Annabi Ayyuba (A.S)

Daga wikishia
(an turo daga Annabi Ayyuba)
Annabi Ayyuba (a.s)

Annabi Ayyuba (Larabci: النبي أيوب (ع)) ɗaya ne daga cikin Annabawan Allah wanda Allah ya jarraba shi da rasa dukiyarsa da ƴaƴansa da kuma ciwo, haƙiƙa ya yi haƙuri kan jarrabawar Allah a kansa bai taɓa raunana cikin ibada da godiya ga Allah ba, da wannan dalili aka ambaci kyautatawarsa a cikin Alkur'ani. Alkuir'ani bai kawo cikakken bayanin kan ibtila'in Ayyuba (A.S) ba amma cikin tsohon Alƙawari (Old Testment) da cikin ba'arin wasu riwayoyin muslunci an naƙalto yanda abun ya faru, haƙiƙa munanar ciwon da aka jarraba Annabi Ayyuba (A.S) ta kai ga mutane suna gudunsa, na'am a imanin Musulmai duk wani abu zai sanya mutane su kyamaci Annabawa an nesanta su da shi babu shi tare da su, cikin tsohon Alƙawari da cikin ba'arin wasu riwayoyin muslunci an hakaito ƙosawa da rashin haƙurin Ayyuba kan bala'in da yake ciki da Allah ya jarraba shi da shi, amma a cikin Alkur'ani an bayyana shi matsayin wanda ya yi haƙuri da juriya cikin wannan ibtila'i. Wasu ba'ari tare da dogara da wannan ayar

«واذْکُرْ عَبْدَنَا أَیُّوبَ إِذْ نَادَىٰ رَبَّهُ أَنِّی مَسَّنِیَ الشَّیْطَانُ بِنُصْبٍ وَعَذَابٍ»،

Kuma ka ambaci bawanmu Ayyuba yayin da ya kirayi Ubangijinsa lallai Shaiɗan ya Shafeni da wahala da kuma wata azaba. Wanann aya ta yi magana kan tasirin Shaiɗan kan Ayyuba wannan ya sanya wasu suka yi shakku da kokwanto kan Ismarsa, sai dai cewa kishiyar haka an ce daidai da abin da ya zo a zahirin ayar tasirin Shaiɗan ya taƙaitu a kan gangar jikin Ayyuba (A.S) bai yi tasiri a kan Nafsu ɗinsa ba da har zai iya haifar da matsala da tawaya cikin ismarsa, haka kuma kan asasin ayoyin Alkur'ani Shaiɗan baya samu iko kan nafsu da ruhin Bayin Allah nagargaru, kuma cikin Alkurt'ani an bayyana Ayyuba a matsayin bawan Allah nagari Malaman tafsiri suna cewa, Ayyuba ya yi rantsuwa da Allah bisa kuskure da matarsa ta aikata sai ya yi mata bulala ɗari, sai dai cewa ya janye bai mata bulalar ba, bayan janyewa, sakamakon rantsuwa da ya yi sai aka yi masa wahayi cewa ya ɗauki siraran sanduna ya buga su kan matarsa kada ya karya rantsuwar da ya yi, sai dai cewa tare da haka akwai saɓani tsakanin Malaman tafsiri kan dalilin da ya sanya shi rantsuwa. Babu cikakken rahoto game da inda aka binne Ayyuba (A.S) amma tare da haka an danganta wasu ƙaburbura a ƙasashe daban-daban zuwa ga Ayyuba (A.S), daga jumlarsu akwai akwai wani ƙabari a garin Ar-Ranajiyyatu da yake da nisan kilomita goma daga kudancin garin Hilla a ƙasar Iraƙi

Nasaba Da Dangi

Ayyuba ɗaya ne daga Annabawan Allah[1] da ya fito daga tsatson Annabi Ibrahim (A.S)[2] nasabarsa ta danganewa ga Annabi Ibrahin bayan mutane huɗu[3] ko biyar,[4] haka kuma ta ɓangaren Mahaifiyarsa ya kasance daga jikokin Annabi Luɗ (A.S)[5] akwai saɓanin Malamai dangane da matarsa, a cewar Allama Majlisi, abin da ya shahara matar Ayyuba (A.S) ta kasance daga jikokin Annabi Yusuf (A.S) ma'ana ƴa ga Misha ɗan Annabi Yusuf (A.S)[6] na'am a wasu riwayoyin an kawo cewa ƴar Yusuf (A.S)[7] a wasu riwayoyin kuma ƴar Annabi Yaƙub (A.S),[8] a wasu ba'ari suna ganin Zul-Kifli matsayin ɗa ga Ayyuba kuma ɗaya daga cikin Annabawa.[9]

