Hayyu ala Kairil Amal

Daga wikishia

Hayyu Ala Kairil Amal (arabic: حي على خير العمل) daya daga cikin juzu’an kiran sallahh da Ikama da yake da ma’anar ku gaggauta ku taho zuwa ga mafi alherin aiki, riwayoyi sun bayyana cewa wannan Kalmar tun zamanin Annabi take cikin juzu’an kiran sallahh da ikama, amma a zamanin Halifa na biyu domin karfafa mutane zuwa ga Jihadi sai ya cireta daga kiran sallahh. Yan shi’a suna karanta Hayyu ala Kairil Amal a kiran sallahh da ikama, amma Ahlus-sunna basa amfani da ita kwata-kwata cikin kiran sallahا, sabada haka ne Hayyu ala Kairil Amal ya sauya ya zama matsayin wani take na yan shi’a da yake kishiyantar Assalatu Kairun minan Naumi (sallah tafi yin bacci) wanda ya zama taken Ahlsu-sunna, wannan take a zamanin Halifa na biyu an shigar da shi cikin Kiran sallahh, a mahangar shi’a wannan sabon take ana kidaya shi cikin bidi’a

Matsayi da muhimmanci

Hayyu ala Kairil Amal yana da ma’anar ku gaggauta zuwa ga mafi alherin aiki, yana daga yankunan kiran sallah da ikama, wannan jumlar tana daga gabar da aka samu sabani tsakanin shi’ da sunna a cikin kiran sallah da ikama [1] wani lokacin yankunan hayyu alal salati , hayyi alal falahi suna zuwa da unwanin (hay’ala) [2]

Shin Hayyu ala Kairul Amal juzui’ ne na Kiran sallah?

Malaman Fikihu suna kidaita Hayyu Ala Kairul Amal juzu’i cikin kiran sallah da ikama da yake zuwa bayan gabar hayyu alal falahi (ku gaggauta zuwa ga rabauta)[3] amma Malaman Fikihun Ahlus-sunna basu karbi hayyu ala Kairil Amal juzu’i daga kiran sallah da ikama, maimakonsa sai kira Assalatu kairun minan naumi a sallah asuba kuma suna kidaya shi a matsayin aiki mustahabbi [4] a mahangarsa kiran hayyu Ala kairul Amal Makruhi ne.[5] Kan asasin riwayoyi ya kasance a zamanin Manzon Allah (S.A.W) ana kidaya Hayyu ala Kairil Amal juzu’in kiran sallah da ikama,[6] bugu da kari akwai wasu bayanai da suke nuna cewa wasu Ba’arin Sahabbai misalin Abdullahi Bn Umar [7] Bilal Habashi [8] Abu Mahzure [9]suna Ambato hayyu ala Kairil Amal cikin kiran sallah.

Cire Hayyu Ala Kairil Amal daga cikin kiran sallah

A zamanin hukumar Umar Bn Kaddab da umarninsa ya sa aka cire Hayyu ala Kairil Amal [10] Shaik Saduk ya nakalto daga Ibn Abbas cewa hadafin Halifa na biyu kan cire Hayyu ala Kairil Amal daga kiran sallah ya kasance sakamakon mutane sun fara Imani cewa sallah ita ce mafi alherin ayyuka kuma ka da mutane su juyawa Jihadi baya [11] a cikin wata riwaya daga Imam Kazim (A.S) dalili na hakika da boyayyen manufar wannan aiki nasa shine datse mutane daga barin karkata zuwa ga wilaya mafi alherin aiki, duk da cewa a zahirinsa shine hana mutane juyawa Jihadi baya [12] a wata riwaya da ta zo cikin littafin Ma’ani Akhbar daga Imam Sadik (A.S) cikin amsar da ya bayar dangane Hayyu ala Kairil Amal ya bayyana cewa wilaya itace mafi alherin aiki. [13]

Taken kiran sallar `Yan Shi’a

Hayyu ala Kairil Amal ya kasance wata shaida ga `yan shi’a, da wannan ne a dauloli shi’a ambaton sa ya yadu, amma Sarakunan Daulolin Ahlus-sunna sun cire shi daga kiran sallah.

