Jump to content

Daƙiƙa:Ruƙayya Ƴar Imam Husaini (A.S)

Daga wikishia

Don sauran ma'anoni, duba shafin Ruƙayya (Bambancewa).

Ruƙayya Ƴar Imam Husaini (A.S)
Haramin Sayyida Ruƙayya, Dimashƙa, Siriya
Haramin Sayyida Ruƙayya, Dimashƙa, Siriya
GudummawaTa halarci Waƙi'ar Karbala•kuma tana cikin fursunonin Karbala
Rasuwa5 ga watan Safar shekara ta 61 Hijira ƙamari a Sham
MahaifiImam Husaini (A.S)
Tsawon rayuwaShekara uku
Fitattun Ƴaƴan Imamai
Abbas Bin Ali•Zainabul Kubra•Sayyida Faɗima Ma'asuma (A.S)•Sayyid Muhammad•Shahcerag•Sayyida Nafisa•


Ruƙayya ƙaramar ƴar Imam Husaini (A.S) ce. An ce ta halarci Waki'ar Karbala, kuma an tafi da ita zuwa Sham tare da Fursunonin Karbala, inda ta rasu a Kangon Sham. Akwai saɓanin ra'ayi game da ko Imam Husaini (A.S) yana da irin wannan ƴa, da kuma sunanta da wurin da ake danganta kabarinta da shi. An bayyana cewa ba a ambaci sunan Ruƙayya a cikin tsofaffin madogara a jerin ƴaƴan Imam Husaini (A.S) ba. Duk da haka, wasu Maraji'an Taƙlidi Na Shi'a, kamar Mirza Jawad Tabrizi, Nasir Makarim Shirazi, Husaini Nuri Hamadani, Sayyid Muhammad Ali Alawi Gurgani da Husaini Mazahiri, sun tabbatar da samuwar Sayyida Ruƙayya, shahadarta a Kangon Sham da kuma kasancewar kabarinta a Sham.

An ce littafi na farko da ya kawo labarin shahadar Ruƙayya a Sham shi ne Kamil Bahayi, wanda Imadud-Din Ɗabari (ya rasu a shekara ta 700H/1281M) ya rubuta. A cikin littafin, an ambaci labarin wata ƴar Imam Husaini (A.S) mai shekara huɗu a Sham, ba tare da an bayyana sunanta ba. A cikin madogara da aka rubuta daga baya, an ambaci sunayen wannan ƙaramar yarinya da suka haɗa da Ruƙayya, Zainab, Faɗima da Zubaida.

A birnin Dimashƙa, akwai wani wurin ziyara da ake dangantawa da Sayyida Ruƙayya. Bayan Haramin Sayyida Zainab (A.S), shi ne wurin ziyara na biyu da ƴan Shi'a suke mai da hankali da kulawa a wannan birni. A tsakanin ƴan Shi'a a Iran, an sanya daren da kuma ranar uku ga watan Muharram a matsayin ranar Ruƙayya, kuma ana yin zaman makoki domin tunawa da ita.

Suna Da Nasaba

Ana lissafa Ruƙayya cikin ƴaƴan Imam Husaini (A.S), Imami na uku a wajen Shi'a. Amma a cikin Daneshname Imam Husain (A.S) (Kundin bayanai game da Imam Husain), an bayyana cewa tsofaffin majiyoyi masu inganci da suka kawo sunayen ƴaƴan Imam Husaini (A.S) ba su ambaci wata ƴa tasa ba mai suna Ruƙayya. Sun ambaci ƴaƴansa mata biyu ne kawai: Sukaina da Faɗima. Wasu kuma sun ambaci wata ƴa ta uku mai suna Zainab.[1] Misali, Shaikh Mufid ya ambaci Sukaina da Faɗima kawai a matsayin ƴaƴan Imam Husaini (A.S).[2]

Bisa binciken marubutan Daneshname Imam Husain (A.S), mutum guda ne kawai ya ambaci cewa Imam Husaini (A.S) yana da ƴaƴa mata huɗu. Wannan mutumin shi ne Ibn Funduƙ Baihaƙi, shahararren masani a ilimin nasaba wanda ya rayu ƙarni na shida bayan Hijira.[3]

