Daƙiƙa:Fiƙihun Gwamnati
Fiƙihun Gwamnati a madadin Fiƙihun ɗaiɗaikun mutane, wata hanya ce ta gaba ɗaya (cikakkiyar kallo) ga dukkan hukunce-hukuncen fiƙihu, inda malami (Faƙihi) ke yin istinbaɗi ya fito da waɗannan hukunce-hukuncen ba don tsara rayuwar ɗaiɗaikun mutane kawai ba, amma da nufin amsa buƙatun gwamnatin addini da gudanar da al'umma. A kan haka, a iyakokin Fiƙihun gwamnati, ba kamar Fiƙihun siyasa wanda yake tattauna matsalolin iko da siyasa ta ƙwarewa ba, ba ya iyakance ga matsalolin siyasa kawai, sai dai yana tattaro dukkan babukan fiƙihu.
Wannan hanya tana gaban Fiƙihun mutum guda ɗaya a kankin kansa; hanya ce wadda galibi ke ƙayyade ayyukan musulmi guda ɗaya ba tare da la'akari da asalin gamayya na al'umma ba, kuma a cikin dogon lokaci na zamanin ɓoyewa (Ghaibar Imam Mahadi) saboda yanayi kamar kasancewar Shi'a tsiraru da kuma taƙiyyar malaman fiƙihu, ta kasance mafi rinjaye a Fiƙihun Shi'a. Wannan tunani a zamaninmu kuma bayan nasarar juyin juya halin Musulunci na Iran, tare da dogaro da ra'ayoyin Imam Khomaini da Sayyid Ali Khamna'i, ya koma zuwa tsarin gwamnati. An faɗi cewa wajabcin tsarin Fiƙihun gwamnati ya samo asali ne daga karɓar alaƙa mafi girma tsakanin fiƙihu da gwamnati, kuma an ɗauki wannan hanya a matsayin mai alaƙa da ikon zamantakewa na malaman fiƙihu da tabbatar da mulkin addini a zamanin ɓoyewa.
Masu bincike sun bayyana wasu alamomi ga Fiƙihun gwamnati; kamar: shigar da lokaci da wuri a cikin ijtihad, kallon fiƙihu da shari'a a matsayin ɗaya, kulawa ta musamman ga manufofin shari'a da ma'aunin hukunce-hukunce, sanya adalcia matsayin jigo. nisanta daga taka-tsantsan na fiƙihu a cikin sababbin al'amura sabon-zuwa, da jaddada ingancin hukunce-hukuncen gwamnati. Tushen Fiƙihun gwamnati kuma sun haɗa da: cikakkiya da dawwamar shari'a, cakuɗar addini da siyasa, wajabcin wanzuwar gwamnati don tabbatar da farin ciki da cigaban ɗan Adam, muhimmancin imamanci da wilaya, da yuwuwar canza hukunce-hukuncen fiƙihu zuwa dokoki masu tilastawa ga ƴan ƙasa.
Daga cikin sakamako mafi muhimmanci na tsarin Fiƙihun gwamnati akwai: bambanci a cikin fitar da hukunce-hukunce daga hujjojin shari'a, fifita kiyaye gwamnatin Musulunci a lokuta da suka ci karo da wasu hukunce-hukuncen shari'a, da kulawa da gaske ga inganci da tasirin aiwatar da hukunce-hukuncen a cikin gudanar da al'umma.
Mene ne Shi ?
Ma'anar taurin kai (ko duhun kai / tahajjur) ita ce, wanda yake so ya yi amfani da tushen Musulunci da fiƙihun Musulunci don gina al'umma, ya dogara ga zahirin hukunce-hukuncen kawai, kuma ya kasa fahimtar iyawar halitta (ko fa'idar) na hukunce-hukuncen da koyarwar Musulunci, a inda suke da fa'ida, kuma ya kasa rubuta magani da umarnin zamani don buƙatun al'umma, tsarin mulki, da ƙasa. Idan a kan shugabancin tsarin siyasar da aka kafa bisa Musulunci, ko kuma za a kafa a nan gaba, akwai irin wannan hali (taurin kai), to tabbas Musulunci zai sha wulakanci, kuma tushen ma'adinai na koyarwa da hukunce-hukuncen Musulunci ba za su iya ciyar da al'umma gaba ba. Imam (Khomeini) ya tsarkake kansa daga wannan annoba. Saboda tsawon shekarun da malaman Shi'a da kuma ƙungiyar Shi'a da kansu ba su da iko da mulki a duniyar Musulunci, kuma fiƙihun Shi'a ya kasance fiƙihuu marar gwamnati da fiƙihun mutum, sai Imam mai girma ya juya da fiƙihun Shi'a zuwa ga fiƙihun gwamnati.[1]
