Harisatu Bn Nu'uman

Daga wikishia
(an turo daga Harisatu Bn Al-Nu'uman)

Harisatu Bin Nu'uman (arabic: حارثة بن النعمان) wanda ya rasu shekara ta 50 h ƙamari, ya kasance ɗaya daga cikin Sahabban Annabi (S.A.W) da Imam Ali (A.S) yaje yaƙe-yaƙen Badar, Uhudu, Hunaini da kuma yaƙe-yaƙen da aka yi zamanin gwamnatin Imam Ali. Harisatu mutum ne da ya yi kyautar gidansa ga Manzon Allah (S.A.W) domin ya zauna tare da matansa, haka nan kuma ya ƙara ba da kyauta wani gidan daban domin Ali (A.S) da Fatima su zauna a ciki. Harisatu ya ga taɓa ganin Mala'ika Jibrilu da surar Dahiyyatu Kalabi har ma ya yi masa sallama. An naƙalto hadisan Annabi (S.A.W) ta hantar Harisatu Bn Nu'uman.

Matsayi

Annabi (S.A.W):
cikin mafarki na ji wani sautin karatun daga cikin aljanna' sai na ce wannan mai karatun wanene shi : sai aka ce Harisatu Bn Nu'uman ne, “Waɗannan su ne masu kyautatawarku”

[1]

Harisatu Bn Nu'uman ya kasance daga Sahabban Manzon Allah (S.A.W) da Imam Ali (A.S) [2] ya je yaƙin Badar [3] Uhudu, Hunaini tare da Annabi (S.A.W) da sauran yaƙe-yaƙe. [4] a cewar Shaik ɗusi lokacin Halifancin Imam Ali (A.S) ya shiga yaƙe-yaƙe da a ka yi a wannan lokaci tare da Imam. [5] Harisatu Bn Nu'uman yana daga cikin mutane da suka tsaya kyam tare da Annabi (S.A.W) suna bashi kariya, ba su gudu a yaƙin Hunaini bayan guduwar wasu adadin musulmai sakamakon harin da Musrikai suka kawo a kansu. [6]

Matsayi A Riwaya

Harisatu yana daga marawaitan hadisi. [7] wanda aka naƙalto riwayoyinsa a litattafan hadisai, tarihi da Ilimin Rijal misalin Musnad Ahmad Bin Hanbal, Kitabul Al-Magazi, Al-Mutalaf wal Al-Muktalaf. [8] marawaitan hadisai misalin Abdullahi Bn Abbas, Abdullahi Bn Amir Bn Rabi'a da Sa'alaba Bn Abi Malik duka sun rawaito hadisai daga Annabi (S.A.W) ta hanyarsa. [9]

Ganin Mala'ika Jibrilu

Cikin Masadir tarjamar Sahabbai an ambaci Harisatu Bn Nu'uman daga Sahabbai masu falala. [10] a cewar Shaik ɗusi, Harisatu ya ga Mala'ika Jibrilu har karo biyu cikin surar Dahiyyatu Kalabi kuma har sallama ya yi masa. [11] Ibn Abdul-Barri cikin littafin Al-Isti'ab ya kawo cewa haƙiƙa Harisatu Bn Nu'uman ya samu shahara ne albarkacin kyautatawa mahaifiyarsa da girmamata. [12]

Bada Kyautar Gidansa Ga Annabi (S.A.W)

ورد عن رسول الله صلی الله عليه وآله وسلم:


نِمْتُ فَرَأَيْتُنِي فِي الْجَنَّةِ فَسَمِعْتُ صَوْتَ قَارِئٍ، فَقُلْتُ: مَنْ هَذَا؟قَالُوا: صَوْتُ حَارِثَةَ بْنِ النُّعْمَانِ. فَقَالَ رَسُولُ اللَّهِ صلی الله عليه وآله وسلم: كَذَلِكَ الْبِرُّ، كَذَلِكَ الْبِرُّ
Na kwanta bacci sai na yi mafarki na ganni ciki aljanna, sai na ji wani sauti mai karatu, nace wanene wannan? sai aka ce: sautin harisatu bin nu'uman ne, sai Manzon Allah (s.a.w) ya ce: haka dama masu kyautatawa suke, haka masu kyatatawa suke.