Jarrabawar Allah

Asalin Maƙala: Haƙurin Ayyuba

Bisa ayoyin Alkur'ani, Ayyuba tare da rasa dukiyarsa da ƴaƴansa da kuma kamuwa da ciwo ya karɓi jarrabawar Allah kuma ya yi haƙuri cikin wannan jarrabawa daga Ubangiji.[10] bayan nan an dawo masa da lafiyarsa da ƴaƴansa,[11] haka kuma kan asasin abin da ya zo a riwayoyi Ayyuba ya kasance ma'abocin dukiya mai tarin yawa sai dai cewa duk ya rasata sakamakon wannan ibtila'i daga Ubangiji,[12] Alkur'ani ya kira Ayyuba da sunan (Bayinmu) Madalla da wannan bawa,[13] (bawan Allah nagari), mai haƙuri, Awwabu (mai komawa ga Allah).[14]

Radif Matanin Aya Sura Aya Game da
1 وَوَهَبْنَا لَهُ إِسْحَاقَ وَیَعْقُوبَ کُلًّا هَدَیْنَا وَنُوحًا هَدَیْنَا مِنْ قَبْلُ وَمِنْ ذُرِّیَّتِهِ دَاوُودَ وَسُلَیْمَانَ وَأَیُّوبَ وَیُوسُفَ وَمُوسَىٰ وَهَارُونَ وَکَذَٰلِکَ نَجْزِی الْمُحْسِنِینَ

kuma muka bashi Is'haƙ da Yaƙubu dukkaninsu mun shiriyar da su kuma mun shiryar da Nuhu tun gabaninsu da zuriyarsa Dauda da Sulaiman da Yusuf da Musa da Haruna haka muke sakawa masu kyautata aiki

An'am 84 kasancewar Ayyuba daga tsatson Nuhu ko Ibrahim[Tsokaci 1]
2 إِنَّا أَوْحَیْنَا إِلَیْکَ کَمَا أَوْحَیْنَا إِلَىٰ نُوحٍ وَالنَّبِیِّینَ مِنْ بَعْدِهِ وَأَوْحَیْنَا إِلَىٰ إِبْرَاهِیمَ وَإِسْمَاعِیلَ وَإِسْحَاقَ وَیَعْقُوبَ وَالْأَسْبَاطِ وَعِیسَىٰ وَأَیُّوبَ وَیُونُسَ وَهَارُونَ وَسُلَیْمَانَ وَآتَیْنَا دَاوُودَ زَبُورًا

lallai mu mun yi wahayi zuwa gareka kamar yanda muka yi wahayi zuwa ga Nuhu da Annabawa daga bayansa kuma mun yi wahayi zuwa ga Ibrahim da Isma'ila da Yaƙubu da jikoki da Isa da Ayyuba da Haruna da Yunusa da Sulaiman kuma mun bai wa Dauda Zabura.

Nisa 163 Annabta
3 وَأَيُّوبَ إِذْ نَادَىٰ رَبَّهُ أَنِّي مَسَّنِيَ الضُّرُّ وَأَنْتَ أَرْحَمُ الرَّاحِمِينَ ﴿83﴾ فَاسْتَجَبْنَا لَهُ فَكَشَفْنَا مَا بِهِ مِنْ ضُرٍّ وَآتَيْنَاهُ أَهْلَهُ وَمِثْلَهُمْ مَعَهُمْ رَحْمَةً مِنْ عِنْدِنَا وَذِكْرَىٰ لِلْعَابِدِينَ

kuma da Ayyuba lokacin da ya kira Ubangijinsa lallai ni Shaiɗan ya shafeni da wahala da azaba alhali kai ne Mafi rahamar masu rahama

Anbiya 83-84 Amsa addu'arsa da dawo masa da lafiya da `ya`yansa.
۴ واذْكُرْ عَبْدَنَا أَيُّوبَ إِذْ نَادَىٰ رَبَّهُ أَنِّي مَسَّنِيَ الشَّيْطَانُ بِنُصْبٍ وَعَذَابٍ ﴿٤١﴾

ka ambaci bawanmu Ayyuba lokacin da ya kira Ubangijinsa lallai ni Shaiɗan ya shafeni da wahala da azaba (41)

ارْكُضْ بِرِجْلِكَ ۖ هَٰذَا مُغْتَسَلٌ بَارِدٌ وَشَرَابٌ٤٢﴾

ka shura da ƙafarƙa wannan abin wanka ne mai sanyi da abin sha (42)