An yi la'akari da Fiƙihun gwamnati a matsayin hanya da hangen nesa na gaba ɗaya (cikakke) ga dukkan hukunce-hukuncen fiƙihu, ba wai wani ɓangare daga gare shi ba wanda bisa gare shi, malami (Faƙihi) yake fitar da hukunce-hukuncen shari'a don biyan buƙatun gwamnatin addini.[2] A kan haka, malaman fiƙihu a cikin istinbaɗi na hukunce-hukuncen shari'a, tare da kula da biyan buƙatun gwamnati, suna kuma la'akari da buƙatun mutum ɗaya daga muminai da masu hukunci a ƙarƙashin manyan buƙatu da yanayin gwamnati da al'umma;[3] saboda haka aka ce faɗin Fiƙihun gwamnati dole ba batutuwan siyasa na ƙwarewa ba ne, sai dai zai rufe dukkan babukan fiƙihu.[4]
An ɗauki Fiƙihun gwamnati a matsayin mai alaƙa da ikon malaman fiƙihu a cikin al'umma;[5] saboda wannan aka ce wannan hanya ta dace da tabbatar da mulkin Shi'a a zamanin ɓoyewa (Ghaiba). Bisa ga wannan ra'ayi, malaman fiƙihu a lokaci guda tare da gudanar da tsarin addini na al'umma a cikin istinbaɗi na batutuwan fiƙihu, suna kuma la'akari da buƙatun mulkin siyasa na Shi'a da kyakkyawan gudanar da al'umma.[6]
Bambancinsa Da Fiƙihun Mutum Ɗaya
An sanya Fiƙihun gwamnati a gaban Fiƙihun mutum guda ɗaya. A tsarin Fiƙihun mutum, malami (Faƙihi) yana bayyana ayyukan musulmi ɗaya ne, yayin da a Fiƙihun gwamnati, asalin gamayya na al'umma ke zama abin la'akari ga malami wajen fitar da hukunce-hukuncen shari'a.[7]
An faɗi cewa Fiƙihun mutum shine tsarin da ya fi rinjaye a Fiƙihun Shi'a a dukkan zamanin ɓoyewa (Ghaiba) har zuwa kafin nasarar juyin juya halin Musulunci na Iran, wanda yake samuwa a matsayin amsa ga tambayoyi, daidai da gudanar da rayuwa ta imani na musulmi ɗaya a cikin al'ummarsa.[8] An faɗi cewa ɗaukar wannan tsarin ya faru ne saboda ƙarancin Shi'a, taƙiyyar malaman fiƙihu daga masu mulki na zalunci, rashin halastacciyar mazhabar Shi'a a ƙasa mai cin gashin kanta, yaɗa ra'ayin raba addini da siyasa (sekularizim) a cikin muhallin ilimi, da rashin tambayar malaman fiƙihu game da batutuwan gwamnati.[9]
An danganta sauyawa daga hangen nesa na mutum a cikin fiƙihu zuwa tsarin gwamnati ga wannan ilimi, mafi yawa ga binciken ijtihadi na malaman fiƙihu na zamani bayan nasarar juyin juya halin Musulunci na Iran, musamman Imam Khomaini[10] da Sayyid Ali Khamna'i[11] kamar yadda Imam Khomaini ya ga ainihin fiƙihu a matsayin mai dogaro da gwamnati, kuma ya kafa alaƙa mai zurfi tsakanin Fiƙihun Shi'a da gwamnati.[12]Haka kuma an faɗi cewa tsarin mulkin Faƙihi (Wilayatul Faƙihi) wanda ya samu bayan juyin juya halin Musulunci ya dace da tsarin gwamnati a cikin fiƙihu.[13]
Bambancinsa Da Fiƙihun Siyasa
An kuma bambance Fiƙihun gwamnati daga Fiƙihun siyasa; domin Fiƙihun siyasa, a matsayin wani sashe na ilimin fiƙihu, yana la'akari da batutuwa da al'amurran siyasa na musamman da hukunce-hukuncen halayen da suka shafi iko, kuma yana guje wa gabatar da batutuwan da ba na siyasa ba, yayin da Fiƙihun gwamnati ba a matsayin wani sashe na ilimin fiƙihu ba, amma a matsayin hanya, yana istinbaɗi (cirewa) da dukkan batutuwa da al'amurran fiƙihu, na siyasa da na rashin siyasa, daidai da gudanar da gwamnatin addini.[14]
Game da Fiƙihun siyasa kuma an faɗi cewa wannan nau'in fiƙihu ba ya buƙatar tabbatar da gwamnatin addini, kuma a dukkan lokutan zamanin ɓoyewa (Ghaiba), ko malaman fiƙihu suna da mulki ko a'a, ana iya yin istinbaɗinsa.[15]
Matsayi Da Muhimmanci
Kamar yadda Abbas Ali Amid Zanjani, masanin fiƙihu kuma farfesa a fannin kimiyyar siyasa, ya faɗa, yarda da alaƙa mafi girma tsakanin fiƙihu da gwamnati yana sa zaɓin tsarin gwamnati ga fiƙihu ya zama dole, kuma a kan haka, aikin fiƙihu, ban da sa'adar lahira, ya haɗa da kula da al'amuran duniya kuma.[16] A kan haka, an faɗi cewa imani da alaƙa mafi ƙanƙanta tsakanin fiƙihu da gwamnati zai hana magana game da Fiƙihun gwamnati.[17]
