Fatawar Haramcin Ƙirƙirar Makamin Ƙaredangi da Yin Amfani da shi
Fatawar haramcin ƙirƙirar makamin ƙare dangi da yin anfani da shi (Larabci: فتوى تحريم صناعة واستخدام الأسلحة النووية) fatawa ce ta fiƙihu ta Assayid Ayatullahi Ali Alkhamna'i ya fitar da ita a matsayin raddi kan ƙasar Isra'ila lokacin da ta yi iƙrarin na cewa Iran tana yunƙurin ƙirƙirar makamin ƙare dangi, Assayid Ali Alkhamna'i yana ganin cewa makamin ƙare dangi barazana ce ga dan adam kuma ya haramta.
Wasu daga cikin malamai sun kafa hujja da ayoyin kur'ani da hadisai kan haramcin mallakar makamin ƙare dangi, sabo da haramcin aikatya ta'addanci kan mutane, bisa abin da Abu ƙasim ali dusti ya faɗa, haƙiƙa malaman Shi'a sun yi fatawar haramta makamin ƙare dangi tin ƙarni goma da suka gabata.
wannan fatawa tana da tasiri mai ƙarfi a siyasance a cibiyioyin masu fashin baƙi na siyasa da na masu tunani a duniya, kuma ita wannan fatawa an rubutata a majalisar ɗankin duniya a matsayin wani ƙuduri abin dogara a hukumance. A cikin wani littafi na ha ɗin gwiwar marubuta mai suna "Fiƙhu Haste'i" da kuma littafi mai suna "Fatawa Annawawi min manzruil al-ƙanun ad-duwali" na jabir Saifani Zade.
Muhimmanci
Sayyid Ali Alkhamna'i jagoran jamhuriyar musulinci ta ƙasar Iran ya yi fatawar haramta ƙirƙira makamin ƙare dangi da kuma yin anfani da shi, wannan ya zo ne sakamakon raddi da ya yi wa kafar yaɗa labarai ta haramtacciyar ƙasar Isra'il, a lokacin da suka bayyana cewa Iran tana da aniyar ƙirƙirar makamin ƙare dangi،[1] wannan fatawa an karantata a taro da aka yi na ƙasa da ƙasa domin lalata makamin gare daangi da kuma hana yaɗuwar shi a shekara ta 2010 miladiya.[2]
Ali Akbar Salihi shugaban tashar makamashi na Iran a lokacin da yake bada amsar wata tambaya kan aniyar ƙasar Iran ta ƙirƙirar makamin ƙare dangi, ya ce abin da ya fi ga ƙasar Iran shi ne kulawa da bin fatawar haramcin anfani da shi..[3]
Tasiri
Fatawar haramta makamin ƙare dangi ta Sayyid Ali Alkhamna'i ta samu karɓuwa a duniya[4] kuma ta ya ɗu da tasiri a guraren da suke fashin baƙi irin na siyasa[5] bisa abin da kamfanin dillancin labarai ya tabbatar da cewa wannan wasiƙa ta Ayatullahi khamna'i an rubutata a ƙudirin hana ya ɗuwar makamin ƙare dangi kuma a cikinta akwai fatawar haramcin ƙirƙira makamin ƙare dangi da kuma yin anfani da shi, a matsayin wani dalili a hukumance na majalisar ɗinkin duniya.[6] kuma Jonasan Jara'if shugaban cibiyar tsaro ta duniya a ƙasar America, ya buƙaci da Sayyid Alkhamna'i ya yin da yake yi mishi tambayoyi cewa ya rubuta wasiƙa zuwa ga malaman addini domin su mara mishi baya kan haramcin anfani da makamin ƙare dangi ta fuskar kowanne dalili..[7]
