Luwaɗi

Daga wikishia
(an turo daga Liwaɗi)
wannan wani rubutu na bayani da siffatawa game da wani mafhumi na fikihu wanda ba zai zamana ma'auni kan ayyukan addini ba, a komawa wasu madogaran kan ayyukan addini
Risala Ilmiyya

Luwadi (Larabci: اللواط) shi ne Saduwar jinsi tsakanin Maza guda biyu, Luwadi tana daga Manya-manyan Zunubai, ya zo a Hadisai cewa Luwadi tafi Zina Muni, Malaman Fikihu, kan asasin Riwayoyi cewa Idan ta tabbata cewa Kan Kaciyar Dayansu ya nutse cikin Duburar dayansu to za ai musu Ukuba ta Hanyar Kisa, amma idan ya zama Kan Kaciyar dayansu bata shiga cikin Duburar dayansu ba za a yiwa Kowannensu Bulala 100. Kan asasin Abin da ya zo cikin Hadisan Imamai, daga cikin Illolin Luwadi akwai hana Hayayyafa da kuma haifar yaduwar Barna cikin Gudanarwa da Tsarin Duniya, haka zalika cikin Sauran Addinan Ibrahimiyya da Mazhabobin Muslunci suma suna ganin Muni da Haramcin aikata Luwadi

Luwadi Zunubi ne da ya fi na Zina Girma

Luwadi tana daga Mafi Girma cikin Manya-manyan Zunubai [1] cikin wani Hadisi daga Imam Sadiƙ (A.S) ya bayyana girmamar Lefin aikata Luwadi fiye da aikata Zina [2] kan asasin wata riwaya daga Annabin Muslunci (S.A.W) Mai aikata Luwadi yana kasancewa cikin Fushin Allah da La’anarsa. [3] Cikin Alkur’ani an ambaci Luwadi da unwanin Munkari, Kazanta, Alfasha, bayyanannen Zunubi [4] an zargi Mutanen Annabi Ludu (A.S) a lokuta da dama sakamakon wannan kazamin aiki [5] kuma shine ya zama dalilin Azabarsu da halakasu [6]

Sanin Mafhumi

Ku duba Makala: Karkata zuwa ga Jinsi daya Luwadi a Isdilahin Fikhu anyi ta’arifinta kamar haka: Mutum ya nutsar da Kaciyarsa cikin Ramin Duburar Dan’waunsa Namiji [7] a cewar Ali Mishkini daga Malaman Shi’a, wasu ba’ari daga Malaman Shi’a suna kirga shigar kasa da Kan Kaciya cikin Ramin Duburar Namiji Matsayin Luwadi [8] wasu kuma sun tafi kan Mudlakin Saduwa tsakanin Namiji da Namiji matsayin Luwadi ko da kuwa Kaciyar dayansu bata shiga Ramin Duburar dayansu ba. [9] Kan asasin Hadisi da aka Nakalto daga Imam Rida (A.S) Mutanen Annabi Ludu (A.S) sun Kasance Mutane na farko a duniya da suka fara aikata wannan Kazanta, Hakika an samo sunan Wannan Mummuna Kazanta ta Luwadi daga wadannan Mutane . [10]

Hukuncin Shari’a

Luwadi aiki ne na Haram kuma tana daga Manya-Manyan Zunubai [11] kari kan Haddi da Shari’a ta tanada kan aikata wannan Kazanta akwai wasu Hukunce-hukunce daban kanta kamar misalin Iyaka cikin aure. [12]

