Ayar shaida

Daga wikishia

Ayar shaida itace ayata goma sha bakwai 17 acikin suratul hud, wadda take tabbatar da haƙiƙanin gaskiyar annabtar manzon Allah (s.a.w.w) wadda ta kasance ta hanyar ƙur'ani maigirma da Muminai na haƙiƙa dakuma littatafanda aka saukar daga sama. Waɗanda suka gabaci Al-ƙurani. Sai wannan aya ta sauka bayan kafurai sun ƙaryata Annabtar manzon Allah (s.a.w.w ) domin tausasar sa dakuma ƙarfafa imaninsa.

Yazo cikin littatafan tafsiri dakuma ruwayoyi na ɓangaren shi’a da sunna cewa abinda ake nufi da shaida a cikin wannan ayar shine imam ali (as) ɗan abi ɗalib. Hakanan wasu ruwayoyin sun ambaci jibrilu dakuma shi kanshi manzon Allah a matsayin shaida , wasu kuma sukace Al-ƙurani ne. Hakanan ana hujjantar da ayar shaida kan tabbatar da wulayar imam Ali ɗan abi ɗalib (imamanci) da khilafarsa (shugabanci) sabida siyaƙin ayar babu makawa manzon Allah shine shaida, Don haka kasancewar ayar mubahala (fito na fito) tanuna imam Ali kansa shine annabi kansa, hakan annabi shine imam ali kansa.

Nassin Aya

Ayata goma sha bakwai 17 tayi shuhura kuma ta sanu da ayar shaida.

(افمن كان على بيينة من ربه ويتلوه شاهد منه ومن قبله كتب موسى اماما ورحمة ، أولئك يؤمنون به ، ومن يكفر به من الأحزاب فالنار موعدهم فلا تك فى مرية منه انه الحق من ربك ولكن أكثر الناس لا يؤمنون)

Abinda Ayar Ta Kunsa

Allama ɗaba ɗaba’i acikin tafsirin Al’mizan yace ana fahimta daga zahirin ayar cewa ta saukane domin tsarkake manzon ALLAH dakuma karfafarsa kan abinda Allah ya saukar masa . Wanda ubangiji ya umar ceshi daya kalubalanci mushirikai akan sukawo koda aya 10 ce kwatan kwacin al-kurani.

Yazo cikin tafsirin amsal dakuma majma'ul bayan mahanga guda biyu. Mahanga Ta Farko

Abinda ake nufi da

افمن كان على بثينة منه به

shine manzon ALLAH ta hanyar tabbatar da gaskiyar annabtakar sa.

Ta hanya uku 3 . 1:- kasancewar al-kurani hujja bayyanan niya akankansa 2:- littattafan da aka saukar daga sama wanda suka gabata irinsu at-taura dasukayi nuni izuwa siffofin manzon ALLAH bayyanannu 3:- imaninda mabiya annabi kedashi wajen temakon sa, da temakon muminai, tayanda kowacce matafiya tana sanuwa da magoya bayan wannan tafiyar.

Mahanga Ta Biyu

Abinda ake nufi da

افمن كان على بينة من ربه

gaba dayan muminan da sukayi imani bayan bayyanar hujjoji daga annabi karara kuma afili, bayaga gasgatashi da littattafan da’aka saukar daga sama sukayi kan annabtar sa.

Sannan ma’anar البيّنة allama daba ɗaba’i yace hujjace wacce take bayyananniya me bayyanar da wasunta kamar haske,

Allama ɗabrasi kuma yace

بينة من ربه

tana nufin hujja daga hankalinsa.

Wanene Shaida

Wasu daga malaman tafsiri na shi’a da sunna suntafi akan cewa shaida acikin ayata goma shabakwai 17 ta suratu hud , shine imam Ali dan abi dalib kasan cewarsa farkon wanda yayi imani da annabi muhammad s.a.w.w Sannan yazo daga riwayar imam Ali kan tabbatar da shine shaida da kansa acikin ayar. Hakim al_haskani ya rawaito cikin littafinsa SHAWAHIDUT-TANZIL riwayoyi shabiyar 15 wadanda ke bayyana imam ali amatsayin shaida cikin ayar.

Daga cikin riwayoyin akwai riwayar anas dan malik kancewa

افمن كان على بينة من ربه

yace shine imam Ali dan abi dalib, sannan imam Ali ya kasance harsher manzon ALLAH (wakilinsa) zuwaga mushirikan makka alokacin da suka saba al-ƙawarinsu da annabi.

Akwai wasu riwayoyin (ƊAB-RASIY) daban akan abinda ake nufi da shaida acikin ayar shine Jibrilu , sakamakon shine me karantawa manzon ALLAH wahayi (al-kurani) daga ALLAH, wasu kuma suka tafi akan cewa shaida shine harsher manzon ALLAH wanda yake karanta al-kurani dashi aduk lokacinda yake karatu, Wasu kuma suka tafi kan cewa al-kurani kansa shine shaida . Saidai allama ɗaba ɗaba’i yayi raddi akan sauran ra’ayoyin sannan ya yakafa hujja da riwayoyi abisa kasancewa imam alai shine shaida acikin wanna ayar.

Dalilai Kan Tabbatar Da Wilayar Imam Ali Da Halifancinsa

Tabbatar da matsayin wulaya (imamanci) dakuma halifancin (shugabanci) imam Ali, . Wasu daga masana dakuma tahkiki sunce kalmarيتلوه dake cikin ayar shaida tana nufin يتّبعه da ma’anar yana binsa ba yana karantashiba , sabida lamirin يتلوه acikin منه yana komawa ne izuwa افمن a farkon ayar, bisa hakane abin nufi da lamirin منه shine wanda yake da alaka ma'anawiyya da zatiyyar manzon ALLAH, kuma na nufin shi annabin akan kansa.

kamar yadda fi’ili mudhari’I yake nuni da cigaba acikin aiki dakuma bada sakamakon manzon allah dai shine shaida acikin dukkanin matakai da zamun, wanda shine dacewar matsayin halifanci da imamanci zuwa ga wasiyyin manzon allah wato imam Ali, wanda aka bayyanashi a matsayin annabin kansa ta hanyar riwayoyi dakuma ayar mubahala (fito na fito) wato imam Ali.

Mahanga A Cikin Attaura

An ambaci littafi daya daga cikin littattafan da aka saukar (AT-TAURA) acikin ayar shaida, dalilin hakan shine watsuwar ra’ayoyin yahudawa da abinda sukayi imani dashi a cikin al’umm, dakuma yanayin da Alkur'ani ya sauka aciki da mabiya addinin nasara dake garuruwan sham da yaman, ƙarin dalili kuma shine ambaton suffofin manzon allah dayazo cikin at-taura a bayyane.