Tuhuma

Daga wikishia
(an turo daga Zargi ko tuhuma)

Tuhuma (Larabci:التُهْمَة) shi ne nuna mummunan zato da kuma danganta ayyukan da ba na gaskiya ba ga wasu. Ana ɗaukar tuhuma daga ayyukan haramun, kuma babban zunubi ce a musulinci. Hukuncin wanda yi tuhuma ga wani shi ne ta'aziri (wato abin da alƙali ya ga ya dace), kuma a cikin kur'ani, Allah Ta'ala ya yi alkawarin yi wa wanda ya aikata tuhuma azaba mai girma. Amma a harshen Larabci akwai bambanci tsakanin kalmar Tuhuma wato ƙage, da kalmar Buhtan da kuma Al'iftirah, Bambance-bambancen da ke tsakanin zarge ko tuhuma da kalmar Albuhtan da kuma Al-iftira da kazafi Duk wanda ya zarge wasu ba tare da ya tabbata da laifinsu ba shi ne tuhuma, amma wanda ya yi tuhunma yana da yaƙinin kan ƙaryar da suka yi a kan wasu. Ruwayoyin Musulunci sun hana mutane halartar wuraren da ake tuhuma da zargin wasu. ɗaya daga cikin sakamakon shi ne rasa imani, kuma maganinsa shi ne kauracewa yin leken asiri kan ayyukan mutane.

Wasu malaman fikihu sun halasta tuhumar `yan bidi'a idan akwai maslaha cikin yin hakan, inda suka kawo hadisin mubahata (kage) matsayin hujja akan haka, sai dai mafi yawan malaman fikihu suna ganin wannan ra'ayi ba daidai ba ne, kuma sun fassara hadisin da cewa kafawa `yan bidi'a hujjar yankan shakku.

Matsayin Tuhuma Da Ma'anarta

Ana la'akarin tuhuma ko zargi a ɗaya daga cikin manya-manyan zunubi,[1] a cikin wani hadisi tuhuma tana ɗaya daga cikin munanan ayyuka har Shaiɗan ba ya karbar mai yinta.[2] haƙiƙa a cikin litatafai na hadisi an ware babi mai zaman kansa domin bayyanin haramcin tuhuma.[3]

Tuhuma tana nufin bayyana mummunan zato.[4] kuma mummunan zato wanda yake shiga zuciyar mutum daga tasarrufi da ayyuka na daban[5] rashin munana fahimta kan ayyukan wasu mutane idan ya wanzu a cikin zuciyar mutum kuma bai bayyana shi ga wani mutum ba, to wannan ana ɗaukarshi a matsayin munana zato ba tuhuma ba.[6]

Ita tuhuma ta haɗa da tuhuma a rubuce ko ta hanayar nuni, ko tuhuma ta hanayar na'urori kamar wayar hannu, kwamfiyuta, da hanyoyin sadarwar zamantakewa.[7]

Mafi munin tuhuma a cikin hadisi ita ce tuhuma ko zargi na cin amana, ma'ana zargin da ake yiwa wanda aka damƙawa amana ta wani aiki amma ya kasa sauke nauyi da ya hau kanshi.[8]

Banbanci Tuhuma Da Wasu Kalmomi Masu Kama Da Ita

Tuhuma da kalmar Buhtan da Al'iftira, suna da kamanceceniya a ma'ana kuma an saba amfani da su tare. a maimako ko wata ɗaya a cikinsu. Sai dai akwai bambance-bambance a tsakaninsu. Zargin shi ne bayyana munanan zato, wanda ya samo asali daga zato da rashin yarda.[9] Wannan zato ko dai bai ta tabbata ba, ko kuma har yanzu ba ta tabbatar da shi ba,[10] amma kalmar Buhtan tana nufin danganta ƙarya ga wani.[11] kuma wanda ya aikata Buhtan, shi kan shi yasan ƙarya yake yi.[12] Amma Al'iftira kawai ana nufin karya.[13] ba tare da hujja ba.[14] kamar jingina ɗa ga Allah madaukaki.[15]

Hukuncin Tuhuma a shari'a

Akwai hujunce-hukunce na Tuhuma a shari'a daga cikin akwai; • Yin tuhuma da yaɗata haramin ne a fiƙihu[16] kuma hukuncin wanda ya aikita shi ne Atta'azir, wato alƙali ne zai yiwa mai tuhuma hukuncin da yake ga ya dace.[17] amma idan yazama tuhumar idan tazaama ƙazafi [shi ne jifan mutum da abin da bai aikataba],to hukuncinta zai zamo hukuncin mai ƙazafi, wato bulala tamanin.[18]

• kan haramcin tuhuma babu banbanci wanda ake tuhuma ya zamo yana gurin ko baya gurin a lokacin da ake tuhumarshi.[19]

