Daƙiƙa:Tattaunawar Imam Husaini Da Umar Bin Sa'ad
Tattaunawar Imam Husaini (A.S) da Umar Bin Sa'ad kafin aukuwar waƙi'ar Karbala an ruwaito ta a wasu madogarai, kamar Maƙtalul Husaini na Abu Mikhnaf. Duk da cewa an amince da samuwar irin waɗannan tattaunawa gaba ɗaya, akwai saɓani game da ainihin lokacin da aka yi su, adadinsu da kuma abubuwan da aka tattauna a cikinsu.
A wasu rahotanni an bayyana cewa shawarar yin ganawa ta fito ne daga Imam Husaini (A.S), sannan aka isar da ita ga Umar Bin Sa'ad. Daga nan ɓangarorin biyu suka taru tare da wasu daga cikin mabiyansu a wani wuri da yake tsakanin rundunonin biyu domin tattaunawa. Sai dai a ruwayoyi daban-daban akwai bambanci game da waɗanda suka halarta da kuma cikakkun bayanan ganawar.
Haka kuma an ruwaito cewa wasu daga cikin sojojin Umar Bin Sa'ad, bayan sun fahimci matsayin Imam Husaini (A.S), sun rabu da rundunarsa suka koma wurin Imam Husaini (A.S). Sai dai ingancin wannan iƙirari yana da shakku a wajen wasu masu bincike.
Game da lokacin da aka gudanar da wannan ganawa, ruwayoyi sun bambanta. Wasu bincike sun nuna cewa an yi su ne kafin isowar Imam Husaini (A.S) Karbala, yayin da wasu rahotanni suka bayyana cewa an yi su ne lokacin da rundunar Kufa ta fuskanci Imam Husaini (A.S).
Abu Mikhnaf ya ambaci cewa an yi waɗannan tattaunawa sau uku ko huɗu a wurare da lokuta daban-daban. Wasu marubutan Shi'a kuma sun bayyana wani lokaci na musamman, kamar tsakanin ranakun huɗu zuwa shida ga watan Muharram.
A cikin abubuwan da suka shafi abin da aka tattauna, akwai babban saɓani tsakanin ruwayoyin masu bincike. Wasu, kamar Mahadi Pishwayi, bisa dogaro da ruwayar Uƙbatu Bin Sam'an, sun ƙaryata iƙirarin cewa Imam Husaini (A.S) ya ba da shawarar yin mubaya'a ga Yazid. A ganinsu, wannan wata karkatar da tarihi ce domin ba da halacci ga mulkin Yazid. Sun ce abin da Imam Husaini (A.S) yake so shi ne kawai fita daga yankin.
A gefe guda, Muhammad Sorush Mahallati, ta wata fahimta daban game da wasiƙar Umar Bin Sa'ad zuwa ga Yazid, yana ganin cewa waɗannan tattaunawa yunƙuri ne daga Imam Husaini (A.S) na neman sulhu da kuma hana yaƙi da Yazid. Sai dai masu bincike kamar Rajabi Duwani da Maruwwiji Ɗabasi sun yi watsi da wannan fahimta, suna ganin wasiƙar Umar Bin Sa'ad ƙarya ce kuma an ƙirƙire ta domin wata manufa ta kansa.
An kuma bayar da fahimtoci daban-daban game da manufar waɗannan tattaunawa. Wasu kamar Sayyid Ali Khamna'i da Nasir Makarim Shirazi sun ɗauke su a matsayin nasiha da gargadi ga Umar Bin Sa'ad da kuma cika hujja a kan maƙiya.
A cikin wannan batu kuma akwai ra'ayin cewa Imam Husaini (A.S) ya yi ƙoƙarin yin sulhu ko yarjejeniya da Yazid, wanda Muhammad Sorush Mahallati da Hassan Ruhani suka gabatar.
A Karbala akwai wani wuri da ake kira wurin ganawar Imam Husaini (A.S) da Umar Sa'ad, inda ake cewa shi ne wurin da wannan ganawa ta faru. Wannan wuri yana cikin unguwar Babussalam, kusan mita 240 a arewacin haramin Imam Husaini (A.S).
