Jump to content

Daƙiƙa:Tarikus Salat

Daga wikishia

Tarikus salat ko mai barin sallah, (Larabci: تارك الصلاة) take ne da yake nuni zuwa ga Musulmi wanda da gangan yake ƙin yin sallah, bisa koyarwar shari'a Muslunci ana la'akari da misalin wannan mutumi a matsayin wanda yake aikata manya-manyan zunubai, idan wani yaƙi yin sallah saboda yana inkarin kasancewarta wajibi, lallai hakan zai zama dalilin riddarsa da fita daga Muslunci. Kur'ani ya bayyana rashin yin sallah yana daga cikin abubuwan da suke hana samun ceto a ranar Alƙiyama.

Haƙiƙa ginshiƙi ce na addinin Muslunci, kuma tana daga cikin rukunan Musulunci, Allah ya yi umarni da tsayar da sallah (Ku tsayar da sallah, ku bayar da zakka).

An naƙalto daga Annabi idan wani ya bar sallah ba tare da wani uzuri ba, Allah zai ɓatar da ayyukansa na alheri. Bisa abin da ya zo a riwayoyi, Shaiɗan yana amfani da barin sallah cikin jefa mutane cikin manya-manyan zunubai, kuma Allah yana da haƙƙin sanya mai barin sallah a sahun munafukai ya kora su zuwa Jahannama. A wasu riwayoyin an kira masu barin sallah da Kafirai.

Musulmai sun yi ijma'i kan cewa da wani zai yi inkarin asalin sallah ya kuma yi shakkun kasancewarta wajibi, to ya yi ridda, sai dai idan ya yi da'awar cewa barin yin sallarsa ya kasance ne bisa shubuha kamar dai sabbin muslunta.

Wasu jama'a daga malaman fiƙihu sun yi imani idan wani bisa sakaci da kasala ya bar sallah ba tare da ya yi inkarin asalin wajabcin sallah ba, to za a ɗauke shi matsayin fasiƙi, amma wanda tare da imani da wajabcin sallah sai ya bar sallah ba tare da wani uzuri da yake da shi ba, to za a ladabtar da shi, a kuma umarce shi ya yi sallah; idan ya ci gaba da barin sallah, kuma wasu lokutan sallar ta zama ramuwa a wuyansa, to za a sake ladabtar da shi ta hanyar ta'azir

Zargi Kan Barin Sallah

Sallah ita ce ginshikin addini kuma umurnin Allah ne a tsayar da ita. Ba a halatta jinkirta ta daga lokacinta sai da uzurin shari'a, kuma kasala ba uzuri ba ne. Dole ne a yi nasiha da kwadaitar da wanda ya bar ta cikin hikima da hakuri, tare da yin addu'a a boye masa, domin addu'ar boye tana da karbuwa sosai.[1]

Barin sallah yana cikin manya-manyan zunubai masu girman gaske,[2] a cikin wasu riwayoyi an kira mai barin sallah da kafiri.[3] Rashin yin sallah da gangan yana matsayin wulaƙanta sallah, kuma hukunci da shari'a ta tanada kan wannan aiki kamar yadda ya zo a wata riwaya daga Imam Sadiƙ (A.S) ya zarce hukuncin da aka tana da a kan wasu daga manya-manyan zunubai (Kamar shan giya), Shaik Hurrul Amili babban malamin fiƙihu na Shi'a a ƙarni na 11 hijira, ya dogara da wannan riwaya kan tabbatar da kafircin mai barin sallah.[4]

Nasir Makarim Shirazi, daga maraji'an taƙlidi na Shi'a, yana da ra'ayin cewa halin mai barin sallah ya fi munana daga mutanen da suke sakaci cikin sallah wanda Kur'ani ya bayyana su matsayin mutanen da suka cancanci bomi da azaba wanda aka yi amfani da jumlar (Wailun Lil musallin)[5] a kansu.[6]

