Daƙiƙa:At-Tibyan Fi Tafsiril Kur'an (Littafi)
| Marubuci | Shaik Ɗusi (Rasuwa: 460 ƙamari) |
|---|---|
| Maudu'i | Tafsir Kur'an |
| Salo | Aƙida |
| Harshe | Larabci |
| Adadin Jildi | Jildi 10 |
| Mai bugawa | Darul Ihya'i Atturasil Arabi |
At-Tibyan Fi Tafsiril Kur'an, (Larabci: التبيان في تفسير القرآن) wani littafi ne na Tafsir Kur'an, na Shaik Ɗusi (Rayuwa: 385-460) wanda ake la'akari da shi matsayin farkon kammalallen tafsirin Kur'ani da Shi'a suka fara gabatarwa, wannan littafi ya yi tasiri mai yawa cikin tsfiri, malaman tasfiri na Shi'a suna ɗauka daga wannan littafi.
Wannan littafi ya tattaro tafsirin dukkanin ayoyin Kur'ani. Daga cikin abubuwan da ya keɓantu da su akwai duba zuwa ga dukkanin ɓangarori, sannan kuma cikin tafsiri yana ɗaukowa daga ilimummuka daban-daban.
Shaik Ɗusi a cikin wannan littafi ya kawo ra'ayoyin malaman tafsiri da malaman aƙidu na sauran mazhabobin Muslunci, bayan nan sai ya yi bincike da suka a kansu. Ibn Idris Hilli da Ibn Kal, daga malaman Shi'a a ƙarni na shida hijira ƙamari, sun taƙaice wannan littafi cikin taken "Talkhisut Tibyan".
Tafsirin al-Tibyan ba shi da shahara sosai a wurin mafi yawan malaman Najeriya, musamman saboda harshen da aka rubuta shi da kuma tsarin tafsirin da ya fi dacewa da mahangar Shi'a, Na'am ɗalibai na shi'a da malamansu suna amfana daga wannan tafsiri
Marubuci
Muhammad Bin Hassan Ɗusi (Rayuwa: 385-460 hijira) wanda ya fi shahara da Shaik Ɗusi, babban malamin fiƙihu na Shi'a a ƙarni na biyar hijira ƙamari.[1] Bayan wafatin Sayyid Murtada, Ɗusi ya kasance jagoran Shi'a. Ya yaye ɗalibai masu yawai haka ya wallafa litattafai masu tarin yawa.[2]
Shaik Ɗusi ya kasance marubcin litattafai biyu daga Kutubul Arba'a wanda suka kasance mafi muhimmancin madogarai na hadisi a wurin Shi'a, sunayensu Tahzibul Ahkam da Al-Istibsar.[3]
Dalilin Rubuta Wannan Littafi
A faɗin Shaik Ɗusi cikin gabatarwa ta littafin, haƙiƙa tafsiran Kur'ani, zuwa wancan zamani, ko dai ba su tattaro dukkanin Kur'ani ko kuma dai ba su amfana daga sauran ilimummuka ba yayin da suke tafsirin; bari dai sun taƙaitu da ilimi guda ɗaya , misalin ilimin sanin lugga ko kuma ilimin sarfu da nahawu. Cikin ba'arin tafsirai ana taƙaituwa da iya ambaton riwayoyi, ba tare da tsayawa an yi bayani dalla-dalla ba kan riwayoyin.[4] Tafsiran da suka kasance kammalallu, sukan wuce gona da iri cikin faifaice bayani wani batu daga batutuwa tare kuma da ɗebo batutuwa da ba su da alaƙa da abin da ake magana kansa.[5]
Ya rubuta cewa tare da la'akari da wannan tawaya da giɓi, babban hadafin malamin ya kasance gabatar da wani sabon tafsiri na Kur'ani wanda ya ƙunshi dukkanin ilimummukan fahimtar Kur'ani; misalin ƙira'a, li'irabi, aƙida da kuma amsa shubuhohin aƙida na sauran mazhabobi. Ya kuma kasance littafi tsakatsaki: babu tsawaitawa ta yadda zai gajiyar da mai karatu kuma babu taƙaicewa da yawa ta yadda zai hana cimma ingantacciyar ma'ana.[6]
