Tawwabin

Daga wikishia

Tawwabin (Tubabbu) wasu jama’a ne daga mutanen garin Kufa ƙarƙashin jagorancin Sulaiman Bn Surad Khuza’i a shekara 65 bayan hijira da suka Mike domin neman fansar jinin Imam Husaini (A.S) kan Banu Umayya, Aksarinsu sun yi shahada a lokacin Yaƙinsu da Dakarun Ibn Ziyad a Ainul Waradatu. [1] wasu ba’ari tare da aika wasiƙa zuwa ga Imam Husaini (A.S) sun gayyace shi ya zo Kufa za su taimake shi, amma kuma tare da haka ba su taimake shi ba a filin Karbala; sai suka yi nadama kan wannan aiki da suka yi na ƙin taimakawa Imam Husaini (A.S) a waƙi’ar Karbala, sai suka tuba sannan suka ɗaura ɗamarar neman fansar jininsa kan waɗanda suka kashe shi, da wannan dalili suka shahara da sunan Tawwabin (Tubabbu). [2] wannan shi ne Miƙewa ta farko tun bayan waƙi’ar Karbala. [3] Adadin Tawwabin ya kai Mutane 4000, [4] Sulaiman bn Surad, Rifa’atu Bn Shaddad Bajali, Musayyab Bn Najaba, Abdullah Bn Sa’ad Azzadi da Abdullah Bn Rawal Taimi suna daga cikin Jagororin Tawwabin, in banda Rifa’atu Mutane huɗu daga cikinsu duk sun yi shahada a wannan Miƙewa. [5]

Bayanin kula

  1. Duba Ibn Sa’ad, Thabaƙat Al-Kubra, 1421H, Mujalladi na 8, shafi na 148.
  2. Ibn Sa’ad, Thabaƙat Al-Kubra, 1421H, juzu’i na 5, shafi na 197.
  3. Sobhani,Buhus Fi Milal wan Al-Nehal, 1428 AH, Mujalladi na 7, shafi na 246.
  4. Ibn Sa’ad, Thabaƙat Al-Kubra, 1421H, juzu’i na 5, shafi na 197.
  5. Dahhabi, "Siyar Al-Alamul Al-Nubala", 1414 AH, juzu'i na 3, shafi na 395

Nassoshi

  • Ibn Saad, Muhammad bin Saad, Thabaƙat Al-Kubra, Ali Muhammad Omar, Al-Khanji , Maktaba Alkahira, 1421 AH/2001 Miladiyya.
  • Dahhabi, Muhammad bin Ahmad, "Siyar Al-Alam Al-Nubalah", Beirut, Risala Est., 1414 AH/1994 AD.
  • Sobhani, Ja'afar, Buhus Almilal Al-Nehal, ƙum, Cibiyar Imam Sadiƙ, 1428H.