  • A shekara ta 169 lokacin mikewar Husaini Bn Ali (Shahidul Fakki) a kwace garin Madina ya tilasta mai kiran sallah da ya ambaci hayyu ala Kairil Amal cikin kiran sallahr Asubahi, Sarkin Madina da yaji wannan Kalmar take sai ya arce,

[14]

  • zamanin Nasir Atrosh wanda ya mutu s shekara 304 hijiri kamari Taken `Yan SHi'a Kiran Sallah shine Hayyu Ala Kairul Amal da kuma fararen Tutoci. [15]
  • A Daular Fatimiyya hijira na da shekara 297-567 a kasar Misra ana ambaton Hayyu ala Kairil Amal, [16] a shekara 359 a karo na farko an ambaci Hayyu ala Kairil Amar a Masallacin Bn Tutun [17] sai dai cewa bayan Salahuddini Ayyubi ya mamaye Misra ya hana ambaton Hayyu Ala Kairil Amal cikin kiran sallahh.[18]
  • A lokacin Daular Alu Babawaihi shekara ta 322-448 an dawo da Hayyu ala Kairil Amal cikin kiran sallahh, yayin da Salujukiyawa suka kwace hukuma sai suka cire shi daga kiran sallahh. [19]
  • A shekara ta 1441 a muhallin Karkh Bagdad a Babban birnin Bagadaza an samu barkewar rikicin addini tsakanin kungiyoyi,`yan shi’a suna ambatar Hayyu ala Kairil Amal cikin kiran sallahrsu, a shekara ta 448 Ahlus-sunna suma suna ambaton Assalatu Kairun minan naumi.[20]
  • Bayan Ulijiyatu ya karbi Mazhabar Shi’anci sai ya bada umarnin dinga Ambato Hayyu Ala Kairil Amal cikin kiran sallah.[21]

Taswibu (Assalatu Kairun Minan Naumi) Wani Take Na Ahlus-sunna

Kishiyar Hayyu ala Kairil Amal an ajiye Assalatu Kairun minan naumi ko kuma abinda ake kir ada (Taswib) [22] matsayin daya daga gabar kiran sallah a wurin Ahlus-sunna wadda ta kasance wata bidi’a da sam bata da waje a addini, [23] saboda zance da ayyukan sahabba ba hujja bane[24] a mahangar Imamiyya da Zaidiyya abinda yake hujja shine zance da kuma ayyuka Ma’asumai kadai

Abin nufi daga mafi alherin aiki

Ya zo a ba’arin wasu riwayoyi cewa mafi alherin aiki shine sallahh,[25] amma a kan asasin ba’arin wasu hadisan kuma abin nufi da mafi alherin aiki shine Wilaya [26] ko kuma kyautatawa Fatima (S) da `ya`yanta.[27]

Nazari

Littafin "Al-Azan Bahayyii Ala Khair Al-Al'mal" na Muhammad Bin Ali Alavi, daya daga cikin malaman Zaidiyya

A cikin littafin Azan bi Hayyu ala Kairil Amal wallafar Muhammad Bn Alawi ya rayu shekara ta 367-445 daya daga Malam Zaidiya, dangane da Hayyu ala Kairil Amal ya rubuta wasu abubuwa daga cikinsu akwai: ya kawo riwaya game da cewa kan kasancewar hayyu ala Kairil Amal ya kasance cikin kiran sallahh, sai aka shirya gamgami hakika zaidiya da Imamiya sun tafi kan cewa Hayyu ala Kairil Amal yana cikin kiran sallahh, wannan littafi ya samu sa’ido da kulawa daga babban muhakkikin Zaidiyya Yahaya Salim Azan sannan Madabba’ar Markaz Badar dake garin San’a ta buga shi a shekara ta 1997 miladiyya. Akwai kuma littafin Hayyu ala Kairul Amal baina Shari’a wal Ibtida’I wallafar Muhammad Bn Salim Azan wannan yana da shafi 80 an buga shi da yada shi a shekara 1419 a Yaman. [28] Littafin Juz’iyyatu Hayyu ala Kairil Amal fil Azan wallafar Abdul Amir Suldani yadawar Mu’assasar Majma’u Jahani Ahlil-Baiti (A.S). Azan bainal Asalati Wat Tahrifi Hayyu ala Kairil ala Kairil Amal Ashshar’iyatu Shu’ariya, wallafar Assayid Ali Shahristani. Hayyu ala Kairil Amal, Masa’il Shar’iyyati baina Sunna wal Bid’iyya, wallafar Sayyid Muhammad Mahadi Kurasani. [29]

