Taron Bikin Barranta Daga Mushrikai

Daga wikishia
Taron Barranta daga Mushrikai

Taron bikin barranta daga Mushrikai, (Larabci:مراسم البراءة من المشركين) ɗaya ne daga tarurrukan mahajjatan ƙasar Iran wanda cikinsa suke yin zanga-zanga tare da ɗaga murya suna faɗin taken alawadai da Amurka, Isra'ila tare da kiran musulmai zuwa haɗin kai.

Barranta daga Mushrikai wani abu ne da ya samo asali daga kur'ani da maginan fiƙihu, karo na farko ya kasance ne bayan Fatahu Makka ƙarƙashin umarnin Annabi (S.A.W) Imam Ali (A.S) ya je taron Mushrikan ƙuraishawa a garin Makka ya karanta ayoyin bara'a, wannan biki ya fara kasancewa a taron aikin hajji a shekara ta 1358 wanda aka shirya shi tare da isar da saƙon Imam Khomaini, gwamnatin Saudiyya ta nuna rashin amincewarta da wannan taron biki, a shekarar 1366 Jami'an Tsaron hukumar Saudiyya sun kai hari kan masu shirya wannan taro lamarin da ya haifar da kashe wani adadi daga masu taro da jiwa adadi mai yawa rauni daga mahajjatan ƙasar Iran.

Muhimmanci Da Asali

Taron barranta daga Mushrikai sunna ce ta addini da siyasa wacce kowacce shekara ake maimaita raya ta lokutan aikin hajji. [1] Jagororin Jamhuriyar Muslunci a kodayaushe sun kasance suna ƙarfafa gudanar da wannan taro domin kiyayen ɓangaren siyasa na cikin aikin hajji. [2]

Wannan taro wani abu ne da ake shirya shi da manufar shelar barranta daga siyasar girman kai ta duniya da kuma mushrikai tare da kiran musulmi zuwa ga haɗin domin ƙalubalantar kafircin duniya. [3] maudu'i shi ne ”Korar Mushrikai” wanda wani abu ne da aka yi ishara kansa cikin Alkur'ani a aya ta 3 suratul Baƙara, aya ta 4 suratul Mumtahana, [4] aya ta 1-3 suratul Tauba da kuma aya ta 19 suratul An'am. [5]

Karo na farko barranta ya kasance bayan samun nasarar Fatahu Makka. [6] Ubangiji ya ɗorawa Annabi (S.A.W) taklifin shelanta barranta daga mushrikai ta hanyar saukar da ayoyin bara'a (Ayoyi daga aya ta 1-10 suratul tauba, Imam (A.S) ne ya je taron mushrikai a shekara ta 9 bayan hijira ya karanta waɗannan ayoyi, [7] game da sha'anin saukar waɗannan ayoyi malamai sun ce, mushrikan Makka sun karya yarjejeniya da suka ƙulla da Annabi (S.A.W) a lokacin Sulhu Hudaibiyya wanda cikinsa suka yarda za su fita daga Makka tsawon kwanaki uku [8] domin baiwa Musulmi damar yin aikin hajji [9] cikin tafsir namuneh an kawo magana yanda mushrikai suka yi ta saɓawa yarjejeniyar da aka yi da su. [10]

