Jump to content

Bal'am Bn Ba'ura

Daga wikishia
(an turo daga Bal'am Bin Ba'ura)

Bal'am Bn Ba'ura (arabic: بلعام بن باعوراء) yana daga cikin Malaman cikin zamanin Hazrat Musa (A.S) kuma ya kasance Mutum da Allah yake amsa addu'arsa, sai dai cewa kuma Shaidan ya batar da shi, hakika an ambaci sunan Bal'am cikin riwayoyin Muslunci da ma littafin At-Taura, haka kuma Malaman Tafsiri suna ganin aya ta 175 Suratul A'araf da ta yi Magana kan batan wani Mutum wanda mutum ne da ya samun tsinkaya kan Ismul A'azam, tana Magana ne kan Bal'am Ba'ura, an nakalto kissoshi mabambanta dangane Bal'am sai dai cewa Malaman Tafsiri suna ganin ba'arin Kissoshin sun kasance daga Isra'iliyat (Tatsuniyoyin Yahudawa)

Husuyoyi; Masanin Littafin Allah

Bal'am[1] ko kuma Bal-Amu[2] wani mutum ne daga Bani Isra'ila[3] da ya rayu a sham[4] hakika Hazrat Musa (A.S) ya yi amfani da shi matsayin Muballigi,[5] an ambaci sunan Mahaifinsa da sunayen misalin Ba'ura[6] Ba'ur,[7] Awur,[8] da kuma matarsa da sunan Basus.[9] A cewar ba'arin Malaman tafsiri ayar

«وَ اتْلُ عَلَیهِمْ نَبَأَ الَّذِی ءَاتَینَاهُ ءَایاتِنَا فَانسَلَخَ مِنْهَا فَأَتْبَعَهُ الشَّیطَانُ فَکاَنَ مِنَ الْغَاوِین؛

Ka karanta kansu labarin wanda muka bashi ayoyinmu sai ya sabule daga gare su sai Shaidan ya bi shi sai ya kasance cikin halakakku.[10] cewa wannan aya tana Magana kan labarin Bal'am[11] amma tare da haka sun samu sabani kan me ayar take nufi, wasu jama'a daga cikinsu sun tafi kan cewa tana Magana ne kan tsinkayen Bal'am kan Ismul A'azam,[12] da wannan dalili ne ake amsa duk addu'ar da ya yi,[13] wasu kuma sun bawa ayar ma'ana da cewa kansacewarsa Masanin littafin Allah ake Magana bawai tsinkaye kan Ismul A'azam ba.[14]

Fadowarsa Daga Madaukakan Mukmamai

Kan asasin aya ta 175 Suratul A'araf, kasancewar Bal'am ya san ayoyin Allah amma tare da haka Shaidan ya yaudare shi ya batar da shi,[15] dangane da sababin batansa akwai ra'ayoyi Mabambanta, daga jumlarsu akwai: Hakika Bal'am ya juya ya koma kishiyantar Hazrat Musa (A.S) ya kuma dinga taimakawa Fir'auna.[16] A rahotan Mas'udi cikin littafin Isbatul Wasiyya ya bayyana cewa Bal'am ya taimaki Sarkin Kasarsa cikin rigimarsa da Yakinsa da Hazrat Yusha'u (A.S) da Banu Isra'ila.[17] Allama Tabataba'i, yana gani sababin batansa ya samu daga karkatuwarsa zuwa ga son jin dadin duniya da damfaruwa da ita.[18]

Mabambantan Kissoshi

Zanen surar Bal'am lokacin da ya tafi la'antar Annabi Musa (A.S) da mutanensa da yadda Jakinsa ya tsaya ƙyam ya ƙi motsawa sakamakon ganin Mala'ika

An nakalto Kissoshi daban-daban dangane da Bal'am, wasu adadin Malaman Tafsiri suna ganin wadannan riwayoyi da suka ka zo kan Kissarsa suna daga cikin Isra'iliyyat ba za a iya dogara da su,[19] ba'arin wadannan riwayoyi sune kamar haka: Bal'am ya nemi ganin bayan Rundunar Annabi Musa (A.S) da wannan dalili ne ma ya nemi Sarki ya tura Mata su je su tarbi Banu Isra'ila me yiwuwa su aikata Zina da su sai Allah ya halaka su.[20] An yiwa Bal'am Alkawarin amsa masa addu'o'i guda uku, sai matarsa ta nemi a kebanceta da guda daya, sai Bal'am ya yarda, ta nemi ya yi addu'a ta zama mafi kyawun matan Banu Isra'ila, sai ta samu hakan albarkacin addu'arsa, lokacin da ta ga cewa babu macen da ta fi ta Kyawu cikin Banu Isra'ila, sai ta juya masa baya, sakamakon haka ne ya yi addu'a ta koma Kare, sai `ya`yansa suka matsa masa lallai sai ya yi addu'a ta dawo yanda take a da, sai ya yarda ya yi addu'a ta dawo.[21] Kan asasin ba'arin wasu Masadir hakika Bal'am ya hau Jaki domin yin addu'ar la'ana kan Hazrat Musa (A.S) da Mutanensa, sai Jakin yaki motsawa ya tsaya kyam inda yake, Bal'am ya doki wannan Jaki, ya maimaita dukan Jakin nan har sau uku, cikin izinin Allah sai wannan Jaki ya yi Magana ya cewa Bal'am ya ga Mala'iku suna tsayawa a gabansa suna hana shi motsawa.[22] wannan Kissa a cikin At-Taura ma ta zo.[23]