وَوَهَبْنَا لَهُ أَهْلَهُ وَمِثْلَهُمْ مَعَهُمْ رَحْمَةً مِنَّا وَذِكْرَىٰ لِأُولِي الْأَلْبَابِ ﴿43

kuma muka bashi mutanensa da misalinsu rahama daga garemu da tunatarwa ga masu hanakli (43)

وَخُذْ بِيَدِكَ ضِغْثًا فَاضْرِبْ بِهِ وَلَا تَحْنَثْ ۗ إِنَّا وَجَدْنَاهُ صَابِرًا ۚ نِعْمَ الْعَبْدُ ۖ إِنَّهُ أَوَّابٌ ﴿٤٤﴾

ka riki ƙulla da hannunka ka buga kada ka karya rantsuwa, lallai mu mun same shi mai haƙuri, madalla da bawa lallai shi mai mayar da ala'ari ne ga Ubangiji (44)

Suratul Sad 41-44 warkewa da ciwo da dawowar iyalansa da labarin rantsuwar da ya yi haƙurin Ayyuba da kuma kasancewarsa mai yawan koma ga Allah.

Labarin Ibtila'in Ayyuba

Addu'a da aka dangantata zuwa ga Ayyuba

Addu'an da aka dangantata ga Ayyuba (a.s)

اللَّهُمَّ إِنِّی أَعُوذُ بِکَ الْیَوْمَ فَأَعِذْنِی وَ أَسْتَجِیرُ بِکَ الْیَوْمَ مِنْ جَهْدِ الْبَلَاءِ فَأَجِرْنِی وَ أَسْتَغِیثُ بِکَ الْیَوْمَ فَأَغِثْنِی وَ أَسْتَصْرِخُک الْیَوْمَ عَلَى عَدُوِّکَ وَ عَدُوِّی فَاصْرُخْنِی وَ أَسْتَنْصِرُکَ الْیَوْمَ فَانْصُرْنِی وَ أَسْتَعِینُ

فَارْحَمْنِی.»بِکَ الْیَوْمَ عَلَى أَمْرِی فَأَعِنِّی وَ أَتَوَکَّلُ عَلَیْکَ فَاکْفِنِی وَ أَعْتَصِمُ‏ بِکَ فَاعْصِمْنِی وَ آمَنُ بِکَ فَآمِنِّی وَ أَسْأَلُکَ فَأَعْطِنِی وَ أَسْتَرْزِقُکَ فَارْزُقْنِی وَ أَسْتَغْفِرُکَ فَاغْفِرْ لِی وَ أَدْعُوکَ فَاذْکُرْنِی وَ أَسْتَرْحِمُکَ

[15].[16]

Kaf'ami, al-Masbah (Jannah al-Aman al-Waqiyyah), 1405 AH, shafi 296-297

Kan asasin wata riwaya da aka naƙalto daga Imam Sadiƙ (A.S) Allah ya baiwa Ayyuba Ni'ima a ko da yaushe baya sakaci da godewa Allah har zuwa wata rana da Shaiɗan ya fahimci yawan godiyar da Ayyuba yake yi ga Ubangijinsa sai ya yi masa hassada yace, ya Allah da za ka kwace wannan ni'imomin da ka yiwa Ayyuba ba zai ƙara maka godiya ba kan ni'ima, sai Allah ya kwace dukiya da ƴaƴan Ayyuba, komai ya tafi babu abin da ya rage gare shi, sai Ayyuba ya ƙara ƙaimi cikin godiya ga Allah, bayan nan sai Iblis ya yi busa kan jikin Ayyuba ya jijji masa ciwo a jikinsa tsutsotsi suka faɗa kan waɗanann ciwuka, sakamakon warin ciwonsa sai mutanen gari suka fitar da shi daga cikin garin, amma duk da haka Ayyuba bai gushe ba yana godiya ga Allah, sai Shaiɗan tare da wasu adadin Sahabban Ayyuba suka je wurinsa suka ce masa, mu fa muna tunanin wannan bala'in ya sameka ne sakamakon wani zunubi da ka aikata! Ayyuba ya ranste da Allah bai taɓa cin abinci sai tare da maraya ko mai rauni, kuma bai taɓa haɗuwa da ɗa'ar Allah guda biyu face ya zaɓi wacce tafi wahala, bayan nan sai Allah ya aiko da Mala'ika ya shimfiɗar da ƙafarsa a kan ƙasa aka zuba ruwa akai Ayyuba ya wanke ƙafarsa ciwon ya tafi ya samu lafiya.[17] Allama ɗabaɗaba'i yana ganin wannan riwaya ba ta dacewa da sauran riwayoyi da suka zo daga Ahlul-Baiti (A.S)[18] an naƙalto daga Imam Muhammad Baƙir (A.S) cewa wani abu mai kama da kamuwa da ciwo, tsutsotsi da munanar fuska samsam bai faru a jikin Ayyuba ba, bari dai dalilin nesantuwar mutane daga gare shi ya faru sakamakon rashin kuɗaɗe da rauni na zahiri, saboda mutane ba su da labari kan matsayinsa a wurin Allah, kuma ba su san cewa zai warke da wuri ba.[19] haka kuma riwayar da aka ambata tana cin karo da sauran riwayoyi da kan asasinsu ake lissafa Ayyuba da sauran Annabawa matsayin Ma'asumai[20] daga duk wani aibu da zai sanya mutane su guje su, saboda nesantuwar mutane daga gare su baya dacewa da hadafin aiko da Annabawa (Isar da saƙon Allah zuwa ga mutane).[21]