( Ibn Abdul-Barr, Al-Isti’ab, 1412H, juzu’i na 1, shafi na 307)


Harisatu shi ne Mutum na farko a Madina da ya fara bada kyautar gidansa ga Annabi (S.A.W), [13] bisa rahotan Ibn Sa'ad malamin tarihi a ƙarni na uku h ƙamari, ɗakunan Harisatu sun kasance kusa da ɗakunan Manzon Allah (S.A.W) duk lokacin da Annabi (S.A.W) ya yi sabon aure sai Harisatu ya matsa zuwa ɗakin gaba ya ɗan nesanta ɗakinsa da na Annabi (S.A.W) [14] a haka har sai da ya yi kyautar bakiɗayan ɗakunan gidansa ga Annabi (S.A.W) domin matan Annabi (S.A.W) su zauna a ciki su rayu. [15] Daga jumlarsu akwai matsugunin Mariya na farko, [16] haka Sannan kuma akwai wani gida da Annabi ya ba Safiyya da A'isha, matan Ansar kuwa sukan je gidan su ganta. [17] Annabi (S.A.W) ya yiwa Harisatu Addu'a sakamakon kyautar gida da ya yi masa da kuma wasu ba'arin Muhajiru da suma ya basu kyautar gida. [18]

Kyautar Gida Ga Hazrat Ali (A.S) Da Fatima (S)

Asalin Maƙala: Gidan Hazrat Fatima (S)

Ibn Sa'ad malamin tarihi na Ahlus-sunna wanda ya rasu shekarar 230 h ƙamari, cikin littafin ɗabaƙatul Al-Kubra ya naƙalto daga Imam Baƙir (A.S), daga Imam Ali (A.S) cewa bayan aurensa da Fatima (S) Annabi (S.A.W) ya tanadi wani gida da yake da nesa kaɗan daga gidansa domin yana so ɗiyarsa ta zauna kusa da shi, sai Fatima (S) ta nemi Annabi (S.A.W) ya yi wa Harisatu magana domin su zauna a gidansa. [19] sai ya ce yana jin kunyar tunkarar Harisatu da wannan maganar, saboda a baya ya yi masa kyautar wani ɓangaren gidansa, da wannan dalili Harisatu ya dinga cirata daga wannan ɗaki zuwa wancan ɗaki na gaba. [20] sai Harisatu ya samu labarin wannan magana sai ya ƙara bada kyautar gidansa ga Annabi (S.A.W) [21] kan asasin naƙalin ba'arin masadir ɗin Shi'a, Ali (A.S) da Fatima (S) bayan aurensu sun zauna a gidan da Harisatu ya bawa Manzon Allah (S.A.W) kyautarsa. [22] Ibn Shabba wanda ya rasu shekarar 262 h ƙamari, marubucin tarihi daga ɓangaren Ahlus-sunna ya kawo cewa gidan Harisatu da ya kasance kusa da gidan Abu Ayyubil Ansari wanda daga baya Imam Sadiƙ (A.S) ya mallake shi, shi ne dai gidan da Imam Ali (A.S) ya zauna [23] a shekarar 1365 h shamsi, a shirin faɗaɗa Madina an rushe wannan gida. [24]

Nasaba Da Wafati

Harisatu Bn Nu'uman Bn Nafa ko Naƙa, [25] Ansari Khazraji [26] da Ja'ada Bint Ubaid Bn Sa'alaba, [27] Laƙabinsa Aba Abdullah [28] kuma shi dan kabilar Bani Najjar ne kuma ya zauna a Madina [29], [30]saboda kasancewarsa a yaƙin badar, a wasu wurare ma ana ambatonsa da Harisatu Bn Numan Ansari Badri. [31] An ce: Muhammad Bn Abdulrahman Bn Abdullah bin Harisatu wanda aka fi sani da Abul al-Rajal. yana daga cikin zuriyarsa. [32] Ibn Hibban wanda ya rasu marubucin Rijal na daga Ahlus-sunna, ka asasin wata riwaya ya ce Harisatu ya yi shahada a lokacin yaƙin Badar, [33] amma wasu ba'arin malamai sun yi martani kan maganar Ibn Hibban sakamakon halartar Harisatu cikin sauran yaƙe-yaƙe da aka yi bayan Badar [34] bisa rahotan Ibn Sa'ad wanda ya rasu a shekara 230 h ƙamari, ya kawo cewa Masana tarihi sun takaitu da cewa Harisatu ya rasu a lokacin halifancin Mu'awiya. [35] na'am Zahabi wanda ya rasu shekarar 748 h ƙamari, yana ganin cewa Harisatu ya rasu shekara hamsin bayan hijira. [36]