Bayanin Kula

  1. Ameli, "Hay Ali Khair al-Alam Fi Al-Azan", shafi na 52.
  2. Ansari, Al-Masu'a Al-Fiqhiyyah Al-Muyassara, 1415 AH, Juzu'i na 13, shafi na 219.
  3. Sayyid Morteza, Al-Intisar, 1415H, shafi na 137.
  4. Duba Jaziri, Fiqhu Ali Al-Mazahib al-Arba, 1424H, Mujalladi na 1, shafi na 283.
  5. Duba Nawi, al-Majmoj Sharh al-Muhazzab, Dar al-Fikr, juzu'i na 3, shafi na 198.
  6. Duba Bayhaqi, Al-Sunan al-Kubra, 1424H, Mujalladi na 1, shafi na 625.
  7. Malik bin Anas, Al-Muwatta, Al-Maktab al-Alamiya, juzu'i na 1, shafi na 55; Bayhaqi, Al-Sunan Al-Kubra, 1424H, juzu’i na 1, shafi na 625.
  8. Bayhaqi, Al-Sunan Al-Kubra, 1424 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 625.
  9. Azan, Hayyu Ala Khairil al-Aml, 1419 AH, shafi na 21.
  10. Taftazani, Sharh al-Maqasid, 1409 AH, juzu'i na 5, shafi na 283.
  11. Sadouq, ilalu Sharayi, 1385, juzu’i na 2, shafi na 368.
  12. Sadouq, Ilalul Sharayi, 1385, juzu’i na 2, shafi na 368.
  13. Sadouq, Ma'ani al-Akhbar, 1399 AH, shafi na 41.
  14. Abolfaraj Esfahani, Muqatil al-Talebein, Daral al-Marefa, shafi na 375.
  15. Sabi, Akhbar al-Dawlah al-Dilami, a cikin: Madelong, Akhbar al-Imam al-Zaidiyyah, 1987, shafi na 24.
  16. Sabi, Akhbar al-Dawlah al-Dilami, dar: Madelong, Akhbar al-Imam al-Zaidiyyah, 1987, shafi na 24
  17. Ibn Khaldun, Diwan al-Mubtada, 1408H, juzu'i na 4, shafi na 61.
  18. Ibn Kathir, al-Badaiya wa al-Nahaiya, 1407H, juzu'i na 12, shafi na 263..
  19. Halabi, Al-Sirah al-Halbiyyah, Dar al-Kitab al-Alamiya, juzu'i na 2, shafi na 136.
  20. Ibn Athir, Al-Kamel, 1385 Hijira, Mujalladi na 9, shafi na 561.
  21. Ibn Athir, Al-Kamel, 1385 Hijira, Mujalladi na 9, shafi na 632.
  22. Ghashani, Tarikh Oljaito, 1348, shafi na 100.
  23. Duba Malik bin Anas, Al-Muwatta, Al-Maktab al-Alamiya, Mujalladi na 1, shafi na 54.
  24. Sayyid Morteza, al-Masal al-Nasiriyat, 1417 AH, shafi na 183.
  25. Mohagheq Damad, Mabahisu Usul Fiqh, 1362, juzu'i na 2, shafi na 45.
  26. Sheikh Sadouq, Ayoun Akhbar al-Reza (AS), 1378 A.H., juzu'i na 2, shafi na 106; Ibn Hayyun, Dua'im al-Islam, 1385 AH, juzu'i na 1, shafi na 142; Kilini, Al-Kafi, 1407 Hijira, juzu'i na 7, shafi na 52.
  27. Sheikh Sadouq, Ilalul Sharayi, 1385, juzu'i na 2, shafi.368, h4; Sheikh Sadouq, Al-Tauhid, 1398H, shafi na 241
  28. Khair, “Tasweeb au Hay Ala Khair al-Alam?”, shafi na 108.
  29. Azan, Hay Ala Khair al-Alam baina Shari'a wa Al-Ibtada, 1419 AH, ID na littafi.