Tattaunawar Imam Husaini (A.S) da Umar Bin Sa'ad Kafin Karbala
Bisa ga rahoton Abu Mikhnaf a cikin littafinsa Maƙtalul Husaini, kafin aukuwar waƙi'ar Karbala an samu tattaunawa da dama tsakanin Imam Husaini (A.S) da Umar Bin Sa'ad.[1] samuwar irin waɗannan tattaunawa abu ne da masana tarihi suka yarda da shi, amma akwai saɓani game da ainihin lokacin da aka yi su da kuma abin da suka ƙunsa.[2]
Bisa ga wasu ruwayoyi, shawarar yin ganawa ta fito ne daga Imam Husaini (A.S), kuma Amru Bin Ƙaraza Ansari ne ya isar da ita ga Umar Bin Sa'ad.[3] Sai dai Sibɗu Bin Jauzi ya danganta wannan shawara ga Bin Umar Bin Sa'ad.
An ce bayan wannan shawara, Imam Husaini (A.S) da Umar Bin Sa'ad kowannensu ya zo tare da mutum ashirin daga cikin mabiyansa, suka haɗu a wani wuri da yake tsakanin rundunonin biyu domin tattaunawa. Sai dai a wata ruwayar ta ƙarshe, an bayyana cewa Imam Husaini (A.S) ya halarta tare da Abbas (A.S) da Ali Akbar (A.S), yayin da Umar Bin Sa'ad ya shiga tattaunawar tare da ɗansa Hafs da bawansa Lahiƙ.[4]
Haka kuma an ruwaito cewa bayan wasu daga cikin sojojin Umar Bin Sa'ad sun fahimci yanayin da Imam Husaini (A.S) yake ciki, mutum talatin daga cikin rundunarsa sun rabu da shi suka koma wajen Imam (A.S). Sun ce:
Ɗan ƴar Manzon Allah yana gabatar muku da shawarwari, amma ba ku karɓar ko ɗaya daga cikinsu?[5] Sai dai wasu masu bincike sun nuna shakku game da ingancin wannan iƙirari.[6]
Ruwayoyi Mabambanta Game da Lokaci Da Yawan Tattaunawa Kafin Karbala
Game da lokacin waɗannan ganawa, akwai saɓanin ra'ayi tsakanin masana tarihi.[7] Mahadi Pishwayi, ɗaya daga cikin malaman tarihin Shi'a, yana ganin cewa Shimru Bin Zil Jaushan kafin isowarsa Karbala ya haɗu da Yazid a ranar 9 ga Muharram shekara ta 61H, inda ya sanar da shi labarin waɗannan ganawa. Saboda haka, a ra'ayinsa, tattaunawar ta faru ne kafin wannan lokaci.[8] Sai dai a cikin littafin Tarjamatul Husaini wa Maƙtaluhu (na ƙarni na uku bayan Hijira), an bayyana cewa waɗannan kalaman Imam Husaini (A.S) sun faru ne lokacin da ya fuskanci rundunar Kufa.[9]
Abu Mikhnaf ya bayyana cewa yawan waɗannan tattaunawa ya kai uku ko huɗu, kuma an yi su ne a wurare da lokuta daban-daban.[10]
Haka kuma Muhammad Sadiƙ Najmi, wani marubuci ɗan Shi'a, yana ganin cewa waɗannan ganawa sun faru ne tsakanin ranakun 4 zuwa 6 ga watan Muharram..[11]
Abun da Ke Cikin Tattaunawar
Ya ɗan Sa'ad! Shin kana son ka yaƙe ni alhali ka san ko ni wane ne, kuma ka san wanene mahaifina? Shin ba ka tsoron Allah wanda gare Shi ne makomarka? Ba ka son ka kasance tare da ni ka bar waɗannan (Banu Umayya)? Hakan shi ne mafi kusantar ka zuwa ga Allah Sai Umar bn Sa'ad ya amsa: Ina tsoron idan na yi haka za su rushe gidana da ke Kufa. Imam ya ce: Ni zan gina maka gidanka da kuɗina. Umar bn Sa'ad ya ce: Ina tsoron za su ƙwace gonata da itatuwan