Bayanin kula

  1. Ibn Abd Al-Barr, Al-Estiy'ab, 1412 AH, juzu'i na 1, shafi na 307.
  2. ɗusi, Rijal ɗusi, 1373, shafi na 37.
  3. Waƙidi, Al-Magazi, 1409 AH, juzu'i na 1, shafi na 24.
  4. Ibn Abd Al-Barr, Al-Estiy'ab, 1412 AH, juzu'i na 1, shafi na 307.
  5. ɗusi, Rijal ɗusi, 1373, shafi na 17.
  6. Ibn Athir, Usudul Al-Ghaba, 1415 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 655.
  7. Haytami, Majma Al-Zawaed, 1414 AH, juzu'i na 9, shafi na 313-314.
  8. Azizi wa Digaran, Al-Ruwat Al-Mushtarikun baina Shi'a wa Sunnah, 1388, juzu'i na 1, shafi na 191.
  9. ɗabarani, Al-Mu'jam Al-Kabir, 1415 AH, juzu'i na 3, shafi na 227; Abi Naim, Marifah Al-As'hab, 1422H, juzu'i na 2, shafi na 58.
  10. Duba Ibn Athir, Usudul Al-Ghaba, 1415H, juzu'i na 1, shafi na 655.
  11. ɗusi, Rijal ɗusi, 1373, shafi na 37.
  12. Ibn Abd Al-Barr, Al-Estiy'ab, 1412 AH, juzu'i na 1, shafi na 307
  13. Abdul Ghani, Buyot Al-Sahaba, 1420 AH, shafi na 69.
  14. Ibn Sa'ad, Thabaƙat Al-Kubra, 1410H, juzu'i na 8, shafi na 132.
  15. Ibn Sa'ad, Thabaƙat Al-Kubra, 1410H, juzu'i na 8, shafi na 132.
  16. Ibn Sa'ad, Thabaƙat Al-Kubra, 1410H, juzu'i na 8, shafi na 171.
  17. Ibn Saad, Thabaƙat Al-Kubra, 1410 AH, juzu'i na 8, shafi na 100; Balazri, Ansab al-Ashraf, 1417 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 444.
  18. Ibn Sa'ad, Thabaƙat Al-Kubra, 1410H, juzu'i na 8, shafi na 133
  19. Ibn Sa'ad, Thabaƙat Al-Kubra, 1410H, juzu'i na 8, shafi na 132
  20. Ibn Jozi, Al-Muntazem, 1412 Hijira, juzu'i na 5, shafi na 246.
  21. Ibn Sa'ad, Thabaƙat Al-Kubra, 1410H, juzu'i na 8, shafi na 132-133
  22. ɗabarasi, Elamul Alwara, 1417 AH, juzu'i na 1, shafi na 161.
  23. Ibn Shabba, Tarikh Al-Madina li Ibn Shabba, 1399 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 259.
  24. Sharrab, Farhang Elam Jografiyya, 2013, juzu'i 1, shafi na 149.
  25. Ibn Hibban, Al-Thuƙat, 1393H, juzu'i na 3, shafi na 79.
  26. Dhahabi, Siyar Alam Al-Nubala, 1414 AH, juzu'i na 2, shafi na 378.
  27. Ibn Abd Al-Barr, Al-Estiy'ab, 1412 AH, juzu'i na 1, shafi na 307.
  28. Ibn Abd Al-Barr, Al-Estiy'ab, 1412 AH, juzu'i na 1, shafi na 307.
  29. Ibn Saad, Thabaƙat Al-Kubra, 1410H, juzu'i na 3, shafi na 371.
  30. Abi Naim, Marifah Al-As'hab, 1422H, juzu'i na 2, shafi na 58.
  31. ɗabarani, Al-Mu'jam Al-Kabir, 1415 AH, juzu'i na 3, shafi na 227; Abi Naim, Marifah Al-As'hab, 1422H, juzu'i na 2, shafi na 58.
  32. Ibn Sa'ad, Thabaƙat Al-Kubra, 1410H, juzu'i na 5, shafi na 402.
  33. Ibn Hibban, Al-Thuƙat, 1393H, juzu'i na 3, shafi na 79.
  34. Ibn Balban Al-Farisi, Al-Ihsan, 1408H, juzu'i na 10, shafi na 510.
  35. Ibn Sa'ad, Thabaƙat Al-Kubra, 1410H, juzu'i na 8, shafi na 132.
  36. Dhahabi, Tarikh Al-Islam, 2003, juzu'i na 2, shafi na 396.