Rahotannin Littafi Mai Tsarki

Kitab Ayyub ɗaya daga cikin littafai guda 39 a tsohon Alƙawari, cikin wannan littafi an kawo rahota daga ni'imon Allah ga Ayyuba,[22] labarin jarraba shi, mamayar Shaiɗan kan duniyarsa da ransa,[23] da kuma yunƙurin wasu adadin matasa domin hana Ayyuba aikata kuskure,[24] sun ce a cikin tsohon Alƙawari da ya zo game da Ayyuba, saɓanin abin da ya zo daga Alkur'an cikin bayyana Ayyuba a matsayin wanda ya yi haƙuri kan jarrabawar Ubangiji, sai ya zamana tsohon Alƙawari ya bayyana shi matsayin wanda bai yi haƙuri ba, kuma bai kasance mai godiya kan jarrabawar Allah ba,[25] haka kuma cikin littafin Mai tsarki ba a kawo batun rantsuwar Ayyuba ba.[26]

Falsafar Ibtila'in Ayyuba

Ibtila'in Ayyuba da ciwo da kuma rasa ƴaƴansa wata jarrabawa ce da ta kasance daga Allah, a cewar Ƙurɗabi daga Malaman tafsiri na Ahlus-sunna, halin Ayyuba bai banbantu ba kafin jarraba shi da lokacin jarrabawa da bayan jarrabawa duka bai gushe ba yana ta godiya ga Allah,[27] haka kan asasin wata riwaya da Allama Ɗabaɗaba'i ya naƙaltota, ibtila'in Ayyuba ya kasance don gudun ka da mutane su jingina masa ubangijintaka sakamakon tarin ni'imomin da Allah ya bashi, da kuma gudun Allantar da shi, haka kuma ya zamana sun wa'aztu da halin ya shiga ka da su dinga wulaƙanta rarrauna ko talaka sakamakon rashin lafiya da talauci, saboda zai iya yiwuwa Allah ya mayar da rarrauna mai ƙarfi haka talaka ya mayar da shi mawadaci ya kuma warkar da mara lafiya, haka kuma su sani cewa shi Allah idan ya so zai iya jarraba kowanne mutum da rashin lafiya ko da kuwa Annabinsa ne, idan ya so zai iya warkar da kowanne mutum daga ciwon da yake fama da shi.[28]