dabinona. Imam ya ce: Zan ba ka a Hijaz gonaki da suka fi waɗanda kake da su a Kufa. Umar bn Sa'ad ya ce: Matata da ƴa'ƴana suna Kufa, kuma ina tsoron za a kashe su. Imam ya ce: Ni na ɗauki alhakin kare lafiyarsu. Sai Umar bn Sa'ad ya yi shiru, bai ba da wata amsa ba. Daga nan Imam Husaini (A.S.) ya tashi yana cewa: Me ya same ka? ... Allah kada Ya gafarta maka... Ina ganin ba za ka ci alkamar Iraki ba, sai kaɗan kawai. Sai Umar bn Sa'ad ya mayar da martani da cewa: Idan ba alkama ba, ai akwai sha'ir.[12]
Game da abin da aka tattauna a tsakanin Imam Husaini (A.S) da Umar Bin Sa'ad, akwai rahotanni mabambanta a cikin ruwayoyin tarihi.[13]
Bisa ga ruwayar Ɗabari, masanin tarihin ƙarni na uku bayan Hijira, su biyun sun yi tattaunawar ne daga nesa da mabiyansu, saboda haka sojoji ba su san cikakken abin da suka faɗa wa juna ba, sai dai kawai suna yin zato ne da hasashe.[14]
A cikin wannan batu, Uƙbatu Bin Sam'an, wanda ya kasance daga cikin mutanen da suke tare da Imam Husaini (A.S) a koyaushe, ya ƙaryata da ƙarfi wannan sanannen iƙirari cewa Imam (A.S) ya ba da shawarar yin mubaya'a ga Yazid. Ya jaddada cewa abin da Imam (A.S) ya nema shi ne kawai a ba shi damar fita daga wannan yanki domin a ga abin da zai kasance game da al'ummar.[15]
A cewar Mahadi Pishwayi, bayan nazarin ruwayoyi daban-daban, ya ɗauki ruwayar Uƙbatu Bin Sam'an a matsayin ingatacciyar riwaya.[16] Ya dogara da tarihin rayuwar Imam Husaini (A.S) da matsayinsa a kan Banu Umayya da Yazid, inda ya bayyana cewa rahotannin da suke cewa Imam (A.S) ya ba da shawarar miƙa wuya ko zuwa wajen Yazid ba daidai ba ne. Pishwayi yana ganin cewa wasu rahotanni, kamar labarin fuskantar rundunar Husaini da rundunar Hurru, ko kuma tattaunawar Imam (A.S) da Umar Bin Sa'ad da aka danganta su da batun mubaya'a ga Yazid, karkatar da tarihi ne da kuma yunƙurin ba da halacci ga mulkin Yazid.[17] Haka kuma yana ganin cewa takardun tarihi da suka nuna cewa Imam Husaini (A.S) ya ƙi yin mubaya'a ga Yazid suna tabbatar da rashin ingancin irin waɗannan ruwayoyi.[18]
A gefe guda, Muhammad Sorush Mahallati, malamin fiƙihun Shi'a, ya ɗauki abin da ke cikin wasiƙar da Umar Bin Sa'ad ya aika wa Yazid Bin Mu'awiya bayan tattaunawarsa da Imam Husaini (A.S) a matsayin mabuɗin fahimtar wannan tattaunawa.[19]
A bisa wannan fahimta, Mahallati yana ganin cewa Imam Husaini (A.S) a cikin wannan tattaunawa ya nemi ganawa da Yazid domin yin mubaya'a ko tattaunawa. Ya kuma ce wannan ba ya karo da kalaman Imam na baya da suka ƙi mubaya'a, domin waɗannan suna da alaƙa da wani lokaci da wani yanayi daban.[20] A ganinsa, Imamai (A.S) shugabanni ne masu fahimtar siyasa, kuma suna iya yin martani daban-daban gwargwadon yanayi da lokaci.[21]