Bayanin kula

  1. Kulaini, Al-Kafi, 1407, juzu'i na 8, shafi na 29.
  2. Alameh Majlisi, Bihar Anwar, 1403 AH, juzu'i na 13, shafi na 379.
  3. Faiz Kashani, Tafsir al-Safi, 1415 AH, juzu'i na 2, shafi na 253.
  4. Tabari, Tarikh Tabari, 1387 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 437.
  5. Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1374 AH, juzu'i na 7, shafi na 14.
  6. Ravandi, Kasasu Anbiya'i, 1409H, shafi na 173.
  7. Kulaini, Al-Kafi, 1407, juzu'i na 8, shafi na 29.
  8. Ibn Asaker, Tarihin Madina Damashk, 1415 Hijira, juzu'i na 10, shafi na 396.
  9. Alousi, Ruh al-Ma'ani, 1415 AH, juzu'i na 5, shafi na 104.
  10. Suratul A'araf, aya ta:175.
  11. Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1374 H., juzu'i na 7, shafi na 14; Tabari, Jame al-Bayan, 1412 AH, juzu'i na 9, shafi na 82.
  12. Ayashi, al-Tafseer, 1380 AH, juzu'i na 2, shafi na 42
  13. Bahrani, al-Barhan, 1416 AH, juzu'i na 2, shafi na 615.
  14. Faiz Kashani, Tafsir al-Safi, 1415 AH, juzu'i na 2, shafi.253; Sheikh Tusi, al-Tabayan, juzu'i na 5, shafi na 32.
  15. Qommi, Tafsirin Qummi, 1404H, juzu'i na 1, shafi na 248.
  16. Qommi, Tafsirin Qummi, 1404H, juzu'i na 1, shafi na 248.
  17. Masoudi, Isbatul Wasiyya, 2004, shafi na 65.
  18. Tabatabaei, Al-Mizan, 1390 AH, juzu'i na 8, shafi na 333.
  19. Rashid Reza, Al-Manar, 1990, juzu'i na 9, shafi na 348.
  20. Tabari, Al-Bayan Jame, 1412 AH, juzu'i na 9, shafi na 85.
  21. Ibn Asaker, Tarikh Madina Dimashk, 1415 Hijira, Mujalladi na 10, shafi na 399.
  22. Ibn Kathir, tafsirul al-kur’an al-Azeem, 1419 AH, juzu’i na 3, shafi na 460.
  23. Attaura, Sefer A'adad, 22: 21-32.

Nassoshi

  • Alousi, Seyyed Mahmoud, Ruh al-Ma'ani fi Tafsir al-Qur'an al-Azeem, Research: Ali Abdulbari Attiyah, Beirut, Dar al-Kutb al-Alamiya, bugu na farko, 1415 AH.
  • Ayashi, Mohammad Bin Masud, al-Tafseer, malami kuma mai karantawa, Seyyed Hashem Rasouli Mahalati, Tehran, Al-Matabah Al-Alamiya, bugu na farko, 1380H.
  • Bahrani, Seyyed Hashem, Al-Barhan fi Tafsirin Qur'an, Tehran, Ba'ath Foundation, bugu na farko, 1416H.
  • Faiz Kashani, Mhilmasan, Tafsir al-Safi, Bincike: Alami, Hossein, Tehran, Sadr Publications, bugu na biyu, 1415 AH.
  • Ibn Asaker, Ali Ibn Hasan, Tarikh Madina Damashk, Beirut, Darul Fikr, 1415 Hijira.
  • Ibn Kathir Damaschi, Ismail bin Amr, Tafsir al-Qur'an al-Azeem, research: Muhammad Hossein Shams al-Din, Beirut, Dar al-Kitab al-Alamiya, Muhammad Ali Bizoon's pamplets, bugu na farko, 1419 AH.
  • Kilini, Muhammad bin Yaqub, al-Kafi, mai bincike kuma mai bincike: Ali Akbar Ghafari, Akhundi, Muhammad, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiyya, bugu na 4, 1407H.
  • Makarem Shirazi, Nasser, Tafsir Namuneh, Tehran, Dar al-Katb al-Islamiyya, bugun farko, 1374.
  • Masoudi, Ali bin Hossein, Isbatul wasiyya Imam Ali bin Abi Talib, Qum, Ansarian Publications, bugu na uku, 2004.
  • Qommi, Ali bin Ibrahim, Tafsir al-Qami, mai bincike kuma mai gyara: Seyyed Tayyeb Mousavi Jazayari, Qum, Darul Kitab, bugu na uku, 1404H.
  • Qutbuddin Ravandi, Saeed bin Hibatullah, Qasas al-Anbiyyah (amincin Allah ya tabbata a gare su), mai bincike kuma edita: Gholamreza Irfanian Yazdi, Mashhad, Cibiyar Nazarin Musulunci, bugu na farko, 1409H.
  • Rashid Reza, Tafsir al-Manar, Egypt, Al-Masriyyah Al-Masriyya na Littafi, 1990.
  • Tabari, Muhammad Bin Jarir, Tarihin Al'ummai da Al-Muluk, Binciken Muhammad Abul-Fazl Ibrahim, Beirut, Dar Al-Tarath, 1387H.
  • Tabari, Muhammad bin Jarir, Jame al-Bayan fi Tafsirin Kur'ani, Beirut, Darul Marafa, bugun farko, 1412H.