Gazwa

Daga wikishia
Wannan ƙasida ce game da yaƙe-yaƙen da Manzon Allah (S.A.W) ya halarta. Domin sanin duk yaƙoƙin Manzon Allah, duba ƙasidar aka Yaƙe-yaƙen Annabi (S.A.W).

Gazwa, (arabic: الغزوة) suna ne na yaƙe-yaƙe da Annabi (S.A.W) ya halarta, a aksarin masadir na tarihi an bayyana cewa Annabi (S.A.W) ya je yaƙi guda 26 zuwa 27, sannan tsakanin wannan adadi kaɗai guda tara ne aka gwabza yaƙi, a cewar wasu ba’arin masu zurfafa bincike, bakiɗayan yaƙe-yaƙen da Annabi (S.A.W) ya je an samu nasara in banda yaƙin Uhudu.

Bambanci Tsakanin Gazwa da Sariyya

Cikin litattafan da aka rubuta su kan maudu’in tarihin muslunci, an kasa yaƙe-yaƙen Annabi (S.A.W) zuwa kashi biyu, Gazwa da Sariyya, [1] ana kiran yaƙe-yaƙen da Annabi (S.A.W) ya halarta tare da ɗaukar nauyin kwamandancinsu kai tsaye da sunan Gazwa, sannan yaƙe-yaƙen da bai halarta ba, amma ya shirya wasu gungun mayaƙa tare da naɗa musu kwamanda sannan ya tura su wani yanki domin yin yaƙi, shi misalin wannan yaƙi ana kiransa da suna Sariyya, [2] tare da haka wasu ba’arin masu nazari sun tafi kan cewa wannan bayani da ta’arifi da aka ambata bai kasance dandaƙaƙƙen ta’arifi ba kan Gazwa da Sariyya, shi Gazwa shi ne yaƙi da ya kasance a bayyane wanda Annabi (S.A.W) ya halarta tare da mayaƙa masu tarin yawa da kuma tsara shi, shi kuma Sariyya shi ne yaƙin da ya kasance a ɓoye da aka yi shi da adadi kaɗan daga mayaƙa, kuma bai kasance tsararre ba, [3] sai dai cewa kuma waɗannan ta’arifai guda biyu basu bambance misdaƙin Gazwa da Sariyya ba, kan asasin ta’arifi na ƙarshe Annabi (S.A.W) baya shiga yaƙin da aka yi shi da adadi kaɗan daga mayaƙa da kuma hadafin cutar da abokan gaba ko saninsu. [4]

Gazwa Da Aka Gwabza Yaƙi A Cikinsu

A cewar Ibn Hisham cikin littafin Al-Siratul An-Nabawiyya, [5] ɗabarasi cikin littafin Elamul Al-wara, sun ce tsakanin yaƙe-yaƙen da Annabi (S.A.W) ya halarta kaɗai cikin Badar, Uhudu, Khandaƙ, Bani Kuraiza, Bani Musɗaliƙ, Khaibar, Fatahu Makka, Hunainu da ɗa’if ne aka gwabza yaƙi, [6] Mas’udi marubucin littafin Murujul Az-Zahab, maimakon kawo sunan yaƙin Bani Musɗaliƙ sai ya rubuta yaƙin Tabuk. [7] haka nan kuma cikin yaƙe-yaƙen da aka gwabza yaƙi guda biyar ne kaɗai suka kasance masu zafi da tsanani. [8]

Samun Nasara Cikin Galibin Gazwa

Zanen Fatihu Khaiber, mai akan zane, na Hassan Ruhu Al-Amin, 2017, 180*280 cm.

Baki ɗayan Gazwa in banda gazwatu Uhudu Muslunci ya samu nasara, [9] a cewar ba’arin masu bincike samar ƙarfaffan tsari cikin Sojoji yana daga muhimman dalilan samun nasara a wannan yaƙe-yaƙe. [10] an ce tsara yanda za a yi yaƙi a cikin Gazwa wani tsari da ba a taɓa samar da irinsa ba a baya kuma ya kasance cikin marhaloli guda huɗu:

  • Tsari tun kafin tafiya yaƙi.
  • Tsari bayan fara tafiya.
  • Tsari cikin Fagen daga kafin fara yaƙi.
  • Tsari bayan fara gwabza yaƙi. [11]

