Shafar Mamaci

Daga wikishia
(an turo daga Shafar Gawar Mamaci)
wannan wata ƙasida ce ta siffanta wata mas'ala ta fiƙihu, baya halasta a dogara da ita domin ayyukan addini, a koma zuwa ga wasu madogaran daban daga risalolin fiƙihu na maraji'an taƙlidi domin ayyukan addini
Littafin Al'urwatul Wuska na Sayyid Muhammad Kazim Tabataba'i Yazdi

Shafar mamaci, (Larabci: مسّ الميّت) yana nufin taɓa jikin mutumin da ya mutu,[1] malaman fikihu sun yi magana kan wannan mas'ala a cikin babin ɗahara a cikin littafansu da Risalolinsu na fiƙihu.[2]

Hukunce-hukunce Da Suke Da Alaƙa Da Shafar Mamaci • Bisa fatawar malaman Shi'a shafar mamaci bayan jikinshi ya yi sanyi kuma kafin ayi mishi wanka, yana wajabta wanka kan mutum baligi.[3]

• Shafa jikin ma'asumai (Su goma sha huɗu ne a shi'a daga manzon Allah zuwa Imamu Mahadi) ko kuma shahidin wanda ya yi shahada a filin yaƙi, ko mutumin da ya yi wankan gawa da kanshi kafin a yanke mishi hukuncin kisa ko hukuncin ƙisasi (Hukuncin kisa saboda ya kashe wani) duk waɗannan idan mutum ya taɓa jikinsu ba wajibi ba ne ya yi wanka taɓa gawa.[4] Sai dai wasu daga cikin malaman fiƙihu su na ganin cewa taɓa jikin shahidi yana wajabta wankan taɓa gawa.[5]

• Bisa ra'ayin sanannun malamai shafar jikin mamaci ba ya karya alwala.[6] amma wasu malaman suna ganin yana karya alwala.[7]

• Bisa fatawar mafi aksariin maraji'an taƙlidi su na ganin cewa shafar wani yanki wanda ya fita daga jikin mutum, idan wannan yankin yana ɗauke da ƙashi, to shafar shi yana wajabta wanka.[8] amma shi Ayatullahi Sistani yana gani cewa shafar shi baya wajabta wanka ko da kowa ya ƙunshi ƙashi da tsoka.[9]

• Wasu malaman suna ganin cewa wanka shafar mamaci wajibine kwai domin aikata duk wani abu da aka sa sharaɗi ne a yi alwala wajan yinshi, kamar sallah da taɓa al-ƙur'ani mai girma da ire-rensu. wasu kuma su na ganin cewa shafar mamaci ya na daga cikin abubuwan da suke tilasta wanka, saboda haka wankan shafar mamaci wajibi ne domin yin duk wani abu da aka sanya sharaɗan yin shi sai da tsarki, kamar sallah da ɗawafi da azumi da zama a masallaci da sauransu.[10]

Bayanin kula

  1. Fadil Al-Lankarani, Tauzihul Al-masa'il , 1426H, shafi 541.
  2. Duba, misali: Tabatabai Yazdi, Al-Urwah Al-Wuthqa, 1419 AH, juzu'i na 2, shafi na 12.
  3. Tabatabai Yazdi, Al-Urwa Al-Wuthqa, 1419 AH, juzu'i na 2, shafi na 3; Al-Isfahani,Wasilatun najat, 1422H, shafi na 60.
  4. Al-Najafi, Jawahir al-Kalam, 1362 AH, juzu'i na 5, shafi na 307.
  5. Al-Tabrizi Al-Gharwi, Al-Tanqih, 1411 Hijira, juzu'i na 8, shafi na 294-298.
  6. Al-Tabatabai Al-Yazdi, Al-Urwa Al-Wuthqa, 1419 AH, juzu'i na 2, shafi na 9, sharhi na 5.
  7. Tabatabai Yazdi, Al-Urwah Al-Wuthqa, 1419 AH, juzu'i na 2, shafi na 9.
  8. Tabatabai Yazdi, Al-Urwah Al-Wuthqa, 1419 AH, juzu'i na 2, shafi na 5.
  9. Al-Sistani, Minhaj al-Salihin, 1417 AH, juzu'i na 1, shafi na 116.
  10. Duba: Tabatabai Yazdi, Al-Urwa Al-Wuthqi, 1419 AH, juzu'i na 2, shafi na 11; Al-Husseini Al-Amili, Miftahul Al-Karama, Mu'assasatu Nahsar Ilsami, juzu'i na 4, shafi na 314-317.

Nassoshi

  • Al-Isfahani, Al-Sayyid Abu Al-Hasan, Wasilatun Najat, Qum, Sharhu: Al-Sayyid Ruhollah Musawi Khomeini, Mu'assasa Tsara da Buga Ayyukan Imam Khumaini, 1422H.
  • Al-Tabrizi Al-Gharwi, Mirza Ali, Al-Tanqih fi Sharh Al-Urwa Al-Wuthqi, rahoton bincike na Ayatullahi Sayyed Abu Al-Qasim Al-Khoei, bugu na biyu, 1411H.
  • Al-Husseini Al-Amili, Al-Sayyid Muhammad Jawad, Miftahul Al-Karamah fi Sharh Qawa'idil Al-Alamah, editan Muhammad Baqir Al-Khalisi, Qum, Islamic Publishing Foundation, D.T.
  • Al-Sistani, Sayyid Ali, Minhaj al-Salihin, Qum, ofishin buga littattafai na Ayatollah al-Sistani, 1417H.
  • Al-Tabatabai Al-Yazdi, Al-Sayyid Muhammad Kazem, Al-Urwah Al-Wuthqa, Qum, Islamic Publishing Foundation, 1419 AH.
  • Fadel Al-Lankarani, Muhammad, Risalatu Tauzihil Al-masa'il, Qum, 1426H.
  • Al-Najafi, Muhammad Hassan, Jawahir al-Kalam fi Sharh al-Islam, bugun Abbas Qochani, Beirut, Dar Ihya al-Turath al-Arabi, bugu na bakwai, 1362H.