Rantsuwar Ayyuba

Lokacin da Ayyuba yake fama da rashin lafiya ya yi rantsuwa duk sanda ya warke ya samu lafiya sai ya yiwa matarsa bulala ɗari,[29] tare da haka bayan ya samu lafiya, sakamakon cika alƙawari da matarsa ta yi cikin yi masa hidima sai ya ƙudurci yafe mata, sai dai cewa rantsuwar da ya yi ta hana shi.[30] da wannan dalili ne aka yi masa wahayi aka umarce shi ya ɗauki siraran sanduna ya buga kan matarsa ba tare da karya rantsuwar da ya yi ba.[31] Dangane da me yasa Ayyuba ya yi rantsuwa akwai saɓani kan wannan Magana a tsakanin Malaman tafsiri: an naƙalto daga Ibn Abbas cewa Shaiɗan ya je wurin matar Ayyuba ya ce mata: zan bawa mijinki magani ya warke, amma da sharaɗi idan ya warke ki gaya masa ni Shaiɗan ni ne sababin warkewarsa, sakamakon gajiyar da matar Ayyuba ta daga fama da wannan ciwo nasa sai ta yarda da sharaɗin Shaiɗan, wannan dalili yasa Ayyuba ya yi rantsuwa sai ya yi mata bulala ɗari bayan samun lafiyarsa,[32] wasu kuma sun ce ainahi shi ne Ayyuba ya aike ta zuwa wani aiki sai ta makara, wanda makararta ya haifar da ƙarin wahala kansa cikin ciwon, sai ransa ya ɓaci sai ya yi wannan rantsuwa,[33] wasu kuma sun ce illar yin rantsuwarsa ta faru ne sakamakon faruwar wani abu[34] tsakaninsa da matarsa sai maganar da ta yi ta cutar da shi.[35] Kan asasin wata riwaya, ƙissar rantsuwar Ayyuba ta faru ne bayan warkewarsa: lokacin da bai da lafiya ya zauna ne a wajen gari, sai matarsa ta shiga cikin gari domin samo gurasa da sai ta sayar da gashin kanta, lokacin da ta dawo wurin Ayyuba tuni ya riga ya warke daga ciwon, sai ya fahimci cewa ta aske gashinta, da wannan dalili ne ya yi rantsuwa sai ya yi mata bulala ɗari, bayan ya gano dalilin da yasa ta aske gashinta sai ya yi nadama,[36] na'am cikin ingancin wannan riwaya daga fuskanin tufka da warwara da take yi tare da Aƙidun Shi'a dangane da Ismar Annabawa[37] da kuma cin karonta da sauran riwayoyi[38] gaggawar yanke hukuncin da Ayyuba ya yi, munana zato kan matarsa da kuma ayyana uƙuba kanta tun kafin tambayarta abin da ya faru da kuma kasancewar ɗaya daga cikin marawaitan wannan riwaya ba a san kowaye shi ba, hakan ya haifar da kokwanto da shakku kan wannan riwaya.[39] Wasu ba'ari Malaman tafsiri Ahlus-sunna sun yi istinbaɗi daga ƙissar Ayyuba cewa Miji zai iya ladabtar da matarsa ta hanyar dukanta.[40]

Isma

Wasu ba'ari tare da jingina da wannan ayar

[41]

«واذْکُرْ عَبْدَنَا أَیُّوبَ إِذْ نَادَىٰ رَبَّهُ أَنِّی مَسَّنِیَ الشَّیْطَانُ بِنُصْبٍ وَعَذَابٍ »

Sun ishara zuwa ga tasirin da Shaiɗan ya yi cikin samuwar Ayyuba sun kuma nuna shakku kan ismarsa, dalilinsu shi ne asasin wannan aya, Ayyuba ya faɗa wahala da azaba sakamakon tasirin shafar Shaiɗan kansa wanda hakan ba ya dacewa da Isma.[42] cikin basu amsa an ce Shaiɗan bai samu iko kan nafsu ɗin Ayyuba da har ismarsa za ta kai ga samun matsala da tawaya, bari dai ya yi tasiri ne kaɗai a kan gangar jikinsa dukiyarsa da ƴaƴansa,[43] saboda kan asasin ayar

«إِنَّ عِبَادِی لَیْسَ لَکَ عَلَیْهِمْ سُلْطَانٌ؛
Makwanci da ake danganta shi ga Annabi Ayyuba (a.s) a garin Bukhara

Lallai baka da iko kan bayina.[44] Shaiɗan bashi da kowacce irin Sulɗa kan bayin Allah nagargaru kan asasin aya ta 41 Suratu Sad, haƙiƙa Ayyuba ya kasance Bawan Allah.[45] Cikin littafin Tazihul Al-Anbiya wanda aka rubuta shi dangane da Ismar Annabawa, an yi bahasi kan ismar Ayyuba.[46] Wurin Da Aka Binne Shi Ayyuba ya rayu a yankin Uwaisi kudu maso yammacin Bahrul Al-mayyit kuma arewacin Khalij Aƙbatu ko kuma a yankin Basaniyya tsakanin Dimashƙ da Azri'at,[47] haka kuma a garin Arufa na ƙasar Turkiyya akwai wani Kogo da ake cewa a cikinsa ne Ayyuba ya zauna lokacin da yake fama da rashin lafiya.[48] Sun ce Ayyuba ya rayu shekaru ɗari biyu,[49] kan asasin rahotan Ahadul Atiƙ (Tsohon Alƙawari) ya rayu shekaru 140 bayan warkewa daga ciwo,[50] haka kuma kan asasin rahotan da ya zo daga riwayoyi Ayyuba ya sha fama da ciwo tsawon shekaru bakwai[51] ko sha takwas[52] ya zauna kusa da idon wani ruwa da a nan wurin ne ya warke daga ciwon da ya yi ta fama da shi kuma anan aka binne shi,[53] babu cikakken bayani da rahoto dangane da wurin da aka binne shi, amma tare da haka akwai ƙaburbura a ƙasashe daban-daban da ake danganta su ga Ayyuba misalin ƙasar Iraƙ, Lubnan, Falasɗinu da Amman,[54] daga jumlarsu akwai maƙabartar da take yankin Ar-Ranajiyya mai nisan kilomita goma da kudancin Hilla da take ƙasar Iraƙi ance sakamakon kusancinta da inda ya zauna wannan gari ya samu shahara sosai.[55] Haka kuma cikin nisan kilomita bakwai Bandar Sulala da yake saman Dutsen Atin a ƙasar Amman, haka cikin wani ƙauye da ake kira Garmab a geffan Bajnawardi ta ƙasar Iran, da kuma garin Bukhara na ƙasar Uzbekistan nan ma akwai Maƙabartu da ake damganta su da Ayyuba,[56] na'am akwai tsammanin Maƙabartar da ake danganta ta da Ayyuba wacce take Uzbekistan ta samu ne alokacin mulkin Taimuri da Taimur Lange.[57]