Masu bincike na fiƙihu sun bayyana wasu buƙatu da yawa don canza tsarin daga Fiƙihun mutum zuwa Fiƙihun gwamnati; kamar: sauyi na dindindin na al'amuran da suka shafi al'umma a zamanin nan,[18] da kuma bambancin al'amuran gwamnati da al'amuran mutum, da kuma cewa Fiƙihun mutum ba shi da inganci wajen bayyana hukunce-hukuncen al'amuran gwamnati.[19] A wani gefe kuma, kiyaye maslahohin al'umma shi ma an ɗauke shi a matsayin ɗaya daga cikin dalilan wajabcin zaɓin tsarin gwamnati ga fiƙihu.[20]
Ƙirƙirar wayewar Musulunci da tsara sabon nau'i na gwamnati ga al'ummomin Musulunci suma an ɗauke su a matsayin wasu dalilan muhimmancin Fiƙihun gwamnati.[21] A kan haka an faɗi cewa gurguzu (sosiyalizim) da ƴanci (liberalizim) ba su da yuwuwar aiwatarwa a cikin al'ummomin Musulunci, kuma saboda wannan dole ne a tsara sabon nau'i na gwamnati a cikin waɗannan al'ummomi, wanda ilimin tafiyar da shi za a samar da shi ta hanyar samun tsarin gwamnati ga fiƙihu, kuma zai kai ga ingantaccen tsarin addini.[22]
Alamomi Da Siffofi
Masu bincike na fiƙihu sun bayyana wasu siffofi da alamomi ga tsarin Fiƙihun gwamnati. Muhimmancin musamman na buƙatun lokaci da wuri a cikin ijtihad, hangen nesa na tsari (cikakken kallo) ga fiƙihu da shari'ar Musulunci, himma ga manufofin shari'a da ma'aunin hukunce-hukunce, da sanya adalci matsayin jigo, da kuma kulawa da ingancin hukunce-hukuncen gwamnati suna daga cikin waɗannan alamomi da siffofi.[23]
Muhimmancin La'akari Da Zamani Da Wuri A Cikin Ijtihadi
Tasirin buƙatun lokaci da wuri a kan ijtihad da fikihu an ɗauke shi a matsayin ɗaya daga cikin muhimman abubuwan Fiƙihun gwamnati.[24] Imam Khomaini yana ɗaukan lokaci da wuri a matsayin abubuwa biyu masu tantancewa a cikin ijtihad, musamman a al'amuran gwamnati; ta yadda saboda sauye-sauye a cikin dangantakar siyasa, zamantakewa da tattalin arzikin da ke kan al'umma, hukuncin wani lamari na iya bambanta da hukuncin da ya gabata;[25] kamar halattar sayar da makamai ga maƙiya a wasu lokuta, ko sayar da kayan da aka ɓoye (taskar dukiya) idan akwai zalunci.[26]
La'akari Da Tsari Ga Fiƙihu Da Shari'ar Musulunci
Kulawa da alaƙar tsari tsakanin sassa daban-daban na shari'a a cikin tsarin istinbaɗi (cirewa) na hukunce-hukuncen an ɗauke shi a matsayin ɗaya daga cikin muhimman siffofi na tsarin Fiƙihun gwamnati; Alhali kuma mai da hankali kan ƙananan bayanai a lokacin istinbaɗi na iya haifar da rashin kyakkyawan aiki na wani hukunci, kuma ya shafi tsarin shari'a da siyasa na aluumma.[27]
Muhimmantar Da Manufofin Shari'a Da Ma'aunin Hukunce-hukunce
A cewar masu bincike, manufar shari'ar Musulunci ta yin hukunce-hukuncen ita ce cimma maslahohi da nisantar ɓarna, kuma rashin kula da waɗannan maslahohi da ɓarna da malami (Faƙihi) a matsayin istinbaɗi zai sa hukunce-hukuncen su zama marasa rai da aiki, da kuma rashin daidaito tsakaninsu. Suna da imani cewa saboda alaƙar da ke tsakanin Fiƙihun gwamnati da batun manufofin shari'a, kulawa da batun manufofin shari'a da ma'aunin hukunce-hukuncen zai haifar da ingancin Fiƙihun gwamnati.[28]
Ingancin Hukunce-hukuncen Gwamnati
Daga cikin siffofin da aka jaddada ga hukunce-hukuncen da ake fitarwa a kan hanyar Fiƙihun gwamnati, akwai cewa ba wai kawai ba su cutar da tsarin jama'a da maslahohin gama-gari ba, amma suna da aiki mai kyau wajen sauƙaƙe tsarin zama ɗan ƙasa;[29] saboda wannan aka faɗi cewa, alal misali, ya kamata a guje wa hukunce-hukuncen taka-tsantsan a Fiƙihun gwamnati ko kuma a rage su sosai don kada su sa ƴan ƙasa cikin wahala,[30] ko kuma a gaban al'amuran sabon zuwa kamar inshora, haraji, Internet (Yanar gizo), da sauransu, a guje wa ɗaukar tsarin hana (haramta) domin hakan zai sa al'umma ta gudu daga addini da gwamnatin addini.[31]
Tushe