Wannan fahimta ta samu suka daga masu binciken tarihi kamar Muhammad Husaini Rajabi Duwani da Muhammad Ali Maruwwiji Ɗabasi.[22] Su suna ganin cewa shawarwarin da Umar Bin Sa'ad ya ambata a cikin wasiƙarsa zuwa ga Yazid ƙarya ne, kuma kawai wani yunƙuri ne daga gare shi na kawo ƙarshen yaƙi da kuma cimma manufofinsa na kansa ba tare da zubar da jini ba.[23]
Haka kuma, bisa rahoton Muhammad Bin Jarir Ɗabari, bayan Umar Bin Sa'ad ya samu amsar wasiƙarsa daga Shimru Bin Zil Jaushan, ya amince da cewa abin da ya rubuta a cikin wasiƙar tasa ba gaskiya ba ne.[24]
Fahimtoci (Ra'ayoyi)
Waɗanda suka yarda da samuwar irin wannan tattaunawa tsakanin Imam Husaini (A.S) da Umar Sa'ad sun gabatar da ra'ayoyi daban-daban game da dalili da manufar wannan ganawa:
- Khamna'i|Sayyid Ali Khamna'i]], Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran, a shekara ta 1394sh (2015–2016 M), ya bayyana cewa kiran tattaunawar Imam Husaini (A.S) da Umar Sa'ad da sunan tattaunawa ta siyasa (Muhawara domin sulhu) yana daga fahimta mai sauƙi da kallon al'amari ta fuskar jama'a kawai. A ra'ayinsa, wannan ganawa an yi ta ne domin yi wa Ibn Sa'ad nasiha da gargaɗi.[25] Nasir Makarim Shirazi, daga cikin maraji'an taƙlidi na Shi'a, ya ɗauki manufar wannan tattaunawa a matsayin yin nasiha da wa'azi ga Umar Sa'ad domin ya janye daga kuskuren da yake shirin aikatawa.[26]
- Tattaunawa domin Sulhu: Muhammad Sorush Mahallati yana ganin cewa waɗannan ganawa an yi su ne domin tattaunawa da neman yarjejeniya da Yazid, da kuma hana yaƙi da zubar da jini daga ɓangaren Imam Husaini (A.S). Ya dogara da wasu madogaran tarihi inda ya ɗauki batun neman ganawa da Yazid a matsayin wani nau'in tattaunawa domin kawo ƙarshen yaƙi.[27]Hassan Ruhani, tsohon shugaban ƙasar Iran, a shekara ta 1393sh (2014–2015 M), yana mai ishara da wannan tattaunawa, ya bayyana cewa darasin Karbala darasi ne na hulɗa mai kyau da tattaunawa bisa tsarin hankali da ƙa'idoji.[28]
- Cika Hujja: Nasir Makarim Shirazi ya bayyana cewa asalin wannan tattaunawa shi ne domin cika hujja da Imam Husaini (A.S) ya yi a kan maƙiyansa, domin kada wani daga baya ya ce bai san gaskiyar lamarin ba.[29]
Wurin Tattaunawar Imam Husaini da Umar Sa'ad

Muƙam Tattaunawar Imam Husaini (A.S) da Umar Bin Sa'ad suna ne na wani wuri mai tarihi da kuma na ziyara, wanda yake a ƙarshen babban kasuwar birnin Karbala, a unguwar Babussalam.
Wannan wuri yana da nisan kusan mita 240 a arewacin haramin Imam Husaini (A.S). Ana cewa shi ne wurin da Imam Husaini (A.S) ya haɗu da Umar Bin Sa'ad domin tattaunawa kafin fara yaƙin.[30]
An gina wannan wuri a shekara ta 1113 bayan Hijira, sannan an sake gyara shi a shekarun 1352H, 1378H, da 1423H.[31]
Bayanin kula
- ↑ Abu Mikhnaf, Maƙtalulul Husain, LaburarenAyatullahi Mar'ashi Najafi, juzu'i na 1, shafi na 100.
- ↑ «متن کامل تحلیل سروش محلاتی از ملاقات امام حسین(ع) با عمر سعد»، Kamfanin Dillancin Labarai na Shafaqna.