Nassoshi

  • Abul Faraj Esfahani, Ali bin Hossein, Muqatil al-Talbeyin, wanda Seyyed Ahmed Saqr ya yi bincike, Beirut, Dar al-Marafa, Bita.
  • Ansari, Muhammad Ali (Khalifa Shushri), Al-Musua'a al-Fiqhiyyah al-Misra, Qum, Majmall al-Fikr al-Islami, 1415H.
  • Bayhaqi, Ahmad bin Hossein, Al-Sunan al-Kubari, Muhammad Abd al-Qadir Atta, Beirut, Darlaktb al-Alamiya ya yi bincike, bugu na uku, 1424H/2003 Miladiyya.
  • Dhahabi, Muhammad bin Ahmad, Tarikhul Islam wa-Wafayat A-Alam, wanda Omar Abd al-Salam Tadmari, Beirut, Dar al-Kitab al-Arabi ya yi bincike, bugu na biyu, 1413 AH/1993 miladiyya.
  • Ghashani, Abdullah bin Muhammad, Tarikh Uljaito, na Mahin Hambali, Tehran, Kamfanin Fassara da Bugawa, 1348.
  • Halabi, Ali Ibn Ibrahim, Al-Sirah al-Halabiyyah, Darul Kutb al-Alamiya, Bija, Bita.
  • Ibn Athir, Ali bin Bikaram, Al-Kamal fi al-Tarikh, Beirut, Dar Sadir - Dar Beirut, 1385H/1965 Miladiyya.
  • Ibn Hayyoun, Nu'man bin Muhammad al-Maghrebi, Dua'im al-Islam wa Zikr Halal wa Haram wa Al-Qadaya wa Al-Ahkam, Qum, Mu'assasa Al-Bait (AS), bugu na biyu, 1385H. .
  • Ibn Kathir, Ismail bin Omar, al-Badaiya wa al-Nahaiya, Beirut, Darul Fikr, 1407H/1986 Miladiyya.
  • Ibn Khaldun, Abd al-Rahman ibn Muhammad, Diwan al-Mubatada wa al-Khobar fi Tarikh al-Arab wa al-Barbar wa Man Aserham Man Dhu al-Shaan al-Akbar, Khalil Shahada, Beirut, Dar al- ya yi bincike. Fikr, 1408H/1988 Miladiyya.
  • Jaziri, Abdurrahman bin Mohammad Awad, Fiqhu Ali al-Mazaheb al-Arba, Beirut, Darlaktab al-Alamiya, 1424H/2003 Miladiyya.
  • Khair, Abdur Rahman, "Al-Thawib Ya Hai Ali Khair Al-Alam?", Al-Hadi, Shekara ta 7, lamba ta 2, Safar 1401H.
  • Kulaini, Muhammad bin Yaqub, al-Kafi, bincike da gyara na Ali Akbar Ghafari da Muhammad Akhundi, Tehran, Dar al-Kitab al-Islamiya, bugu na hudu, 1407H.
  • Malik bin Anas, Barwayah Muwatta Malik na Muhammad bin Al-Hassan Al-Shibani, bincike na Abdul Wahab Abdul Latif, Bija, Al-Maktab Al-Alamiya, bugu na biyu, Bina.
  • Nawi, Yahya bin Sharaf, al-Majmoj Sharh al-Muhazzab, Dar al-Fikr, bija, bita.
  • Sayyed Morteza, Ali bin Hossein, Al-Intisar Fi Infradat Al-emamiya, Qum, ofishin wallafe-wallafen Musulunci, 1415H.
  • Sayyid Morteza, Ali bin Hossein, Al-Masail al-Nasiriyat, Tehran, Al-Taqwa da Al-Islamic Relations, 1417H.
  • Sheikh Sadouq, Muhammad Bin Ali, Ayoun Akhbar al-Reza (AS), Tehran, Nash Jahan, bugun farko, 1378H.
  • Sheikh Sadouq, Muhammad Bin Ali, Ilalu Sharayi, Qum, Davari Publications, 1385.
  • Sheikh Sadouq, Muhammad Bin Ali, Ma'ani al-Akhbar, Beirut, Darul Merfa'a na bugawa da bugawa, 1399 Hijira.
  • Sheikh Sadouq, Muhammad Bin Ali, Man Laihzara Al-Faqih, Qum, Ofishin Daba'ar Musulunci, 1413H.
  • Sheikh Sadouq, Muhammad bin Ali, Al-Tawhid, Kum, Jamia Modaresin, bugun farko, 1398H.
  • Taftazani, Saad al-Din, Sharh al-Maqasid, Abd al-Rahman Umira, Qom, al-Sharif al-Razi, Qom, 1409 AH.
  • خرسان، سید محمدمهدی، حی علی خیر العمل، قم، دلیل ما، ۱۳۸۶ش
  • عاملی، سید جعفرمرتصی، «حی علی خیر العمل فی الاذان»، الهادی، سال پنجم شماره۶، محرم ۱۳۹۸.
  • عزان، محمد سالم، «حی علی خیر العمل بین الشریعة و الابتداع»، یمن، چاپ اول، ۱۴۱۹ق.