An ɗauka cewa zaɓin tsarin Fiƙihun gwamnati ya dogara da bincike da karatu na waje da fiƙihu; ma'ana cewa malami (Faƙihi) ta hanyar karatu da tunani a cikin ilimomi kamar ilimin tauhidi (kalam) yana samun wannan hanya.[32] Masu bincike na fiƙihu sun lissafa tushe (mabani) da yawa ga Fiƙihun gwamnati; ciki har da: imani da Faɗaɗuwa da dawwamar shari'ar Musulunci da iyawarta ta amsa dukkan buƙatun fannin gwamnati, haɗin kai (cakuɗa) addini da siyasa a cikin yankin fiƙihu, wajabcin gwamnati da rawar da take takawa wajen tabbatar da sa'ada da farin cikin mutum da gamayya na ɗan adam, karɓar yanayin zamantakewa na Musulunci da faɗaɗa yankin addini zuwa fagen gudanar da al'umma, muhimmancin imamanci da gwamnati a Musulunci da imani da matsayin gwamnati da walaya na Annabi (S.A.W), kulawa da yanayi, buƙatu da sauye-sauyen rayuwa tare da la'akari da abubuwan tsayayyu da masu canzawa da manufofi a cikin tsarin istinbaɗi na hukunce-hukuncen, ingancin hukunce-hukuncen gwamnati, canza waɗannan hukunce-hukuncen zuwa dokoki masu tilastawa, da kuma a ƙarshe, ƙa'idar ƙarfin ijtihad.[33]
Faɗaɗuwa Da Dawwamar Shari'ar Musulunci
Tushe na farko na tabbatar da Fiƙihun gwamnati shine Faɗaɗuwa da dawwamar shari'ar Musulunci;[34] ma'ana akwai koyarwa a cikin addini don cimma kamala da sa'adarmu ta duniya da lahira, kuma ba za a iya ɗaukar wani fanni na rayuwar ɗan adam a matsayin wanda ya fita daga kewayar shari'a ba.[35] Bisa ga wannan tushe an faɗi cewa ilimin fiƙihu yana iya amsa dukkan buƙatun ɗan adam a fagen gwamnati, kuma gwamnati a zamanin ɓoyewa (Ghaiba) ba ta dakatarwa ba, kuma Mujtahidi wanda ya cika sharuɗɗa a matsayin wakilin Imam yana iya tabbatar ayyukan ma'asumi (Imam).[36]
Caƙuɗuwar Addini Da Siyasa
Daga cikin muhimman tushe na Fiƙihun gwamnati akwai alaƙar addini da siyasa.[37] tushe na gwamnatin Allah,[38] kasancewar koyarwa a cikin addini don yaƙi da fasadi da mulkin zalunci,[39] da kuma ƙayyade shiri ga gwamnati a cikin nassosin addini[40] suna daga cikin dalilan haɗin addini da siyasa da masu bincike na addini suka jaddada.[41] Bisa ga wannan tushe an faɗi cewa idan muka yarda da haɗin kai tsakanin fiƙihu da gwamnati da kallo mafi girma ga fiƙihu, to wannan fiƙihu a matakin fahimta da istinbaɗi yana buƙatar hangen nesa daga tushen gwamnati, kuma a matakin aiwatarwa kuma yana buƙatar tsari da ƙungiyar gwamnati don a iya aiwatar da shi daidai.[42]
Larurar Samuwar Gwamnati don Tabbatar Da Sa'adar Ɗan Adam
Daga cikin wasu tushe na Fiƙihun gwamnati akwai wajabcin wanzuwar gwamnati don biyan buƙatun zamantakewa da hana rikici da kafa tsari.[43] Bisa ga wannan tushe, gwamnati tana da muhimmiyar rawa wajen tabbatar da sa'adar lahira da duniya ta ɗan adam, kuma don wannan buri tana buƙatar dokoki waɗanda fiƙihu ke fitarwa.[44]
Karɓar Yanayin Zamantakewa na Addinin Musulunci
Masu bincike na fiƙihu, ta hanyar gabatar da wannan tambayar cewa shin mai shari'a (Allah) lokacin da yake yin hukunce-hukuncen shari'a yana la'akari da ɗaiɗaikun mukallafai a ware ne kawai, ko kuma yanayin gamayya na al'umma ma yana cikin la'akari? Suna nuni ga cewa a tsarin masu goyon bayan Fiƙihun gwamnati an jaddada cewa yawancin hukunce-hukuncen Musulunci an saukar da su ne ga al'umma,[45] har ma wasu sun yi imani cewa mafi yawan koyarwar shari'a ta keɓe ga al'amuran zamantakewa;[46] don haka, tare da la'akari da yanayin zamantakewa na addini, dole ne a yi istinbaɗi na hukunce-hukuncen ta yadda za a iya aiwatar da su a cikin tsarin zamantakewa da gwamnati.[47]
Muhimmancin Imamanci Da Gwamnati
