Saklaini

Daga wikishia
Wannan kasida ce game da kalmar Sakaini. Domin sanin Hadisin Saklain, iduba Hadis Salaini.

Saklaini (Larabci: الثقلين) ko Siklaini ishara ce zuwa ga Alkur’ani da Ahlil-Baiti, hakika Annabi (S.A.W0 cikin Hadis Saklaini ya umarci Al’ummarsa zuwa ga da’a ga wadannan abubuwa guda biyu, wannan Kalma ta Saklaini an cirota ne daga Hadis Saklaini. A harshen Larabci idan aka ce siklu yana nufin kaya [1] Sikal Kuma na nufin Nauyi [2] Sakal na nufin abu mai daraja [3] da wannan ne ma Kalmar Saklaini take bada ma’anar abubuwa biyu masu daraja da kima, Kalmar Sakalan da ta zo a aya ta 31 cikin Suratul Rahman Malaman tafsiri sun fassara ta da Gungun Jama’a guda biyu daga Aljanu da Mutane [4] daidai lokacin da wasu suka tafi kan cewa abin nufi daga sakalan shine Alkur’ani da Tsatso mai tsarki da Ahlin gidan Annabi (S.A.W) [5] Annabin Muslunci (S.A.W) a cikin Hadis Saklaini ya umarci Al’ummarsa da riko da wadannan abubuwa guda biyu wadanda matukar suka yi riko da su ba za su taba ba taba [6] a cikin ba’arin nakalin wannan hadisi Annabi (S.A.W) ya ambaci Alkur’ani da Siklul Akbar (Siklu Mafi Girma) Ahlil Baiti kuma da Siklul Asgar (Karamin Siklu) [7]

Bayanin kula

  1. Ibn Manzoor, Lasan Al-Arab, 1414 AH, juzu'i na 11, shafi na 85.
  2. Ibn Manzoor, Lasan al-Arab, 1414 AH, juzu'i na 11, shafi na 85.
  3. Qureshi, Kamus Kur’ani, 1412 AH, Juzu’i na 1, shafi na 307-310.
  4. Ibn Kathir, Tafsir Alkur’anil Al-Azeem, 1415 AH, juzu’i na 4, shafi:447; Abul Fatuh Razi, Tafsirin Raudatul Al-Jinan, 1387, juzu'i na 10, shafi na 396.
  5. Qommi, Tafsir Qummi, 1405 AH, juzu'i na 2, shafi na 345; Bahrani, Al-Barhan, 1334 Hijira, juzu'i na 4, shafi na 267.
  6. Nasa’i, Al-Sunan Al-Kubra, 1411 AH, juzu’i na 5, shafi:45; Kilini, Al-Kafi, Dar al-Kitab al-Islamiya, juzu'i na 1, shafi na 294.
  7. Ayyashi, Tafsir al-Ayyashi, 1380 AH, juzu'i na 1, shafi na 5.

Nassoshi

  • Alqur'ani Alkareem
  • Ibn Kathir, TafsirKur'an Al-Azeem, Ali Shiri, Beirut, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, 1415H.
  • Ibn Manzoor, Muhammad Ibn Makram, Lasan Al'arab, Ahmad Fars, Beirut, Darul Fikr Lal-Taba'ah da Al-Nashar da Al-Tawzi'ah, 1414H.
  • Abul Fattouh Razi, Tafsir Rauzatul Al-Jinnan wa Ruh al-jinan, Abolhasan Shearani da Ali Akbar Ghafari, Tehran, Bina, 1387 suka gyara kuma suka gyara su.
  • Bahrani, Hashim bin Suleiman, al-Barhan fi Tafsir al-Qur'an, editan Mahmoud bin Jafar Mousavi Zarandi, Tehran, gidan buga littattafai na Aftab, 1334.
  • Eyashi, Mohammad Bin Masoud, Tafsir Al-Ayyashi, bincike: Seyyed Hashem Rasouli Mahalati, Ilmia Printing House, Tehran, 1380H.
  • Qurashi, Sayyid Ali Akbar, Kamus Qur'an, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya, 1412H.
  • Qummi, Ali bin Ibrahim, Tafsir Qammi, Tayyab Musawi Al-Jazairi, Qum, Darul-Kitab, 1404H.
  • Kulaini, Mohammad bin Yaqub, Al-kafi, Tehran, Dar al-Kutb al-Islamiya, Beta.
  • Nasa'i, Ahmad bin Shoaib, Al-Sunan Al-Kubari, Beirut, Darul Katb Al-Alamiya, 1411H.