Daƙiƙa:Suratul Hujurat
- Domin ganin kammalallen nassi na wannan shafi. ku duba: Nassin: Suratul Hujurat
Ƙaf Hujurat Suratul Fatahi | |
| Lambar Sura | 49 |
|---|---|
| Juzu'i | 26 |
| Jerantuwa Ta Sauka | 107 |
| Adadin Ayoyi | 18 |
| Adadin Kalmomi | 353 |
| Adadin Haruffa | 1533 |
| Makkiya/Madaniyya | Madaniyya |
Suratul Hujurat (Larabci: سورة الحجرات ) sura ce ta 49 cikin juzi'i na 26 a cikin ƙur'ani, kuma sura ce da ta sauka a Madina, an ciro sunanta daga aya ta huɗu a cikinta, tana magana kan hukunce-hukunce na addini, kamar ladabin bawa tsakaninshi da Allah maɗaukaki da tsakaninshi da Manzonsa (S.A.W) da kuma alaƙarshi da ɗan'adam irinshi, da bayani kan mutane a ɗai-ɗaiku, kazalika tana nuni kan haƙiƙanin imani da musulinci da ni'imar da Allah yake yiwa ɗan'adam daga hasken imani.
Daga cikin shahararrun ayoyinta akwai:
- Faɗin Allah cikin aya ta 6:Ya ku waɗanda suka yi imani! Idan wani mai fasikanci ya zo muku da wani labari, ku bincika shi da kyau, kada ku kai wa wani ƙungiya hari cikin jahilci, sai ku zama masu nadama a kan abin da kuka aikata
- Faɗin Allah cikin aya ta 10:Lalle muminai ƴan uwa ne. Ku gyara tsakanin ƴan uwanku, ku kuma ji tsoron Allah, domin ku sami rahama.
- Faɗin Allah cikin aya ta 12:Ya ku waɗanda suka yi imani! Ku guji yawancin zato, domin wasu zato zunubi ne. Kada ku yi leƙen asiri, kuma kada ku yi giba da juna. Shin wani daga cikinku yana son ya ci naman ɗan’uwansa matacce? Lalle za ku ƙi shi. Ku ji tsoron Allah, lalle Allah Mai karɓar tuba ne, Mai jin ƙai>
- Faɗin Allah cikin aya ta 13:Ya ku mutane! Lalle Mu ne muka halicce ku daga namiji da mace, muka kuma sanya ku al’ummomi da kabilu domin ku san juna. Lalle mafi karamcin ku a wurin Allah shi ne wanda ya fi tsoron Allah. Lalle Allah Mai sani ne, Mai labari.
Ruwayoyi da yawa sun zo kan falalar karanta wannan sura, daga ciki akwai abin da aka rawaito daga Imam Sadiƙ (A.S) cewa duk wanda ya karanta wannan sura ko wace rana ko dare zai sami rabauta da shiga cikin waɗanda suka ziyarci Muhammad (S.A.W).
Sanya Mata Suna Da Kuma Ayoyinta
Wannan sura ana kiranta da Hujurat, saboda zuwan wannan kalma cikin aya ta 4, inda take cewa: Lalle waɗanda suke kiran ka daga bayan dakunan (Annabi), mafi yawansu ba su da hankali.
