،Portal Imam Khumaini; "A mataki tare da babban nasara; 13 ga Nuwamba - kame gidan leken asirin Amurka", a cikin Mujallar Pasdar Islam, p. 11.
- ↑ Wasu manzarta، «اشغال لانه جاسوسی امریکا زمینهها و پیامدها»، Portal Imam Khomaini.
- ↑ Shah Ali, "Inqilabe Dubom Barsi Waqieh Taskhir Laneh Jasusi," shafi na 76
- ↑ Dubi: Beheshtipour, Hossein, Naqshe Imam Khomeini dar Mudiriyate Buhrane Girogangiri Dar Laneh Jasusi Amirka, a cikin Jarida na Nazarin Tarihi, No. 30, Fall 2010, shafi na 30. 17..
- ↑ «معرفی کتابهایی با موضوع تسخیر لانه جاسوسی+عکس»، Labaran Masreq da gidan yanar gizon nazari.
- ↑ «چه کتابهایی درباره تسخیر لانه جاسوسی آمریکا بخوانیم؟»،Yanar Gizo na Kamfanin Dillancin Labarai na Iran (IBNA)..
- ↑ «معرفی کتابهایی با موضوع تسخیر لانه جاسوسی+عکس»، Labaran Masreq da gidan yanar gizon nazari.
Tsokaci
- ↑ Imperiyalism” kalma ce da ake amfani da ita a wasu lokuta don nuni da tasirin tattalin arziki da rashin adalci da ƙasashe ke yi wa wasu ƙasashe. A wasu lokuta kuma ana fassara ta da ma’anar sabon salon mulkin mallaka.Farrokhi, Meysam:Bincike na nazari kan al’amuran duniya da imperiyalismin al’adu da kafafen yaɗa labarai: Daidaitawa da kama-kama na al’adu,” a cikin mujallar Nazarin Kafafen Yaɗa Labarai, lamba ta 29, lokacin bazara na shekarar 1394 Hijira Shamsiyya (daidai da Summer 2015), shafi na 14.
Nassoshi
- Aminabadi, Sayyid Ruhollah, “Asnade Lāneh Jāsūsī fitinagearan ra Roswa mi konad / watan Shahrivar da Mehr na shekarar 1358,” a cikin mujallar Pasdar-e Islam, lamba ta 383, watan Aban da Azar na shekarar 1392 Hijira Shamsiyya.
- «اقدامات سیاسی آمریکا بعد از تسخیر سفارت آمریکا»، Shafin Cibiyar Takardun Juyin Juya Halin Musulunci, Ranar da aka wallafa labarin: 16 ga watan Aban, shekarar 1394 Hijira Shamsiyya (daidai da 7 Nuwamba 2015),
- Beheshtipour, Hossein, “Rawar da Imam Khomeini ya taka wajen sarrafa rikicin kama garkuwa a Lāneh Jāsūsī na Amurka,” a cikin mujallar Nazarin Tarihi (مطالعات تاریخی), lamba ta 30, lokacin bazara na shekarar 1389 Hijira Shamsiyya (daidai da Fall 2010 Miladiyya)
- A cikin tunawa da ranar mamayar Lāneh Jāsūsī: Ƙaramin nazari kan abubuwan da suka faru a ranar 13 ga watan Aban”, an wallafa shi a cikin mujallar Tarbiyat, lamba ta 4, a watan Aban na shekarar 1368 Hijira Shamsiyya (daidai da Nuwamba 1989).
- «بیانات در دیدار دانشآموزان و دانشجویان»، Yanar Gizo na ofishin kiyayewa da buga ayyukan Ayatollah Khamenei, ranar shiga: 1 ga Nuwamba, 2016, ranar ziyarar: 16 ga Yuni, 2023.
- Ƙungiyar masu bincike, «اشغال لانه جاسوسی امریکا زمینهها و پیامدها»، Portal Imam Khumaini, ranar shigowa: Nuwamba 1, 2017, ranar ziyarar: Yuli 17, 2023.
- «چرا آمریکا تختجمشید را برای سفارتخانه خود انتخاب کرد؟», Yanar Gizo na Kamfanin Dillancin Labarai na Jamhuriyar Musulunci ta Iran (IRNA), kwanan watan shiga: 4 ga Nuwamba, 2013, ranar ziyarar: Yuli 15, 2023.
- «چه کتابهایی درباره تسخیر لانه جاسوسی آمریکا بخوانیم؟»،Gidan yanar gizo na Kamfanin Dillancin Labarai na Iran (IBNA), kwanan ranar shigarwa: Nuwamba 4, 2019, kwanan wata ziyarar: Yuli 14, 2023.
- «حضور معنادار مردم ایران در راهپیمایی ۱۳ آبان/ خط و نشان راهپیمایان برای "آمریکا و اغتشاشگران" + فیلم»،Yanar Gizo na Kamfanin Dillancin Labarai na Tasnim, kwanan wata: Nuwamba 1, 1401, kwanan wata ziyara: Yuli 1, 1402.
- Heydari, Asghar,Taskhir Laneh Jasusi Amrika Wa Safre Komisiyone Tahqiq Sazimane Melal Beh Iran," a cikin Mujallar Pazdah Khordad, No. 18, Winter 2008.
- «چرا حضرت امام خمینی(ره) قاطعانه از تسخیر لانه جاسوسی آمریکا حمایت کردند؟»،Gidan yanar gizon Cibiyar Takardun Juyin Juya Halin Musulunci, kwanan watan shiga: Nuwamba 1, 1401, kwanan wata ziyara: Yuni 10 ۱۴۰۲ش.
- Rouhani Moghadam, Zeinab, «بازخوانی ۶ روایت کمتر شنیده شده از تسخیر لانه جاسوسی»،Gidan yanar gizon Kamfanin Dillancin Labarai na Shabestan, kwanan watan aikawa: Nuwamba 1, 1401, kwanan wata ziyara: Yuni 16, 1402.
- «معرفی کتابهایی با موضوع تسخیر لانه جاسوسی+عکس»،Yanar Gizo na Analytical News-Mashreq, Ranar Buga: Nuwamba 4, 2017, Ranar Ziyara: Yuli 14, 2023
- Nawazani, Bahram, Bahaye Shararat: Zamineha Wa Payamadha Eshqale Sefarat Amrika Dar Tehran, a cikin Mujallar Zamaneh, No. 14, Nuwamba 2003.
- Hashempour Yazdanparast, Seyyed Mohammad, Taskhir Laneh Jasusi Amrika; Ilala Wa Zamineha", a cikin Mujallar Khordad ta 15, No. 17, Fall 2008.
- Huntington, Samuel, Ambiratori Amrika Tenha yek Afsaneh Ast, wanda Mojtaba Amiri Vahid ya fassara, a cikin Mujallar Watsa Labarai na Siyasa da Tattalin Arziki, Na 211 da 212, Afrilu da Mayu 2005.
- "A Matakin da Babban Nasara; 13 ga Nuwamba - Taskhir Laneh Jasusi Amrika", a cikin Mujallar Pasdar-e-Islam, No. 107, Nuwamba 2000.