Nassoshi

  • Abdul Ghani, Muhammad Ilyas, Bayot na Sahabbai, Allah Ya yarda da su, kewayen Masjidul Nabawi al-Sharif, Madina Munura, Bina, 1420H.
  • Abi Naim, Ahmad bin Abdullah, Marifah Al-sahaba, Beirut, Dar al-Kitab al-Alamiya, 1422H.
  • Azizi, Hossein wa Digaran, Al-Ruwaat Al-Mushtarikun baina Shi'a wa Sunnah, Tehran, Al-Majma Al-alami for approɗimation tsakanin addinin Musulunci, 1388.
  • Balazri, Ahmad bin Yahya, Kitab Jamal Min Ansab Al-Ashraf, wanda Sohail Zakar da Riaz Zarkali suka yi bincike a Beirut, Darul Fikr, 1417H.
  • Belazari, Ahmad bin Yahya, Kitab Jamal Min Ansab al-Ashraf, wanda Sohail Zakkar da Riyadz Zarkali suka yi bincike a Beirut, Darul Fikr, 1417 bayan hijira.
  • Beyhaƙi, Ahmad bin Hussain, Dala'il Al-Nubuwa, Beirut, Darul Katb al-Alamiya, 1405H.
  • Dhahabi, Muhammad bin Ahmad, Siyar Aalam Al-Nubala, wanda Shoaib Arnout, Beirut, Al-Risalah Foundation ya yi bincike, 1414 AH.
  • Dhahabi, Muhammad bin Ahmad, Tarikh Al-Islam, bincike na Bashar Awad Maruf, Bija, Dar al-Gharb al-Islami, 2003.
  • Ibn Abd al-Barr, Yusuf bin Abd Allah, Al-Istiy'ab fi Marafah al-Ashab, bincike na Ali Muhammad Bejawi, Beirut, Sobh Piruzih, 1412 AH.
  • Ibn Athir, Ali Ibn Muhammad, Usud Al-Ghabafi fi Marafah al-Sahaba, bincike na Ali Muhammad Maawad, Adel Ahmad Abd al-Mawat, Beirut, Dar al-Katb al-Alamiya, 1415H.
  • Ibn Balban Al-Farisi, Alauddin Ala, Al-Ihsan fi Al-Karam Al-Sahih Ibn Hibban, bincike na Shuaib Arnout, Beirut, Al-Risalah Foundation, 1408H.
  • Ibn Hibban, Muhammad Bin Hibban, Al-Thuƙat, bincike na Muhammad Abd al-Maeed Khan, India, Ottoman Encyclopaedia in Hyderabad, Al-Dakn, India, 1393 AH.
  • Ibn Jozi, Abd al-Rahman bin Ali, Al-Muntazem, Tahaƙi Muhammad Abd al-ƙader Atta, Mostafa Abd al-ƙader Atta, Beirut, Dar al-Kitab al-Alamiya, bugu na farko, 1412H.
  • Ibn Saad, Muhammad Ibn Saad, Thabaƙat Al-Kubra, Bincike na Muhammad Abd al-ƙadir Atta, Beirut, Dar al-Kitab al-Alamiya, bugun farko, 1410H.
  • Ibn Shabah, Umar, Tarikh Al-Madina li Ibn Shabah, bincike na Fahim Muhammad Shaltut, Jeddah, Bina, 1399 AH.
  • Sharab, Mohammad Hossein, Al'adun Sanarwa na Tarihi a cikin Hadisi da Rayuwar Annabci, Mohammad Reza Nemati ya fassara, Hamid Reza Sheikhi, Tehran, Mashaar, 2003.
  • Waƙidi, Muhammad bin Omar, Al-Maghazi, bincike na Marsden Jones, Beirut, Al-Alami Foundation for Press, 1409 AH.
  • ɗabarani, Suleiman bn Ahmad, Al-Mu'ajm Al-Kabir, wanda Hamdi bn Abdulmajid al-Salfi ya yi bincike a birnin Alkahira, mazhabar Ibn Taimiyyah, 1415H.
  • ɗabarasi, Fazl bin Hasan, Elamul Al-Waria bi Alamul Al-Huda, ƙum, Al-Bait (A.S.), 1417H.
  • ɗusi, Muhammad bin Hassan, Rijal al-Tousi, Jamaat al-Madrasin fi Al-Hawza Al-Alamiya Baƙom, Al-Nashar al-Islami Foundation, 1373.