Hujurat jam'i ne na Hujura, abin da ake nufi da su shi ne ɗakunan matan Annabi (S.A.W)[1] kuma ayoyinta 18 ne tana da kalmomia 353 da haruffa 1533 tana cikin surori Mufassalat hakan yana nufin surori gajeru da ayoyi da yawa[2] kuma tana daga surori mumtahanat.[3]
Jerantuwa Ta Sauka
Wannan sura tana cikin surorin da suka sauka a Madina a wurin Annabi (S.A.W)[4] bisa jerin sauka ita ce ta 107 amma cikin ƙur'ani tana cikin juzi'i na 26, sannan ita ce ta 49 cikin surorin ƙur'ani.[5]
Ma'anar Kalmominta
Kalmar (لَعَنِتُّمْ) tana nufin wahala mai tsanani. Kalmar (بَغَتْ) tana nufin zalinci da ƙeta iyaka wajan zalinci. Kalmar (يَغْتَب) tana nufin ambaton mumini da aibu a bayan idonshi ko yayin da bayanan. Kalmar (الأَعْرَابُ) tana nufin mazauna ƙauye waɗanda ba suyi karatun addini ba.[6]
Abin da Yake Cikinta
Wannan sura tana ɗauke da wasu mas'aloli na shari'a waɗanda da su ne mutum zai sami tsira da shi ne kuma zamantakewar al'umma za ta yi kyau, daga cikin abin da ke cikin wannan sura akwai; ladabi tsakanin bawa da Allah da tsakaninshi da manzonsa, kamar yadda ya zo cikin ayoyi biyar na farkon surar, daga ciki akwai abin da ya shafi mutum tsakaninshi da ɗan uwanshi mutum, sakamako rayuwa guri guda, daga ciki akwai abin da yake bayyana ɗaukakar wasu mutane kan wasu, wannan yana daga cikin abin da yake tsara rayuwar zamantakewa kuma ya nusar da mutum zuwa rayuwa ta gari da bambance addini na gaskiya da naƙarya, duk wannan bisa sunna da dokokin zaman takewa, kuma surar tana ƙarƙarewa da nusar da mutane kan imani na gaskiya da Muslunci da ni'imar Allah wacce yake yi ma al'umma saboda hasken imani.[7]
Shahararrun Ayoyinta
Ayar Naba'i
Faɗar Allah maɗakaki:Ya ku waɗanda suka yi imani! Idan wani fasiƙi ya zo muku da wani labari, ku bincika shi da kyau, kada ku kai wa wani ƙungiya hari cikin jahilci, sai ku zama masu nadama a kan abin da kuka aikata.[8] ya zo cikin litattafai na tafsiri cewa wannan ayar ta sauka ne kan Walid Bin Uƙba ɗan Abi Ma'aɗiyya, Manzon Allah (S.A.W) ya aikeshi ya karɓo zakka daga ƙabilar Banu Musɗalaƙ, sai suka fito suna tarbarshi cikin farin ciki, amma da yake a akwai adawa a tsakaninsu a lokacin jahiliyya, to shi kuma sai ya yi tinanin suna so su kashe shi ne, kawai sai ya koma gurin Annabi (S.A.W) ba tare da ya aiwatar abin da aka umarce shi ba, sai ya cewa Annabi sun hana zakka, alhalin abin ba haka ba ne, sai Annabi ya yi fishi, har abin ya kai ga ya yi shirin yaƙarsu, sai wannan ayar ta sauka.[9]
Ayar Ƴan uwantaka
Faɗar Allah maɗaukaki: Lalle muminai ƴan uwa ne. Ku gyara tsakanin ƴan uwanku, ku kuma ji tsoron Allah, domin ku sami rahama.[10] ya zo cikin litattafan tafsiri cewa Annabi (S.A.W) ya haɗa ƴan uwantaka tsakanin Musulmi, sai ya haɗa Abubakar da Umar, Usman da Abdur-Rahman, kowa da dai-daishi har sai da ya haɗa kowa da abokin haɗinshi cikin dukkan sahabbansa, sannan sai ya cewa Ali (A.S) kai ɗan'uwanane ni kuma ɗan'uwanka ne.[11]
Ayar Giba