Domin Neman ƙarin Bayani Ku Duba: Isar Da Ayoyin Bara'a

Hanyar Aiwatarwa

Tsakankanin Shekarun 1358-1366 h shamsi, mahajjatan ƙasar Iran da wasu ba'ari mahajjatan wasu ƙasashe, kafin fara aikin sun taru a wani wuri a Makka bayan sauraren lacca da ta ƙunshi bayani kan abubuwan da suke gudana a duniyar muslunci, sai suka shiga zanga-zanga. [11] Daga shekarar 1380 h shamsi da shekarun da suka biyo bayanta a ka fara yin wannan taro a safiyar ranar tsayuwar Arafat a ayarin gayyar Mahajjatan ƙasar Iran a Saharar Arafat, [12] tare da ɗaga murya a faɗin take ”Mutuwa Kan Amerika” da ”Mutuwa Kan Isra'ila” da taken ”Ya ku Musulmai ku haɗa kai ku haɗa kai”, “rarrabuwa da saɓani ɗa'a ce ga Shaiɗan” ana fara wannan taro ne bayan karatun kur'ani. [13] cikin cigaba da taron Jagoran Mahajjatan ƙasar Iran ya na miƙewa ya karanta saƙon Jagoran Jamhuriyar muslunci ta Iran cikin harsuna guda biyu; Larabci da Farisanci, daga ƙarshe sa ak karanta wasiƙar hukunci kan kowacce gaɓa cikin wasiƙa Mahajjata suna ɗaga murya cikin kabbara da goyan baya. [14]

Maginan Fiƙihu

An bada rahoto cewa An rawaito cewa, akwai inkarin shirka da nisantar da mushirikai a kowane yanki na taron aikin Hajji, Jifar Shaiɗan da talbiya suna daga mafi bayyana a cikinsu da ake ganin korar shirka. [15] Imam Khomaini cikin bayanin Bara'a daga mushrikai, yana ganin larurar shirya wannan taro cikin shakalai Mabambanta kuma wajibi ayi la'akari da zamani cikin shirya shi, kan wannan asasi ne mafi dacewar lokaci da wuri cikin zartar da barranta daga Mushrikai shi ne kwanakin aikin hajji a kuma cikin Harami, saboda idan aka yi cikin wannan sura zai fi tasiri da isar da saƙo. [16] Imam Khomaini cikin wannan umarni da ya fitar ya jingina da Asalan wilaya da bara'a. [17] Ba'arin Ahlus-sunna sun suka da ishkali kan wannan taro bisa la'akari da haramcin yin jidali a aikin hajji, kishiyarsu malaman fiƙihun Shi'a sun bayyana cewa gabaɗayan wannan taro babu inda ya yi kamanceceniya da jidali da zama sababin rigima da sauran Musulmai. [18]

Taƙaitaccen Tarihi

An bada rahoto cewa wannan al'ada bata kasance ana gudanar da ita ba a taron hajji kafin nasarar juyin juya halin muslunci na Iran, [19] an bayyana Imam Khomaini matsayin mutum na farko ya dawo da raya wannan al'ada ta barranta daga mushrikai a lokacin taron hajji, bayan nasarar juyin juya halin muslunci a Iran ana gudanar da wannan al'ada a taron aikin Hajji. [20] da wannan dalili ne ake ganin Imam Khomaini matsayin wanda ya assasa ranar barranta daga Mushrikai ta duniya. [21]

Hajjin Jini

Asalin Maƙala: Hajjin jini

Gwamnatin Saudiya lokuta daman gaske ta kasance tana nuna adawarta da kuma rashin amincewarta da shirya wannan taro a. [22] a shekarar 1366 h shamsi, bayan Mahajjatan Iran sun yanke shawarar haƙura da yin wannan taro sun yi niyyar komawa masallacin Harami sai ƴan sandar ƙasar Saudiya suka buɗe musu wuta, cikin wannan waƙi'a fiye da Mahajjata 500 ne suka rasa rayukansu sannan Mahajjata 700 suka ji rauni. [23] bayan wannan waƙi'a daga shekarar 1366 h shamsi har 1369 an dagatar da gudanar da wannan taro, a shekarar 2001 an dawo da gudanar da wannan taro a Mina da Arafat. [24]

Nazari

Littafin Mabani Dini wa Siyasi Bara'at az Mushrikin, na Jawad Wara'i, ya wallafa wannan littafi cikin harshen Farisanci, Cibiyar Intisharat Mash'ar ce ta buga wannan littafi. [25]