Iyakoki cikin Aure

Sanya Iyakoki cikin aure tsakanin `Dan Luwadi da ba’arin wasu Mata ana kirga shi cikin Kufaifayin Shari’a kan Zunubin Luwadi, kan Fatawar Maraji’an Taklidi bai Halasta Dan Luwadi ya yi aure da Mahaifiya ko `yar wanda ya yi luwadi da shi ba, kuma wannan Haramci ne na har abada [13] wannan hukunci [14] cikin Doka mai Lamba 1056 cikin Dokokin Gari a Jamhuriyar Muslunci ta Iran tana nan a rubuce [15] na’am wasu Jama’a daga Malaman Fikihu sun tafi kan cewa wannan hukunci yana kasancewa idan Dan luwadi ya kasance Baligi [16] haka zalika idan ya aikata Luwadi da wani bayan auren Mahaifiyar wanda ya yi wa Luwadi ko kuma `diyarsa da `yar’uwarsa, to aure tsakaninsu yana nan daram bai baci ba. [17]

Ukuba

Kan asasin Fatawar Malaman Fikihu, Ukubar Dan Luwadi da wanda akayi Luwadi da shi idan Baligi ne to kashe shi za ayi [18] kowanne daya daga cikinsu idan ya kasance ba Baligi ba, to za a ladabta shi [19] Ladabtarwa wani hukunci da Alkali ke zartar da shi kan Mai lefi da bai kai shekarun Balaga ba, sannan Mikdarinsa yana kasancewa kasa da Haddin Shari’a. [20] Na’am wasu ba’ari daga Malaman Fikihu Kamar Misalin Abu Kasim Kuyi suna da na su ra’ayin da ya saba da Mashhur, cikin aminta da Hukuncin Kisa kan wanda akayi Luwadi da shi, suna laminta da Hukunci kan Kisa kan wanda ya aikata Luwadin idan ya kasance yana da Aure kuma yana da cikakkiyar samun damar Saduwa da Matarsa, sabanin haka sai dai ayi masa Bulala 100 kawai [21] Haka zalika a cewar Malaman Fikihu idan ya zamana Kaciyar Dayansu bata shiga Ramin Dubarar daya ba, to za a wadatu da yiwa kowannensu Bulala 100 kawai [22] cikin kowacce sura da yanayi idan Dan Luwadi ya Tuba Haddi yana faduwa daga kansa.

Hanyoyin da Ake bi cikin Zartar da Ukubar Kisa

Cikin Riwayoyi [23] da cikin litattafan Fikihu [24] an yi bayanin wasu hanyoyin zartar da hukuncin Kisa kan wanda ya aikata Luwadi, hanyoyin kuwa sune kamar haka: Sare wuyansa, Konashi da Wuta, Wurgo shi daga Dogon Gini ko wani wuri Mai tsayi kamar misalin Dutse, Jefe shi ko danno Bango Kansa ya danne shi Waliyul Al-fakihu na Musulunci kan asasin Maslaha zai zabi daya daga wadannan Hanyoyin kisa ya bada umarni zartarwa kan Dan Luwadi, [25] na’am idan ya kasance zartar da Hukuncin zai haifar da Rauni da Bakanta Fuskar Muslunci to Waliyul Al-fakihu yana da zabi dagatar da zartar da Hukunci domin Kare Maslahar Muslunci [26] ko kuma ya bada Umarni Kashe Mai lefin ta wata Hanyar Misalin Hanyar Rataya da ko Harbi da Bindiga. [27]

Falsafar Haramta Luwadi

Game da hikimar haramta aikata Luwadi, ya zo a cikin wani Hadisi daga Imam Rida (A.S) cewa Allah ya halicci Mata tareda dacewa da Dabi’ar Namiji, sannan ita Luwadi tana zama sababin Yankewar Al’umma da kuma haifar da barna da lalata Gudanarwa da tsarin Duniya. [28] Allama Tabataba’i cikin Almizan cikin Kiyasin Luwadi da Zina ya rubuta cewa Hakika Alkur’ani ya yi amfani da jumlar

«تَقْطَعُونَ السَّبِيلَ؛

Kuna yanke Hanya. [29] kan Luwadi [30] amma kan Zina sai ya yi amfani da jumlar:

«سَاءَ سَبِيلًا»؛

Hanya ta Munana. [31] a cikin Natija a Mahangar Alkur’ani Kufaifayin Luwadi na zahiri sun fi na Zina tsanani, saboda ita Zina bata Toshe Hanyar Haihuwar Al’umma sabanin Luwadi da Kacokan take yanke hanyar [32]

Ra’ayoyin Addinai da Mazhabonbi Dangane da Luwadi

A wurin Ahlus-Sunna Luwadi wani aiki ne da yake Haram kuma an ayyana Haddi kan wanda ya aikata ta [33] na’am ba’arin wasu Mazhabobin kamar misalin Mazhabar Hanafiyya sun tafi kan Ladabtar da Mai aikata Luwadi Maimakon tsayar da Haddi a kansa. [34] a Sauran Addinai suna kallon Luwadi matsayin Kazanta kuma Haram, a [35] cikin Addinin Zartusht Hakika Luwadi ta kasance Mafi munin Aiki kuma ana zartar da Kisa kan wanda ya aikata, [36] haka sauran Addinan Ibrahimiyya suma suna ganin Luwadin matsayin Kazanta Kuma Haram, cikin Attaura an kirayi Luwadi da Fajirci, [37] cikin Ahadul Jadid (Sabon Alkawari) an ajiye Masu Luwadi jikin Fasikai, Azzalumai Masu Bautar Gunki, ance misalin wadannan Kazaman Mutane ba za su taba zama Magadan Malakut Din Ubangiji ba [38]

