Hamidat

Daga wikishia

Hamidat, (arabic: الحامدات) suna ne da ake amfani da shi kan surorin Fatiha, Kahaf, Sab'i, da Faɗir, dukkaninsu surori ne da suka fara da kalmar Alhamdulillahi [1] haka zalika ana kiransu da "Ha'at" da "Hamdu" ko "Ma ƙasir Kur'an" [Tsokaci 1][2] jigo shi ne kasancewar sun yi tarayya cikin tauhidi, Annabta da Ma'ad (Ranar Al ƙiyama) wanda ake kira da Asalan Addini, [3] Suyuɗi cikin littafin Al-Itƙan ya naƙalto daga littafin Jamalul Al- ƙurra, cewa cikin Alkur'ani akwai Mayadin Jam'in kalmar Maidan, Basatin jam'in kalmar Bustan, wacce take nufin lambuna, Riyad jam'in kalmar Rauda wacce take nufin lambu, Ara'is jam'in kalmar Arus, Dayabiju jam'in Dibaj wanda yake da ma'anar Alhariri, Mayadinul Kur'an surori ne da suke farawa da Alif Lamin, Basatinul Kur'an surori ne da suke farawa da Alif lamra, Maƙasirul Kur'an surori ne da suke farawa da Hamidat, Ara'isul Kur'an surori ne da suke farawa Musabbahat, sannan kuma Dabayijul Kur'an surori ne da suke farwa da Hamimat (Ha-mim) Riyadul Kur'an Surori ne Mufassalat. [4]

Bayanin kula

  1. Markaz Farhang Ma'arif Kur'an, Da'iratu Al-Maarif Kur'an Kareem, juzu'i na 8, shafi 418
  2. Suyu ɗi, Al-It ƙan fi Ulum al- ƙur’an, 1394 Hijira, Juzu’i na 1, shafi na 201; Hojjati, Fajuheshi dar Tarikh Kur’an Kareem, 1395, shafi na 105.
  3. Akbarzadeh, Tanasub Suwar Hamedat.
  4. Suyu ɗi, Al-It ƙan fi Ulum al- ƙur’an, 1394 AH, juzu’i na 1, shafi na 201.

Tsokaci

  1. Maqasir shi ne jam'in Maqsourah wanda ke nufin falo, falo da baranda. (Sashen yada farfagandar Musulunci, Kamus na ilimomin Alqur’ani shafi na 3442).

Nassoshi

  • Hojjati, Seyyed Mohammad Bagher, Fajuheshi dar Tarikh kur'an Kareem, Farhang Islamic Publishing House, 2015.
  • دفتر تبلیغات اسلامی، «[https:/* Markaz Farhang Ma'arif Kur'an, Da'iratu Al-Maarif, ƙum, Bostan Kitab, bugu na uku, 2013.
  • اکبرزاده، فاطمه، تناسب سور حامدات، پایان‌نامه کارشناسی ارشد، دانشگاه الزهرا، ۱۳۹۲ش.

/lib.eshia.ir/26683/1/3442 فرهنگ‌نامه علوم قرآن]»، بی‌تا.