A cikin littafinsa Lubabul Ansab, Ibn Funduƙ ya ambaci ƴaƴan Imam Husaini (A.S) mata huɗu da sunayensu: Faɗima, Sukaina, Zainab da Ummu Kulsum. Ya kuma ƙara da cewa Zainab da Ummu Kulsum sun rasu tun suna ƙanana. [4] A wani wuri cikin littafinsa kuma, ya rubuta cewa daga cikin ƴaƴan Imam Husaini (A.S), babu wanda ya tsira sai Zainul Abidin, Faɗima, Sukaina da Ruƙayya.[5]

Muhammad Bin Ɗalha malamin Shafi'iyya (ya rasu a shekara ta 652H/1254M), a cikin littafinsa Maɗalibus Sa'ul,[6] da Ali BinIsa Irbili, a cikin littafinsa Kashful Ghumma,[7] sun bayyana cewa Imam Husaini (A.S) yana da ƴaƴa mata huɗu. Sai dai sun ambaci sunayen Zainab, Sukaina da Faɗima kawai, ba tare da bayyana sunan ƴa ta huɗun ba.

Najmud-Din Ɗabasi ya yi amfani da bayanan Ibn Funduƙ da Muhammad Bin Ɗalha wajen fahimtar cewa sunan ƴa ta huɗun ta Imam Husaini (A.S) shi ne Ruƙayya, yayin da Ummu Kulsum ya kasance Alkunya (sunan girmamawa) nata.[8] Sai dai marubutanDaneshname Imam Husain (A.S), sun nuna shakku kan wannan fahimta.[9]

Wasu daga cikin majiyoyin baya-bayan nan sun bayyana cewa Ruƙayya laƙabi ne na ɗaya daga cikin ƴaƴan Imam Husaini (A.S), [10] yayin da ainihin sunanta yake Zainab,[11] ko Faɗima.[12]

Ba a ambaci sunan mahaifiyar Ruƙayya a cikin litattafan tarihi ba.[13] Sai dai wasu masu bincike na wannan zamani sun ce mahaifiyarta ita ce Ummu Is'haƙ, ƴar Ɗalha. [14]


  1. ↑ Muhammadi Rai Shahri, Daneshname Imam Husain (A.S), juzu'i na 1, shafi na 382.
  2. ↑ Shaikh Mufid, Al-Irshad, juzu'i na 2, shafi na 135.
  3. ↑ Muhammadi Rai Shahri, Daneshname Imam Husain (A.S), juzu'i na 1, shafi na 382.
  4. ↑ Ibn Funduƙ, Lubabul Ansab, shafi na 350.
  5. ↑ Ibn Funduƙ, Lubabul Ansab, shafi na 355.
  6. ↑ Shafi'i, Maɗalibus Sa'ul shafi na 257.
  7. ↑ Irbili, Kashful Ghumma, juzu'i na 2, shafi na 38.
  8. ↑ Ɗabasi, Ruƙayya Bintul Husain, shafi na 8-9.
  9. ↑ Muhammadi Rai Shahri, Daneshname Imam Husain (A.S), juzu'i na 1, shafi na 383.
  10. ↑ Ƙa'idan, Amakine Ziyarati Siyahati Suriye, shafi na 57; Muƙaddas, Rahnamaye Amakine Ziyarti Dar Keshware Suriye, shafi na 117.
  11. ↑ Ƙa'idan, Amakine Ziyarati Siyahati Suriye, shafi na 57
  12. ↑ Muƙaddas, Rahnamaye Amakine Ziyarti Dar Keshware Suriye, shafi na 117.
  13. ↑ Waridi, Ruzshomare Tarikhe Islam, juzu'i na 2, shafi na 66.
  14. ↑ Hadi Manesh، پژوهشی-در-هویت» -تاریخی-حضرت-رقیه-علیهاا/ پژوهشی در هویت تاریخی حضرت رقیه (علیهاالسلام)»، Gidauniya mai cikakken bayani da sanarwa Imamat.