Litattafan Ɓata

Daga wikishia
(an turo daga Litattafan ɓata)

Litattafan ɓata sune litattafai da ake rubutawa domin ɓatar da mai karantasu,wasu malamai suna ganin litattafan ɓata sune duk wani lattafi da akayishi domin ɓata ko kuma wanda yake kaiwa ga ɓata, wanda ya fara ƙirƙiro wannan Isɗilahi a Shi'a [litattafan ɓata shi ne sheik Mufid bayan shi ne sai wannan kalma tabayyana a litattafan fiƙihun wasu malamai,kuma akayi binciken hukuncisu a fiƙihu.

Kalmar litattafai wanda ta zo a cikin wannan kalma litattafan ɓata yana nufin duk wani abu da aka rubuta wanda yake kai wa zuwa ga ɓata, shin littafi ne ko kuma maƙala ce ko risala, hakanan kuma ɓata bai keɓanta da ɓata irin na aƙida ba, a a ya shafi ɓata na hukunce-hukuncen shari'a.

Malaman fiƙihu na Shi'a sun yi fatwa kan haramcin ajiye litattafai na ɓata da sayar da su da sayan su da yin fotokwafi da kuma yaɗa su da koyar da su da kuma koyan su kuma wajibi ne a lallata su, a yanayi ɗaya ne ya halitta ayi amfani da su, a lokacin tabbatar da gaskiya da nuna ɓata ta hanyarsu ne kawai ya halitta ayi amfani da su.

Gabatarawa Na Fiƙihu

Litattafan ɓata ko masu ɓatarwa, a al'ada duk wasu littafai da za su kai ga mai karantasu ga ɓata, to su ne ake kira da litattafan ɓata,[1] amma a litattafai na fiƙihu suna da ma'ana daban-daban, wasu malaman fiƙihu sun zaɓi ma'anarsu ta Urfi,[2] amma sun bayyana su da cewa duk wani littafi da aka yi shi domin ɓatar da mutane,[3] amma wasu suna ganin litattafan ɓata sune duk wani littafi da aka rubuta shi domin ɓata sannan kuma yana kai wa ga ɓata.[4]

Ita kalmar litattafai na ɓata tana nufin duk wani abu da aka rubuta kuma yana kai wa ga ɓata, shin ya kasance littafi ko Maƙala ko risala.[5]

Tarihi Da Matsayin Wannan Mas'ala

Bisa ra'ayin wasu masu bincike kalmar litattafan ɓata a karon farko ta zo ne ta hanyar shaik mufid a cikin littafin shi mai suna Al-muƙni'a a ƙarƙashin unwanin litattafan kafirci da litattafan ɓata,[6] to daga nan ne sai wasu malaman fiƙihu suka yi amfani da wannan kalmomi guda biyu, daga cikinsu akwai Shaik Ɗusi.[7] da Ibn Barraj,[8] da Ibn Idris Hili,[9] da kuma Allama Alhilli.[10]

Daga nan ne wannan suna na litattafan ɓata ya fara faɗaɗa kaɗan-kaɗan a litattafan fiƙihu,[11] masamman a cikin litattafan fiƙihu na wannan zamanin.[12]

Mas'alar litattafan ɓata da hukunce-hukuncensu na masamman ba a kawo su ba a matsayin masu zaman kansu, sai dai an kawo su a babuka daban-daban kamar babin tijara da Waƙafi da haya da Wasiyya da Aro, kamar yadda Shassik Ansari a cikin littafin shi na Makasib a ƙarƙashin unuwanin Abin da ya haramta a nemi kuɗi da shi saboda shi haramune a kanshi, a cikin mas'ala ta bakwai mai ɗauke da unuwanin Ajiye litattafan ɓata.[13]

Ɓata Kan Wane Abu Da Kuma Ɓata Ga Wa?

Malaman fiƙihu sun yi fatwa cewa duk wani littafi da karanta shi yake kai wa ga ɓata a ginshiƙan mazahaba ko kuma hukunci na sharia'a, ana ganin shi a matsayin littafin ɓata,[14] Ayatullah Muntazari ya ce litattafan ɓata su ne waɗanda suke ɓatar da mafi yawancin masu karanta su, litattafan ɓata ba sa nufin dan wani mutum ɗaya ya zo ya karanta wani littafi ya ɓata sai ya zamo wannan littafin yana daga cikin litattafan ɓata ba, idan ya zamo ma'auni shi ne ɓatan mutum ɗaya, to duk litattafai za su zamo na ɓata hatta Al-ƙur'ani mai girma da litattafan hadisi duk za su iya zama litattafan ɓata ga masu rauni ko kuma Jahilai.[15]

Wasu Daga Cikin Litattafan Ɓata

Ya zo a cikin litattafai na fiƙihu wasu da yawa daga cikin litattafan ɓata, amma akwai saɓani tsakanin malaman fiƙihu, misali Allama Hilli (Rayuwa:648 -726) da Muhaƙiƙ Karki (Wafati: 940. h. q) suna ganin cewa Attaura da lnjila suna cikin litattafan ɓata, saboda an jirkita su,[16] amma shi kuma Shaik Ansari yana ganin litattafai ne da aka gogesu kuma basa ɓatar da musulmi.[17]

Kamar yadda Shaik Yusuf Albahrani (Rayuwa: 1107-1186. h. q) ɗaya ne daga cikin malaman Ahkhbariyun na Shi'a, yana ganin litattafan Usul na Ahlus-sunna da wasu daga cikin litattafai na Usul na Shi'a waɗanda suka yi koyi da Ahlus-sunna daga cikin litattafai na ɓata,[18] sai da cewa Sayyid Jawadi Amili, (Rayuwa: 1160-1226.q) wanda shi ne marubucin littafin nan mai suna Mafatihul Karama yana ganin maganar Shaik Yusuf Al-bahrani tana daga cikin misalai na ɓata.[19]