Bayanin kula

  1. Allameh Hilli, Tahrir al-Ahkam al-Sharia, Al-Bait Institute (A.S.), Mujalladi na 2, shafi na 224
  2. Kulaini, Al-Kafi, 1407 AH, juzu'i na 5; shafi na 543.
  3. Kulaini, Al-Kafi, 1407 AH, juzu'i na 5; shafi na 544.
  4. Suratul Ankabut, aya ta 28 da ta 29; Suratul A'araf, aya ta 80.
  5. Faqihi, Tarbiyyat Jinsi, 2007, shafi na 311.
  6. Faiz al-Islam, Tarjameh wa tafsir Al-kur’anil Al-Kareem, 1378, juzu’i na 2, shafi na 443.
  7. Mashkini, Mustalahat Al-Fiqh, 2001, shafi na 457.
  8. Mashkini, Mustalahat Al-Fiqh, 2001, shafi na 457.
  9. Mashkini, Mustalahat Al-Fiqh, 2001, shafi na 457.
  10. Ali Ibn Musa, Fiqhul Mansub le-Imam al-Reza (a.s.), 1406 bayan hijira, shafi na 276.
  11. Allameh Hilli, Tahrir al-Ahkam al-Sharia, Al-Bait Institute (AS), juzu'i na 2, shafi na 224;Sabzevari, Mahdhab al-Ahkam, 1413 AH, juzu'i na 27, shafi na 303.
  12. Allameh Hilli, Tahrir al-Ahkam al-Sharia, Al-Bait Institute (AS), juzu'i na 2, shafi na 13; Khoi, Minhaj al-Salehin, 1410 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 265.
  13. Imam Khumaini, Tauzihul Almasa'il (Mohashi), 1424H, juzu’i na 2, shafi na 473.
  14. Shabiri Zanjani, Kitab Nikah, 1419 AH, juzu'i na 7, shafi 2109; Farhang Fiqh, 1426 AH, juzu'i na 2, shafi na 365.
  15. Emami, Seyyed Hassan, Hukuk Madani, Islamic Publications, juzu'i na 4, shafi na 328.
  16. Imam Khumaini, Tauzihul Almasa'il (Mohashi), 1424H, juzu’i na 2, shafi na 473.
  17. Imam Khumaini, Tauzihul Almasa'il (Mohashi), 1424H, juzu’i na 2, shafi na 473.
  18. Misali, duba Mohaghegh Hilli, Shara'e al-Islam, 1408 AH, juzu'i na 4, shafi na 147; Allameh Hilli, Tahrir al-Ahkam al-Sharia, Al-Bait Institute (AS), juzu'i na 2, shafi na 224; Shahid Sani, Masalak al-Afham, 1413 AH, juzu'i na 14, shafi na 402; Najafi, Jawahairul Kalam, 1404 AH,Juzu'i na 41, shafi na 389-379; Imam Khumaini, Tahrir al-Wasila, Cibiyar Kimiyya, Mujalladi na 2, shafi na 469, M4.
  19. Misali, duba Allameh Hilli, Tahrir al-Ahkam al-Sharia, Institute of Al-Bait (AS), juzu'i na 2, shafi na 224; Shahid Sani, Masalak al-Afham, 1413 AH, juzu'i na 14, shafi na 403; Imam Khumaini, Tahrir al-Wasila, Cibiyar Kimiyya, Mujalladi na 2, shafi na 469, M4.
  20. Tarhini Aamili, Al-Zubdatul al-Fiqhiyyah, 1427 AH, juzu'i na 9, shafi na 305.
  21. Khoei, Takmilatul al-Minhaj, 1410 AH, juzu'i na 2, shafi na 38-39.
  22. Misali, duba Mohaghegh Hilli, Shara'e al-Islam, 1408 AH, juzu'i na 4, shafi na 147; Alameh Hilli, Tahrir al-Ahkam al-Sharia, Al-Bait Institute (A.S.), Mujalladi na 2, shafi na 224.
  23. Kulaini, Al-Kafi, 1407 Hijira, juzu'i na 7, shafi na 200
  24. Mohaghegh Hilli, Shara'e al-Islam, 1408 AH, juzu'i na 4, shafi na 147; Alameh Halli, Tahrir al-Ahkam Al-Sharia, Al-Bait Institute (AS), juzu'i na 2, shafi na 224.
  25. Imam Khumaini, Tahrir al-Wasila, Cibiyar Darul Alam, juzu'i na 2, shafi na 470, M5.
  26. Imam Khumaini, Sahifa Imam, 2009, juzu’i na 20, shafi na 452.
  27. Makarem Shirazi, Nasser, Estefta'at Jadid, 1427 AH, Vol.3, shafi.369, shafi.948
  28. Ibn Baboyeh, Ayoun Akhbar al-Reza (a.s.), 1378 AH, juzu'i na 2, shafi na 97; Sadouq, Dalilan Dokoki, Al-Haydriya Charters Library, Juzu'i na 2, shafi na 547
  29. Suratul Ankabut, aya ta:29.
  30. Tabatabai, Al-Mizan, 1393 AH, juzu'i na 16, shafi na 123
  31. Suratul Isra, aya ta 32, Suratul Namal, aya ta 54.
  32. Tabatabaei, Al-Mizan, Manshurat Ismailian , juzu'i na 18, shafi 63, juzu'i na 13, shafi na 88.
  33. Mousawi Ardabili, Fiqhul Hudud wa Ta'azirat, 1427H, juzu'i na 2, shafi na 49.
  34. Mousawi Ardabili, Fiqhul Hudud wa Ta'azirat, 1427 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 52.
  35. Sarakhsi, Al-Mabsut, 1414 AH, juzu'i na 9, shafi na 77; Mousawi Ardabili, Fiqhul Hudud wa Ta'azirat, 1427 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 52.
  36. Rezaei, Tarikh Adayn Jahan, 1380, juzu'i na 1, shafi na 197.
  37. Kiatbu Mukaddas, Ktab Lawiyan, sura 18, aya ta 22.
  38. Kitab Mukaddas,Kitab Korintiyan, sura 6, aya ta 9-10.

