Daƙiƙa:Suratul Jasiya
Dukhan Suratul Jasiya Ahƙaf | |
| Lambar Sura | 45 |
|---|---|
| Juzu'i | 25 |
| Jerantuwa Ta Sauka | 65 |
| Adadin Ayoyi | 37 |
| Adadin Kalmomi | 489 |
| Adadin Haruffa | 2085 |
| Makkiya/Madaniyya | Makkiyya |
Suratul Jasiya sura ce ta 45 cikin juzi'i na 25 a Alƙur'ani, wannan sura an sauke ta a Makka, sunanta ya samo asali daga aya ta 28 a cikinta, tana magana kan girman Alƙur'ani da muhimmancinshi, kuma tana bayani kan dalili na Tauhidi tana kuma ishara kan makomar wasu al'ummu da suka gabata, tana kira kan yin afuwa da magana kan yadda ranar alƙiyama za ta kasance, da magana kan littafin aiki na kowanne ɗan Adam.
Daga cikin ayoyinta Mashahurai akwai aya ta 15 Faɗinsa maɗaukaki: (Duk wanda ya yi aiki na ƙwarai, to don kansa ya aikata shi; wanda kuma ya aikata mugunta, to a kansa ta koma. Sannan zuwa ga Ubangijinku za a mayar da ku). Akwai ruwayoyi da yawa kan falalar karanta wannan sura, daga cikin an rawaito daga Annabi (S.A.W) cewa duk wanda ya karanta Suratul Jasiya, to Allah zai rufe mishi sirrinshi kuma zai kwantar mishi da firgicinshi a ranar alƙiyama.
Sanya Suna Da Kuma Ayoyi
Ana kiranta da Jasiya saboda faɗar Allah maɗaukaki cikin aya ta 28 (Kuma za ka ga kowace al'umma tana durƙushe a kan gwiwowinta).[1] ta samo wannan suna ne daga aya ta 18,[2] kuma ana kiranta Suratud Dahri.[3] Ta nada ayoyi 37 kalmomi 489 haruffa 2085[4] Wannan sura tana cikin surori Hawamim, abin nufi surorin da suka fara da Hamim.[5]
Tsarin Da Aka Saukar Da Ita
Suratul Jasiya sura ce da aka sauke ta a Makka,[6] a jerin sauka ita ce 65 amma a cikin Alƙur'ani a yanzu ita ce 45.[7]
Ma'anonin Wasu Kalmominta Mafi muhimmanci ma'anoni na wasu kalmominta: (Dabbatu): Duk wani abu da yake motsi yake tafiya a doran ƙasa. (Rijzu): Azaba mai tsanani, asalinsa shi ne raurawa (Al-Fulku): Jiragen ruwa (Jasiyatu): Daga Jaswu, tsugunawa kan gwiwa, tsugunawa kan gwiwa cikin tsoro saboda tsanin firgicin ranar alƙiyama. (Haƙƙa Bihim): Azaba tana kewayi da su.[8]
Abun Ciki
Abin da wannan sura ta ƙunsa za a iya raba shi gida shida a taƙaice:
- Wannan sura tana magana kan girman Alƙur'ani da muhimmancinshi.
- Tana bayani kan dalilai na Tauhidi ga Mushirikai.
- Wannan sura tana ambaton iƙrari ko dalilai na waɗanda ba su yi imani da Allah ba sai dai imani da zamani, da raddi da aka yi musu.
- Tana bayani kan al'ummun da suka gabata da girbar sakamakon aikin da suka aikata, kamar Banu Isra'il.
- Wannan sura tana gargaɗi da bayani na azabar da aka tanada ga mutanen da suka ɓata kuma suka dage da dogewa kan aƙidarsu ta ɓata.
- Wannan sura tana kira da yin afuwa ga duk wanda bai kauce daga kan gaskiya ba.
- Surar tana nuni da bayani kan yanayin firgici da tsoro na ranar alƙiyama, da bayani na masamman kan littafin abin da mutum ya aikata ba tare da ƙari ba ko ragi.[9]
Shahararrun Ayoyi
Faɗar Allah maɗaukaki, (Duk wanda ya yi aiki na ƙwarai, to don kansa ya aikata shi; wanda kuma ya aikata mugunta, to a kansa ta koma. Sannan zuwa ga Ubangijinku za a mayar da ku),[10] Ya zo a littattafan tafsiri cewa: Wannan bayani da ya zo a cikin Alƙur'ani Mai Girma sau da dama, ta lafuzza daban-daban, amsa ce ga wanda yake cewa: "Me ya sa rashin biyayyarmu ga Allah zai cutar da Shi, kuma mene ne biyayyarmu za ta amfane Shi? Me ya sa ake dagewa sosai a kan bin umarninSa da nisantar saɓo?" Sai wannan aya ta ce: "Lallai duk wata cutuwa da duk wata fa'ida tana komawa gare ku. Ku ne kuke hawa matakan kamala ta hanyar ayyukan ƙwarai, kamar yadda ku ne kuke faɗawa zuwa mafi ƙasƙancin matsayi sakamakon aikata zunubai da saɓo. Saboda haka, dukkan hukunce-hukuncen wajibai, aiko da Manzanni da saukar da littattafai, suna da wannan manufa mai girma.[11]
Falaloli Da Fa'idoji
Akwai falaloli da yawa kan karanta wannan sura:
- An rawaito daga Annabi (S.A.W) cewa duk wanda ya karanta Suratul Jasiya, to Allah zai rufe mishi sirrinshi kuma zai kwantar mishi da firgicinshi a ranar alƙiyama.[12]
- An rawaito daga Imam Sadiƙ (A.S) duk wanda ya karanta wannan sura, sakamakonshi shi ne ba zai ga wuta ba a ranar alƙiyama, kuma zai kasance tare da Annabi Muhammad (S.A.W).[13]
Akwa abubuwa da yawa da suka keɓanta da wannan sura:
- An rawaito daga Manzon Allah (S.A.W) duk wanda ya rubuta ta ya rataya a jikinshi, zai aminta daga zaluncin kowane Shaiɗan da duk wani mai ji da kai da Azzalumi mai girman kai, kuma zai zamo mai kwarjini da abin ƙauna ga duk wanda ya ganshi a cikin mutane.[14]
Bayanin kula
- ↑ Musawi, Al-Wadihu Fit Tafsir, juzu'i na 14, shafi na 350.
