Amin (Laƙabi)
- Wannan ƙasida ce da ta shafi la ƙabin Amin. Domin sanin rayuwa da halayen Manzon Allah, duba ƙasidar Hazrat Muhammadu (S.A.W)
Amin (laƙabi) (Larabci: الأمين (لقب)) yana daga cikin laƙubban Annabin Muslunci (S.A.W) tun kafin aiko shi da Annabta ya kasance ana kiransa da wannan laƙabi, Amin laƙabi ne da ake amfani da shi kan Mutumin da aka aminta da shi daga ha'inci daga gare shi, ɗaya daga hususiyoyin Manzon Allah (S.A.W) da tuntuni da ya kasance sababin kiransa da Amin, riwayoyin A'imma sun ƙarfafi kasancewar Manzon Allah (S.A.W) Amintacce tun kafin Annabta, a ba'arin wasu ziyarori za ka samu ana masa sallama da Kalmar
Amincin Allah ya tabbata a gareka ya Amintaccen Allah a kan Manzanninsa.
Mafhumi Da Matsayi
Amin yana daga cikin laƙubba Annabi (S.A.W) da tsawon shekara gabanin aiko da Annabta ya kasance ana kiransa da wannan laƙabi,[1] Amin shi ne mutumin da mutane suka yarda da shi ba sa tsammanin ha'ainci daga gare shi,[2] Ibn Sa'ad Marubucin Tarihi a ƙarni na uku cikin littafin Aɗɗabaƙat Al-Kubra yana cewa: ya isa kyawawan halayen da husuyoyin Annabi (S.A.W) sun kai kamalarsu,har ya zamanto ba shi da suna sai Amin a Makka sai Amin (Amintacce).[3] kan asasin rahotan da ya zo daga littafin Tarikh ɗabari talifin shekara ta 303 an naƙaltoio cewa ƙuraishawa suna kiran Annabi (S.A.W) da sunan Amin tun kafin a fara yi masa wahayi.[4] Haka an rawaito Ibn Abbas cewa ƙuraishawa suna kiran Manzon Allah (S.A.W) da laƙabin Amin kuma sun sani sarai cewa ba zai taɓa yi musu ƙarya ba, amma kuma tare da haka bayan aiko masa da Annabta sai suka yi inkari.[5] hatta Maƙiya Annabi (S.A.W) suma sun masa shaida da furuci kan Amana, malaman Tarihi sun bada rahoton ƙissar furucin Abu Jahal kan wannan mas'ala.[6] an bada rahotan dalilin inkarinsu kan Annabi (S.A.W) bai kasance kan rashin yarda da maganarsa ba, bari dai gasar da take tsakanin gidajen ƙuraishawa da ƙabilunsu shi yasa su inkarin Annabtarsa.[7] Muhammad da Amin suna daga cikin sunayen da Musulmai suke raɗawa ƴaƴan da aka Haifa musu, sunan Amin yana jerin sunaye guda 100 da aka fi amfani da su a cikin ƙasar Iran tsakanin shekaru 1297-1380 hijira shamsi.[8]
Ya Kasance Mai Kula Da Amanar Mutane
ɗaya daga cikin husuyoyin Annabi (S.A.W) da ta sanya ake kiransa Amin, shi ne kasancewarsa wurin Ajiye Amanar Mutane,[9] dangane da Amanar Manzon Allah (S.A.W) an bada rahotanni daban-daban daga cikin litattafan Tarihi, daga jumlarsu shi ne lokacin da Annabi (S.A.W) ya kasance yana kasuwanci da jarin Hazrat Khadija ya dawo daga tafiyar kasuwanci da ya yi cikin nasara, sai Khadija ta ce masa: ya kai ɗan Kawuna, ina alfahari da kai kan girmamar nasabarka, kusancinka, gaskiyarka, kyawawan halayenka da riƙon Amanarka tsakankanin Mutane, bayan wani ɗan lokaci sai Hazrat Khadija ta nemi auren Annabi (S.A.W)[10] haka kuma ya kasance Mutum Mai riƙon amana da kula da amanar mutane, lokacin da Annabi (S.A.W) ya yanke shawarar yin hijira zuwa garin Madina, ya nemi Imam Ali (A.S) ka da ya biyo shi zuwa Madina sai bayan ya tabbatar da ya mayarwa da mutane Amanar su da suka ajiye a wurin Manzon Allah (S.A.W),[11] haka an bada rahoton cewa a lokacin Yaƙin Khaibar an fuskanci ƙarancin abinci, a wannan lokacin ne wani Makiyayi da yakewa yahudawa kiwo ya zo wurin Annabi (S.A.W) bayan tattaunawa tare da Annabi (S.A.W) sai ya muslunta, ya ce Dabbobin Yahudawa suna hannuna amana to kuma yanzu na Muslunta ya zan yi da su ? tare da tsananin buƙatuwar Musulmai suke da shi zuwa ga kayan abinci, sai Annabi (S.A.W) ya buƙaci wannan Makiyayi da yaje ya mayarwa da Yahudawa Dabbobinsu.[12]
Amintacce Kan Wahayi
Annabtar Annabi (S.A.W) ita kanta tana shiryarwa kan kasancewarsa mai kiyaye Amana, saboda ita Annabta amanar Allah ce kuma dole wurin Amintacce ake ajiye amana.[13] an rawaito daga Imam Ali (A.S): Allah ya aiko da Hazrat Muhammad domin ya kasance mai gargaɗin Mutanen Duniya da kuma kasancewa Amintacce kan wahayi.[14] cikin littafin tafsirul ƙummi cikin wannan aya (Muɗa'in samma Amin) an fassara ta da amanar Annabi (S.A.W), haka dangane da wannan aya an naƙalto daga Imam Sadiƙ (A.S) : (Umurninsa wurin Ubangiji zartacce ne kuma Ranar Kiyama shi Amintacce ne)[15] Haka cikin ba'arin ziyarori daga A'imma (A.S) an rawaito daga Manzon Allah (S.A.W) da Kalmar (Amintaccen Allah a kan Manzanninsa)[16] An bada rahotan wata waƙa daga Abu ɗalib Baffan Annabi cikin wannan waƙa ya kira Manzon Allah (S.A.W) da Amintaccen Allah:
Haƙiƙa kai Amintaccen Allah ne da bai taɓa faɗin ƙarya ba* haƙiƙa kai mutum ne mai gaskiyar zance da bai taɓa yin wargi da shiririta ba.[17]
Bayanin kula
- ↑ Duba Tabari, Tarikh Tabari, 1378H, juzu'i na 2, shafi na 290.