A wannan zamani namu ana kiran marhaloli biyun farko da sunan matakin tsara yaƙi (strategy) Marhalolin biyun ƙarshe kuma da sunan dabarun yaƙi (Tactics) [12]

Adadin Gazwa

Aksarin masadir na tarihi sun tafi kan cewa adadin gazwa sun kasance guda 26 zuwa 27. [13] amma tare da haka a wasu litattafai an ambaci wasu adadin daban misalin sha takwas, [14] sha huɗu, sha biyar, ashirin da ɗaya [15] da ashirin da takwas, [16] gazwowi misalin gazwa banu ƙunaiƙa, da Wadil Al-ƙura da Umratul Al-ƙadha suna cikin jumlar gazwowi da aka samu saɓani ra’ayi cikin ƙidaya su jerin Gazwa, [17] an ce duk da cewa Annabi (S.A.W) bai halarci yaƙin Mutatu ba, amma wasu sun kira wannan yaƙi da sunan gazwa, [18] Muhammad Ibrahim marubucin littafin Tarikh Payambare Islam, ya bayyana adadin yaƙoƙi guda 27 kamar yanda sunansu zai zo a ƙasa: [19]

Sunan yaƙi Sojojin Muslunci Sojojin Maƙiya Wurin da aka yi yaƙi lokacin da aka yi yaƙi taƙaitacciyar Natijar da aka samu daga yaƙi
1 Gazwatu Abwa(wuddan) Sojoji 200 Ayarin ƙuraishawa Abwa (wani babban ƙauye kusa da wuddan tsakanin Makka da Madina) Safar Shekara ta biyu bayan hijira[20] A wannan gazwa ɗin ba a yi wani rikici na soji ba kuma an yi yarjejeniya da ƙabilar Bani Dhamrah da kada su kai hari musulmai ba.[21]
2 Gazwatu Buwaɗ Sojoji 200[22] cikin jogarantar Sojoji 100Umayyatu Bn Khalaf[23] buwaɗ Rabi'u awwal[24]ko اRabi'us Sani shekara ta biyu bayan hijira[25] a wannan Gazwa ba gwabza yaƙi ba.[26]
3 Gazwatu Ashira ko zil Ushaira Sojoji 150-200[27] Ayarin ƙuraishawa[28] Dhul-Ushaira (Wani wuri tsakanin Makka da Madina)[29] Jimada Awwal shekara ta biyu bayan hijira[30] Babu wani rikici kuma an yi yarjejeniya ta abokantaka da ƙabilar Mudlej da ƙawayenta.[31]
4 Badar na farko wani adadi daga muhajirun[32] Wasu adadin varayi ƙarƙashin jaogarancin kwamandancin Kurz bin Jaber[33] yankin Badar[34] Jimada Akar shekara ta biyu bayan hijira[35] ko rabiu awwal shekara ta uku bayan hijira[36] guduwar varayi[37]
5 Gazwatu Badar Kubra Sojoji 313[38] mutane 950[39] Yankin Badar[40] 17 ga watan Ramadan Nasarar da musulmi suka samu akan ƙuraishawa, kashe mushrikai 70 da kame 70 daga cikinsu.[41]
6 ko Gazwatu ƙarƙara Sojoji 200[42] ƙabilar Bani Gaɗfan[43] Yankin ƙargara al-Kudr mai nisa takwas «Manzil» (kusan kilomita 170) از madina[44] watan Sahawwal shekara ta biyu [45] Bani Salim sun gudu sun bar dukiyarsu a yaƙin[46]
7 Gazwatu Bani ƙunaiƙa Musulman Madina yahaudawan Bani ƙunaiƙa bani ƙunaiƙa[47] Madina 15 ga watan Shawwal shekara ta biyu bayan hijira[48] Tsaftace Madina daga Yahudawa[49]
8 gazwatu suwaiƙi Sojoji 200 daga Muhajirun da Ansar [50] 200 daga Mushrikai ƙarƙara alkudr Zul-Hijja, shekara ta biyu bayan hijira[51] guduwar mushrikai daga Makka[52]
9 ko Gazwatu zi Amri Sojoji 450 ƙarƙashin kwamandancin Dusur Bn Haris Bani Tha'laba daga ƙabilar Ghatafan[53] yankin Najd[54] Safar shekara ta uku bayan hijira[55] Abokan gaba sun tsere zuwa saman dutsen[56]
10 Gazwatu Bahran Sojoji 300 [57] Bani Sulaimi[58] buhran (Wani mahakar ma'adinai a Wadi Fura a cikin Hijaz)[59] Rabi al-Akhr shekara ta uku bayan hijira[60] A wannan Gazwa, babu wani rikicin soji da ya faru.[61]