Kamar yadda Shaik Ansari ya faɗa cewa dalilin haramcin ajiyar litattafan ɓata ya ƙunshi litattafan da suke kai wa zuwa ga ɓata ne kawai, kuma da yawa daga cikin litattafan waɗanda ba ƴan shi'a ba basa kai wa ga ɓata,[20] Shaik Ansari yana ganin wasu ne daga cikin litattafan Ahlus-sunnan suke kaiwa ga ɓata, kamar waɗanda suka ƙunshi aƙidu marasa kyau, to sune liitattafan ɓata, kamar waɗanda suke ɗauke da aƙidar tabbatar da Jabar (wato duk abin da ya gangaro daga mutum bayin kanshi bane Allah ne ya tilasta mishi) da kuma aƙidar fifita kalifa Abubaka da Umar da Usman kan Imam Ali (A.S) [21] wasu daga cikin malamai sun tafi kan cewa litattafan Falsafa da Irfani waɗanda suke kai wa ga ɓata koda wasu abubuwa a cikinsu gaskiya ne to suma suna cikin litattafan ɓata [22]

Wasu gungun malamai na wannan zamani daga cikinsu akwai Shaik Nasir Makarim shirazi da Ludufullahi Safi Gulfaigani suna ganin cewa jaridu da majallu waɗanda suke ɗauke da abin da yake kai wa ga ɓatar da al-umma suna cikin litattafan ɓata,[23]

Hukunce-hukunce

Malaman fiƙihu sun tafi kan wajabcin lalata litattafan ɓata[24] kuma waɗannan abubuwan masu zuwa suma sun haramta: • Ajiye litattafan ɓata da niman kuɗi da su [25] • Yawaita su da yaɗa su [26] • Sayan su da sayarwa [27] • Karanta su da koyar da su da kuma koyan su [28] • Bada kuɗi domin yaɗa su [29] • Yin wasicci kan bada kuɗi domin yaɗa su [30] • Ya haramta a karɓi lada domin bugawa da tsarasu [31]

Maraji'an taƙlidi sun yi fatawa cewa babu laifi a karanta litattafan ɓata da kuma koyar da su, amma ga wanda yake da ƙudurar kan tabbatar da gaskiya da kuma rusa ɓata ta hanyar litattafan ɓata,[32] shi kuma shaik Wahid Alkurasani ya yi fatawa ta haramcin sayan su da kuma yaɗa su idan akwai yiwuwar ɓata ta hanyar su.[33]

Fatawowi

Sheik Muntazar yana ganin cewa sakamakon a wannan zamani cigaba kan abin da ya shafi buga litattafai da yaɗa su lallata litattafan ɓata baya warware matsalarsu, kai hakamma yana ƙarawa mutane muhimmanci kulawa da su ne, kamar yadda ajiye litattafan ɓata da yaɗa su duk da ɓatan da suke ɗauke da shi na shirme da wahami, to hakan yana kai ga su ruguje kansu da kansu, saboda haka ajiye su ba haramun bane kuma ba tilas ba ne a lallata su. [34]

Dalili Na Fiƙihu

Malaman fiƙihu sun kafa hujja da dalilai guda huɗu wajan tsamo hukunce-hukunce na litattafan ɓata, ayoyin ƙur'ani daga cikinsu akwai aya ta shida a cikin suratul Luƙman da aya ta 30 a cikin suratul hajji [35] kuma akwai ruwayoyi daga cikinsu akwai ruwayar da aka rawaito daga Imam Sadiƙ (A.S) a cikin littafin Tuhaful Uƙul,[36] kuma akwai Ijma'i, [37] da dalili na hankali kamar hana yin fasadi,[28] da kuma ture ko magance matsalar da ake tinanin faruwar ta, [39]

Litattafan Ɓata A Kundin Tsarin Mulki Na Ƙasar Iran

Wannan kalma an yi amfani da ita a wajan gyaran kundin mulki na ƙasar Iran a shekara ta 1285 hijirar Shamsiyya,[40] Mada ta ashirin a cikin dokokin Iran kan abin da ya shafi ƴancin jaridu da majallu yana cewa jaridu suna da cikakkiyar dama kan buga jaridunsu, banda litattafan ɓata waɗanda suke cutar da addini[41] kuma a Mada ta 24 cikin kundun mulki na ƙasar Iran ba tare da anbatan litattafan ɓata ba, Ya zo cewa jaridu da harkar buga takardu suna da ƴanci nayi bayani kan maudu'ai daban-daban matsawar basu saɓawa dokokin musulinci da hakki na gamagari ba.[42]

Litattafan Ɓata Da ƴancin Fadin Albarkacin Baki

Wasu daga cikin hukunce-hukunce na litattafan ɓata sun saɓawa ƴanci magana da tinani da bincike na ilimi,[43] amsa ga wannan magana ita ce shi addinin musulinci yana kwaɗaitar da mutane kan bincike da gano abubuwa sababbi da kuma neman sani, kuma shi musulinci ba ya karo da yin tinani da ƴancin magana, sai dai cewa shi musulinci ya bawa tinani mai kyau da aƙida ta al'umma mai kyau muhimmanci, shi musulinci saboda yana so ya hana ɓata a ƙida da aklaƙ a cikin al'uma sai ya iyakance ƴancin mutum a tinani da kuma ƴancin yin magana.[44]