An naƙalto daga Annabi (S.A.W), idan wani ya bar sallah ba tare da wani uzuri ba, Allah zai ɓatar da ayyukansa na alheri.[7] Kan asasin riwayoyi, Shaiɗan na amfani da barin sallah da mutane suke yi ya cuna su da hankaɗa su zuwa aikata manya-manyan lefuka[8] Allah yana da haƙƙin sanya masu barin sallah cikin sahun munafukai tare da aika su jahannama[9] Haka nan an naƙalto wata riwaya daga Imam Baƙir (A.S), ka da ku yi sanyin jiki cikin sallah, saboda manzon Allah a numfashinsa na ƙarshe-ƙarshe ya ce: ba ya tare da ni duk wanda yake wulaƙanta sallah.[10]

Hanyoyin Barin Sallah

Haƙiƙa Musulmi sun yi ijma'i idan wani ya yi inkarin asalin sallah ya ƙaryata wajabcinta, to lallai ana lissafa shi cikin wanda ya fice daga Muslunci[11] kuma murtaddi,[12] Sai dai idan ya yi da'awar cewa barin sallarsa ya faru ne bisa shubuha da ya samu kansa a ciki, kamar sabon muslunta,[13] Amma da wani zai kasance ya yarda da wajabcin sallah amma sai ya bar sallah ba tare da uzuri ba, to za a masa ta'azir (ladabtarwa ta shari'a), a umrace shi da yin sallah, idan bayan ɗaukar wannan matakai a kansa ya ci gaba da barin sallah, wata sallah ta zama ƙara'i da ramuwa a kansa, to za a sake masa ta'azir (ladabtawa ta shari'a)[14] Idan wani bisa kasala da sakaci sai ya bar sallah bai yi ba, amma ba ya inkarin asalin sallar, za a masa hukunci da kasancewa fasiƙi.[15]

Kafircin Mai Barin Sallah

A wasu riwayoyi, an yi ishara kan kafircin mai barin sallah: Annabin Muslunci ya ce: wanda bisa ganganci ya bar sallah shi kafiri ne,[16] Imam Kazim (A.S) bisa maganar Annabi (S.A.W) a cikin wata riwaya ya lissafa manya-manyan zunubai, ya bayyana barin sallah da gangan da duk abin da Allah ya wajabta cikin manya-manyan zunubai.[17][Tsokaci 1]tsakanin bauatr Allah da kafirce masa, barin sallah ne tsakankani.[18] Imam Sadiƙ (A.S) a wata magana ya kira mai barin sallah da kafiri.[19]

A cewar Muhammad Baƙir Majlisi, malamin hadisi na Shi'a a ƙarni na 11 hijira, yana cewa imani bai taƙaitu da imani a zuciya ba, wajibi ne ya kasance tare da sauke wajibai na shari'a da abubuwan da shari'a ta haramta, a ra'ayin malamin, da wannan dalili ne a cikin riwayoyi aka kira mai barin sallah da kafiri.[20] Allama Hilli, babban malamin fiƙihu na Shi'a a ƙarni na bakwai da takwas hijira, ya yi da'awar cewa ijma'i ya ƙullu kan tabbatar kiran mai barin sallah da wanda ya yi ridda ya fita daga Musulunci.[21]

Musulmi sun yi saɓani kan mutumin da duk da cewa ya yi imani da wajabci sallah amma tare da haka yana barin sallah.[22] Wasu malamai sun bayar da umarni ta'azir kan mutumin da tare da cewa yarda da wajabcin sallah amma kuma yana barin sallah da gangan, idan ya sake maimaita barin sallah har karo uku ko huɗu[23] za a kashe shi[24] Tare da haka, Sayyid Ali Sistani ɗaya daga cikin maraji'an taƙlidi na Shi'a, yana da ra'ayin cewa barin sallah kaɗai ba ya jawo kafirci, duk da cewa hakan yana daga manya-manyan zunubai.[25] Mirza Jawad Tabrizi daga maraji'an taƙlidi na Shi'a, ba ya ganin mai barin sallah a matsayin najasa.[26]