• Idan aka yi zargi mutum a gaban shi to misali ne na cin fuskar mutum, kuma hakan haramun ne.[20] Ba ya halatta a saurari tuhumar da ake yi wa wasu, amma idan an saurare tuhumar tofa dola ne a kareshi a nuna wannan tuhumar ba dai dai bace.[21]

• Wajibi ne wanda yayi tuhuma ya tuba daga zunubin shi, kuma bisa ihtiyaɗi da mustahabi ya kamata ya nemi yafiyar wanda ya tuhuma idan babu tinanin cutar da shi.[22]

Tasirin tuhuma da abin da yake biyu bayanta

Akwai tasiri da abubuwa da suke faruwa bayan aikata tuhuma, daga cikinsu akwai: • Azaba daga Ubangiji: a cikin ruwaya daga Imam Sadik, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, cewa aya ta 23 a cikin Suratul Nur tana nuna girman laifin tuhuma.[23] A cikin wannan aya Allah Ta'ala ya la'ance mai yin tuhuma a duniya da lahira, kuma an yi mashi tanadin azaba mai girma, duk wanda ya zargi mata masu kame kai ko masu aure, kuma ya jefe su da yin zina, kazalika ya zo a cikin ayatul Ifik, cewa duk wanda ya tuhumi matan Manzan Allah (s.a.w),[24] to zai sha babbar azaba.[25]

• Yin zargi da tuhuma yana kawar da imanin mumini.[26]

• Tuhuma tana kai ga yankewar alaƙa a tsakanin `yan'uwa da kuma gushewar alaƙa ta addini.[27]

Hanyoyin Kubuta Da Magance Tuhuma

Akwai hanyoyi da yawa domin magance yin tuhuma ga mutane, daga cikin akwai: • Ka guji cuɗanya da waɗanda aka san suna da mugun nufi.[28]

• Rashin halartar tarukan da ake ambatan abubuwa marasa kyau.[29]

• Rashin halartar gurare da tarukan da ake danganta su ga mutane masu halayyar banza da masu sharri da lalacewa.[30]

• Yana da kyau kada a yi leken asiri a kan ayyukan mutane, da kuma fassara maganar mutane marar kyau ga abu mai kyau.[31]

Hadisul Mubahatati

Tushen Kasida: Hadis Mubahatatu

Mubahatati kalma ce ta fikihu da aka samo daga kalmar Bahituhum wadda ta zo a cikin hadisi daga Manzon Allah (s.a.w),[32] amma ta fuskar fiƙihu, wasu suna ganita a matsayin tuhuma ko zargi, kuma sabo da haka suka halasta tuhumar mutane `yan bidi'a.[33] Amma wasu sun ce ma'anarta shi ne kafawa `yan bidi'a da dalilai da hujjojin yankan shakku, da kuma ɗimauta su da hujja mai ƙarfi.[34] to a ƙarshe su wanna malama suna ganin rashin halascin tuhumar ‘yan bidi'a.[35]

