Daƙiƙa:Hablullahi
Hablullahi, (Larabci: حَبْلُالله) ma'ana igiyar Allah, wata jumla ce ta Kur'ani wace Allah a cikin ayar I'itisam yake umartar Musulmi baki ɗayansu su yi riƙo da igiyar Allah ƙam-ƙam ka da su rarraba su zama ƙungiya-ƙungiya.[1]
A cikin Tafsirin Ayyashi (Rasuwa: 320H) ya naƙalto wata riwaya da cikinta aka gabatar da iyalan Muhammad ko kuma Imam Ali (A.S) matsayin misali na igiyar Allah.[2] Allama Ɗabaɗaba'i shima yana da ra'ayin cewa abin nufi igiyar Allah cikin وَاعْتَصِمُوا بِحَبْلِ اللَّهِ جَمِیعًا، (Ku yi riƙo da igiyar Allah baki ɗayanku) shi ne Kur'ani da Annabi (S.A.W) haka kuma abin da ake nufi da jumlar «و مَنْ یعْتَصم بالله» (Duk wanda ya yi riƙo da Allah) a cikin aya 101 suratul alu imran shi ne riƙo da ayoyin Allah da Annabi (S.A.W) ma'ana littafi da sunna.[3] A cikin tafsirin Ad-Durrul Mansur na Suyuɗi (Rasuwa:911H) daga malaman Ahlus-Sunna, an naƙalto wata riwaya da take cewa jama'a, Kur'ani, tsatson Annabi, alƙawari da ɗa'a suna daga misalai na igiyar Allah.[4] Tafsirul Al-Manar daga tafsiran Ahlus-Sunna, ya fassara umarni da kyakkyawa da hani da mummuna a matsayin misali na igiyar Allah.[5]
Bisa dogara da wannan kiran da Musulunci ya yi kan haɗin kai da riko da igiyar Allah. ƙungiyar ɗalibai Musulmi a jami'o'in Najeriya lokaci bayan lokaci sun kasance suna shirya taron haɗin kai tare da kira zuwa ga riƙo da igiyar Allah.[6]
Lalle ni ina barin muku halifofi biyu (magada biyu) a cikinku: Littafin Allah Mai girma da ɗaukaka, wanda igiya ce shimfiɗaɗɗiya tsakanin sama da ƙasa, da kuma zuriyata Ahlulbaitina. Hakika su biyun ba za su rabu da juna ba har sai sun zo wurina a bakin Tafki (Hawd).”Ma’ana: Annabi (SAW) ya bayyana cewa Alƙur’ani da Ahlulbaiti su ne ginshiƙai biyu na shiriya bayan sa, kuma riƙo da su ne hanyar tsira daga ɓata.[7]
A cewar Fadlu Bin Hassan Ɗabrisi (Rasuwa:548H) malaman tafsiri suna da saɓani game da mene ne igiyar Allah. Wasu sun fassara ta da Kur'ani, wasu daban sun ce ana nufin addinin Musulunci wasu kuma daban sun ce Ahlul-Baiti. Ɗabrisi yana ganin cewa dukkanin wuraren da aka ambata suna ƙarƙashin ma'anar igiyar Allah. Domin tabbatar da wannan magana ya jingina da hadis saƙlaini wanda a cikinsa aka gabatar da Kur'ani da Ahlul-Baiti a matsayin misali na igiyoyi biyu, cikin naƙalinsa maimakon saƙlaini sai aka yi amfani da "Hablaini"[Tsokaci 1][8]
A cewar Ayatullahi Makarim Shirazi, fassarori da aka kawo game da Hablullahi (Igiyar Allah) babu saɓani a tsakaninsu, saboda abin nufi daga igiyar Allah shi ne duk wata hanya da ake amfani da ita domin isa zuwa ga Allah, wannan hanya tana iya kasancewa Kur'ani, Annabi (S.A.W), Ahlul-Baiti (A.S) da dama wasu abubuwan daban.[9] Haka nan, malamin ya yi imani da cewa hablullahi tana Ishara da cewa mutum domin tsira daga duhun jahilci da rashin sani yana buƙatar jagora ko wata igiya wace zai riƙe ta domin fitowa daga rijiyar gafala.[10]
Bayanin kula
- ↑ Suratu Ali-Imran, Aya ta 103
- ↑ Ayyashi, Tafsir al-Ayyashi, 1380 Hijira (1960-1961 Miladiyya), juzu'i na 1, shafi na 194.