Barin Sallah Da Kuma Sauran Zunubai

Bisa abin da ya zo cikin riwayoyi biyu da aka kawo su a litattafan Al-Kafi da Irshadul Ƙulub, zunubin barin sallah yana iya fin zunubin ƙona Kur'ani da aikata zina, kuma ana ɗaukar mai barin sallah ya matsayin kafirta da Allah da manzonsa,[27] Amma Shaik Saduƙ a cikin littafin Ilalush Shara'i da marubucin La'alil Akhbar, suna ganin cewa babban dalili nauyayar zunubin mai barin sallah shi ne, mutum ba tare da wani dalili ba, kuma ba tare da hatta jin daɗin haramun ba sai a same shi yana wulaƙanta wannan ibada, alhali a sauran lefuka, galabar sha'awa ko wani jin daɗin zunubi ne suke jawo shi zuwa ga aika waɗannan lefuka.[28]

Bayanin kula

  1. Darur Ifta Egypt:https://www.dar-alifta.org/ha/fatwa/details/19940/barin-sallah
  2. Tayyib, Atyab al-Bayan, 1999, Juz'i na 14, Shafi na 168.
  3. Tayyib, Atyab al-Bayan, 1999, Juz'i na 14, Shafi na 168.
  4. Hurr al-Amili, Wasa'il al-Shia, Beirut, Juz'i na 3, Shafi na 28.
  5. Taleqani, Partovi az Quran, 1983, Juz'i na 4, Shafi na 273.
  6. Makarem Shirazi, Tafsir-e Nemuneh, 1995, Juz'i na 27, Shafi na 361.
  7. Majlisi, Bihar al-Anwar, 1983 AH, Juz'i na 79, Shafi na 202.
  8. Majlisi, Bihar al-Anwar, 1983 AH, Juz'i na 79, Shafi na 202.
  9. Sheikh Saduq, Uyun Akhbar al-Ridha, 1959 AH, Juz'i na 2, Shafi na 31.
  10. Kulayni, Al-Kafi, 1987 AH, Juz'i na 3, Shafi na 269.
  11. «حکم تارک الصلاه» Gidan yanar gizo na Muflihun.
  12. Sheikh Tusi, Al-Khilaf, 1987 AH, Juz'i na 5, Shafi na 359.
  13. Shahid Awwal, Al-Durus, 1997 AH, Juz'i na 1, Shafi na 144.
  14. Sheikh Tusi, Al-Khilaf, 1987 AH, Juz'i na 1, Shafi na 689.
  15. Sheikh Tusi, Al-Khilaf, 1987 AH, Juz'i na 5, Shafi na 359.
  16. Ibn Abi Jumhur, Awali al-La'ali, 1985 AH, Juz'i na 2, Shafi na 224.
  17. Kulayni, Al-Kafi, 1987 AH, Juz'i na 2, Shafi na 287.
  18. Shu'ayri, Jami' al-Akhbar, Najaf, Shafi na 74.
  19. Kulayni, Al-Kafi, 1987 AH, Juz'i na 2, Shafi na 279.
  20. Majlisi, Bihar al-Anwar, 1983 AH, Juz'i na 66, Shafi na 127.
  21. Hillí, Tadhkirat al-Fuqaha, 1994 AH, Juz'i na 2, Shafi na 391.
  22. «حکم تارک الصلاه» Shafin yanar gizo na Muflihun.
  23. Shahid Awwal, Al-Durus, 1997 AH, Juz'i na 1, Shafi na 144.
  24. Sheikh Tusi, Al-Khilaf, 1987 AH, Juz'i na 1, Shafi na 689.
  25. «پرسش و پاسخ، تارک نماز»،Shafin yanar gizo na ba da bayanai daga ofishin Ayatullah Sistani
  26. Tabrizi, Istifta'at-e Jadid, ba a kwanan wata ba, Juz'i na 2, Shafi na 115.
  27. Kulayni, Al-Kafi, 1987 AH, Juz'i na 2, Shafi na 287; Daylami, Irshad al-Qulub ila al-Sawab, Juz'i na 1, Shafi na 190.
  28. Sheikh Saduq, Ilal al-Sharai', Juz'i na 2, Shafi na 339 «لئالی الاخبار، ص۱۲۹۷»،Cibiyar Karatun Dijital na Cibiyar Koyar da Kimiyyar Elektaronik ta Jami'ar Alkur'ani da Hadisi.