A shekara ta 2013 ne mutum shida daga masu hango abin da zai faru da kwararrun masana doka na ƙasar Amurka suka haɗu da wasu daga cikin malaman shi'a domin tattauna ingancin fatawar Sayyid Ali khamna'i ta haramta yin makamin ƙare dangi da kuma haramcin anfani da shi, kuma sun isar da saƙon hana ƙirƙirar makamin ƙare dangi a fiƙihun shi'a da sakamakon ziyarar da suka kai ƙasar Iran ga gwamnatin ƙasar Amurka, domin shigar da su cikin tattaunar Iran da ƙasashan yammacin duniya kan makamin ƙare [8] a shekara ta 2021 gidan talbijin na BBC Farisi ya yaɗa wani fim mai ɗauke da take ko sunan Fatawar makamin ƙare dangi a wani shiri mai suna yiwar canji fatawar Ayatullahi Al-khamana'i[9] sai dai malamai sun kore yiwuwar canzawarta. sabo da rashin alaƙar wannan fatawa da wani lokacin na masamman ko wani guri daban.[10]
Tarihin Mas'alar
Makamin nukiliya shi ne wanda akafi sani da makaman kare dangi[11] A cewar Abu al-ƙasim alidust, a cikin shekarar 2014, malaman fikihu na Shi'a sun ba da fatawa da ke hana amfani da makamin ƙare dangi da kayan aikin da ke haddasa kisan kare dangi, da kashe halittu da lalata muhalli.[12] tun daga ranar 19 ga watan Fabrairun 2010 Ayatullah Khamna'i ya sha bayyana fatawa da ra'ayinshi na adawa da kera da kuma amfani da makaman nukiliya[13].[13]
Fatawar Da Ittifaƙin Maraji'ai
A ranar 17 ga watan Afrilu, 2010, Ali Akbar wilayati ya karanta fatawar Ayatullah khamna'i a cikin wasiƙarsa ta hukuma zuwa taron farko na duniya ga ƙasashe masu ƙawance domin lalata makamin ƙare dangi[14] ga abin da yake cewa; Baya ga makaman nukiliya, mun yi imanin cewa sauran nau'o'in makaman kare dangi, irin su makamai masu guba da ƙananan makamai, suna haifar da mummunar barazana ga bil'adama, kuma muna ganin haramun ne yin amfani da waɗannan makamai .[15]
Fatawowin wasu Maraji'u na Taƙalidi, kamar Makarim Shirazi, Nuri Al-Hamdani, Jafar Subhani, da Jawadi Amoli, sun tabbatar da fatawar Ayatullah Khamna'i[16] Abu Al-ƙasim Alidust, darektan taron ƙasa kan harkokin shari'a na nukiliya, da Ahmed Muballigi, ɗaya daga cikin wakilan majalisar kwararru ta jagoranci, sun yi imanin cewa wannann fatawa hukunci ne na Ubangiji madawwami wanda ba za a iya canza taba.[17]
Dalilan Fatawar Haramta Makamin Ƙare dangi
An ambaci dalilai daban-daban shari'a da suka haramta kira da amfani da makaman nukiliya, kuma a akidar Ayatullah Khamna'i, dalilin hana kerawa da amfani da makaman kare dangi shi ne cin karon amfani da makaman kare dangi tare da manufofin Musulunci. kamar yadda amfani da irin waxannan makaman yana lalata noma da tsirrai, kuma wannann shi ne abin da ya zo a cikin aya ta 205 daga cikin Suratul Baƙarah; Kuma idan ya juya sai ya yi gaggawa don yaɗa fasadi a cikinta. Kuma Ya halakar da shuka da ƴaƴan dabbobi. Kuma Allah ba ya son ɓarna.)[18] Dangane da hakan, Abu Al-ƙasim Alidust ya bayyana cewa, gyara yanayin da mutane ke ciki da alakarsu da Allah da juna, yana daga cikin manufofin shari'a, kuma ba a taba samun gyara tare da fasadi da amfani da makaman kare dangi.[19]
Ayoyin Kur'ani
Ahmad Muballigi Malamin fiƙihu a shi'a ya yi imani cewa abubuwan da suka yi sanadiyyar wannan fatawa suna da yawa, da cikin su akwai ginshiƙai guda uku a kur'ani ،[20] ga su kamar haka;
- Dogaro bisa ƙa'idatul Wizir, "ولا تَزِرُ وازرةٌ وزرَ أُخرى" Kuma wani rai ba ya ɗaukar nauyin wani. wannan aya tana hana hukunta wani da laifin wani, wato yayin da ake so a hukunta masu laifi ba zai yiwu a haɗa da marasa laifi ba.