- ↑ Dehkhoda, Luggatnameh Dehkhoda, 1377, juzu'i na 3, shafi na 3408.
- ↑ Ibn Sa’ad, Tabaƙat Al-Kbara, Dar Sadr, juzu’i na 1, shafi na 156.
- ↑ Tabari, Tarikh Tabari, 1378H, juzu'i na 2, shafi na 290.
- ↑ Zamakhshari, Al-Kashaf, 1407 AH, Juzu'i na 2, shafi na 19-18.
- ↑ Duba Zamakhshari, Al-Kashaf, 1407 AH, juzu'i na 2, shafi na 19-18
- ↑ Duba Zamakhshari, Al-Kashaf, 1407 AH, juzu'i na 2, shafi na 19-18
- ↑ <a class="eɗternal teɗt" href="http://www.itel.ir/page131.aspɗ">«گزارشی جالب از یکصد نام برتر ایرانیان در قرن حاضر»</a>
- ↑ Duba Farajullahi, “Amanatdari Payambar (S.A.W) rahamat”, shafi na 31-34.
- ↑ Tabari, Tarikh Tabari, 1378H, juzu'i na 2, shafi na 281
- ↑ Sheikh Mufid, Al-Ershad, 1413 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 53.
- ↑ Ibn Hisham, Al-Siratu Al-Nabawiya, Dar al-Marifah, juzu'i na 2, shafi na 344-345.
- ↑ Farajullahi, “Amanatdari Payambar (S.A.W) rahamat”, shafi na 31.
- ↑ Nahj Al-Balagheh, 1414 AH, shafi na 68.
- ↑ ƙommi, Tafsir ƙummi, 1367, juzu'i na 2, shafi.409.
- ↑ Ibn ƙuluyeh, Kamel Al-Ziyarat, 1356, shafi na 201.
- ↑ Ibn Shahr Ashub, Al-Manaƙib Al Abi Talib, 1379 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 56.
Nassoshi
- Nahj al-Balagheh, Tahkik Sobhi Saleh, ƙum, Hijira, 1414H.
- Ibn Saad, Muhammad, Tabaƙat Al-Kubra, Beirut, Dar Sader, Bita.
- Ibnshahrashob, Muhammad Bin Ali, Manaƙib Al Abi Talib (AS), ƙum, Allameh, 1379H.
- Ibn ƙolwieh, Jafar bin Muhammad, Kamel Al-Ziyarat, Najaf Ashraf, Darul Mortazwieh, 1356.
- Ibn Hisham, Abd al-Malik bin Ayyub, Al-Sirah al-Nabiwiyah, Beirut, Dar al-Marafa, Bita.
- Dekhoda, Ali Akbar, luggatnameh Dekhoda, Tehran, Jami'ar Tehran, 1377.
- Zamakhshari, Mahmoud, Al-Kashaf an Ghawamaz Al-Tanzil, Beirut, Dar al-Kitab al-Arabi, 1407H.
- Sheikh Mofid, Muhammad bin Muhammad, Al-Ershad fi Mafarah Hajjullah Ali al-Abad, ƙum, Congress of Sheikh Mofid, 1413 AH.
Tabari, Muhammad bin Jarir, Tarikh Tabari, Beirut, Darul Trath, 1387H.
- فرجاللهی، فرجالله، «امانتداری پیامبر(ص) رحمت»، در مجله درسهایی از مکتب اسلام، شماره۶۷۳، خرداد ۱۳۹۶ش.
- «گزارشی جالب از یکصد نام برتر ایرانیان در قرن حاضر»، پایگاه کشوری فون واژه، بازدید ۲۸ آبان ۱۴۰۲ش.
- ƙommi, Ali bin Ibrahim, Tafsir ƙummi, ƙum, Darul Kitab, 1367.