Madyana (Ƙabila)
Madyana, wata ƙabilar larabawa ce, mutanen Annabi Shu'aibu (A.S) Allah ya aiko shi domin ya shiryar da su, Annabi Musa (A.S) ya zauna a cikinsu na tsawon shekaru. ba'arin ma su bincike cikin tarihi sun ambaci cewa madyana sun kasance daga zuriyar ƴaƴan Annabi Ibrahim (A.S), wasu ba'ari kuma sun ce sun kasance zuriyar Annabi Isma'il (A.S) ne, mutane ne da suka kasance su na zaune a cikin birnin Madyana, wanda yake kusa da tekun aƙaba; Saboda munanan ayyukansu, da rashin imani da Allah, da ƙin amsa kiran Annabinsu, sai Allah ya halaka su da azaba.
Nasaba
Mutanen Madyana suna daga cikin ƙabilun da suka jirkita suka zama Larabawa ta hanyar cuɗanya da Larabawa.[1] An ambace su a cikin Alƙur'ani a wurare goma,[2] wasu daga cikinsu ana kiran su kabilar Madyana,[3] wasu kuma da ake ana kiransu da sunan birnin Madyana,[4] an samu saɓani tsakanin masu bincike a tarihi game da tsatson wannan ƙabilar: Wasu daga cikinsu sun ce zuriyarsu ta na komawa zuwa Madyana ɗan Annabi Ibrahim (A.S)[5] kamar yadda ya zo a cikin littafin Attaura.[6] Kuma wasu masadir na musulunci,[7] sun ce Annabi Ibrahim ya auri wata mace bayan rasuwar matarsa Saratu, sai ta haifa masa Madayna (Madiyan), sannan Madyana ya auri ɗiyar Annabi Luɗu, zuriyarsu ta fito daga gare su.[8]
Ibn Kasir ya ambaci cewa zuriyarsu ta na komawa ne zuwa ga Madyana bin Madyana bin Ibrahim,[9] wasu masu bincike suna ganin zuriyar Annabi Isma'il ne.[10]
Garinsu
- Tushen ƙasida: Birnin Madyana
Mutanen Madyana sun zauna a birnin Madayana, an ciro sunan wannan gari ne daga sunansu.[11] garin ya kasance a gabas da Tekun Aƙaba,[12] a bakin Bahar Maliya.[13] kusa da yankin Tabuka.[14] Kusa da birnin Annabi Lud.[15] Shaikh Saduƙ ya ambaci cewa wani ƙaramin ƙauye ne mai dauke da gidaje guda arba'in kacal.[16]
Wasu masu bincike suna ganin cewa madyana ɗaya ne daga cikin biranen sham.[17] har ila yau akwai ma su tsammanin cewa birnin Ma'an na ƙasar Jodan.[18] ya maye gurbinsa.[19] kuma wasu sun yi imanin cewa Madyana ya tashi daga arewa maso yamma. na Hijaz zuwa sham.[20]
Faɗan Mutanan Madyana Da Bani Isra'il
Annabi Musa kamar yadda Kur'ani mai girma,[21]bda Attaura,[22] suka nuna, bayan guduwa daga Misra a cikin tsoro yana halin taka tsantsan sai ya tafi Madyana, ya auri ƴar Annabi Shu'aibu (A.S)[23] ya rayu da ita tsawon shekaru ma su yawa[24] a cikin kabilar Madyana,[24] ya shagaltu da kiwon dabbobi a wurin Annabi Shu'aibu (A.S).[25]
Akwai lokuta a cikin tarihi mutanen Madyana sun yi arangama da Bani Isra'ila, kuma labarinsu ya zo a cikin Littafi Mai Tsarki a cikin Littafin Mahukunta, inda aka ambata cewa Bani Isra'ila sun yi nasara a kan madyanawa bayan shekaru da dama su na shan kashi da wulakanci a hannunsu.[26]
Ma'amalar Mutanan Madyana Tare da Annabi Shu'aibu (A.S)
Shu'aibu ya kasance daga cikin mutanen Madyana.[27] sai Allah ya aiko shi matsayin Annabi zuwa gare su. Domin ya shiryar da su zuwa ga gaskiya,[28] Sai ya kira su zuwa ga addinin Allah, da tauhidi, da nisantar ha'inci da algus da tauye mudu,[29] da nisantar fasadi a cikin ƙasa,[30] da tsoron azabar ranar tashin ƙiyama.[31] kuma Allah ta'ala ya ambaci zancensa da abokan hamayyarsa a cikin suratul a'araf.[32]
Azabar Allah
Da yawa daga cikin mutanen Madyana sun yi watsi da amsa kiran Annabi Shu'aibu, sai azabar Ubangiji ta sauka a kansu.[33] bisa ayoyin kur'ani an halaka su ne ta hanyar girgizar ƙasa,[34] kai ka ce ba su taɓa zama a Madyana ba.[35]
Bayanin kula
- ↑ Ibn Ashour, Tafsir al-Tahrir wa al-Tanwir, juzu'i na 8, shafi na 186.
- ↑ Al-Qurashi, Kamus Kur’an, juzu’i na 6, shafi na 245
- ↑ Al-Husaini, Tabyinul Alqur’an, shafi na 243.
- ↑ Hud: 84.
- ↑ Shubar, Tafsir Alkur’anil karim, shafi na 178; Al-Tabari, Jami’ al-Bayan, juzu’i na 8, shafi na 166.
- ↑ Kitabul Mukaddas,Sifrul Takwin,Al-ashahu: 25, Aya: 1.
