Daƙiƙa:Kullu Yaumin Ashura
Kullu yaumin ashura wa kullu ardin Karbala (Larabci: کُلُّ یَومٍ عاشوراء و کُلُّ أرضٍ کَربَلاء) ko wace rana Ashura ce kuma ko wace ƙasa ma Karbala ce, wata shahararriyar jumla ce da ake jinginawa Imam Sadiƙ (A.S), wasu jama'a daga malaman addini suna amfani da wannan jumla cikin maganganu da bayanansu. Tare da haka masana masu zurfafa bincike sun ce wannan jumla babu inda ta zo cikin madogaran hadisi na Shi'a.
A cewar Imam Khomaini, wannan jumla tana bayanin wajabcin yaƙar zalunci a kodayaushe. Murtada Muɗahhari, ya bayyana cewa wannan jumla tana nuni da ci gaba da gwagwarmaya da zalunci da kuma raya gaskiya da kuma raya gaskiya a a tsawon tarihi, Sayyid Ali Khamna'i ya yi bayani a fili da cewa idan mutane a cikin ko wane zamani suka taka rawar da ya kamata, komai zai daidaita.
Taƙaitaccen Tarihi
Ba a san takaimaiman lokaci da madogara da aka fara bayanin wannan jumla ba, amma Muhammad Bin Sa'id Sanhaji Busiri (Rasuwa:694H) shi ne mutum na farko da ya fara gabatar da jumlar (Ko wace rana Ashura ce kuma ko wace ƙasa ma Karbala ce) a cikin ƙasidarsa mai suna Hamziya.[1] Haka nan, a cikin wani baiti na ƙasidar Ra'iyya ta Abdul-Husaini A'asam (Rasuwa:1247H) yana ishara da wannan ma'ana inda yake cewa: (Kai kace ko wane wuri ma Karbala ne a idona/kuma ko wane zamani ma ranar Ashura ce).[2]
Haka nan Ali Shari'ati (Rayuwa:1933 – 1977M) a cikin littafin Husaini Warisu Adam, ya jingina wannan jumla zuwa ga Imam Sadiƙ (A.S).[3] Ƙari kan haka, wannan jumla an yi amfani da ita cikin bayanan malaman addini, Imam Khomaini a cikin laccoci da saƙonninsa ya yi amfani da wannan jumla,[4] Haka Sayyid Ali Khamna'i, ba tare da la'akari da ita a matsayin hadisi ba, ya yi ishara zuwa ga wannan jumla.[5] Murtada Muɗahhari shi ma (Ba tare da ishara zuwa ga kasancewar ta hadisi ba ko rashin kasancewar ta ba) a cikin nazarin wannan magana ta cewa Imam Husaini (A.S) ya yi yaƙi ne domin farfaɗo da tunanin Musulunci, kuma ya samu dama da nasarar raya wannan tunani a faɗin duniya, ya bayyana cewa a tsawon shekaru 1300 ne juyin juya halin Imam Husaini yake samun sabbin nasarori, ma'ana ko wace shekara Ashura ce, ma'anar (Kullu Yaumin Ashura) shi ne ko wace rana da sunan Imam Husaini ana yaƙi da zalunci da ƙarya, kuma ana farfaɗo da gaskiya.[6]
Madogara
Muhammad Sihati Sardarudi, marubucin abubuwan da suka shafi Imam Husaini (A.S), yana da ra'ayin cewa jumlar "Kullu Yaumin Ashura Wa Kullu Ardin Karbala" ba wai kaɗai babu ita cikin hadisai ba, bari ma dai tama saɓa da aƙidun shi'anci, saboda babu wata ƙasa da ta kai ƙimar kasar Karbala kuma babu wata rana da za a kwatanta da ranar Ashura.[7] Da wannan dalili ne yake tsammani cewa asalin wannan jumla daga Zaidiyya ta fito.[8]
Tafsiri
Imam Khomaini cikin maganganunsa ya bayyana cewa "Kullu Yaumin Ashura Wa Kullu Ardin Karbala" ba ta nuni da larurar kuka kan musibun Imam Husaini (A.S) a kodayaushe, bari dai ya yi imani wannan jumla tana bayanin wajabcin ci gaba da gwagwarmaya da zalunci a kodayaushe.[9] Haka nan, Murtada Muɗahhari cikin bayyana nasara ta haƙiƙa ta Imam Husaini (A.S) cikin yunƙurin Ashura, yana cewa wannan yunƙuri a kodayaushe yana halin samun sabbin nasarori kuma ma'anar "Kullu Yaumin Ashura" shi ne ko wace rana da sunan Imam Husaini (A.S) ana yaƙi da zalunci da ƙarya da kuma farfaɗo da gaskiya da adalci.[10] Sayyid Ali Khamna'i shima ya fassara wannan jumla kamar haka "A ko wane zamani akwai nauyi da yake wuyan mutane idan har mutane suka sauke wannan nauyi ta hanyar da ta dace a lokacin da ya dace, komai da komai zai daidaitu, al'umma za su samu bunƙasa, ƴan adamtaka za ta yaɗu"[11]
Maƙaloli Masu Alaƙa
Bayanin kula
- ↑ Al-Ash'ari al-Qatifi, Al-Rasa'il al-Ahmadiyya, 1419 AH / 1998-99 CE, Juzu'i na 2, Shafi na 273; Al-Amin, A'yan al-Shi'a, edited by Hassan Al-Amin, Juzu'i na 1, Shafi na 652..