Bayanin kula

  1. Ibn Shu'bah al-Harani, Tohaf al-Aqool, shafi na 331; Dastgheeb, Al-Zhanub al-Kabir, juzu'i na 2, shafi na 382.
  2. Al-Kulayni, Al-Kafi, juzu'i na 2, shafi na 358.
  3. Al-Kafi, Al-Kulayni, juzu'i na 2, shafi na 361; Al-Hurr u Al-Amili, Wasa'il Al-Shi'a, juzu'i na 12, shafi na 302.
  4. Al-Zubaidi, Taj Al-Arous, juzu'i na 34, shafi na 64; Al-Farahidi, Al-Ain, juzu'i na 4, shafi na 100.
  5. Al-Tahrani, Al-Akhlaq Al-ilahiyya, juzu'i na 4, shafi na 155.
  6. Al-Tahrani, Al-Akhlaq Al-ilahiyya, juzu'i na 4, shafi na 155-156
  7. Al-Sistani, Tauzihul Al-masa'il Jami', juzu'i na 2, shafi na 208.
  8. Al-Kulayni, Al-Kafi, juzu'i na 5, shafi na 298.
  9. Al-Tahrani, Al-Akhlaq Al-ilahiyya, juzu'i na 4, shafi na 156
  10. Odeh, Jurmi wa Arkan An, juzu'i na 1, shafi na 300.
  11. Al-Tahrani, Al-Akhlaq Al-ilahiyya, juzu'i na 4, shafi na 141
  12. Dastghaib,Al- Zunubul Al-kabira, juzu'i na 2, shafi na 360.
  13. Al-Tusi, Majma' al-Bayan, juzu'i na 6, shafi na 201.
  14. Ibn Manzur, Lisan al-Arab, juzu'i na 15, shafi na 154; Al-Farahidi, Al-Ain, juzu'i na 8, shafi na 280.
  15. Suratul Baqarah, aya ta:116.
  16. Al-Najafi, Jawahir al-Kalam, juzu'i na 41, shafi na 59; Shahidi Na Biyu, Kashaful riba, shafi na 21.
  17. Khumaini, Istifta'at Imam Khomaini juzu'i na 6, shafi na 413; Al-Fadil Lankarani, Jami' al-Mas'il, juzu'i na 1, shafi na 488; Makarem Al-Shirazi, Al-fatawa al-jadida, juzu'i na 3, shafi na 349.
  18. Allama Al-Hilli, Qawa'iodul Ahkam, juzu'i na 3, shafi na 547.
  19. Al-Tahrani,Al-Akhlaq Al-ilahiyya, juzu'i na 4, shafi na 157
  20. Al-Tahrani,Al-Akhlaq Al-ilahiyya, juzu'i na 4, shafi na 159
  21. Al-Tahrani,Al-Akhlaq Al-ilahiyya, juzu'i na 4, shafi na 159-160
  22. Al-Sistani, Tauzihul Al-Mas'il Al-Jami', juzu'i na 2, shafi na 209.
  23. Al-Saduq, Ilal al-Shara'i, juzu'i na 2, shafi na 480.
  24. Al-Tabatabai, Al-Mizan, juzu'i na 15, shafi na 89.
  25. Makarem Al-Shirazi, Al-Athmal, juzu'i na 11, shafi na 46.
  26. Al-Kulayni, Al-Kafi, juzu'i na 2, shafi na 361.
  27. Al-Kulayni, Al-Kafi, juzu'i na 2, shafi na 361.
  28. Al-Tahrani, Al-Akhlaq Al-ilahiyya, juzu'i na 4, shafi na 163.
  29. Al-Tahrani, Al-Akhlaq Al-ilahiyya, juzu'i na 4, shafi na 163; Al-Saduq, Al-Amali, shafi na 587.
  30. Al-Tahrani, Al-Akhlaq Al-ilahiyya, juzu'i na 4, shafi na 163; Al-Majlisi, Hilyat al-Muttaqin, shafi na 555.
  31. Al-Kulayni, Al-Kafi, juzu'i na 2, shafi na 362; Al-Hamdani, Misbah al-Faqih, juzu'i na 2, shafi na 672.
  32. Al-Kulayni, Al-Kafi, juzu'i na 2, shafi na 375; Al-Majlisi, Rawdat al-Muttaqin, juzu'i na 9, shafi na 327; Al-Majlisi, Madubin Hankali, juzu'i na 11, shafi na 77.
  33. Al-Khoei, Misbah al-Faqaha, juzu'i na 1, shafi na 458; Al-Kalbaikani, Al-Durr Al-Mandhud, juzu'i na 2, shafi na 148; Al-Tabrizi, Irshad al-Talib, juzu'i na 1, shafi na 281.
  34. Al-Fayd al-Kashani, Al-Wafi, juzu'i na 1, shafi na 245; Al-Majlisi, Mir'atul Al'uqool, juzu'i na 11, shafi na 81
  35. معنى المباهتة لأهل البِدَع.. الكذب عليهم أم الاحتجاج عليهم؟ / سماحة الشيخ محمد صنقور.

