Babbar Shaiɗaniya (Amurka)

Daga wikishia
Zanen Barkwanci: Babbar Shaitaniya, zanen Kalos Latuf dan kasar birazil

Babbar Shaiɗaniya (Larabci: الشيطان الأكبر) siffa ce da Imam Khomaini ya danganta kan amurka a cikin laccarsa da ya yi bayan karɓe ikon ofishin jakadancin ƙasar amurka da ya kasance a babban birnin tehran ƙasar Iran.[1] cikin laccarsa da ya yi ya ciro wannan siffa ta babbar shaiɗaniya daga riwayar da take bayyana Iblis matsayin babban shaiɗani cikin shaiɗanu, wannan riwaya ta kasance bayan aiko Annabi (S.AW), sakamakon Iblis ya tattaro dukkanin shaiɗanu a wurinsa tare da yin bayanin game da wahalar da yake fuskanta cikin ɓatar da mutane.[2][Tsokaci 1] da wannan ne kuma kan asasin adabin Imam Khomaini lokacin juyin juya halin muslunci ya bayyana cewa haƙiƙa amurka babbar shaiɗaniya ta tattara ƙananan shaiɗanu na cikin gida da na waje tare da ita domin haifar da fitina da hayaniya.[3]

Ana cewa wannan siffantawa an ciro shi ne daga kur'ani ; saboda kur'ani yana ɗaukar shaiɗan matsayin kafiri,[4] maƙiyin mutum,[5] mutakabbiri,[6] mai kawo rabuwar kai,[7] ba abin yarda ba,[8] fasiƙi maɓarnaci,[9] yana da ƙungiyoyi[10] kuma yana ƙayatar da miyagun ayyuka.[11] a mahangar Imam Khomaini bakiɗayan waɗannan siffofi sun tattarui cikin siyasar da take mulkar ƙasar amurka.

Imam Khomaini a lokuta daban-daban ya yi amfani da kalmar “Babban Shaiɗani” abin nufi daga wannan jumla cikin batutuwa na akjlaƙ, kur'ani da aƙida shi ne Iblis ko zuciya mai umarni da miyagun ayyuka cikin bahasosin siyasa kan ƙasar amurka,[12] haka kuma cikin laccarsa da ya yi kan taimakon da ƙasashen musulmi suke yi wa haramtacciyar ƙasar sahayoniya ya siffanta gwamnatin sahayoniya da ƙamar shaiɗaniya.[13]

Kone Samfurin Shaitan tare da tutar kasar amurka lokacin jerin gwanon ranar 22 ga watan Bahman a babban birnin tehran na kasar Iran

Sayyid Ali Khamna'i Jagoran juyi juya halin bayan Imam Khomaini ya yi amfani da laƙabin mafi girman shaiɗan a wurare da daman gaske kan amurka.[14] a ra'ayinsa Iblis tare da cewa shi ne shugaban dukkanin shaiɗanu, sai dai cewa babu abin da yake iyawa in banda wasiwasi, ita ko amurka ba ta tsaya iya haka ba ita kam kacokam tana halakarwa tare kuma dai kai hare-hare da kuma haifar da fitintinu.[15] kamar dai yadda ake amfani da wannan siffa matsayin take a lokutan jerin gwanon adawa da mummunar siyasar amurka.[16]