Hana mutane daga ƙetare iyakoki da ƙa'idoji, wanzuwar al'umma da aiwatar da hukunce-hukuncen addini suna daga cikin dalilan da aka yi amfani da su wajen tabbatar da wajabcin kasancewar Imam a cikin al'umma. A cewar masu ƙa'idar Fiƙihun gwamnati, yin doka kawai ga al'umma bai isa ba, kuma akwai buƙatar aiwatar da ita, wanda wannan muƙamin a cikin al'ummar musulmi an ɗora shi ga Imam. A ra'ayinsu, idan babu Imam a cikin al'umma, sa'adar duniya da lahira ta ɗan adam ba za ta tabbata ba; don haka kamar yadda Allah Ya sanya wa Annabi Muhammad (S.A.W) matsayin gwamnati don aiwatar da hukunce-hukuncen Musulunci, shi ma ya nada Imamai bayansa don wannan aikin, kuma bayan Imamai na Shi'a, wannan mukamin ya koma ga malaman fiƙihu masu cikakken sharudda.[48]
Canza Hukunce-hukuncen fiƙihu Zuwa Doka
Daga cikin muhimman tushe a Fiƙihun gwamnati akwai canza hukunce-hukuncen shari'a zuwa doka[49]. A kan haka an faɗi cewa tun da masu sauraron Fiƙihun gwamnati su ne ƴan ƙasa na al'umma (ba masu hukunci (mukallafin) na hukunce-hukuncen shari'a ba), kuma a wani gefe kuma tun da gwamnatoci suna tilasta buƙatunsu a cikin sigar dokoki na tilastawa ga ƴan ƙasa, don haka Fiƙihun gwamnati ma, a kan hanyar tsara gudanar da al'umma, dole ne ya iya canza hukunce-hukuncen fiƙihu zuwa dokoki masu tilastawa ga dukkan ƴan ƙasa.[49]
Sakamako
A cikin binciken fiƙihu, an gabatar da sakamako da netice da yawa ga tsarin gwamnati a cikin fiƙihu.
- Bambancin istinbaɗi daga Hujjojin Shari'a: Daga cikin sakamako masu muhimmanci na hangen nesa na gwamnati ga fiƙihu akwai bambancin istinbaɗi wanda zai iya faruwa daga ayoyi da hadisai; alal misali, a tsarin mutum ga hujjojin khumusi, Khumusi na dukiyar mutum ce ga Imam da sharifai (zuri'ar Annabi), wanda malami (Faƙihi) ya kamata ya kashe shi a wuraren da aka ƙayyade; amma bisa ga hangen nesa na gwamnati, khumusi yana da alaƙa da mukamin imamanci da gwamnati, kuma ana yin la'akari da shi don gudanar da al'umma da biyan kuɗaɗen gwamnati.[50]
- Fifita Kiyaye Gwamnati a kan Hukunce-hukuncen Shari'a na Farko: Bisa ga tsarin Fiƙihun gwamnati, kiyaye gwamnatin Musulunci ya fi muhimmanci fiye da dukkan hukunce-hukuncen farko na Musulunci, kuma a inda aka samu cin karo tsakanin kiyaye waɗannan hukunce-hukuncen da kiyaye gwamnati, to tabbas kiyaye gwamnati ne ake fifita, kuma za a yi watsi da hukunce-hukuncen da suka saɓawa kiyaye gwamnati.[51]
- Kulawa da Inganci da Yankin Aiwatarwa na Hukunce-hukuncen Shari'a: A Fiƙihun gwamnati, tasiri da sakamako na hukunce-hukuncen da aka istinbatɗi su ne abin da malami (Faƙihi) ke la'akari da shi; yayin da a hangen nesa na mutum ga fiƙihu, ga malaman fiƙihu, kawai inganci da hujja (hujja) na hukunce-hukuncen da aka istinbata su ke da muhimmanci, kuma sakamakon hukunce-hukuncen da aka fitar ba damuwarsu ba ce.[52]
Bayanin kula
- ↑ «Bayanat Dar Marasim bisto-Dowomin Salgarde Rehlate Imam Khomaini».
- ↑ «Payam Be Jam'eye Mudarrisine Hauzeye Ilmiyye-ye Qom Be Munasebate Tashkile Shuraye Siyasat Gozariye Hauze,» shafin Khamenei.ir; Mehrizi, «Fiƙhe Hukumati,» shafi na 141-142; Nawa'i, Fiƙhe Wa Ijtihad Hukumati, shafi na 290-291; Mushkani, Daramadi bar Falsafe Fiƙhe Hukumati, shafi na 84.
- ↑ Ɗalibi Ɗadi, Fiƙhe Hukumati, shafi na 40; Ziyai-Far, «Ruyekerd Hukumati Dar Fiƙh,» shafi na 10; Zulfaƙari da Sayyidiyan, «Fiƙhe Hukumati; Chisti, Chirayi, Chigunagi,» shafi na 52.
- ↑ Muntaziri, Dirasat fi Wilayatil Faƙihi, juzu'i na 1, shafi na 15 da 21; Izedahi, Fiƙhe Siyasi Imam Khomaini, shafi na 10-37; Izedahi da Siddiƙ, «Mahiyat wa Wijegihaye Fiƙhe Hukumati,» shafi na 9.
- ↑ Izedahi da Siddiƙ, «Mahiyat wa Wijegihaye Fiƙhe Hukumati,» shafi na 8-9.
- ↑ Izedahi da Siddiƙ, «Mahiyat wa Wijegihaye Fiƙhe Hukumati,» shafi na 8-9.