- ↑ Shubbar, Adab al-Taff, 1409 AH / 1988-89 CE, Juzu'i na 1, Shafi na 12.
- ↑ Shari'ati, Husain Waarith-i Adam, 1380 SH / 2001-02 CE, Shafi na 49.
- ↑ Imam Khomeini, Sahifeh-ye Imam, 1389 SH / 2010-11 CE, Juzu'i na 9, Shafi na 445; Juzu'i na 10, Shafi na 10, 122, 191, 315; Juzu'i na 16, Shafi na 151.
- ↑ «بیانات در مراسم مشترک دانشآموختگی دانشجویان دانشگاه امام حسین(ع)»،Shafin yada labarai na Ayatullah Khamenei.
- ↑ Mutahhari, Haqq wa Batil (Majmu'a Athar, Juzu'i na 3), 1375 SH / 1996-97 CE, Shafi na 434-435.
- ↑ Sehati Sardrudi, "Chand Hadith Ma'ruf Darbarah-ye Ashura", Shafi na 136-137.
- ↑ Sehati Sardrudi, "Chand Hadith Ma'ruf Darbarah-ye Ashura", Shafi na 137.
- ↑ Sehati Sardrudi, "Chand Hadith Ma'ruf Darbarah-ye Ashura", Shafi na 137.
- ↑ Mutahhari, Haqq wa Batil (Majmu'a Athar, Juzu'i na 3), 1375 SH / 1996-97 CE, Shafi na 434-435.
- ↑ «بیانات در مراسم مشترک دانش آموختگی دانشجویان دانشگاه امام حسین(ع)»،Shafin yada labarai na Ayatullah Khamenei.
Nassoshi
- Amin, Sayyid Muhsin, A'yan al-Shi'a, edited by Hassan Amin, Beirut, Dar al-Ta'aruf lil-Matbu'at, Babu kwanan wata.
- Imam Khomeini, Sayyid Ruhullah, Sahifeh-ye Imam, Tehran, Mu'assasah-yi Tanzim wa Nashr-i Athar-i Imam Khomeini, 1389 SH / 2010-11 CE.
- Kotifi, Ahmed Al Taan, Al-Rasa'il al-Ahmadiyya, edited by Dar al-Mustafa (SAW) li-Ihya' al-Turath, Qom, Dar al-Mustafa li-Ihya' al-Turath, 1419 AH / 1998-99 CE.
- Mutahhari, Murtadha, Nabard-i Haqq wa Batil (a cikin Majmu'a Athar, Juzu'i na 3), Tehran, Intisharat-i Sadra, 1375 SH / 1996-97M.
- Sahhati Sardarudi, Muhammad,«بازخوانیِ چند حدیث مشهور درباره عاشورا»،A cikin Mujallar Ulumul Hadisi (Majallat-e ‘Ulum-e Hadith), lamba ta 26.
- Shari'ati, Ali, Husain Waarith-i Adam (a cikin Majmu'a Athar, lamba 19), Tehran, Intisharat-i Qalam, 1380 SH / 2001-02 CE.
- Shubbar, Jawad, Adab al-Taff, Beirut, Dar al-Murtada, 1409 AH / 1988-89 CE.
- «بیانات در مراسم مشترک دانشآموختگی دانشجویان دانشگاه امام حسین(ع)»،Shafin yada labarai na Ayatullah Khamenei.