11 Gazwatu Uhudu Sojoji 700[62] Mutane 3000 daga Mushrikan ƙuraishawa[63] Kasan dutsen uhudu Shawwal shekara ta uku[64] Mushrikai sun yi Nasara kuma Musulmi saba'in ne suka yi shahada.[65]
12 Gazwatu Hamra'i Al-Asadi Sojoji 630[66] Mushrikan ƙuraishawa[67] Yankin Hamra al-Asad, mil goma (kimanin kilomita 20) kudu da Madina[68] Shawwal na shekara ta uku[69] guduwar Mushrikan ƙuraishawa[70]
13 Gazwatu Bani Nadir wasu jama'a daga Muhajirun da Ansar[71] Bani Nadhir Bani Nadhir Wani yanki a Madina[72] Rabi'ul-Awwal shekara ta huɗu bayan hijira[73] Korar Bani Nadhir daga Madina[74]
14 Gazwatu zatu Ruƙa Mutum 400 daga Sahabbai[75] Bani maharib[76] Dutsen Zaat al-Raƙƙa a yankin Najd[77] Rabi Al-Awwal shekara ta huɗu[78] Guduwar maƙiya zuwa saman dutse da komawar Manzon Allah Madina[79]
15 Gazwatu Badar Al-Mau'id Sojoji 1500[80] Mutane 2000 daga Mushrikan Makka[81] Badar [82] Sha'aban shekara ta hudu[83] A wannan Gazwa babu wani rikicin soji.[84]
16 Gazwatu Dumatu Al-Jandal Mutum 1000[85] ƙabilar Duma Al-Jandal[86] Duma Al-Jandal[87] Rabi'ul-Awwal shekara ta biyar[88] Guduwar ƙabilar Duma Al-Jandal[89]
17 Gazwatu Khandaƙ Musulmai 3000 [90] Mutane 10,000 ne daga ƙuraishawa da abokansu[91] Madina Shawwal shekara ta biyar[92] tare da kashe Amru Bn Abdi Wuddi،Cin nasara da dawowar arna ba tare da nasara ba[93]
18 Gazwatu Bani ƙuraiza Sojoji 3000[94] ƙabilar Bani ƙuraiza[95] Kuduncin garin, Bani ƙurizah Castle[96] Dhu ƙadah da Dhul Hijjah na shekara ta biyar[97] Nasarar da sojojin musulunci suka samu akan Bani ƙuraizah[98]
19 Gazwatu Bani Lihiyan Sojoji 200[99] ƙabilar Lihiyan[100] garran [101] Jimada Ula shekara ta shida[102] guduwar Bani Lihiyan [103]
20 Gazwatu zi ƙiradi Sojoji 500-700 ko Gazwatu Gaba [104] Gaɗfan[105] ƙurad [106]da Rabi al-Thani na shekara ta shida[107] Kwato dukiyar Annabi da 'yanta matar Abu Dharr Ghafari[108]
21 Gazwatu Bani Musɗalaƙ Sojojo Mahayan Dawakai guda 100[109] Bani Mustalaƙ Karkashin jagorancin Harith bin Abi Zarar[110] Kusa da ruwan Murassi a yankin ƙodid[111] Shaban na shekara ta shida[112] ( ko ta biyar [113]) rashin cin nasarar Bani Musɗalik da kame su[114]
22 Sulhu Hudaibiyya Mutane 1400 zuwa 1600[115] ƙuraishawa[116] hudaibiyya[117] Zul-ƙaida, shekara ta 6 Hijiriyya[118] Yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Musulmi da ƙuraishawa[119]
23 Gazwatu Khaibar Mutum 1400[120] Yahudawan Khaibar Khaibar Safar na shekara ta bakwai bayan hijira [121] shan kashi mutanen Khaibar da mamaye sansaninsu Imam Ali (A.S)[122]
24 Fatahu Makka mutum 10000[123] ƙuraishawa[124] Makka Ramadan shekara ta takwas[125] shan kashin mushrikai da fatahu Makka[126]
25 Gazwatu Hunaini Mutum 12000[127] ƙabilar Hawazen da Thaƙif[128] hunaini Shawwal na shekara ta takwas[129] Nasara Musulmi[130]
26 Gazwatu ɗa'if mutum 12000[131] ƙabilar saƙif[132] ɗa'if[133] Shawwal na shekara ta takwas[134] Komawa Makka ba tare da nasara ba[135]
27 Gazwatu Tabuk mutum 30000 [136] Roma da abokan tarayya[137] Tabuk[138] Rajab, shekara ta tara[139] Yarjejeniyar cutar da ƙabilun Kirista da ke zaune a Tabuk[140] da kuma tarwatsa sojojin Romawa [141]