kuma anfani da makamin nukiliya yana kai ga kisan kiyashi da kashe ƴan ba ruwana, kai anfani da shi yana kai ga cutar da mutaanan da za su zo a nan gaba.
- Bisa dokar hana fasadi a doran ƙasa aya ta 205 a cikin Baƙara, Allah ya hana aikata duk wani aiki wanda zai kai ga fasadi a doran ƙasa da kuma lalata shuka da ƴaƴan dabbobi.
- ƙa'idatul Ismi, «إثمُهُما اَكْبَرُ مِنْ نَفْعِهِما» daga wannan ana fahimtar cewa, duk wani abu da sharrinshi da fasadinshi idan yafi yawa ya rinjayi anfanin shi zai zamo haramun, to a bayyane yake cewa fasadin makamin nukiliya yafi anfanin shi da ake sa rai.
Haka kuma Nasir ƙurbani niya ya kafa hujja da cewa aya ta 190 da ta 205 a cikin Suratul Baƙarah da aya ta 8 da 32 a cikin Suratul Ma'idah sun ƙunshi haramcin makaman kare dangi.[21]
Dalili Na Riwaya
A cikin binciken fikihun haramta makaman kare dangi, an kawo wasu ruwayoyi, kamar ruwayoyin da suka haramta sanya guba a cikin ruwan makiya.[22] waɗanda Abu al-ƙasim Alidust da Muhammad Jawad Fadil lankarani suka kawo a matsayin hujja, da ruwayoyin haramta cin zarafi ga wasu kamar, yara, mata, dattijai, ƴantattu, da dabbobi).[23]
Bayanin kula
- ↑ «تسجيل رسالة قائد الثورة الإسلامية كوثيقة عند الأمم المتحدة»، دفتر حفظ ونشر آثار آية الله الخامنئي.
- ↑ «التعريف بالمؤتمر الدولي لنزع السلاح وعدم انتشار الأسلحة النووية»، موقع همشهري أونلاين.
- ↑ «صالحي: وحده قائد الثورة يستطيع أن يعطي رأي صائب حول صناعة الأسلحة النووية»، وكالة أخبار فارس.
- ↑ «مراجعة لفتوى تحريم الأسلحة النووية الصادرة عن قائد الثورة الإسلامية»، موقع بصيرة.
- ↑ «تسجيل رسالة السيد الخامنئي كوثيقة عند الأمم المتحدة»، جريدة كيهان.
- ↑ «زعماء دينيون ينضمون إلى آية الله خامنئي»، مكتب حفظ ونشر آثار آية الله الخامنئي.
- ↑ «زعماء دينيون ينضمون إلى آية الله خامنئي»، مكتب حفظ ونشر آثار آية الله الخامنئي.
- ↑ «ذهبنا إلى قم للتحقيق في فتوى النووي لآية الله الخامنئي/أرسلنا تقرير رحلتنا إلى البيت الأبيض/من المؤكد دراسة هذا التقرير من قبل الحكومة الأمريكية»، موقع المشرق.
- ↑ «فتوى نووية - بین السطور»، موقع BBC News الفارسي.
- ↑ «هل يمكن تغير فتوى تحريم السلاح النووي؟»، وكالة أخبار فارس.
- ↑ «صناعة واستخدام أسلحة الدمار الشامل من منظور الفقه الإسلامي»، موقع المرکز الأئمة الأطهار الفقهي.