- ↑ Ɗabrisi, Majma'ul Bayan, juzu'i na 9, shafi na 172.
- ↑ Alusi, Ruhul Ma'ani, juzu'i na 25, shafi na 190.
- ↑ Khurramshahi, Mausu'at Qur'an Wad Dirasatul Qur'aniyya, juzu'i na 2, shafi 1250.
- ↑ Ma'arifat, At-Tamhid Fi Ulumil Qur'an, juzu'i na 1 shafi na 313.
- ↑ Ɗusi, Tafsir At-Tibyan, juzu'u na 10, shafi na 473.
- ↑ Ma'arifat, At-Tamhid Fi Ulumil Qur'an, juzu'i na 1, shafi na 169.
- ↑ Musawi, Al-Wadihu Fit Tafsir, juzu'i na 14, shafi na 351-378.
- ↑ Makarim Shirazi, Tafisr Al-Amsal, juzu'i na 16, shafi na 181, Ɗabaɗaba'i, Tafsir Almizan, juzu'i na 18, shafi 157.
- ↑ Suratul Jasiya: aya ta 15.
- ↑ Makarim Shirazi, Tafsir Al-Amsal, juzu'i na 16, shafi na 201
- ↑ Zamakhshari, Tafsir Al-Kashshaf, juzu'i na 4 shafi na 1484.
- ↑ Ɗabrisi, Jawami'ul Jami, juzu'i na 3, shafi na 331.
- ↑ Bahrani, Al-Burhan, juzu'i na 9, shafi na 19.
Nassoshi
- Qur'an Karim.
- Ɗabrisi, Fadlu Bin Hassan, Tafsiru Jawami'il Jami, Qom, Iran, Cibiyar Annashrul Islami ta Jama'atu Mudarrisin, bugu na 2, 1430H.
- Alusi, Mahmud Bin Abdullah, Ruhul Ma'ani fi Tafsiril Qur'anil Azim Was Sab'ul Masani, Beirut, Lebanon, Dar Ihya'it Turasil Arabi, bugu na 1, 1421H.
- Bahrani, Hashim Bin Sulaiman, Al-Burhan fi Tafsiril Qur'an, Beirut, Lebanon, Dar Ihya'it Turasil Arabi, bugu na 1, 1429H.
- Fakrur Razi, Muhammad Bin Umar, At-Tafsirul Kabir, Beirut, Lebanon, Darul Kutubil Ilmiyya, bugu na 4, 1434H.
- Khurramshahi, Bahaud-Din, Mausu'atul Qur'an Wad Dirasatul Qur'aniyya, Iran, Tehran, Cibiyar Al-Asdiƙa', 1377Sh.
- Ma'arifat, Muhammad Hadi, At-Tamhid Fi Ulumil Qur'an, Qom, Iran, Zawil Qurba, bugu na 1, 1428H.
- Makarim Shirazi, Nasir, Al-Amsal Fi Tafsiri Kitabillahil Munzal, Beirut, Lebanon, Cibiyar Al-Amira, bugu na 2, 1430H.
- Musawi, Abbas bin Ali, Al-Wadihu Fit Tafsir, Beirut, Lebanon, Cibiyar Al-Ghadir, bugu na 1, 1433H.
- Zamakhshari, Mahmud Bin Umar, Al-Kashshaf, Beirut, Lebanon, Dar Sadir, bugu na 1, 1431H.
- Ɗabaɗaba'i, Muhammad Husain, Almizan fi Tafsiril Qur'an, Qom, Iran, Darul Al-Mujtaba, bugu na 1, 1430H.
- Ɗabrisi, Fadlu Bin Hassan, Majma'ul Bayan fi Tafsiril Qur'an, Tehran, Iran, Darul Uswa, bugu na 1, 1426H.
- Ɗusi, Muhammad Bin Hassan, At-Tibyan fi Tafsiril Qur'an, Qom, Iran, Cibiyar Annashrul Islami, bugu na 1, 1431H.