Bayanin kula

  1. Sobhani, Farazhaye az Tarikh Payambar Islam, 2006, shafi na 216.
  2. Sobhani, Farazhaye az Tarikh Payambar Islam, 2006, shafi na 216.
  3. ƙaidan, “Sazimandahi Jangi dar Gazwat Asre Payambar”, shafi na 79-80.
  4. ƙaidan, “Sazimandahi Jangi dar Gazwat Asre Payambar”, shafi na 80.
  5. Ibn Hisham, Al-Sirah al-Nabiwiyah, Daral al-Marafa, juzu'i na 2, shafi na 608
  6. Tabarsi, Elamul Alwara, 1417 AH, juzu'i na 1, shafi na 163.
  7. Masoudi, Moruj Al-Dhahab, 1409 AH, juzu'i na 2, shafi na 280.
  8. Alikhani, “Tahlil Siyasi Jangahaye Payambare AKRAM Raheburdi baraye Imruz” shafi na 71.
  9. ƙaidan, “Sazimendahi Jangi dar gazwat Asre Payambar”, shafi na 75.
  10. ƙaidan, “Sazimendahi Jangi dar gazwat Asre Payambar”, shafi na 75.
  11. ƙaidan, “Sazimendahi Jangi dar gazwat Asre Payambar”, shafi na 75.
  12. ƙaidan, “Sazimendahi Jangi dar gazwat Asre Payambar”, shafi na 75.
  13. Duba : Waƙidi, Al-Magazi, 1409 AH, juzu'i na 1, shafi na 7; Masoudi, Moruj Al-Dahahab, 1409 AH, juzu'i na 2, shafi na 280; Ibn Sa'ad, Thabaƙat Al-Kubra, 1414 AH, juzu'i na 2, shafi na 3; Ibn Hisham, Al-Sirah al-Nabawiyyah, Dar al-Marifah, juzu'i na 2, shafi na 608; Tabari, Tarikh Al-ɗabari, 1387 Hijira, juzu'i na 3, shafi na 152.
  14. Fasowi, Al-Marifa wa Al-Tarikh, 1401 Hijira, juzu'i na 3, shafi na 261.
  15. Beyhaƙi, Dala'ilul An-Nubuwati, 1405 Hijira, juzu'i na 5, shafi na 460.
  16. Masoudi, al-Tanbihu wa Al-Ashraf, Dar al-Sawi, shafi na 241.
  17. Misali, duba: Ibn Hisham, Al-Sirah al-Nabawiyyah, Darul Marafa, juzu'i na 3, shafi na 173; Salehi Shami, Sabl al-Hadi, 1414 AH, juzu'i na 4, shafi na 8; Tabari, Tarikh Al-ɗabari, 1387 AH, juzu'i na 3, shafi na 152; Masoudi, Moruj Al-Dahahab, 1409 AH, juzu'i na 2, shafi.281; ƙazi Abarƙawah, Sirat Rasool Khoda (a.s), 1377, juzu'i na 2, shafi na 848
  18. Jafarian, Sira Rasool Khoda (SAW), 2003, shafi na 464.
  19. Aiti, Tarikh Payambare Islam, 1369 AH, shafi na 238-240.
  20. Waƙidi, Al-Magazi, j 1 shafi na 11.
  21. Waƙidi, Al-Magazi, j 1 shafi na 12.
  22. ɗabari, Tarikh Al-ɗabari, 1387 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 407.
  23. Waƙidi, Al-Magazi, j 1 shafi na 12
  24. .Tarikh Al-ɗabari, 1387 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 407
  25. Bayhaƙi, Dala'ilul Al-Nubuwah, 1405 Hijira, juzu'i na 5, shafi na 469.
  26. Waƙidi, Al-Magazi, j 1 shafi na 12.
  27. Waƙidi, Al-Magazi, j 1 shafi na 12.