Bayanin Kula

  1. Mousavi Khomeini, Sahifa Imam, 1378, juzu'i na 10, shafi na 489
  2. Mousavi Khomeini, Sahifa Imam, 1378, juzu'i na 10, shafi na 489
  3. Mousavi Khomeini, Sahifa Imam, 1378, juzu'i na 10, shafi na 489
  4. Rakabian, “Mabani Kur’ani Az didgahe Imam Khomeini a Amurka “Shaitan Bozorg,” shafi na 94.
  5. Rakabian, “Mabani Kur’ani Az didgahe Imam Khomeini a Amurka “Shaitan Bozorg,” shafi na 94-96
  6. Rakabian, “Mabani Kur’ani Az didgahe Imam Khomeini a Amurka “Shaitan Bozorg,” shafi na 96-98
  7. Rakabian, “Mabani Kur’ani Az didgahe Imam Khomeini a Amurka “Shaitan Bozorg,” shafi na 98.
  8. Rakabian, “Mabani Kur’ani Az didgahe Imam Khomeini a Amurka “Shaitan Bozorg,” shafi na 98-99.
  9. Rakabian, “Mabani Kur’ani Az didgahe Imam Khomeini a Amurka “Shaitan Bozorg,” shafi na 99-100.
  10. Rakabian, “Mabani Kur’ani Az didgahe Imam Khomeini a Amurka “Shaitan Bozorg,” shafi na 100.
  11. Rakabian, “Mabani Kur’ani Az didgahe Imam Khomeini a Amurka “Shaitan Bozorg,” shafi na 101.
  12. Faghi wa Rafi’i, “Wajeh“Shaidan” dar adabaiyat inkilabe islami wa kalame Imam Khumaini (RA), shafi na 62.
  13. Mousavi Khomeini, Sahifa Imam, 1378, juzu'i na 15, shafi na 265.
  14. «فیش‌های شیطان بزرگ»، سایت دفتر حفظ و نشر آثار آیت‌الله خامنه‌ای.
  15. «بیانات در دیدار اقشار مختلف مردم»، سایت دفتر حفظ و نشر آثار آیت‌الله خامنه‌ای.
  16. برای نمونه نگاه کنید: «خداحافظ ای داغ بر دل نشسته»، پایگاه خبری جماران؛ «طنین شعار "الله الله اکبر آمریکا شیطان الاکبر"در سراسر عراق»، پایگاه خبری انقلاب‌نیوز؛ ««التحریر» علیه امریکا»، روزنامه ایران.

Tsokaci

  1. ku duba: Majlisi, Biharul Al-anwar bugun shekara 1403 qamari, j 15 shafi na 258. Iblis tsinannen Allah sai ya yi ihu cikin Iblisai sai suka taru wurinsa.

Nassoshi

  • «بیانات در دیدار اقشار مختلف مردم»، سایت دفتر حفظ و نشر آثار آیت الله خامنه‌ای، تاریخ درج مطلب ۱۸ شهریور ۱۳۹۴ش، تاریخ بازدید ۳۱ اردیبهشت ۱۴۰۳ش.
  • ««التحریر» علیه امریکا»، روزنامه ایران، تاریخ درج مطلب ۱۵ دی ۱۳۹۹ش، تاریخ بازدید ۳۱ اردیبهشت ۱۴۰۳ش.
  • توانایی، محمد حسین و حسین رفیعی، «واژه «شیطان» در ادبیات انقلاب اسلامی و کلام امام خمینی (ره)»، مجله پژوهش‌های سیاسی، شماره ۱۵، زمستان ۱۳۹۴ش.
  • «خداحافظ ای داغ بر دل نشسته»، پایگاه خبری جماران؛ تاریخ درج مطلب ۱۶ دی ۱۳۹۸ش، تاریخ بازدید ۳۱ اردیبهشت ۱۴۰۳ش.
  • رکابیان، رشید، «مبانی قرآنی دیدگاه امام خمینی ره درباره آمریکا «شیطان بزرگ»»، مجله معرفت، شماره ۲۷۹، اسفند ۱۳۹۹ش.
  • «طنین شعار "الله الله اکبر آمریکا شیطان الاکبر"در سراسر عراق»، پایگاه خبری انقلاب نیوز؛ تاریخ درج مطلب ۱۱ دی ۱۳۹۸ش، تاریخ بازدید ۳۱ اردیبهشت ۱۴۰۳ش.
  • «فیش‌های شیطان بزرگ»، سایت دفتر حفظ و نشر آثار آیت الله خامنه‌ای، تاریخ بازدید ۳۱ اردیبهشت ۱۴۰۳ش.
  • موسوی خمینی، روح‌الله، صحیفه امام، تهران، موسسه تنظیم و نشر آثار امام خمینی(ره)، ۱۳۷۸ش.