Ayyuka Fasaha

Asalin Maƙala: Annabi Ayyuba (Fim)

ƙissar Ayyuba a cikin ayyukan fasahar Fim din Ayub Annabi, wanda ya bada umarni Farajullahi Salehshu, wanda aka yi shi a shekara ta 1372 kuma aka watsa shi a gidan talabijin na Iran, ya shafi rayuwar Ayyuba da rashin lafiyarsa.[58]

Bayanin kula

  1. Suratul Nisa’i, aya ta 163
  2. Suratul An'am, aya ta 84.
  3. Ibn Habib, Al-Muhabbar, Dar Afaƙ al-Jadideh, shafi na 5.
  4. Majlesi, Hayat al-ƙulob, 2004, juzu'i na 1, shafi na 555; Thaalbi, Al-Kashf wa Al-Bayan, 1422H, Mujalladi na 6, shafi na 287.
  5. Majlesi, Hayat al-ƙulob, 2004, juzu'i na 1, shafi na 555; Thaalbi, Al-Kashf wa Al-Bayan, 1422H, Mujalladi na 6, shafi na 287.
  6. Tabataba'i, Al-Mizan, Manshurat Ismailian, juzu'i na 17, shafi na 214; Majlisi, Hayat al-ƙulob, 2004, juzu'i na 1, shafi na 555
  7. ƙommi, Tafsirul ƙummi, 1404H, juzu'i na 2, shafi na 242-239
  8. Majlisi, Hayat al-ƙulob, 2004, juzu'i na 1, shafi na 555
  9. Tabari, Tarikh Al-Umam wa al-Muluk, 1387 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 325.
  10. Suratul Saad, aya ta 44.
  11. Suratul Anbiya, aya ta:84.
  12. Misali duba ƙommi, Tafsirul ƙummi, 1404H, juzu'i na 2, shafi na 242-239.
  13. Jazayeri, ƙasasul Al-Anbiya, 1404H, shafi na 198.
  14. Suratul Sad, aya ta 41-44; Tabataba'i, Al-Mizan, 1417 AH, Mujalladi na 17, shafi na 210-211.
  15. کفعمی، المصباح (جنة الامان الواقیة)، ۱۴۰۵ق، ص۲۹۶-۲۹۷.
  16. Kaf'ami, al-Masbah (Jannah al-Aman al-Waqiyyah), 1405 AH, shafi 296-297
  17. ƙommi, Tafsirin ƙummi, 1404 AH, juzu'i na 2, shafi na 242-239; Majlisi, Hayat al-ƙulob, 2004, juzu'i na 1, shafi na 559-565.
  18. Tabataba'i, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 17, shafi na 214-217.
  19. Sadouƙ, Al-Khisal, 1362, juzu'i na 2, shafi na 399-400.
  20. Tabataba'i, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 17, shafi na 214-217
  21. Abul-Fatuh Razi, Roz al-Janan, 1408 AH, juzu'i na 13, shafi na 213; Sobhani, Manshuru aƙa'id Imamiyya, Mu’assase Imam Al-Sadiƙ, shafi na 114.
  22. Littafi Mai Tsarki, Ayuba, 1:1-6
  23. Littafi Mai Tsarki, Ayuba, 1-2
  24. Littafi Mai Tsarki, Ayuba, 3-27
  25. Kolbasi, “ nakhade wa barasi araye Mufassiran dar tafsiri ayeh 44 Suratul Sad Taziyane zadan beh hamsares” shafi na 120.
  26. Kolbasi, “ nakhade wa barasi araye Mufassiran dar tafsiri ayeh 44 Suratul Sad Taziyane zadan beh hamsares” shafi na 120.
  27. ƙurtubi, Al-Jame Al-Ahkam Al-ƙur'an, 1364, juzu'i na 16, shafi na 216.
  28. Tabataba'i, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 17, shafi na 214-217.
  29. Tabataba'i, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 17, shafi na 210.