- ↑ «بحث في تحريم أسلحة الجمار الشامل في تاريخ التشيع»، موقع آية الله عليدوست.
- ↑ برای نمونه نگاه کنید به؛ «بیانات خلال لقاء مع العالمين على المدمرة جماران»، مكتب حفظ ونشر آثار آية الله الخامنئي؛ «بیانات قائد الثورة الإسلامية خلال لقاء مسؤلين وعاملين في الحكومة»، مكتب حفظ ونشر آثار آية الله الخامنئي؛ «الفتوى التي وصلت إلى الأمم المتحدة بعد 10 سنوات»، وكالة أخبار مهر.
- ↑ «رسالة إلى المؤتمر العالمي لنزع السلاح النووي ومنه انتشاره»، مكتب حفظ ونشر آثار آية الله الخامنئي.
- ↑ «رسالة إلى المؤتمر العالمي لنزع السلاح النووي ومنع انتشاره»، مكتب حفظ ونشر آثار آية الله الخامنئي.
- ↑ «تحریم أسلحة الدمار الشامل في تاريخ التشيع»، وكالة أخبار ايسنا.
- ↑ «لوازم فتوى قائد الثورة حول تحريم السلاح النووي»، موقع تسنيم؛ «هل يمكن تغير الحكم بحرمة السلاح النووي؟»، وكالة أخبار فارس.
- ↑ «بيانات خلال لقاء مع العاملين في بناء المدمرة جماران»، مكتب حفظ ونشر آثار آية الله الخامنئي.
- ↑ Rukunin marubuta, “Fiƙh Haste'i” (Fiƙh al-Nawawi), 1397 AH, shafi 113.
- ↑ «الأدلة الفقهية لتحريم السلاح النووي»، مكتب حفظ ونشر آثار آية الله الخامنئي.
- ↑ Majmu muallifin, “Fiƙhu Haste'i” (Fiƙh al-Nawawi), 1397 AH, shafi na 182-184.
- ↑ Majmu muallifin, “Fiƙhu Haste'i” (Fiƙh al-Nawawi), 1397 AH, shafi na 87-112
- ↑ Majmu muallifin, “Fiƙhu Haste'i” (Fiƙh al-Nawawi), 1397 AH, shafi na 85-87.185. 231.343
Nassoshi
- «التعريف بالمؤتمر الدولي لنزع السلاح وعدم انتشار الأسلحة النووية»، موقع همشهري أونلاين، تاريخ النشر: 3 اردبهشت 1389ش، تاريخ المشاهدة: 27 فبراير 2024م.
- «هل يمكن تغيير فتوى حرمة الأسلحة النووية»، وكالة أخبار فارس، تاريخ النشر: 16 بهمن 1400ش، تاريخ المشاهدة: 27 فبراير 2024م.
- «مراجعة لفتوى تحريم الأسلحة النووية الصادرة عن قائد الثورة الإسلامية»، موقع بصيرة، تاريخ النشر: 25 فرفردين 1399ش، تاريخ المشاهدة: 27 فبراير 2024م.
- «تحقيق في تحريم أسلحة الدمار الشامل في تاريخ الشيعة»، موقع آية الله عليدوست، تاريخ النشر: 9 مهر 1393ش، تاريخ المشاهدة: 27 فبراير 2024م.
- «ذهبنا إلى قم للتحقيق في فتوى النووي لآية الله الخامنئي/أرسلنا تقرير رحلتنا إلى البيت الأبيض/من المؤكد دراسة هذا التقرير من قبل الحكومة الأمريكية»، موقع المشرق، تاريخ النشر: 18 آبان 1393ش، تاريخ المشاهدة: 27 فبراير 2024م.
- «بيانات خلال لقاء مع العاملين في بناء المدمرة جماران »، مكتب حفظ ونشر آثار آية الله الخامنئي، تاريخ النشر: 30 بهمن 1388ش، تاريخ المشاهدة: 27 فبراير 2024م.