Faɗar Allah maɗaukaki:Ya ku waɗanda suka yi imani! Ku guji yawancin zato, domin wasu zato zunubi ne. Kada ku yi leƙen asiri, kuma kada ku yi giba da juna. Shin wani daga cikinku yana son ya ci naman ɗan’uwansa matacce? Lalle za ku ƙi shi. Ku ji tsoron Allah, lalle Allah Mai karɓar tuba ne, Mai jin ƙai.[12] Ya zo a litattafan tafsiri cewa a wannan ayoyi guda uku akwai mas'aloli guda uku na aklaƙ: nisantar munana zato da tajassusi (leƙa asirin wani) da yin giba (Gulma), waɗannan abubuwa guda uku suna da alaƙa da juna, saboda shi munata zato yana kai mutum da ya leƙa asirin wani, da giba shi kuma leƙa asirin wani yana kai ga tuna mishi asiri alhalin da abin ya ɓuya ga mutane, to idan suka sami sirrinshi, to hakanne zai kaisu da yin giba, saboda haka Muslunci yake hannasu gaba ɗaya.[13]
Tsoron Allah Shine Ma'auni
Faɗar Allah maɗaukaki:Ya ku mutane! Lalle Mu ne muka halicce ku daga namiji da mace, muka kuma sanya ku al’ummomi da kabilu domin ku san juna. Lalle mafi karamcin ku a wurin Allah shi ne wanda ya fi tsoron Allah. Lalle Allah Mai sani ne, Mai labari.[14] Ya zo a litattafan tafsiri cewa, wannan aya tana magana da dukkan mutane, kuma tana bayyana abin da ya fi muhimmanci wajan tabbar da tsari da tsayuwa cikin al'umma, ƙur'ani ya yi watsi da wurgi da babban ma'auni na yin alfahari a lokacin jahiliyya, yana fatali da nuna fifiko cikin nasabar mutum da ƙabilarshi, sai ƙur'ani ya ce, wannan ba ma'auni bane ba, ma'auni na gaskiya shi ne tsoron Allah.[15]
Falala Da Hususiyar Wannan Sura
Akwai falaloli da yawa idan mutum ya karanta wannan sura:
- An rawaito daga Annabi (S.A.W) cewa duk wanda ya karanta suratul Hujurat, za a ba shi lada yawan duk wanda ya bi Allah da lada addadin wanda ya saɓamashi.[16]
- An rawaito daga Imam Sadiƙ (A.S) cewa duk wanda ya karanta wannan sura a ko wace rana ko dare, za a yi la'akarinshi cikin waɗanda suka ziyarci Muhammad (S.A.W).[17]
Abubuwan da suka keɓanta da wannan sura sun zo cikin ruwaya kamar haka:
- An rawaito daga Imam Sadiƙ (A.S) duk wanda ya rubuta wannan sura ya yi laya da ita ya rataya kan wanda ake bi (Shugaba ko jagora) , to zai aminta daga Shaiɗancinsa, ba zai zo mishi ba, kuma zai aminta daga duk abin da ake tsoro, idan mace mai ƙarancin nono ta rubuta tasha, zata sami ruwan nono bayan rashin zuwanshi, kuma za a kiyaye jaririnta kuma ita ma zata zamo cikin aminci daga duk abin da ake tsoro da yardar Allah[18]
Bayanin kula
- ↑ Al‑Musawi, Al‑Wadih fi al‑Tafsir, Juzu’i na 15, shafi na 69–71.
- ↑ Al‑Kharmashahi, Mausu’at al‑Qur’an wa al‑Buhuth, Juzu’i na 2, shafi na 1252.
- ↑ Maʿrifa, Al‑Tamheed fi ʿUlum al‑Qur’an, Juzu’i na 1, shafi na 313
- ↑ Al‑Tusi, Tafsirin al‑Tibyan, Juzu’i na 10, shafi na 572; Al‑Razi, Al‑Tafsīr al‑Kabīr, Juzu’i na 28, shafi na 95
- ↑ Maʿrifa, ʿUlum al‑Qur’an (Ilimin Qur’ani), Juzu’i na 2, shafi na 166
- ↑ Al‑Musawi, Al‑Wadih fi al‑Tafsir, Juzu’i na 15, shafuka 81–98
- ↑ Al‑Tabataba’i, Tafsirin al‑Mizan, Juzu’i na 18, shafi na 309
- ↑ Suratul al‑Ḥujurāt, aya ta 6
- ↑ Al‑Tabrasi, Majmaʿ al‑Bayān, Juzu’i na 9, shafuka 323–324.