  30. Makarem, Tafsir Namuneh, 1374, juzu'i na 19, shafi na 299.
  31. Suratul Sad, aya ta 44; Tabataba'i, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 17, shafi na 210.
  32. Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1374, juzu'i na 19, shafi na 299; Jazayeri, ƙasasu Anbiya, 1404H, shafi na 198.
  33. Duba Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1374, juzu'i 19, shafi na 299.
  34. Mughniyeh, Tafsir al-Kashif, 1424 AH, juzu'i na 6, shafi na 382.
  35. Tabarsi, Majma Al-Bayan, 1372, juzu'i na 8, shafi na 746.
  36. ƙomi, Tafsirin ƙummi, 1404 AH, juzu'i na 2, shafi na 242-239; Majlesi, Hayat al-ƙulob, 2004, juzu'i na 1, shafi na 5565-559.
  37. Abul-Fatuh Razi, Ruz al-Janan, 1408 AH, juzu'i na 13, shafi na 213; Sobhani, Manshur aƙa'id Imamiyya, Mu’assaseh Imam Al-Sadiƙ, shafi na 114.
  38. Tabataba'i, Al-Mizan, 1417 AH, juzu'i na 17, shafi na 214-217.
  39. Kolbasi, “Nakhade wa barasi Araye Mufassirin dar tafsir aye 44 sureh Sad wa Taziyaneh zadane Hamsaresh” shafi na 117.
  40. Jasas, Ahkamul ƙur'an, 1405 AH, juzu'i na 5, shafi na 260.
  41. سوره ص، آیه۴۱.
  42. Duba Nasri, Mabani Risalat Anbiya dar ƙur'an, 2008, shafi na 261-260.
  43. Tabatabai, Al-Mizan, juzu'i na 17, shafi na 209
  44. Suratul Isra, aya ta 65.
  45. Nasri, Mabani Risalat Anbiya dar ƙur'an, 2008, shafi na 261-260.
  46. Seyed Morteza, Tanziyeh al-Anbia, 1250 AH, shafi na 59-64.
  47. Shoghi, Atlas Kur'an, 2008, shafi na 109.
  48. Bayazar Shirazi, Bastanshinasi wa Jografiyayi tarikhi ƙasas ƙur'an, 2006, shafi na 350.
  49. Ibn Habib, Al-Muhabbar, Dar Afaƙ al-Jadideh, shafi na 5.
  50. Littafi Mai Tsarki, Ayuba 1:42.
  51. Jazayeri, ƙasas Anbiya, 1404 Hijira, shafi na 198 da 200.
  52. Bahrani, Al-Burhan, 1416 AH, juzu'i na 4, shafi na 672; Jazayeri,ƙasas Anbiya, 1404H, shafi na 207.
  53. Bahrani, Al-Burhan, 1416 AH, juzu'i na 4, shafi na 675.
  54. <a class="eɗternal teɗt" href="http://mk.iƙ/ɓiew.php?id=241&amp;amp;amp;amp;ids=3">مرقد نبی الله ایوب (علیه‌اسلام)</a>
  55. Raminnejad, Mazare Payambaran, 2007, shafi na 59-63.
  56. Raminnejad, Mazare Payambaran, 2007, shafi na 59-63.
  57. Raminnejad, Mazare Payambaran, 2007, shafi na 59-63.
  58. <a class="eɗternal teɗt" href="http://www.sourehcinema.com/Title/FullOutline.aspɗ?FilmId=138109211661&amp;amp;amp;amp;IsTowLine=False">خلاصه داستان فیلم ایوب پیامبر</a>

Tsokaci

  1. Allama Tabataba'i lamirin da ya zo a kalmar zurriyatuhu yana komawa zuwa ga Nuhu, na'am wannan baya karo da kasancewa Ayyuba a zuriyar Ibrahim.(Tabataba'i, Almizan , 1417 shams Q. j 7 shafi na 242)

