Yaƙin Ƙarƙaratul Alkudri

Daga wikishia

Yakin ƙarƙarat al-Kudri (Larabci: غزوة قَرْقَرَةُ الكُدْر) ɗaya ne daga cikin yaƙe-yaƙen Annabi (S.A.W) da ya yi a shekara ta uku bayan hijira a yankin al-kudri,wata ruwayar tace ya faru ne a shekara ta biyu bayan hijira, inda da dama daga cikin ƙabilar Bani Salim da Gaɗfan suka taru a yankin al-Kudir suna son su yaƙi Madina, amma kasantuwar Sojojin Musulunci suna gurin sai suka bar wurin, kuma Imam Ali (A.S), shi ne wanda yake riƙe da tuta a wannan yakin, kuma musulmi sun samu ganima a karshe.

Abin da Ya sa Aka Kira Wannan Yaƙi da ƙarƙaratul Kudri

Yankin Kudir yana da nisa kamar kimanin kilo mita 170 daga birnin Madina,[1] ana kiranta da suna ƙarƙaratul Kudri, akwai wanda yake kiranta da ƙararatu Kudri,[2] kuma a wannan yankin akwai rijiya ta ruwa ta ƙabilar Bani salim,[3] kuma a wannan yankin ne kabilun Gaɗfan da Bani Salim suka taru domin yaƙar musulmi sabo da haka sai aka kira wannan yaƙi da ƙararatul Kudri.[4] kuma ambaci wannan yakin da ƙarƙaratu Bani Salim da Gaɗfan.[5]

Abubuwan Da Suka Faru

ƙabila guda biyu Banu Salim da Gaɗfan sun taru a shekara ta 3 bayan hijira domin yaƙar Madina, kuma labarinsu ya isa ga Manzon Allah (S.A.W),[6] don haka Annabi ya naɗa Ibni Abi Maktum a matsayin magajinshi a Madina,[7] amma bisa wata ruwaya ya naɗa Muhammad ɗan Muslama Al-Ansari,[8] ko Siba'a ɗan Arafaɗa Al-Gaffari,[9] sai shi da musulmi suka yi tattaki zuwa ga Mushrikai.[10] kuma a wannan lokacin tutar yaƙi ta musulmi tana hannun Imam Ali(A.S).[11]

Sojojin Banu Salim da Gaɗfan sun bar wurin kafin isowar sojojin musulmi, sai Manzon Allah (SAW S) ya tura dakarunshi da dama zuwa saman kwarin. Don su gurin da makiya suke, sai haɗu da masu kiwan rakuma, a cikinsu akwai wani yaro mai suna Yusara, sai suka kama shi suka mika wa Manzon Allah (S.A.W) taguwar shi, sai Musulmi suka koma Madina, suka raba ganima a gidan Surar, to kasantuwar shi Yusara yana sallah kuma yana daga cikin rabon Annabi na ganimar sai Manzon Allah (S.A.W) ya sake shi.[12]

Tarihi

Ya zo a cikin litattafan tarihi cewa yakin ƙarƙaratu al-kudar ya faru ne bayan yaƙin Suwaiƙ,[13] kuma wasu malaman tarihi sun bayyana cewa lokacin yaƙi ya kasance a watan Shawwal shekara ta 2 bayan hijira,[14] wasu kuma suka ce, ya kasance a cikin watan Muharram shekara ta 3 bayan hijira,[15] kamar yadda fitar annabi daga Madina da dawor shi ya ɗauki tsawan kwana goma shabiyar.[16]

Bayanin kula

  1. Al-Hamawi, Majam al-Baldan, juzu'i na 4, shafi na 441.
  2. Al-Balazari, Ansab al-Ashraf, juzu'i na 1, shafi na 310.
  3. Al-Hamawi, Majam al-Baldan, juzu'i na 4, shafi na 441.
  4. Ibn Saad, Al-Tabaqat Al-Kubra, juzu'i na 2, shafi na 23.
  5. Al-Maqrizi, Imti’ al-Asma’, juzu’i na 1, shafi na 124.
  6. Ibn Saad, Al-Tabaqat Al-Kubra, juzu'i na 2, shafi na 23; Al-Baladhuri, Ansab al-Ashraf, juzu'i na 1, shafi na 310.
  7. Al-Baladhuri, Ansab al-Ashraf, juzu'i na 1, shafi na 310; Ibn Saad, Al-Tabaqat Al-Kubra, juzu'i na 2, shafi na 23.
  8. Ibn Abd al-Barr, Al-Isti’ab, juzu’i na 3, shafi na 1377.
  9. Ibn Hisham, Sira Annabawiyya, juzu'i na 2, shafi na 43.
  10. Ibn Saad, Al-Tabaqat Al-Kubra, juzu'i na 2, shafi na 23.
  11. Ibn Saad, Al-Tabaqat Al-Kubra, juzu'i na 2, shafi na 23.
  12. Al-Waqidi, Al-Magazi, juzu'i na 1, shafi na 183.
  13. Al-Baladhuri, Ansab al-Ashraf, juzu'i na 1, shafi na 374; Al-Waqidi, Al-Magazi, juzu'i na 1, shafi na 181-182.
  14. Ibn Hisham, Seerah al-Nabawiyyah, juzu'i na 2, shafi na 43.
  15. Al-Balazari, Ansab al-Ashraf, juzu'i na 1, shafi na 310; Al-Waqadi, Al-Magazi, juzu'i na 1, shafi na 182; Ibn Sa’d, Tabaqat al-Kubra, juzu’i na 2, shafi na 23.
  16. Ibn Saad, Al-Tabaqat Al-Kubra, juzu'i na 2, shafi na 23.

Nassoshi

  • Al-Balazari, Ahmad bin Yahya, "Ansab al-Ashraf (Juzu'i na 1)", bincike: Muhammad Hamidullah, Masar, Dar al-Maarif, 1959 miladiyya.
  • Al-Hamowi, Yaqut bin Abdullah, "Mu'jam al-Baldan", Beirut-Lebanon, Dar Sadir, 1995.
  • Al-Maqrizi, Ahmed bin Ali, "Imta'a al-Isma'", bincike: Muhammad Abdulhamid al-Namisi, Beirut-Lebanon, Dar al-Kutub Al-Elamiya, 1420 AH/ 1999 AD.
  • Al-Waqadi, Muhammad bin Omar, "Al-Maghazi", bincike: Marsdon Jones, Beirut-Lebanon, Al-Alami Foundation, 1409 AH/1989 AD.
  • Ibn Abd al-Barr, Youssef bn Abdullah, 'Al-istiy'ab fi marifat Sahaba, edita: Ali Muhammad Al-Bajjawi, Beirut - Lebanon, Dar Al-Jeel, 1412 Hijira / 1992 Miladiyya.
  • Ibn Hisham, Abd al-Malik, 'Sirah Annabawiyyta, edita daga: Mustafa Saqqa, Ibrahim Abiary, da Abd al-Hafiz Shibli, Beirut - Lebanon, Dar al-Ma'rifa, D.T.
  • Ibn Saad, Muhammad bin Saad, tabaqat Al-kubra, editan: Muhammad Abdulkadir Atta, Beirut - Lebanon, Dar Al-Kutub Al-Ilmiyya, 1410AH/1990 AD.