- ↑ Surat al‑Ḥujurāt, aya ta 10
- ↑ Al‑Bahrani, Tafsirin al‑Burhān, Juzu’i na 9, shafi na 86
- ↑ Surat al‑Ḥujurāt, aya ta 12
- ↑ “Makarem al‑Shirazi, Tafsirin al‑Amthal, Juzu’i na 16, shafuka 548–55
- ↑ Surat al‑Ḥujurāt, aya ta 13
- ↑ “Al‑Alusi, Ruh al‑Maʿani, Juzu’i na 26, shafuka 435–436; Mughniya, Tafsirul al‑Kashif
- ↑ Al‑Zamakhshari, Tafsirul al‑Kashshaf, Juzu’i na 4, shafi na 1537
- ↑ Al‑Tabrasi, Jawāmiʿ al‑Jāmi
- ↑ Al‑Bahrani, Tafsirin al‑Burhān, Juzu’i na 9, shafi na 79.
Sadarwa Ta Waje
Nassoshi
- AlKur’ani Mai Tsarki
- Alusi, Mahmud bn Abdullahi, Ruh al‑Ma’ani fi Tafsiril Qur’anil Azim was‑Sab’ul Mathani, Beirut – Lebanon, Dar Ihya’ at‑Turath al‑Arabi, bugu na 1, 1421 H.
- Bahrani, Hashim bn Sulayman, al‑Burhan fi Tafsiril Qur’an, Beirut – Lebanon, Dar Ihya’ at‑Turath al‑Arabi, bugu na 1, 1429 H.
- Khurramshahi, Baha’uddin, Mawsu’atul Qur’an wad‑Dirasat al‑Qur’aniyya, Iran – Tehran, Mu’assasat al‑Asdiqa’, 1377 Sh.
- Makarem Shirazi, Naser, al‑Amthal fi Tafsīr Kitabillahil Munazzal
- Ma’rifa, Muhammad Hadi, Tadrīs al‑‘Ulūm al‑Qur’aniyya, tarjama: Abu Muhammad Faqili, Dar Nashr ad‑Da’wa al‑Islamiyya, 1371 Sh.
- Ma’rifa, Muhammad Hadi, at‑Tamheed fi ‘Ulūm al‑Qur’an, Qum – Iran, Dhawi al‑Qurba, bugu na 1, 1428 H.
- Mughniya, Muhammad Jawad, Tafsīr al‑Kāshif, Beirut – Lebanon, Dar al‑Anwar, bugu na 4, ba tare da shekara ba.
- Musawi, Abbas bn Ali, al‑Wadih fi at‑Tafsīr, Beirut – Lebanon, Markaz al‑Ghadir, bugu na 1, 1433 H.
- Razi, Muhammad bn Umar, at‑Tafsīr al‑Kabīr, Beirut – Lebanon, Dar al‑Kutub al‑‘Ilmiyya, bugu na 4, 1434 H.
- Tabataba’i, Muhammad Husayn, al‑Mizan fi Tafsiril Qur’an, Qum – Iran, Dar al‑Mujtaba, bugu na 1, 1430 H.
- Tabrasi, al‑Fadl bn al‑Hasan, Majma’ al‑Bayān, Tehran – Iran, Dar al‑Uswa, bugu na 1, 1426 H.
- Tabrasi, al‑Fadl bn al‑Hasan, Tafsīr Jawāmi’ al‑Jāmi’, Qum – Iran, Mu’assasat an‑Nashr al‑Islami, bugu na 2, 1430 H.
- Tusi, Muhammad bn al‑Hasan, at‑Tibyān fi Tafsiril Qur’an, Qum – Iran, Mu’assasat an‑Nashr al‑Islami, bugu na 1, 1431 H.
- Zamakhshari, Mahmud bn Umar, al‑Kashshaf, Beirut – Lebanon, Dar Sader, bugu na 1, 1431 H.