- ↑ Mehrizi, «Fiƙhe Hukumati,» shafi na 141-142.
- ↑ Izedahi da Siddiƙ,«Mahiyat wa Wijegihaye Fiƙhe Hukumati,» shafi na 7.
- ↑ Gulami da Mirahmadi, «Fiƙhe Fardi Wa Fiƙhe Hukumati Bayesteha Wa Kasastiha,» shafi na 88–97; Izdehi, «Imam Khomaini Wa Irteƙaye Jayegahe Fiƙhe Hukumati,» shafi na 58.
- ↑ Khurasani, «Raweshshenasiye Fiƙhe Hukumati Dar Sepehre Andisheye Fiƙhi Siyasiye Imam Khomaini,» shafi na 48; Izdehi, «Imam Khomaini Wa Negareshe Hukumati Be Fiƙh,» shafi na 116.
- ↑ Mushkani, «Paradame Fiƙhe Hukumati ba Mehwariyate Didgahaha-ye Ayatullahi Uzma Khamna'i,» shafi na 54.
- ↑ Imam Khomaini, Sahifeye Imam, juzu'i na 21, shafi na 289.
- ↑ Hasanlu da Mahmudi, «Jayegah Fiƙhe Hukumati; Ahammiyat Wa Zarurate Tawajjoh be An Dar Tamaddune Nowine Islami,» shafi na 20.
- ↑ Ziyai-Far, «Ruykarde Hukumati dar Fiƙhe,» shafi na 10–11; Mehrizi, «Fiƙhe Hukumati,» shafi na 141–142.
- ↑ Izdehi da Siddiƙ, «Mahiyyat Wa Wijegihaye Fiƙhe Hukumati,» shafi na 11–12.
- ↑ Amid Zanjani, Fiƙhe Siyasi, juzu'i na 2, shafi na 170–171.
- ↑ Zulfiƙari da Sayyidiyan, «Fiƙhe Hukumati; Chisti, Cherayi, Cheguneghi,» shafi na 56–57.
- ↑ Gulami da Mirahmadi, «Fiƙhe Fardi Wa Fiƙhe Hukumati Bayesteha Wa Kasastiha,» shafi na 98.
- ↑ Parwar, «Fiƙhe Hukumati; Cherayi, Chisti wa Cheguneghi,» shafi na 192–193.
- ↑ Mushkani, Daramadi bar Falsafe Fiƙhe Hukumati, shafi na 106–108.
- ↑ Khamna'i, «Bayanat Dar Ijlase Jahani Ulama Wa Bidariye Islami,» shafin Khamna'i.ir; Mushkani, Daramadi bar Falsafe Fiƙhe Hukumati, shafi na 101–103.
- ↑ Ɗalibi Ɗadi, Fiƙhe Hukumati, shafi na 41–47
- ↑ Nawa'i, Fiƙhe Wa Ijtihad Hukumati, shafi na 289–301; Izdehi, «Mahiyyat Wa Wijegihaye Fiƙhe Hukumati,» shafi na 22–23; Mushkani, Daramadi Bar Falsafeye Fiƙhe Hukumati, shafi na 285.
- ↑ Mushkani, Daramadi Bar Falsafeye Fiƙhe Hukumati, shafi na 290.
- ↑ Imam Khomaini, Sahifeye Imam, juzu'i na 21, shafi na 289.
- ↑ Mushkani, Daramadi Bar Falsafeye Fiƙhe Hukumati, shafi na 290.
- ↑ Nawa'i, Fiƙhe Wa Ijtihade Hukumati, shafi na 299–300; Mushkani, Daramadi Bar Falsafeye Fiƙhe Hukumati, shafi na 291–293.
- ↑ Mushkani, Daramadi Bar Falsafeye Fiƙhe Hukumati, shafi na 307–315.
- ↑ Saifi Mazandarani, Mabaniyul Fiƙhil Fa'al, juzu'i 1 shafi na 13.
- ↑ Nawa'i, Fiƙhe Wa Ijtihade Hukumati, shafi na 298–299.
- ↑ Imam Khomaini, Sahifeye Imam, juzu'i na 21, shafi na 218; Izdehi, «Mahiyyat Wa Wijegihaye Fiƙhe Hukumati,» shafi na 22–23.
- ↑ Ziyai-Far, «Ruykarde Hukumati dar Fiƙhe,» shafi na 16.
- ↑ Mushkani, Daramadi bar Falsafeye Fiƙhe Hukumati, shafi na 153–222; Khurasani, «Raweshshenasiye Fiƙhe Hukumati Dar Sepehre Andisheye Fiƙhi Siyasiye Imam Khomaini,» shafi na 59–66; Sarami, «Daramadi bar Fiƙhe Hukumati,» shafi na 15–30; Mehrizi, «Fiƙhe Hukumati,» shafi na 159; Ziyai-Far, «Ruykarde Hukumati dar Fiƙhe,» shafi na 16–21; Izdehi da Siddiƙ, «Mahiyyat wa Wijegihaye Fiƙhe Hukumati,» shafi na 18–24; Gulami da Mirahmadi, «Fiƙhe Fardi Wa Fiƙhe Hukumati Bayesteha Wa Kasastiha,» shafi na 99–101.