- ↑ Sibɗu Ibn Jauzi, Tazkiratul Khawas, juzu'i na 2, shafi na 152.
- ↑ Khawarizmi, Maƙtalulul Husain, juzu'i na 1, shafi na 347.
- ↑ Ibn Ƙuɗaiba Diniwari, Al-Imama was-Siyasa, juzu'i na 2, shafi na 11 da 12.
- ↑ Pishwayi, Maƙtal-e Jami'-e Sayyidush Shuhada, juzu'i na 1, shafi na 709.
- ↑ Pishwayi, Maƙtal-e Jami'-e Sayyidush Shuhada, juzu'i na 1, shafi na 709.
- ↑ Pishwayi, Maƙtal-e Jami'-e Sayyidush Shuhada, juzu'i na 1, shafi na 709.
- ↑ Ibn Sa'ad Baghdadi, Tarjamatul Husain wa Maƙtaluhu, shafi na 69.
- ↑ Abu Mikhnaf, Maƙtalulul Husain, LaburarenAyatullahi Mar'ashi Najafi, juzu'i na 1, shafi na 100.
- ↑ «چه سخنانی بین امام حسین و عمر سعد در خیمه میان دو لشگر رد و بدل شد؟»، Kamfanin Dillancin Labarai na Khabar Online.
- ↑ Khawarizmi, Maƙtalul Husain, juzu'i na 1, shafi na 347.
- ↑ Pishwayi, Maƙtal-e Jami'-e Sayyidush Shuhada, juzu'i na 1, shafi na 710 da 711.
- ↑ Tabari, Tarikhut Tabari, juzu'i na 5, shafi na 413.
- ↑ Tabari, Tarikhur Rusul wal Muluk, juzu'i na 5, shafi na 415.
- ↑ Pishwayi, Maƙtal-e Jami'-e Sayyidush Shuhada, juzu'i na 1, shafi na 710 da 711.
- ↑ Pishwayi, Maƙtal-e Jami'-e Sayyidush Shuhada, juzu'i na 1, shafi na 710 da 711.
- ↑ Pishwayi, Maƙtal-e Jami'-e Sayyidush Shuhada, juzu'i na 1, shafi na 709.
- ↑ «متن کامل تحلیل سروش محلاتی از ملاقات امام حسین(ع) با عمر سعد»، Kamfainin dillancin labarai na Shafaqna.
- ↑ «متن کامل تحلیل سروش محلاتی از ملاقات امام حسین(ع) با عمر سعد»، Kamfainin dillancin labarai na Shafaqna.
- ↑ «متن کامل تحلیل سروش محلاتی از ملاقات امام حسین(ع) با عمر سعد»، Kamfainin dillancin labarai na Shafaqna;«چه سخنانی بین امام حسین و عمر سعد در خیمه میان دو لشگر رد و بدل شد؟»، Kamfainin dillancin labarai na Online.
- ↑ Rajab Duwani، «مذاکره امام حسین(ع) و «عمر سعد» خطرناکترین تحریف واقعه کربلاست»، Kamfanin dillancin labarai na Tasnim؛ «گفتوگوی امام حسین(ع) با عمرسعد؛ موعظه یا مذاکره؟/ نقدی بر سخنان سروش محلاتی»، Kamfanin dillancin labarai na ƙasa da ƙasa na IQNA.
- ↑ Jafariyan، «راهبردهای امام حسین (ع) در مراحل مختلف نهضت کربلا»، Kamfanin dillanin labarai na Tasnim؛ Mazahiri، «نقدی بر ادعای مذاکره امام حسین با عمر سعد»، Shafin yanar gizo na Rasikhun.
- ↑ Tabari, Tarikhur Rusul wal Muluk, juzu'i na 5, shafi na 415.
- ↑ Khamna'i، «بیانات در دیدار فرماندهان و کارکنان نیروی دریایی سپاه پاسداران انقلاب اسلامی و خانوادههای آنان»،Shafin yanar gizo na Ofishin Kiyaye da Yaɗa Ayyukan Ayatullahi Khamna'i..
- ↑ Makarim Shirazi, Ashura: Rizheha, Angizeha, Ruydadha, Payamadha, juzu'i na 1, shafi na 388.