- ↑ Tabatabai, Al-Mizan, 1393 Hijira (1973-1974 Miladiyya), juzu'i na 3, shafi na 369.
- ↑ Suyuti, Al-Durr al-Manthur, Dar al-Fikr, juzu'i na 2, shafi na 284-288.
- ↑ Rashid Rida, Tafsir al-Qur'an al-Hakim (Tafsir al-Manar) , 1990 Miladiyya, juzu'i na 4, shafi na 39.
- ↑ Newtelegraph:https://newtelegraphng.com/muslim-women-urged-to-hold-firmly-to-allahs-rope/
- ↑ Suyuti, Al-Durr al-Manthur, Beirut, Dar al-Fikr, juzu'i na 2, shafi na 285.
- ↑ Tabrisi, Majma' al-Bayan, Dar al-Ma'rifah, juzu'i na 2, shafi na 805.
- ↑ Makarim Shirazi, Tafsir Namuna, 1373-1374 Hijira Shamsi (1994-1996 Miladiyya), juzu'i na 3, shafi na 29.
- ↑ Makarim Shirazi, Tafsir Namuna, 1373-1374 Hijira Shamsi (1994-1996 Miladiyya), juzu'i na 3, shafi na 32.
Tsokaci
- ↑ «إنی قد ترکت فیکم حبلین إن أخذتم بهما لن تضلوا بعدی أحدهما أکبر من الآخر کتاب الله حبل ممدود من السماء إلی الأرض و عترتی أهل بیتی ألا و إنهما لن یفترقا حتی یردا علی الحوض»Na bar muku abubuwa biyu (hanyoyi biyu na shiriya) a tsakaninku; muddin kuka riƙe su ƙam-ƙam, ba za ku taɓa ɓacewa bayana ba. Ɗaya daga cikinsu ya fi ɗaya girma (kuma matsayinsa ya fi ɗaukaka): Littafin Allah, wanda igiya ce da aka shimfiɗa daga sama zuwa ƙasa, da kuma Ahlulbaitina (iyalaina da zuriyata). Ku sani, waɗannan biyun ba za su rabu da juna ba har sai sun zo wurina a bakin Tafki (Hawd)Dar al-Ma‘rifa, juzu’i na 2, shafi na 805
Nassoshi
- Ayyashi, Muhammad ibn Mas'ud, Tafsir al-Ayyashi, gyara: Sayyid Hashim Rasuli Mahallati, Tehran, Al-Matba'ah al-'Ilmiyyah, bugu na farko, 1380 Hijira (1960-1961 Miladiyya) .
- Makarim Shirazi, Nasir, Tafsir Namuna, Tehran, Dar al-Kutub al-Islamiyyah, 1373-1374 Hijira Shamsi (1994-1996 Miladiyya) .
- Rashid Rida, Muhammad, Tafsir al-Qur'an al-Hakim (Tafsir al-Manar) , Al-Hay'ah al-Misriyyah al-'Ammah lil-Kitab, 1990 Miladiyya.
- Suyuti, Abdurrahman ibn Abi Bakr, Al-Durr al-Manthur, Beirut, Dar al-Fikr, babu ranar bugawa.
- Tabatabai, Sayyid Muhammad Husayn, Al-Mizan fi Tafsir al-Qur'an, Beirut, Mu'assasat al-A'lami lil-Matbu'at, bugu na uku, 1393 Hijira (1973-1974 Miladiyya) .
- Tabrisi, Fadl ibn Hasan, Majma' al-Bayan fi Tafsir al-Qur'an, Dar al-Ma'rifah, babu ranar bugawa.
- Newtelegraph:https://newtelegraphng.com/muslim-women-urged-to-hold-firmly-to-allahs-rope/