Nassoshi

  • Odeh, Abdel Qader, 'Jurm waarkan Ann' (barasi tadbiki hukuki jazaye islami wa kawanin urfi"), (At-tashri jana'i islami mukarinan bil kanun dabi'i ) , Fassarar: Hassan Farhodnia, Tehran, Yadawran Publications , 1390 AH.
  • "Al-Qur'ani Mai Girma".
  • Al-Fadil Lankarani, Muhammad, Jami' al-Masa'il, Qum, bugun Amir, 1383 H.
  • Al-Farahidi, Al-Khalil bin Ahmed, Al-Ain, Qum, Darul Hijra Foundation, 1409H.
  • Al-Fayd al-Kashani, Muhammad bin Murtada, Al-Wafi, Isfahan, Library of Amirul Muminina Ali (amincin Allah ya tabbata a gare shi), bugu na 1, 1406H.
  • Al-Hamdani, Aqa Reda bin Muhammad Hadi, Misbah al-Faqih, Tehran, An-Najah Library Publications, d.
  • Al-Hurr Al-Amili, Muhammad bin Al-Hasan, Wasa'il Al-Shi'a, Kum, Mu'assasa Al-Baiti Template:A.s don raya al'adun gargajiya, na daya. shekara, 1409 AH.
  • Al-Kalbaykani, Muhammad Reda, 'Al-Durr al-Mandud fi Ahkam al-Hudud, Qom, Darul Qur'an al-Karim, 1412 AH.
  • Al-Khoei, Abu al-Qasim, 'Misbahul Fakaha, Qum, Mu'assasar Ansariyya, 1417H.
  • Al-Kulayni, Muhammad bin Yaqoub, Al-Kafi, edita: Ali Akbar al-Ghafari da Muhammad al-Akhundi, Tehran, Darul Kutub al-Islamiyyah, bugu na 4, 1407H.
  • Al-Majlisi, Muhammad Baqir, 'Hilyat al-Muttaqin fi Adab, Sunnah, and Ethics, fassarar: Khalil Rizq Al-Amili, Qum, Dhul-Qirba, bugu na 1, 1424H.
  • Al-Majlisi, Muhammad Baqir, 'Mir'atul Al-aqool, edita kuma ya gyara shi: Sayyed Hashim Rasul Mahallati, Tehran, Dar Al-Kutub Al-Islamiyyah, bugu na biyu. 1404 AH.
  • Al-Majlisi, Muhammad Taqi, Rawdat al-Muttaqin fi Sharh Min La Hudhuruh al-Faqih Qom, Farhangi Islamic Foundation, 1406 AH.
  • Al-Najafi, Muhammad Hassan, Jawahir Al-Kalam fi Sharh Al-Islam', Beirut, Dar Ihya Al-Turath Al-Arabi, bugu na 7, 1404H.
  • Al-Saduq, Muhammad bin Ali bin Al-Hussein, Al-Amali, Qum, Mu'assasa Tambuwal, 1417H.
  • Al-Saduq, Muhammad bin Ali, “'Illāl al-Sharā'ī',” edited by: Muhammad Sadiq Bahr al-Ulum, Al-Najaf Al-Ashraf, Al-Haidariyya Library, 1385 AH/1966 AD.
  • Al-Sistani, Ali, 'tauzihul masa'il,Mashhad, Library of Grand Ayatullah Al-Sistani, 1396H.
  • Al-Tabarsi, Al-Fadl bin Al-Hasan, 'Majma' al-Bayan fi Tafsirul Qur'an, Beirut, Al-Alami Foundation, bugu na daya, 1415 Hijira.
  • Al-Tabatabai, Muhammad Hussein, 'Al-Mizan a Tafsirin Alqur'ani, Beirut, Al-alami Publications Foundation, bugu na daya, 1417 AH/1997 AD.
  • Al-Tabrizi, Jawad, Irshadul dalibi ila talik almakasib, Qum, Ismaili, 1416 AH.
  • Al-Tahrani, Mojtaba, Dabi'un Allah, wanda ya fassara: Diya al-Din al-Khazraji, Beirut, Al-Ghadeer Center, bugu na daya, 1432 AH/2011 AD.
  • Al-Zubairi,Muhammad bin Muhammad, 'Tajul Aroos min jawahirul Alqamus, Beirut, Darul Fikr, 1414H.
  • Allamah Al-Hilli, Al-Hasan bn Yusuf bn Al-Mutahhar, Qawa'idul Al-ahkam', Qum, Mu'assasar Daba'ar Musulunci, bugu na daya, 1413H.
  • Dastghib, Abd al-Hussein, Alzunubul al-kabira', Tehran, Islamic Andesheh-e-Baghdad Canon, 1361H.
  • Ibn Manzur, Muhammad bin Makram, Lisan al-Arab, Beirut, Dar Sader, bugu na uku, 1414H.
  • Ibn Shu'bah al-Harraniy, Al-Hasan bn Ali, Tuhaf al-Uqul ya ruwaito daga Iyalan gidan Manzo (Allah Ya jikansa da iyalansa), Gyara da Sharhi: Ali Akbar Al- Ghafari, Qum, Mu'assasar Buga Musulunci, bugu na biyu, 1404H.
  • Khomeini, Ruhollah, Istifta'atu Imam Khumaini', Qum, Islamic Publishing Foundation, 1372H.
  • Makarem Al-Shirazi, Nasser, Al-Amsal fi Tafsiril Kitabillahi munazzal L Qum, Mazhabar Imam Ali Template:A.s, bugu na 1, 1426 Hijira.
  • Makarem Al-Shirazi, Nasser, 'Istifta'at jadida, Mazhabar Ali bin Abi Talib (amincin Allah ya tabbata a gare shi), bugu na biyu, 1385H.
  • Shahidi na biyu, Zainul-Din bin Ali, kashful ar-riba an ahkamil al-giba, Tehran, Mortazavi Publications, 1390H.
  • معنى المباهتة لأهل البِدَع.. الكذب عليهم أم الاحتجاج عليهم؟ / سماحة الشيخ محمد صنقور، موقع الاجتهاد، تاريخ الإدراج: 22/ 2/ 2022 م، تاريخ المشاهدة: 7/ 3/ 2024 م.