- ↑ «متن کامل تحلیل سروش محلاتی از ملاقات امام حسین(ع) با عمر سعد»، Kamfanin dillancin labarai na Shafaqna.
- ↑ «هشدار رییس جمهور نسبت به اجرای ناصحیح امر به معروف و نهی از منکر»، Kamfanin dillancin labarai na ISNA.
- ↑ Makarim Shirazi, Ashura: Rizheha, Angizeha, Ruydadha, Payamadha, juzu'i na 1, shafi na 388.
- ↑ «زیارتگاه های کربلا؛ مقام گفتوگوی امام حسین(ع) با عمر بن سعد»،Cibiyar Musamman ta Imam Husaini (A.S).
- ↑ Faqih Bahrul Ulum da Khamahyar, Ziyaratgahā-ye Irāq (Ma'arifi Ziyaratgahā-ye Mashhur dar Keshwar-e Irāq),Hukumar Hajji da Ziyara, juzu'i na 1, shafi na 246.
Nassoshi
- «متن کامل تحلیل سروش محلاتی از ملاقات امام حسین(ع) با عمر سعد»، (Rubutun cikakken nazarin Soroush Mahallati game da ganawar Imam Husaini (A.S.) da Umar Sa'ad), Kamfanin Dillancin Labarai na Shafaqna, ranar wallafa labarin: 17 Oktoba 2016 Miladiyya, ranar dubawa:23 Mayu 2023 Miladiyya.
- «زیارتگاههای کربلا؛ مقام گفتوگوی امام حسین (ع) با عمر بن سعد»، پایگاه تخصصی امام حسین علیه السلام، (Wuraren Ziyara na Karbala; Wurin Tattaunawar Imam Husaini (A.S.) da Umar ɗan Sa'ad, Cibiyar Musamman ta Imam Husaini (A.S.).), Ranar wallafa labarin:18 Nuwamba 2016 Miladiyya, ranar dubawa: 5 26 Mayu 2023 Miladiyya.
- «چه سخنانی بین امام حسین و عمر سعد در خیمه میان دو لشگر رد و بدل شد؟»، (Wadanne kalamai ne aka yi musayar su tsakanin Imam Husaini (A.S.) da Umar Sa'ad a cikin tanti da ke tsakanin rundunonin biyu?) Kamfanin Dillancin Labarai na Khabar Online, ranar wallafa labarin: 18 Oktoba 2015 Miladiyya, ranar dubawa: 23 Mayu 2023 Miladiyya.
- Abu Mikhnaf Al-Azdi, Lut Bin Yahya, Maƙtalull Husain, Qum, Laburaren Ayatullahi Mar'ashi Najafi, ba tare da shekarar bugawa ba.
- Ibn Sa'ad Al-Baghdadi, Muhammad Bin Sa'ad, Tarjamatul Imam Husaini wa Maƙtaluhu (A.S.), Qum, Mu'assasatu Ahlil Baiti (A.S.) li Ihya'it Turath, ba tare da shekarar bugawa ba.
- Ibn Ƙuɗaiba Dinawari, Abu Muhammad Abdullah Bin Muslim, Al-Imamatu was Siyasatu (wanda aka fi sani da Tarikhul Khulafa), Beirut, Darul Adwa', 1410H.
- Tabari, Muhammad Bin Jarir, Tarikhut Tabari: Tarikhur Rusuli wal Muluk, Masar, Darul Ma'arif, 1387H / 1967 Miladiyya.
- Pishwayi, Mahadi, Maƙtal Jami'u Sayyidush Shuhada, Qum, Cibiyar Ilimi da Bincike ta Imam Khumaini, 1397sh (2018–2019 Miladiyya).
- Jafariyan, Rasul, Rahbordhā-ye Imam Husain (A.S.) dar Marahil-e Mokhtalef-e Nahzat-e Karbala.(Dabarun Imam Husaini (A.S.) a Matakai Daban-daban na yunkurin Karbala), Kamfanin Dillancin Labarai na Tasnim, ranar wallafa labarin: 20 Shahrivar 1398sh (11 Satumba 2019 Miladiyya), ranar dubawa: 31 Ordibehesht 1402sh (21 Mayu 2023 Miladiyya).