- ↑ Mushkani, Daramadi bar Falsafe Fiƙhe Hukumati, shafi na 169 da 171.
- ↑ Imam Khomaini, Wilayate Faƙih, shafi na 19–21; Khurasani, «Raweshshenasiye Fiƙhe Hukumati Dar Sepehre Andisheye Fiƙhi Siyasiye Imam Khomaini,» shafi na 51–52.
- ↑ Gulami da Mirahmadi, «Fiƙhe Fardi Wa Fiƙhe Hukumati Bayesteha Wa Kasastiha,» shafi na 99; Izdehi da Siddiƙ, «Mahiyyat Wa Wijegihaye Fiƙhe Hukumati,» shafi na 18–19.
- ↑ Mushkani, Daramadi bar Falsafe Fiƙhe Hukumati, shafi na 177.
- ↑ Muntaziri, Dirasat fi Wilayatil Faƙihi, juzu'i na 1, shafi na 31.
- ↑ Muɗahhari, Nahzathaye Islamiye Mu'asir, shafi na 21, 36 da 41.
- ↑ Imam Khomaini, Wilayate Faƙih, shafi na 12.
- ↑ Sarami, «Daramadi bar Fiƙhe Hukumati,» shafi na 15–23.
- ↑ Mushkani, Daramadi bar Falsafeye Fiƙhe Hukumati, shafi na 184.
- ↑ Imam Khomaini, Wilayate Faƙih, shafi na 18; Mushkani, Daramadi bar Falsafeye Fiƙhe Hukumati, shafi na 184–190.
- ↑ Mushkani, Daramadi bar Falsafeye Fiƙhe Hukumati, shafi na 191.
- ↑ Khurasani, «Raweshshenasiye Fiƙhe Hukumati Dar Sepehre Andisheye Fiƙhi Siyasiye Imam Khomaini,» shafi na 58–59.
- ↑ Imam Khomaini, Sahifeye Imam, juzu'i na 6, shafi na 42–43 da juzu'i na 10, shafi na 18.
- ↑ Ziyai-Far, «Ruykarde Hukomati dar Fiƙh», shafi na 17–18.
- ↑ Imam Khomaini, Wilayate Faƙih, shafi na 20–21; Ziyai-Far, «Ruykarde Hukumati dar Fiƙhe,» shafi na 10–11; Mehrizi, «Fiƙhe Hukumati,» shafi na 18–19.
- ↑ Lakzai, «Masa'il Fiƙhe Siyasi,» shafi na 131; Izdehi, «Mahiyyat wa Wijegihaye Fiƙhe Hukumati», shafi na 23–24.
- ↑ Imam Khomaini, Kitabul Ba'i, juzu'i na 2, shafi na 659–660; Imam Khomaini, Wilayate Faƙih, shafi na 22.
- ↑ Imam Khomaini, Sahifeye Imam, juzu'i na 2, shafi na 452; Mushkani, Daramadi bar Falsafeye Fiƙhe Hukumati, shafi na 321–324.
- ↑ Ziyai-Far, «Ruykarde Hukomati dar Fiƙh», shafi na 24–25; Khurasani, «Raweshshenasiye Fiƙhe Hukumati Dar Sepehre Andisheye Fiƙhi Siyasiye Imam Khomaini,» shafi na 65–66.
Nassoshi
- Imam Khomaini, Sayyid Ruhullah, Sahifeye Imam, Tehran, Cibiyar Tanzim Wa Nashre Asare Imam Khomaini, 1378Sh.
- Imam Khomaini, Sayyid Ruhullah, Kitabul Ba'i, Cibiyar Tanzim Wa Nashre Asare Imam Khomaini, 1379Sh.
- Imam Khomaini, Sayyid Ruhullah, Wilayate Faƙih, Cibiyar Tanzim Wa Nashre Asare Imam Khomaini, 1377Sh.
- Izedahi, Sayyid Sajjad, Fiƙhe Siyasi Imam Khomaini, Tehran, Mawallafar Aruj, 1390Sh.
- Saifi Mazandarani, Ali Akbar, Mabaniyul Fiƙhil Fa'al, Qom, Ofishin Tabligate Islami, 1425H.
- Ɗalibi Ɗadi, Behnam, Fiƙhe Hukumati (Daramadi bar Mahiyat, Usul wa Mantiƙ Nazari, Tehran, Mawallafar Daneshgahe Imam Saɗik (A.S), 1397Sh.
- Amid Zanjani, Abbas Ali, Fiƙhe Siyasi, juzu'i na biyu, Tehran, Mawallafar Amir Kabir, 1377Sh.
- Mushkani Sabzewari, Abbas Ali, Daramadi bar Falsafe Fiƙhe Hukumati, Qom, Mawallafar Kitabe Farda, 1399Sh.
- Muɗahhari, Murtaza, Nahzathaye Islamiye Mu'asir, Tehran, Mawallafar Sadra, 1367Sh.
- Muntaziri, Husain Ali, Dirasat fi Wilayatil Faƙihi wa fiƙihu Ad-Daulat al-Islamiyya 1409H.
