Hafhaf Bin Munnad Rasibi

Daga wikishia

Hafhaf Bin Muhannad Rasibi (Larabci: هَفْهاف بن مُهَنَّد الراسِبي) wanda ya yi shahada a shekara ta 60 bayan hijira, ya kasance dan shi'ar Basra, kuma ɗaya daga cikin shahidan karbala, wanda ya yi shahada bayan Imam Husaini (A.S). Tarihi ya shaida halartarshi kasance cikin sahabban Imam Ali (A.S) a yaƙin Siffin, kuma da ya ji labarin tafiyar Imam Husaini (A.S) zuwa Iraki, sai ya tafi wurinshi. Amma ya isa Karbala a ranar ashura bayan shahadar Imam Husaini (A.S), kuma ya yaƙi rundunar Umar bin Sa'ad har ya yi shahada. Al-imam ƙani malamin Rijal na Shi'a (ya rasu a shekara ta 1351 bayan hijira) yana cewa Hafhaf bin Muhannad jarumin `yan Shi'a ne jajirtacce kuma mai imani kuma mabiyi ne na gaske ga Ahlul-bait (A.S).[1] Ya kasance ɗaya daga cikin sahabban Imam Ali (A.S) a yakin Siffin, inda Imam Ali (A.S) ya naɗa shi shugaban Basranawa daga kabilar Azdi.[2] kuma ana daukarshi ɗaya daga cikin sahabban Imam Hassan (A.S)[3] kalmar Hafhaf a zahiri tana nufin mutum marar ƙiba.[4]

An ruwaito daga Fudailu ɗan Zubairu Al-kufi (wanda ya rasu a karni na biyu bayan hijira), kuma Murshid Billah ɗaya daga cikin malaman mazhabar zaidiyya (a shekara ta 479 bayan hijira) da Hamid ɗan Ahmad Al- muhalli wanda yana cikin mawallafin sira na Zaidiya (a shekara ta 652 bayan hijira), cewa da Hafhaf ya ji labarin fitar Imam Husaini (A.S) zuwa Iraki, sai ya tafi wurinsa. Amma ya isa fagen fama ne bayan shahadar Imam Husaini (A.S). Sai ya shiga cikin rundunar Umar bin Sa'ad, sai ya zare takobinshi ya ce:"Ya ku sojojin da da aka tanada, ni ne Hafhaf bin Muhannad, ina neman iyalan Muhammadu (S.A.W) Sai aka shirya shi zuwa yaki da rundunar Umar bin Sa'ad, kuma ya kashe wasu daga cikinsu har ya yi shahada[5] a ci gaban wannan riwaya an naƙalto daga Imam Sajjad (A.S) a ranar ashura kan Hafhaf cewa, mutane ba su ga wani jarimi ba, kamar Hafhaf tun bayan aiko Annabi, bayan Ali ɗan Abi ɗalib (A.S).[6]

Ya zo a cikin (Encyclopedia) littafin Mausu'a na Imam Husaini (A.S) cewa, ba a ambaci sunan Hafhaf a cikin litattafan da suka gabata ba, face a cikin littafin Sunayen wadanda aka kashe tare da Husaini, na Fudail Bin Zubair Al-kufi.[7] Haka nan ba a ambaci sunan Hafhaf ba a cikin ziyarar shahidai da aka jingina ga Imam Zaman(A.F).[8] da ziyarar Rajabiyya ta Imam Husaini (A.S).[9]

Bayanin kula

  1. Al-Mamqani, Tankihul Makal, Najaf, juzu'i na 3, shafi na 304.
  2. Majmu'atu Min Kuttab, Thakhira al-Darayn, 1422 AH, juzu'i na 1, shafi na 457.
  3. Al-Mamaqani, Tanqih al-Maqal, juzu'i na 3, shafi na 304.
  4. Duba: Ibn Duraid, Al-Ishtiqāq, 1411H, shafi na 230.
  5. Al-Murshid Balleh, Al-Amali al-Khamisiyah, 1422 AH, juzu'i na 1, shafi na 227; Al-Molishi, al-Hadaiq al-Wardiyah, 1423 AH, juzu'i na 1, shafi na 212.
  6. Fazil bin Al-Zubayr, Tasmiyyah Man Qatal al-Hussein, 1406 AH, shafi 156; Al-Murshid Balleh, Al-Amali al-Khamisiyah, 1422 AH, juzu'i na 1, shafi na 227; Al-Molishi, al-Hadaiq al-Wardiyah, 1423 AH, juzu'i na 1, shafi na 212.
  7. Al-Mohammadi al-Alari Shahri,Danheshnameh Imam Hussein (A.S), 1387, juzu'i na 6, shafi na 435.
  8. Duba: Ibn Al-Moshhadi, Al-Mazar, 1419 Hijira, shafi na 487-495.
  9. Duba: Al-Majlisi, Bihar Al-Anwar, 1403 AH, Juzu'i na 101, shafi na 339-341.

Nassoshi

  • Ibn Duraid, Muhammad bin Hassan, Al-Ishtikaq, bugun: Abdul Salam Muhammad Haroun, Beirut, Dar Al-Jeel, 1411H.
  • Ibn Mashhadi, Muhammad, Al-Mazar, edited by: Jawad Al-Qayomi Al-Isfahani, Qum, Islamic Evil Foundation, 1419 AH.
  • Al-murshid Ilallah, Yahya bin Husain, 'Al-Amali Al-Khamisiya, ya inganta daga: Muhammad Hassan Ismail, Beirut, Dar Al-Kutub Al-Ilmiyyah, 1422H.
  • Majmu'atu Min Kuttab, Thakhirat al-Darayn', editan: Baqir Daryab al-Najafi, B.M., 1422H.
  • Fadil bin Zubair, Tasmiya Man Katala ma'a Al-Husaini, (A.S),, wanda Sayyid Muhammad Reza Al-Husseini Al ya inganta. -Jalali, Qum, 1406H.
  • Al-Mamaqani, Abdullah, Tankihuil Makal, Najaf, B.T.
  • Al-Majlisi, Muhammad Baqir, “Bihar Al-Anwar”, Al-Wafa Foundation, 1403H.
  • Al-Mahli, Hamid bin Ahmed, 'Al-hada'iku Wardiyya Fi Makibi A'immatil Zadiyya, edita: Murtada Al-Mahatwari, Sana'a, Laburaren Al-Badr, 1423H.
  • Al-Muhammadi Al-Rai Shehri, Muhammad, Danshanama Imam Husayn, (A.S)', Ayar Al-Qur'ani, Hadisi da Tarihi, 1387H.