Daƙiƙa:Jalsatul Istiraha
Jalsatul Istiraha ko Jilsat al-Istiraha shi ne zaman da mai salla yake yi cikin natsuwa bayan sujjada ta biyu, kafin ya tashi tsaye zuwa raka'a ta gaba, a raka'o'in da ba a yin tashahhudi.[1]
Wasu daga cikin malaman fikihu, irin su Allama Hilli da Sahibul Jawahir, sun bayyana cewa yin wannan zaman mustahabbi ne (abin so) a cikin sallah, kuma wannan shi ne mashahurin ra'ayi a tsakanin malaman Shi'a.[2] Sai dai Sayyid Murtada ya yi hukuncin cewa, bisa ga ijma'i da kuma ƙa'idar ihtiyaɗi ( Yin taka-tsantsan), yin zaman hutun wajibi ne.[3] Haka kuma, Sayyid Muhammad Kazim Ɗabaɗaba'i Yazdi a cikin littafinsa Al-Urwatul Wusƙa ya bayyana cewa yin wannan zaman ya dace a yi shi bisa ihtiyaɗi, har ma ya nuna cewa yiwuwar wajibcinsa tana da ƙarfi.[4] Amma Allama Hilli, malamin fikihu na ƙarni na takwas Hijira, ya ƙalubalanci ra'ayin wajibci, yana jingina da ruwayoyi da kuma ƙa'idar bara'a (wato asalin rashin ɗaukar nauyin hukunci har sai hujja ta tabbata).[5]
Dangane da fatawowin wasu manyan maraji'an taƙlidi na Shi'a na ƙarni na goma sha huɗu Hijirar Shamsi, wasu sun ɗauki yin zaman hutun a matsayin ihtiyaɗi na wajibi, yayin da wasu suka ɗauke shi a matsayin ihtiyaɗi na mustahabbi.[6]
A ra'ayin Imam Khomaini, Sayyid Muhammad Rida Gulfaigani, Luɗfullah Safi Gulfaigani, Sayyid Ali Sistani, da Husaini Nuri Hamadani, yin zaman hutun yana cikin ihtiyaɗi na wajibi.[7]
Amma malamai irin su Sayyid Abul Ƙasim Khuyi, Mirza Jawad Tabrizi, Muhammad Fadil Lankarani, Muhammad Taƙi Bahjat, Nasir Makarim Shirazi, da Sayyid Musa Shubairi Zanjani suna ganin yin wannan zaman yana cikin ihtiyaɗi na mustahabbi.[8]
A cikin littattafan fiƙihu kuma an bayyana cewa, yayin zaman hutun, tawarruk ga maza abu ne mustahabbi,[9] yayin da ga mata ake son su yi tarabbu'i.[10] Wasu malaman kuma sun ce wannan hukunci ya shafi maza da mata baki ɗaya.[11]
Malamai sun bambanta wajen fassara ma'anar tarabbu'i; wasu sun ce yana nufin zama kafa huɗu (gicciye ƙafafu), wasu kuma sun ce yana nufin zama a kan gwiwoyi biyu.[12]
Haka kuma, a lokacin zaman hutun, iq'a'u an ɗauke shi a matsayin makruhi.[13] Iqa'a'u wani irin zama ne da mutum yake shimfiɗa saman ƙafafunsa a ƙasa, sannan ya zauna a kan diddigen ƙafafunsa.[14]
Bayanin kula
- ↑ Najafi, Jawahirul Kalam, juzu’i na 5, shafi na 466.
- ↑ Allama Hilli, Mukhtalafush Shi‘a, juzu’i na 2, shafi na 171; Najafi, Jawahirul Kalam, juzu’i na 5, shafi na 466.
- ↑ Sayyid Murtada, Al-Intisar, juzu’i na 1, shafi na 312.
- ↑ Tabataba’i Yazdi, Al-Urwtul al-Wusƙa, juzu’i na 2, shafi na 576.
- ↑ Allama Hilli, Mukhtalafush Shi‘a, juzu’i na 2, shafi na 172.
- ↑ Bani Hashimi Khomaini, Risalat Tawdhih al-Masa’il Maraji, juzu’i na 1, shafi na 584.
- ↑ Bani Hashimi Khomaini da Usuli, Risalat Tawdhih al-Masa’il Maraji, juzu’i na 1, shafi na 584.
- ↑ Bani Hashimi Khomaini da Usuli, Risalat Tawdhih al-Masa’il Maraji, juzu’i na 1, shafi na 584.
- ↑ Najafi, Jawahirul Kalam, juzu’i na 5, shafi na 463.
- ↑ Najafi, Jawahirul Kalam, juzu’i na 5, shafi na 463.
- ↑ Khuyi, Al-Mustanad, juzu’i na 14, shafi na 261.
- ↑ Mu’assase Da’irat al-Ma’arif Fiqh Islami, Farhang-e Fiqh Farsi, juzu’i na 2, shafi na 436–437.
- ↑ Tabataba’i Yazdi, Al-Urwatul al-Wusƙa, juzu’i na 2, shafi na 575.
- ↑ Mu’assase Da’irat al-Ma’arif Fiqh Islami, Farhang-e Fiqh Farsi, juzu’i na 1, shafi na 656.
Nassoshi
- Allama Hilli, Hassan Bin Yusuf, Mukhtalafush Shi’a fi Ahkam ash-Shari’a, Qum, Ofishin Wallafe-wallafen Musulunci mai alaƙa da Jama’at al-Mudarrisin na Hauzar Ilmi ta Qum, 1413H/1992M.
- Bani Hashimi Khomaini, Muhammad Hassan da Ihsan Usuli, Tawdih al-Masa’il Maraji’ (Mutabiƙ ba Fatwoyin Sizada Nafar az Maraji'a-ye Mu'azzam-e Taƙlid), Qum, fishin Wallafe-wallafen Musulunci, 1392Sh..
- Khuyi, Sayyid Abul Ƙasim, Al-Mustanad fi Sharh al-Urwatul Wusƙa, bincike: Murtadha Burujerdi, Qum, Cibiyar Ihya Athar al-Imam al-Khuyi, 1421H/2000M.
- Mu’assase Da’irat al-Ma’arif Fiqh al-Islami, Farhang-e Fiqh-e Farsi, Qum, Cibiyar Da'irar Ma'arifin Fikihun Musulunci, 1382Sh/2003M.
- Najafi, Muhammad Hassan bin Baƙir, Jawahirul Kalam fi Sharh Shara’i al-Islam, binciken Cibiyar Da'irar Ma'arifin Fikihun Musulunci bisa Mazhabar Ahlul Baiti (AS), Qum, cibiyar Da'irar Ma'arifin Fikihun Musulunci bisa Mazhabar Ahlul Baiti (AS), 1421H/2000M.
- Sayyid Murtada, Ali bin Husain, Al-Intisar Lima Infaradat Bihi al-Imamiyya, bincike: Husain Musawi Burujerdi, Mashhad, Majma’ al-Buhuth al-Islamiyya, 1441H/2019M.
- Ɗabaɗaba’i Yazdi, Sayyid Muhammad Kazim, Al-Urwatul Wutsƙa, Qum,Cibiyar wallafe-wallafen Musulunci, 1419H/1998M.