- Nawa'i, Ali Akbar, Fiƙhe Wa Ijtihad Hukumati, Mashhad, Mawallafar Hauze Ilmiyye Khurasan, 1399Sh.
- Izedahi, Sayyid Sajjad da Siddiƙah Siddiƙ Taƙizadeh,
«ماهیت و ویژگیهای فقه حکومتی»، (Hali da Siffofin fiƙihun Gwamnati), Mujallar Hukumat Islami, lamba 95, 2020M.
- Izedahi, Sayyid Sajjad، «امام خمینی و نگرش حکومتی به فقه»، (Imam Khomainida hangen nesa na gwamnati ga fiƙihu), Mujallar Ulum Siyasi, lamba 70, 2015M.
- Izedahi, Sayyid Sajjad، «امام خمینی و ارتقاء جایگاه فقه حکومتی»، (Imam Khomainida haɓaka matsayin fiƙihun gwamnati) Mujallar Hukumat Islami, lamba 64, 2012M.
- Isma'il Parwar، «فقه حکومتی؛ چرایی، چیستی و چگونگی»، (Fiƙihun Gwamnati; Me yasa, Menene, da Yaya), Mujallar Sureh (ko Surah), lamba 56-57, 2011M.
- Hasanlu, Amir Ali da Ali Mahmudi,
«جایگاه فقه حکومتی؛ اهمیت و ضرورت توجه به آن در تمدن نوین اسلامی»، (Matsayin Fiƙihun Gwamnati; Muhimmancinsa da Wajabcin Kulawa da shi a Wayewar Musulunci ta Zamani), Mujallar Pazhuheshnameh Ulum Insani, lamba 14, 2021M.
- Sayyid Ali Khamna'i، «پیام به جامعه مدرسین حوزه علمیه قم به مناسبت تشکیل شورای سیاستگذاری حوزه»، (Saƙo zuwa ga Al'ummar Malaman Makarantar Addini ta Qom, bisa samuwar Majalisar Tsara Manufofin Makarantar), Shafin yanar gizon Khamenei.ir, ranar bugawa 14 Nuwamba 1992M, ranar duba Janairu 2026M.
- Sayyid Ali Khamna'i،«بیانات در مراسم بیست و دومین سالگرد رحلت امام خمینی»، (Jawabai a bikin tunawa da rasuwar Imam Khomainina shekara ta ashirin da biyu), Shafin yanar gizon Khamenei.ir, ranar bugawa: 4 Yuni 2011M, ranar duba: 23 Fabrairu 2026M.
- Sayyid Ali Khamna'i،«بیانات در اجلاس جهانی علما و بیداری اسلامی»، (Jawabi a cikin Taron Duniya na Malamai da Farkawar Musulunci ), Shafin yanar gizon Khamenei.ir, ranar bugawa 29 Afrilu 2013M, ranar duba: 23 Fabrairu 2026M.
- Rida Khurasani، «روششناسی فقه حکومتی در سپهر اندیشه» فقی - سیاسی امام خمینی»، (Hanyar fiƙihun Gwamnati a cikin tunanin fiƙihuu da Siyasa na Imam Khomeini), Mujallar Pazhuheshnameh Inqilabe Islami, lamba 9, 2013M.
- Zulfiƙari, Muhammad da Sayyid Mahdi Sayyidiyan، «فقه حکومتی؛ چیستی، چرایی، چگونگی»، (Fiƙihun Gwamnati; Menene shi, Me ya sa yake da muhimmanci, Yaya yake?), Mujallar da ake wallafawa sau biyu a shekara ta Marifat Siyasi, shekara ta hudu, lamba ta 1, 2012M.
- Sarami, Saifullah، «درآمدی بر فقه حکومتی»، (Gabatarwa kan Fiƙihun Gwamnati) Mujallar wata uku-uku ta Fiƙh, shekara ta 18, lamba ta 4, 2011M.
- Ziyai-Far, Sa'id، «رویکرد حکومتی در فقه», Mujallar wata uku-uku ta Ulume Siyasi, lamba ta 53, 2011M.
- Gulami, Najaf Ali da Mansur Mirahmadi، «فقه فردی و فقه حکومتی بایستهها و کاستیها»، (Fiƙihun Mutum da Fiƙihun Gwamnati: Abubuwan da ake Buƙata da Kasawarsu), Mujallar wata uku-uku ta Siyasate Muta'aliya, shekara ta biyu, lamba ta 4, 2014M.
- Lakzai, Najaf، «مسائل فقه سیاسی»، (Batutuwan Fiƙihun Siyasa), Mujallar da ake wallafawa sau biyu a shekara ta Danishe Siyasi, lamba ta 11, 2010M.
- Mushkani, Abbas Ali, da Abdulhusain Mushkani، «پارادایم فقه حکومتی با محوریت دیدگاههای آیتاللّه العظمی خامنهای»، (Tsarin Fiƙihun Gwamnati bisa ra’ayoyin Ayatullahi Uzma Khamna'i.), Mujallara wata-wata ta Marifat, lamba ta 168, 2011M.
- Mehrizi, Mahdi، «فقه حکومتی»، (Fiƙihun Gwamnati), Mujallar wata uku-uku ta Naƙd wa Nazar, lamba ta 12. 1997M.