Jump to content

Tawarruk

Daga wikishia
Halin Tawwarrul a sallah

Tawarruk, (Larabci: التورك) yana daga cikin ladubban sallah a fiƙihun Shi'a, wanda yake nuni ga wani tsari da hanya ta musamman na zama wanda cikinsa mai sallah yake zama kan cinyar hagunsa, sannan ya ɗora ƙafar damansa a kan tafin ƙafar hagunsa[1] Malaman fiƙihu suna ɗaukar yin wanan aiki cikin tashahhud (Tahiyya)[2] da tsakanin sujjada biyu,[3] a matsayin mustahabbi. Na'am a ra'ayin Sahibul Jawahir wannan mustahabbi ya keɓantu ne da maza kawai ba ya haɗawa da mata.[4]

Bisa wata riwaya, wannan tsari na zama da ake yinsa a cikin sallah Imam Sadiƙ (A.S) ya aikata shi, yayin da Hammad Bin Isa ya tambaye shi game da ƙyamar (Makaruhanci) yin haka, ya danganta ƙyamar yin hakan ga Banu Isra'il.[5]

Abdullahi Jawad Amoli, daga malaman fiƙihu na Shi'a, tare da jingina da riwaya "Ya Allah ka kashe ƙarya ka raya gaskiya",[6] ya fassara Tawarruk matsayin wata alama ta galabar gaskiya kan ƙarya. A fahimtar malamin ƙafar dama alama ce ta gaskiya, ita kuma ƙafar hagu alama ce ta ƙarya.[7]

Wasu daga malaman Ahlus-Sunna a cikin zaman tahiya. Suna ɗaukar Iftirash (Zama kan cinyar ƙafar hagu a lanƙwashe a naɗe, sannan ita kuma ƙafar dama da kasance a miƙe tsaye) a matsayin Mustahabbi.[8] Wasu daban kuma suna ganin ya kamata cikin zaman tahiya na farko a yi Iftirash zaman tahiya na biyu kuma a yi Tawarruk.[9]

Tawarruk a cikin tsayuwa na cikin sallah yana nufin jingina ko ɗora nauyin jiki tsakanin ƙafar hagu da dama[10] haka kuma yana da ma'anar Jingina hannaye kan cinyoyi wanda a fiƙihu ake lissafa shi a matsayin abin ƙyama (Makaruhi).[11]

Bayanin kula

  1. Tabatabai Yazdi, Al-Urwat Al-Wuthƙa, 1419ƙ, J. 2, Shafi na 574.
  2. Muhaƙƙiƙ Al-Hilli, Al-Mu'tabar fi Sharh Al-Mukhtasar, 1407ƙ, J. 2, Shafuffuka na 214 da 228; Khu'i, Sharh Urwat Al-Wuthƙa, 1418ƙ, Shafuffuka na 177 da 343.
  3. Allamah Al-Hilli, Tadhkirat Al-Fuƙaha', 1414 ƙ, J. 3, Shafi na 197.
  4. Najafi, Jawahir Al-Kalam, 1362 ƙ, J. 10, Shafi na 182.
  5. Hurrul Al-Amili, Wasa'il Al-Shi'a, Mu'assasat Aal Al-Bayt (A.S.) Li Ihya' At-Turath, J. 12, Shafi na 107.
  6. Sheikh Saduƙ, Man La Yahduruhu Al-Faƙih, 1413ƙ, J. 1, Shafi na 320.
  7. Jawadi Amoli, Razhaye Namaz, 1389, Shafi na 143.
  8. Nawawi, Al-Majmu' Sharh Al-Muhadhdhab, Dar Al-Fikr, J. 3, Shafi na 450; Muhaƙƙiƙ Al-Hilli, Al-Mu'tabar fi Sharh Al-Mukhtasar, 1407ƙ, J. 2, Shafi na 228.
  9. Muhaƙƙiƙ Al-Hilli, Al-Mu'tabar fi Sharh Al-Mukhtasar, 1407ƙ, J. 2, Shafi na 228.
  10. Najafi, Jawahir Al-Kalam, 1362ƙ, J. 11, Shafi na 91; Shahid Al-Awwal, Al-Alfiyya wa An-Nafliyya, 1408ƙ, Shafi na 114; Tabatabai Yazdi, Al-Urwat Al-Wuthƙa, 1420ƙ, J. 3, Shafi na 38.
  11. Allamah Al-Hilli, Tadhkirat Al-Fuƙaha', 1414ƙ, J. 3, Shafuffuka na 298 da 299.

Nassoshi

  • Allamah Al-Hilli, Hasan bin Yusuf, Tadhkirat Al-Fuƙaha', Qom, Cibiyar Aal Al-Bayt (A.S.), 1414 ƙ.
  • Hurrul Al-Amili, Muhammad bin Hasan, Wasa'il Al-Shi'a, Qom, Cibiyar Alul Al-Bait (A.S) domin raya al'adu, babu kwanan wata.
  • Javadi Amoli, Abdullah, Razhaye-e Namaz Mai bincike: Husayn Shafi'i, Qom, Gidan bugawa na Isra', Bugu na sha shida, 1389 SH,
  • Khyi, Sayyid Abul Ƙasim, Sharh Urwat Al-Wuthƙa, Mai bincike: Muhammad Reza Musawi Khalkhali, Qom, Gidan bugawa naTawhid, 1418ƙ.
  • Muhaƙƙiƙ Al-Hilli, Ja'far bin Hasan, Al-Mu'tabar fi Sharh Al-Mukhtasar, Qom, Cibiyar Sayyid Al-Shuhada' (A.S.), Bugu na farko, 1407 ƙ.
  • Najafi, Muhammad Hasan, Jawahir Al-Kalam, Beirut, Mawallafar Gidan raya al'adun Laranci, Bugu na bakwai, 1362 SH,
  • Nawawi, Yahya bin Sharaf, Al-Majmu' Sharh Al-Muhadhdhab, Beirut, Gidan bugawa na Al-Fikr, babu kwanan wata
  • Shahid Al-Awwal, Muhammad bin Makki, Al-Alfiyya wa An-Nafliyya, Qom, Ofishin Yaɗa Labarai na Musulunc, 1408ƙ.
  • Sheikh Saduƙ, Muhammad bin Ali, Man La Yahduruhu Al-Faƙih, Qom, Ofishin Bugawa na Musulunci, 1413ƙ.
  • Tabatabai Yazdi, Sayyid Muhammad Kazim, Al-Urwat Al-Wuthƙa, Masu bincike: Cibiyar Ofishin Bugawa na Musulunci, Ƙungiyar Malaman Hauza, Bugu na farko, 1420ƙ.