Matsayi
At-Tibyan shi ne cikakke kammalallen littafin tafsiri na Shi'a.[7] A faɗin Muhammad Hadi Ma'arifat, At-Tibyan haƙiƙa ya ciri tuta kan baki ɗayan litattafan tafsiri na zamaninsa; saboda saɓaninsu, ya kasance littafin tafsiri na farko a zamanin wanda bai taƙaitu da iya ɓangaren tafsiri ba, ya tattaro dukkanin ra'ayoyin malaman tafsiri da suka gabace shi.[8] Malamin yana ganin littafin matsayin tsakatsakin tafsiri kuma tare da kammala da ya tattaro baki ɗayan kyawawan fuskokin tafsiran da suka gabace shi.[9] Haka kumma marubucin maƙalar "Binciken hanyoyin kusantar fahimta tsakanin tafsirin al-Tibyan da Majma'ul al-Bayan wajen kawo ruwayoyin Ahlul Baiti." At-Tibyan shi ne tafsirin na ijtihadi na farko a Shi'a da cikinsa aka shaida motsin karkatuwa ga hankali a ƙarni na huɗu da biyar hijira ƙamari.[10] A cewar Marubucin Shaik Ɗusi cikin rubuta wannan tafsiri ya yi amfani daga rubuce-rubucen Shi'a da Ahlus-Sunna.[11]
Muhammad Ali Mahadawi Rad (Haihuwa: 1935m), masanin Kur'ani, ya rubuta cewa At-Tibyan ya yi matuƙar tasiri kan malaman tafsiri da suka zo bayansa. Daga jumla Ɗabrisi wanda ya yi yabo kan wannan littafi tare da bayyana cewa salon wannan littafi ya kwaikwaya cikin rubuta littafinsa mai suna Majma'ul Bayan.[12]
Abubuwan Da Wannan Littafi Ya Keɓantu Da Su
Shaik Ɗusi cikin At-tibyan yana yin kallon mai faɗin gaske, kuma ya yi amfani da baki ɗayan ilimummukan Kur'ani a cikin tafsirin Kur'ani; ilimummuka misalin sanin lugga, ƙira'a, asbabun nuzul, nasikh da mansukh, Surori makkiya da madaniyya.[13] Haka kuma tafsiri da tawili, muhkam da mutashabihu, fuskokin i'ijazin Kur'ani da binciken sunayen Kur'ani da surori.[14]
Cikin suran abubuwa da aka jinginawa wannan littafi akwai: Tafsirin Kur'ani da Kur'ani,[15] Rashin amfani da raunanan riwayoyi da amfani da ingantattu, tare da sharaɗin cewa ba su saɓawa Kur'ani da hankali ba[16] da kuma bijiro da bahasin aƙida mai faɗin gaske.[17]
Cikin wannan littafi bayan ambaton ko wace aya, za a fara da bincike da nazarin kalmomi da ma'anoni ba su da bayyana, da kuma bayani bambance-bambancen ƙira'o'i. Bayan nan za a yi nazarin mabambantan ra'ayoyi da mahangu na tafsiri, sai a fitar da ma'anar ayar tare da kiyaye gajartawar lafazi da kamalar ma'ana. Haka kuma cikin girmamawa za ayi suka kan asbabun nuzul na ayar da batutuwa na aƙida da suka shafi wannan aya wanda aka bijiro da su da kuma tunannukan masu adawa.[18]
Bayanin kula
- ↑ Gorji, Tarikhe Fiƙhe Wa Fuƙaha, 2013, shafi na 181.
- ↑ Gorji, Tarikhe Fiƙhe Wa Fuƙaha, 2013, shafi na 183.
- ↑ Gorji, Tarikhe Fiƙhe Wa Fuƙaha, 2013, shafi na 185.
- ↑ Tusi, Al-Tabyan, Dar Ihyaa Al-Turahat Al-Arabi, juzu'i. 1, shafi. 1.