Tsokaci

  1. وَ تَرْكُ الصَّلَاةِ مُتَعَمِّداً أَوْ شَيْئاً مِمَّا فَرَضَ اللهُ لِأَنَّ رَسُولَ اللهِ ص قَالَ مَنْ تَرَكَ الصَّلَاةَ مُتَعَمِّداً فَقَدْ بَرِئَ مِنْ ذِمَّةِ اللهِ وَ ذِمَّةِ رَسُولِ اللهِ. Tarjama:Kuma barin sallah da gangan, ko wani abu daga cikin abin da Allah ya wajabta, domin Manzon Allah (S.A.W.) ya ce: "Wanda ya bar sallah da gangan, to lalle ya fita daga amanar Allah da amanar ManzonSa."

Nassoshi

  • "La'ali al-Akhbar, p. 1297", Digital Library of the E-Learning Center of Quran and Hadith University, accessed: October 25, 2022.
  • Darur Ifta Egypt:https://www.dar-alifta.org/ha/fatwa/details/19940/barin-sallah
  • Daylami, Hasan ibn Muhammad, Irshad al-Qulub ila al-Sawab, Qom, al-Sharif al-Radi, bugu na farko, 1992 AH.
  • Hilli, Hasan ibn Yusuf, Tadhkirat al-Fuqaha, Qom, Mu'assasat Al al-Bayt (A.S.), bugu na farko, 1994 AH.
  • Hurr al-Amili, Muhammad ibn al-Hasan, Wasa'il al-Shia ila Tahsil Masa'il al-Sharia, gyara: Abd al-Rahim Rabbani Shirazi, Beirut, Dar Ihya al-Turath al-Arabi,babu tarihi.
  • Ibn Abi Jumhur, Muhammad ibn Zayn al-Din, 'Awali al-La'ali al-'Aziziyyah fi al-Ahadith al-Diniyyah,Gyara: Mujtaba Iraqi, Qom, Dar Sayyid al-Shuhada, 1985M.
  • Kulayni, Muhammad ibn Ya'qub, Al-Kafi, gyara: Ali Akbar Ghaffari and Muhammad Akhundi, Tehran, Dar al-Kutub al-Islamiyyah, bugu na hudu, 1987 AH.
  • Majlisi, Muhammad Baqir, Bihar al-Anwar, Beirut, Dar Ihya al-Turath al-Arabi, bugu na biyu, 1983 AH.
  • Makarem Shirazi, Nasser, Tafsir-e Nemuneh, Tehran, Dar al-Kutub al-Islamiyyah, bugu na farko, 1995.
  • Shahid Awwal, Muhammad ibn Makki, al-Durus al-Shar'iyyah fi Fiqh al-Imamiyyah, Daftar-e Intisharat-e Islami, Qom, bugu na biyu, 1997 AH.
  • Sheikh Saduq, Muhammad ibn Ali, Ilal al-Sharai', Qom, Kitabforushi-ye Davari, bugu na farko, 2006.
  • Sheikh Saduq, Muhammad ibn Ali, Uyun Akhbar al-Ridha (A.S.), gayra: Mahdi Lajavardi, Tehran, Nashr-e Jahan, bugu na farko, 1959 AH.
  • Sheikh Tusi, Muhammad ibn al-Hasan, Al-Khilaf, Gyara: Ali Khorasani, Sayyid Jawad Shahristani, Mahdi Taha Najaf, and Mujtaba Iraqi, Qom, Daftar-e Intisharat-e Islami, bugu na farko, 1987 AH.
  • Shu'ayri, Muhammad ibn Muhammad, Jami' al-Akhbar, Najaf, Matba'at al-Haydariyyah,bugu na farko, babu tarihi.
  • Taleqani, Sayyid Mahmoud, Partovi az Quran, Tehran, Sherkat-e Sahami-ye Intishar, bugu na hudu, 1983.
  • Tayyib, Sayyid Abdul Husayn, Atyab al-Bayan fi Tafsir al-Quran, Tehran, Intisharat-e Islam, bugu na biyu, 1999.
  • «Mai Barin Sallah (Tarik al-Salah)»Gidan Yanar Gizo na Muflihun, ranar dubawa: 24 ga Satumba, 2022.
  • «Tambaya da Amsa: Mai Barin Sallah (Tarik al-Salah)», Gidan Yanar Gizo na Ayatullah Sistani, ranar dubawa: 24 ga Satumba, 2022.