Nassoshi

  • Alqur'anil Al-Kareem.
  • Kitab Mukaddas.
  • Imam Khumaini, Sayyid Ruhollah, Tahrir al-Wasila, Qum, Dar Alam Press Institute, bugun farko, beta.
  • Imam Khumaini, Ruhollah, Sahifa Imam, Tehran, Imam Khumaini Cibiyar Gyara da Bugawa, bugu na 5, 1389.
  • Emami, Seyd Hassan, Hukuk Madani, Tehran, Islamia Publications, Beta.
  • Bani Hashemi Khomeini, Sayyid Mohammad Hasan, tauzihul Al-Masa'il Al-Maraja'ah, Qum, ofishin wallafe-wallafen Musulunci na kungiyar Seminary Seminary Qum, 1424H.
  • Tarhini Ameli, Sayyid Muhammad Hossein,Alzubdatul al-Fiqhiyah fi Sharh al-Rauda al-Bahiya, Dar al-Fiqh na bugu da bugawa, Qum, bugu na 4, 1427H.
  • jam'i Az Fajuheshgaran zire Nazare Shahroudi, Sayyid Mahmoud Hashemi, farhnag fikih Mutabik Mazhab Ahlul-Baiti (a.s), Qum, Cibiyar Encyclopaedia ta Musulunci kan Ahlul Baiti (a.s.), 1426 bayan hijira. .
  • Khoi, Sayyid Abul Qasim, Takmila al-Minhaj, bugun Madina Al Alam, Qum, bugu na 28, 1410H.
  • Sabzevari, Sayyid Abd al-Ali, Mahazzab Al-Ahkam, Qom, Cibiyar Al-Manar, bugu na 4, 1413H.
  • Shahid Thani, Zain al-Din bin Ali, Masalak al-Afham ili Tankih Shaaree al-Islam, Islamic Encyclopaedia Foundation, Qum, bugu na farko, 1413H.
  • Sheikh Sadouq, Mohammad Bin Ali, Ayoun Akhbar al-Reza (a.s.), Tehran, Nash Jahan, bugun farko, 1378H.
  • Rezaei, Abdul Rahim, Tarikh Adyan Jahan, Tehran, wallafe-wallafen Kimiyya, bugu na biyu, 1380.
  • Allameh Hilli, Hasan bin Youssef, Tahrir al-Ahkam al-Sharia Ali Madhhab al-Imamiyah, Al-Al-Bayt Institute (A.S.), Mashhad, first edition, beta.
  • Shabiri Zanjani, Seyyed Musa, Kitab Nikahe, Qom, Cibiyar Bincike ta Rai Pardaz, bugu na farko, 1419H.
  • Ali Ibn Musa (Imami na 8), Fiqhul Almansub le Imam Al-Reza (AS), Mashhad, Mu’assasa Al-Baiti (AS), bugu na farko, 1406H.
  • Kulaini, Muhammad bin Yaqub, Al-kafi, Tehran, Dar Al-Kitab al-Islamiyya, bugu na 4, 1407H.
  • Faqihi, Ali Naqi, Tarbiyyat Jinsi, Qum, Cibiyar Kimiyya da Al'adu ta Dar Al Hadith, bugun farko, 2007.
  • Najafi, Mohammad Hassan, Jawahiru Al-Kalam Fi Sharha Shara'i Islam, Beirut, Dar Ihya al-Trath al-Arabi, 1404H.
  • Mohaghegh Hali, Najmuddin, Shara'e al-Islam fi Al-halal wa haramun, Kum, Cibiyar Ismailiya, bugu na biyu, 1408H.
  • Meshkini, Mirza Ali, Mustalahat Al-Fiqh, Qum, Al-Hadi Publishing House, bugu na 3, 2001.
  • Makarem Shirazi, Nasser, New Estefta'at Jadid, Wallafar Makarantar Imam Ali Bin Abi Talib (A.S.), Qum, bugu na biyu, 1427H.
  • Mousavi Ardabili, Seyyed Abdul Karim, Fikihul Al-Hudud wa Al-Tazirat, Kum, Est.