- Khamna'i, Sayyid Ali، «بیانات در دیدار فرماندهان و کارکنان نیروی دریایی سپاه پاسداران انقلاب اسلامی و خانوادههای آنان»، (Jawabin Jagora a ganawar da kwamandoji da ma’aikatan Rundunar Sojojin Ruwa ta Sepah na Jamhuriyar Musulunci ta Iran da iyalansu.), Gidan yanar gizon Ofishin Kula da Yaɗa Ayyukan Ayatullahi Khamna'i, ranar wallafa labarin: 7 Oktoba 2015 Miladiyya, ranar dubawa: 29 Mayu 2023 Miladiyya.
- Khwarazmi, Muwaffaq Bin Ahmad, Maƙtalul Husain, Qum, Anwarul Huda, 1423H.
- Rajabi Duwani, Muhammad Husaini، «مذاکره امام حسین(ع) و «عمر سعد» خطرناکترین تحریف واقعه کربلاست»،(Tattaunawar Imam Husaini (A.S.) da Umar Sa'ad ita ce mafi hatsarin karkatar da tarihin lamarin Karbala.), Kamfanin Dillancin Labarai na Tasnim, ranar wallafa labarin: 15 Oktoba 2016 Miladiyya, ranar dubawa: 23 Mayu 2023 Miladiyya.
- Sibɗu Ibn Jauzi, Yusuf Bin Qizawghali, Tazkiratul Khawas min al-Ummah bi Zikri Khasa'is al-A'immah, Qum, Cibiyar Bugawa da Yaɗa Ayyukan Cibiyar Duniya ta Ahlul Baiti (A.S.), 1426H.
- Tabari, Muhammad Bin Jarir, Tarikhut Tabari: Tarikhut Tabari: Tarikhur Rusul wal Muluk wa Silat Tarikhut Tabari". ba tare da wurin bugawa ba, ba tare da shekarar bugawa ba.
- Faƙih Bahrul Ulum, Muhammad Mahadi, da Khamayyar, Ahmad, Ziyaratgahā-ye Irāq (Ma'arifi Ziyaratgahā-ye Mashhur dar Keshwar-e Irāq), Tehran, Hukumar Hajji da Ziyara, Wakilcin Jagoran Fikihu a Harkokin Hajji da Ziyara, ba tare da shekarar bugawa ba.
- «گفتوگوی امام حسین(ع) با عمرسعد؛ موعظه یا مذاکره؟/ نقدی بر سخنان سروش محلاتی»، (Tattaunawar Imam Husaini (A.S.) da Umar Sa'ad; Nasiha ce ko Tattaunawa ta Sulhu? / Sukar Maganganun Surush Mahallati.),Kamfanin Dillancin Labarai na Duniya na Kur’ani (IQNA), ranar wallafa labarin: 10 Oktoba 2019 Miladiyya, ranar dubawa: 8 Yuli 2025 Miladiyya.
- Mazahiri، «نقدی بر ادعای مذاکره امام حسین با عمر سعد»، سایت راسخون، تاریخ درج مطلب: ۱۱ مهر ۱۳۹۶ش، تاریخ بازدید: ۷ خرداد ۱۴۰۲ش.
- Makarim Shirazi, Nasir, Ashura: Tushen Ta, Dalilai, Abubuwan da Suka Faru, da Sakamakonta, 1387sh (2008–2009 Miladiyya), Qum, ba tare da wurin bugawa ba.
- «هشدار رییس جمهور نسبت به اجرای ناصحیح امر به معروف و نهی از منکر»، (Hanyar da Shugaban ƙasa ya yi gargaɗi game da aiwatar da umarni da kyakkyawan aiki da hani daga mummunan aiki ta hanyar da ba daidai ba.),Kamfanin Dillancin Labarai na ISNA, ranar wallafa labarin: 30 Oktoba 2014 Miladiyya, ranar dubawa: 8 Yuli 2025 Miladiyya.