Nassoshi

  • Alƙur'anul Al-kareem.
  • Kitabu Muƙaddas.
  • Ibn Habib al-Baghdadi, Muhammad ibn Habib, Al-Mohbar, Ilza Lichten-Steiter's research, Beirut, Dar Afaƙ al-Jadideh, Bita.
  • Abul Fattouh Razi, Hossein bin Ali, Rouzul al-Jinan wa Ruh al-Jinan fi Tafsir al-ƙur'an, bincike na Mohammad Jaafar Yahaghi da Mohammad Mahdi Naseh, Mashhad, Astan ƙuds Razaɓi Research Foundation, 1408H.
  • Bahrani, Sayyid Hashim, Al-Burhan fi Tafsirin Kur’ani, sashen bincike na Mu’assasa Ba’ath ƙom, Tehran, Mu’assasar Ba’ath, 1416 Hijira.
  • Biazar Shirazi, Abdul Karim, Bastanshinasi Garafiyaye Tarikhi
  • ƙasas ƙur'an, Farhang Publishing House, Tehran, 2006.
  • Thaalbi, Ahmed Ibn Ibrahim, Al-Kashf wa Al-Bayan akan Tafsirin Kur'ani, Beirut, Dar Ahya al-Trath al-Arabi, 1422H.
  • Jazayeri, Nematullah bin Abdullah, Al-Nur al-Mubin fi ƙasas Anbiya wal Musralin, ƙum, maktabat Ayatullah Al-Mar'ashi al-Najafi, 1404H.
  • Jasas, Ahmad bin Ali, Akhmul al-ƙur'an, Mohammad Sadiƙ ƙomhari, Beirut, Darahia al-Trath al-Arabi, ya yi bincike, 1405H.
  • Raminnejad, Ramin, Mazare Payambaran, Mashhad, Astan ƙuds Razaɓi Research Foundation, 1387.
  • Sobhani, Ja'afar, Manhsur Akayid Imamiyya, ƙum, Imam al-Sadiƙ Foundation (AS), Beta.
  • Sayyid Morteza, Tanziyeh al-Anbiya, Kum, al-Sharif al-Razi, 1250H.
  • Shoghi, Abu Khalil, Atlas ƙur'an, fassara Kermani, Mashhad, Astan ƙuds Razaɓi, 2008.
  • Sadouƙ, Muhammad bin Ali, Al-Khisal, editan Ali Akbar Ghafari, Kum, Jamia Modaresin, 1362.
  • Tabatabaei, Seyyed Mohammad Hossein, Al-Mizan fi Tafsirin Al-ƙur'an, ƙum, ofishin wallafe-wallafen Musulunci na kungiyar Seminary Community, 1417H.
  • Tabarsi, Fazl bin Hassan, Majma Al-Bayan fi Tafsir al-ƙur'an, gabatarwar Mohammad Jaɓad Balaghi, Tehran, Nasser Khosrow, 1372.
  • Tabari, Muhammad bin Jarir, Tarikh Al'umam wa Al-Muluk, Binciken Muhammad Abulfazl Ibrahim, Beirut, Darul-Trath, 1387/1967 Miladiyya.
  • ƙortubi, Muhammad bin Ahmad, Al-Jamee Al-Ahkam Al-ƙur'an, Tehran, Nasser Khosrow Publishing House, 1364.
  • ƙommi, Ali bin Ibrahim, Tafsirul ƙummi, Tayyab Musawi Jazayeri, ƙum, Darul Kitab, 1404H.
  • Kafami, Ibrahim bin Ali, Al-Misbah (Jannah al-Aman al-Waƙiyyah), Kum, Dar al-Razi (Zahidi), 1405H.
  • کلباسی، زهرا و دیگران، «نقد و بررسی آرای مفسران در تفسیر آیه ۴۴ سوره ص و تازیانه زدن ایوب به همسرش»، آموزه‌های قرآنی، شماره۲۲، ۱۳۹۴ش.
  • Majlesi, Mohammad Baƙir, Bihar al-Anwar al-Jame'ah Ledurarul Akhbar Al-Aima al-Athar, Beirut, Darahia al-Trath al-Arabi, 1403 AH.
  • Majlesi, Mohammad Baƙer, bincike na Ali Imamian, Hayat al-ƙulob, ƙum, Sarwar, 2004.
  • مرکز تراث الحله، العتبة العباسیة المقدسة، مشاهده ۱۵ اردیبهشت ۱۳۹۹ش.
  • Moghniyeh, Mohammad Jaɓad, Tafsir Al-Kashif, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya, 1424H.
  • Makarem Shirazi, Nasser, Tafsir namuneh, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya, 1373.
  • Nasri, Abdullah, Mabani Risalat Anbiya dar ƙur'an, Tehran, Soroush, 2008.
  • خلاصه داستان فیلم ایوب پیامبر، بانک جامع اطلاعات سینمای ایران، مشاهده ۲۴ فروردین ۱۳۹۹ش.