- «بيانات قائد الثورة الإسلامية خلال لقاء مسؤولين في الحكومة»، مكتب حفظ ونشر آثار آية الله الخامنئي، تاريخ النشر: 11 آبان 1382ش، تاريخ المشاهدة: 27 فبراير 2024م.
- «رسالة إلى المؤتمر الدولي الأول لنزع السلاح النووي»، مكتب حفظ ونشر آثار آية الله الخامنئي، تاريخ النشر: 28 فرفردين 1389ش، تاريخ المشاهدة: 27 فبراير 2024م.
- «تسجيل رسالة قائد الثورة الإسلامية إلى مؤتمر طهران كوثيقة عند الأمم المتحدة »، جريدة كيهان، تاريخ النشر: 4 اردبهشت 1389ش، تاريخ المشاهدة:27 فبراير 2024م.
- «تحريم أسلحة الدمار الشامل في تاريخ الشيعة»، وكالة أخبار ايسنا، تاريخ النشر: 27 خرداد 1393ش، تاريخ المشاهدة: 27 فبراير 2024م.
- «صنع واستخدام أسلحة الدمار الشامل من منظور الفقه الإسلامي»، موقع مركز الأئمة الأطهار الفقهي، تاريخ المشاهدة: 27 فبراير 2024م.
- «تسجيل رسالة قائد الثورة الإسلامية كوثيقة عند الأمم المتحدة»، مكتب حفظ ونشر آثار آية الله الخامنئي، تاريخ النشر: 28 فرفردين 1389ش، تاريخ المشاهدة: 27 فبراير 2024م.
- مجموعة مؤلفين، فقه هستهأي "فقه النووي"، تحقيق أبو القاسم عليدوست، طهران، انديشه إسلامي، الطبعة الأولى، 1397ش.
- «الأدلة الفقهية على تحريم السلاح النووي»، مكتب حفظ ونشر آثار آية الله الخامنئي، تاريخ النشر: 4 اردبهشت 1389ش، تاريخ المشاهدة: 26 دي 1402ش.
- «الزعماء الدينيون ينضمون إلى آية الله الخامنئي»، مكتب حفظ ونشر آثار آية الله الخامنئي، تاريخ النشر: 1 اردبهشت 1389ش، تاريخ المشاهدة: 26 دي 1402ش.
- «صالحی: تنها رهبر انقلاب میتوانند درباره ساخت سلاح هستهای نظر صائب بدهند»، خبرگزاری فارس، تاریخ انتشار: 24 مهر 1401ش، تاریخ بازدید: 30 دی 1402ش.
- «عرض كتاب "فقه هستهاي" (فقه النووي) في معرض الكتاب الثاني والثلاثين)»، موقع الفكر الإسلامي، تاریخ انتشار: 8 اردیبهشت 1398ش، تاریخ بازدید: 1 بهمن 1402ش.
- «الفتوى التي وصلت إلى الأمم المتحدة بعد 10 سنوات»، وكالة أخبار مهر، تاريخ النشر: 3 مهر 1392ش، تاريخ المشاهدة: 27 دي 1402ش.
- «انتشار كتاب الفتوى النووية لقائد الثورة من منظور القانون الدولي في أمريكا»، وكالة أخبار فارس، تاریخ النشر: 25 بهمن 1395ش، تاريخ المشاهدة: 27 دي 1402ش.
- «لوازم فتوى السيد الخامنئي حول حرمة السلاح النووي»، موقع تسنيم، تاريخ النشر: 30 بهمن 1392ش، تاريخ المشاهدة: 26 دي 1402ش.
- محمد بور، محمد، «فتوى بمثابة مصدر حقوق أممي»، في مجلة "شهر قانون"، العدد 13، ربيع 1394ش.
- «فتوى نووية - بین السطور»، موقع BBC News الفارسي، تاریخ النشر: 9 بهمن 1400ش، تاريخ المشاهدة: 15 بهمن 1402ش.