- ↑ Ibn Ashour, Tafsir al-Tahrir wa al-Tanwir, juzu'i na 8, shafi na 185.
- ↑ Al-Tabarsi, Tafsir Jami’ ul-Jami’, juzu’i na 1, shafi na 451.
- ↑ Ibn Kathir, Al-bidaytu Wan nihaya, juzu'i na 1, shafi na 185.
- ↑ Makarem Al-Shirazi, Al-Amsal, juzu'i na 7, shafi na 33.
- ↑ Al-Hamawi, Mujam Al-buldan, juzu'i na 5, shafi na 77.
- ↑ Al-Shabestari, A-lam Al-Qur’an, shafi na 488.
- ↑ Ibn Ashour, Tafsir al-Tahrir wa al-Tanwir, juzu'i na 8, shafi na 185.
- ↑ Al-Hamawi, Majam al-Baldan, juzu'i na 1, shafi na 291.
- ↑ Al-Qurashi, Kamus Kur’ani, juzu’i na 6, shafi na 245.
- ↑ Al-Sadooq, Kamal al-Din, juzu'i na 1, shafi na 220.
- ↑ Makarem Al-Shirazi, Al-amsal, juzu'i na 5, shafi na 111.
- ↑ Al-Qurashi, Kamus Kur’ani, juzu’i na 6, shafi na 245.
- ↑ Al-Balaghi, Hujjatul al-Tafaseer, juzu'i na 1, shafi na 267.
- ↑ Al-Mustafawi, Al-tahqiq fi Kalmat al-qur'an, juzu'i na 6, shafi na 71.
- ↑ Qasas: 22.
- ↑ Al-Kitab al-Muqaddas, Sifrul al-khuruj , Al-as-hah 2, aya ta 15.
- ↑ Qasas: 24 da 28
- ↑ Taha:40
- ↑ Taha:40
- ↑ Al-Kitab al-Muqaddas, Sifrul al-khuruj , Al-as-hah 1, aya ta 1.
- ↑ Al-Razi, Mafatiy al-Gheeb, juzu'i na 14, shafi na 313.
- ↑ Al-Araf: 85.
- ↑ Al-Araf: 85.
- ↑ Al-Ankabut: 36.
- ↑ Hudu: 84.
- ↑ A'araf: 85-90.
- ↑ Makarem Al-Shirazi, Al-Amsal, juzu'i na 8, shafi na 471.
- ↑ Al-Araf: 91.
- ↑ Al-Araf: 92.
Nassoshi
- Qur'ani.
- Bible'.
- Ibn Ashour, Muhammad Taher, Tafsir Ibn Ashour, Lebanon - Beirut, mawallafi: Mu'assasar Tarihin Larabawa, bugu na 1, 1420H.
- Ibn Kathir, Ismail bin Omar, 'Al-bidaya Wan Nihaya, Beirut - Lebanon, Mawallafi: Dar Al-Fikr, 1986 Miladiyya.
- Al-Balaghi, Abd al-Hajja, Hujjat al-Tafsir wa Balagh al-Ixir, Qom - Iran, mawallafi: Hikmat, 1386H.
- Al-Husseini, Muhammad, 'Tabyinul Kur'ani, Beirut - Lebanon, bugun: Dar Al-Ulum, 1423 Hijira.
- Al-Hamwi, Shihab al-Din, 'Kamus Buldan, Beirut - Lebanon, mawallafi: Dar Al-Sadir, bugu na biyu, 1995 miladiyya.
- Al-Razi, Muhammad bin Omar, 'Mafatihul gaibi, Beirut - Lebanon, mawallafi: Gidan Tarurrukan Tarihi na Larabawa, bugu na uku, 1420 AH.
- Shubbar, Abdullah, 'Tafsirul Alkur'an Kareem, Beirut - Lebanon, mawallafi: Dar Al-Balagha na Bugawa da Bugawa, bugu na 1, 1412 Hijira.
- Al-Shabestari, Abdul Hussein, 'A'lamul Alkur'an, Qom - Iran, Mawallafi: Ofishin Yada Labarai na Musulunci a Qom, 1379H.
- Al-Saduq, Muhammad bin Ali, 'Kamalud-dini wa itmam niima, editan: Ali Akbar Al-Ghafari, Tehran - Iran, mawallafi: Dar Al-Kutub Al-Islamiyyah, bugu na biyu , 1395 AH.
- Al-Tabarsi, Al-Fadl bn Al-Hasan, Tafsir Jami' Al-Jami, Tehran - Iran, Publisher: Jami'ar Tehran kuma Daraktan Cibiyar Seminary na Kum, bugu na 1, 1377H.
- Al-Tabari, Muhammad bin Jarir, Jami' al-Bayan fi Tafsir al-Qur'an, Beirut - Lebanon, bugun: Dar al-Ma'rifah, bugu na 1, 1412H.
- Al-Qurashi, Ali Akbar, 'Kamus Kur'ani, Tehran - Iran, mawallafi: Dar Al-Kutub Al-Islamiyyah, bugu na 6, 1371H.
- Al-Mustafawi, Hassan, At-tahqiq Fi Kalemat Al-Kur'an Kareem Tehran - Iran, Mawallafi: Cibiyar Tarjama da Buga Al-Kitab, bugu na 1, 1402H.
- Makarem Al-Shirazi, Nasser, 'Al-amsal Fi Tafsiri Kitabullahi Munazzal, Muhammad Ali Azarshab, Qum - Iran, mawallafin: Imam Ali bin Abi Talib Mazhabar {{A.S}, ya fassara shi. Bugu 1, 1421 AH.