- ↑ Tusi, Al-Tabyan, Dar Ihyaa Al-Turahat Al-Arabi, juzu'i. 1, shafi. 1-2
- ↑ Tusi, Al-Tabyan, Dar Ihyaa Al-Turahat Al-Arabi, juzu'i. 1, shafi. 2.
- ↑ Kariminia, "Sheikh Tusi Wa Manabi Tafsiri We Dar Al-Tibyan," shafi. 82; Marafet, Tafsiri, da Mufassirs, 1379, juzu'i. 2, shafi. 247.
- ↑ Ilimi, Tafsiir Wa Mufassirun, 1379, juzu'i. 2, shafi na 247.
- ↑ Ilimi, Tafsiir Wa Mufassirun, 1379, juzu'i. 2, shafi na 248
- ↑ Mousavi Darabeidi Wa Ahmadnejad, “Barrasi Ruyekerde Taqribi Do Tafsirie Al-Tabiyah Wa Majma’ Al-Bayyan Dar Naqle Rewayate Ahlul Baiti (AS),” shafi na 342.
- ↑ Mousavi Darabeidi Wa Ahmadnejad, “Barrasi Ruyekerde Taqribi Do Tafsirie Al-Tabiyah Wa Majma’ Al-Bayyan Dar Naqle Rewayate Ahlul Baiti (AS),” shafi na 342.
- ↑ Mahdavi Rad, “Al-Tabyan fi Tafsir al-Quran”, shafi na 186-187.
- ↑ Irani, Rabeshe Sheikh Tusi Dar Tafsirie Tibyan, 1992, shafi na 62.
- ↑ Ma'arifat, Tafsir Wa Mufassirun, 1379 AH, shafi na 248.
- ↑ Irani, Rabeshe Sheikh Tusi Dar Tafsirie Tibyan, 1992, shafi na 93.
- ↑ Irani, Rabeshe Sheikh Tusi Dar Tafsirie Tibyan, 1992, shafi na 127-128.
- ↑ Irani, Rabeshe Sheikh Tusi Dar Tafsirie Tibyan, 1992, shafi na 159.
- ↑ Ma'arifat, Tafsir Wa Mufassirun, 1379 AH, shafi na 248.
Nassoshi
- Mishkini Ardebili, Ali, Nubeshtarehaye Fiqhi, Qom, Cibiyar Kimiyya da Al'adu ta Dar Al-Hadith, 2013.
- Makarim Shirazi, Nasser, "Hukme Taglize Shodane Diye Dar Qatle",Ayatullah Makarim Shirazi's Website Website,Lokacin Ziyara:13 Azar 1403.
- Makarim Shirazi, Nasser, Tafsir Nomune, Tehran, Dar Al-Kutb Al-Islamiyya, 1374.
- Muntaziri, Hossein Ali, Pasokh Be Furseshehaye Piramune Majazathaye Islami Wa Huquqe Bashar, Qom, Iran, Arghawan Danesh, 2008.
- Muntaziri, Hossein Ali, asokh Be Furseshehaye Dini, Qum, Ofishin Ayatullahi Montazeri, 2010.
- Najafi (Sahibul Jawaher), Muhammad Hassan bin Baqir, Jawaher Al-Kalam Fi Sharh Shara’e Al-Islam, Beirut, Dar Ihya’ Al-Turaht Al-Arabi, Beta.
- Hashemi Shahroudi, Mahmoud, Farhange Fiqhe Mutabiq Mazhab Ahlul Bayt (AS), Qom, Muassase Da'iratil Ma'arif Fiqhe Islami Bar Mazhabe Ahlul Bayt, 2003.
- Mousavi Darabeidi, Seyed Hossein and Amir Ahmadnejad, «بررسی رویکرد تقریبی دو تفسیر التبیان و مجمعالبیان در نقل روایات اهلبیت(ع)», Binciken Tafsiri Tadbiki, Lamba ta 15, Farvardin 1401.
- Mahdavi Rad, Mohammad Ali, “Al-Tabyan fi Tafsir al-Quran”, in Baynat, No. 3, 1994.