Bayanin kula

  1. “Bar'at az Mushrikin Dar Hajji, amali siyasi munɗabiƙ bar dasturi ƙur'an", kamfanin dillancin labaran IKNA.
  2. "Cera Hashimi wa Rouhani Mukhalif Ijraye Marasim bara'at az Mushrikin budan ?", Kamfanin Dillancin Labarai na Fars.
  3. Jam'i az Nawisandegani, Rahe Tusheh Hajji, 2006, juzu'i na 2, shafi na 363.
  4. “Bar'at az Mushrikin Dar Hajji, amali siyasi munɗabiƙ bar dasturi ƙur'an", kamfanin dillancin labaran IKNA.
  5. Warei, Mabani Dini wa Siyasi Bara'at az Mushrikin, 1379, shafi na 51 da 90.
  6. Dashti, “Bara'at az mushirikin”, 1377, juzu'i na 2, shafi na 628.
  7. Ibn Kathir, Al-Bidaya wa Al-Nihaya, 1407 AH, juzu'i na 5, shafi na 36-37.
  8. Yaƙoubi, Tarikh Eliyaƙoubi, Beta, juzu'i na 2, shafi na 54.
  9. Duba Ibn Kathir, Tafsir Al-Kur'anul Azeem, 1419 Hijira, juzu'i na 4, shafi na 89-90.
  10. Makarem Shirazi, Tafsir Namuneh, 1371, juzu'i na 7, shafi na 272.
  11. Dashti, “Bara'at az Mushirikin”, 1377, juzu'i na 2, shafi na 630.
  12. Bayat, Hajj 29, 2008, shafi na 163.
  13. Bayat, Hajj 29, 2008, shafi na 172-170.
  14. Bayat, Hajj 29, 2008, shafi na 163.
  15. Warei, mabani Dini wa Siyasi Bara'at az Mushrikin, 1379, shafi na 91.
  16. Imam Khumaini, Sahifa Imam, 1378, juzu'i na 20, shafi na 98.
  17. Dashti, “Bara'at az mushirikin”, 1377, juzu'i na 2, shafi na 628 da na 630.
  18. jam'i az Nawisandegan, Rehtoshe Hajj, 2006, juzu'i na 2, shafi na 356.
  19. "Imam Khumaini Ihyager Sunnat bara'at az mushrikin", Kamfanin Dillancin Labarai na Jam Jam Online.
  20. Warei, Mabani Dini wa siyasi Bara'at Az Mushrikin, 1379, shafi na 7.
  21. "Manafi Hajji az Manzare ƙur'an wa taba'at bi tadbirihaye Alu Sa'ud ", kamfanin dillancin labaran IKNA.
  22. Marasim, Bara'at Az mushrikin, kamfanin dillancin labaran ISNA
  23. Dashti, “Bara'at az mushirikin”, 1377, juzu'i na 2, shafi na 630.
  24. Dashti, “Bara'at az mushirikin”, 1377, juzu'i na 2, shafi na 632.
  25. Rai, Mabani Dini wa siyasi Bara'at az Mushrikin, 1379, shafi 8.

Nassoshi

  • Ibn Kathir, Ismail Ibn Kathir, Al-Bidaya wa Al-Nihaya, Beirut, Darul Fikr, 1407 AH/1986 Miladiyya.
  • Ibn Kathir, Ismail bin Umar, Tafsirin Kur'an al-'Azeem, bincike na Muhammad Hossein Shams al-Din, Beirut, Dar al-Kitab al-Ulamiya, 1419H.
  • Imam Khumaini, Sayyid Ruhollah, Sahifa Imam, Tehran, Cibiyar gyara da buga ayyukan Imam Khumaini, 1378.Dashti, Mohammad, "Bara'at az Mushrikin", Encyclopaedia of the Islamic World, Tehran, Cibiyar Encyclopaedia Musulunci, 1377.
  • Makarem Shirazi, Nasser, Tafsir Namuneh, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya, 1371.
  • Warei, Javad, Mabani Dini wa Siyasi Bara'at az Mushrikin , Tehran, Mashaar, 1379.
  • Yaƙoubi, Ahmed bin Ishaƙ, Tarikh Al-Yaƙoubi, Beirut, Dar Sadir, Bita.