  28. Tarikh Al-ɗabari, 1387 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 408.
  29. Yaƙut Hamawi, Mujam Al-Buldan, 1995, juzu'i na 4, shafi na 127.
  30. Ibn Hisham, Al-Sirah Al-Nabawiyyah, Dar al-Marifa, juzu'i na 1, shafi na 599; ɗabarasi, Elamul Alwara, 1417 AH, juzu’i na 1, shafi na 164.
  31. Baihaƙi, Dala'ilul Al-Nubuwah, 1405 AH, juzu'i na 3, shafi na 16.
  32. Baihaƙi, Dala'ilul Al-Nubuwah, 1405 AH, juzu'i na 3, shafi na 16
  33. Waƙidi, al-Magazi, 1409 AH, juzu'i na 1, shafi na 12.
  34. Waƙidi, Al-Magazi, j 1 shafi na 12.
  35. Ibn Khayat, Tarikh Khalifa, 1415H, shafi na 20.
  36. Waƙidi, Al-Magazi, j 1 shafi na 12.
  37. Waƙidi, Al-Magazi, j 1 shafi na 12.
  38. Balazri, Ansab al-Ashraf, 1959, juzu'i na 1, shafi na 290.
  39. Balazri, Ansab al-Ashraf, 1959, juzu'i na 1, shafi na 290.
  40. Ibn Hisham, Al-Sirah al-Nabawiyyah, Darul Marifa, juzu'i na 1, shafi na 626.
  41. Sobhani, Jafar, Forough Abdit, 2005, shafi na 496.
  42. Salehi Shami, Subulul Al-Huda, 1414 AH, juzu'i na 4, shafi na 172.
  43. Salehi Shami, Subulul Al-Huda, 1414 AH, juzu'i na 4, shafi na 172.
  44. Yaƙut Hamawi, Mujam Al-Buldan, 1995, juzu'i na 4, shafi na 441.
  45. Ibn Hisham, Al-Sirah al-Nabawiyyah, Dar al-Marifa, juzu'i na 2, shafi na 43-44.
  46. Salehi Shami, Subulul Al-Huda, 1414 AH, juzu'i na 4, shafi na 172.
  47. Waƙidi, al-Magazi, 1409 AH, juzu'i na 1, shafi na 177.
  48. Waƙidi, al-Magazi, 1409 AH, juzu'i na 1, shafi na 176; Masoudi, al-Tanbihu wa Al-Ashraf, Dar al-Sawi, shafi na 206.
  49. Sobhani, Forough Abdit 2005, Juzu'i na 1, shafi na 516.
  50. Tarikh Al-ɗabari, 1387H, juzu’i na 2, shafi na 484.
  51. Waƙidi, Al-Magazi, 1409 AH, juzu'i na 1, shafi na 181.
  52. Salehi Shami, Subulul Al-Huda, 1414 AH, juzu'i na 4, shafi na 174.
  53. Baihaƙi, Dala'il Al-Nubuwah, 1405H, juzu'i na 3, shafi na 168
  54. ɗabari, Tarikh Al-ɗabari, 1387 Hijira, juzu'i na 3, shafi na 153.
  55. Ibn Hisham, Al-Sirah al-Nabiwiyah, Dar al-Marifah, juzu'i na 2, shafi na 46.
  56. Baihaƙi, Dala'il Al-Nubuwah, 1405H, juzu'i na 3, shafi na 168
  57. Ibn Saad, Thabaƙat Al-Kubra, 1414 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 27.
  58. Waƙidi, al-Magazi, 1409 AH, juzu'i na 1, shafi na 196.
  59. Ibn Saad, Thabaƙat Al-Kubra, 1414 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 27
  60. Ibn Hisham, Al-Sirah al-Nabawiyyah, Dar al-Marifa, juzu'i na 2, shafi na 46.
  61. Waƙidi, Al-Magazi, 1409 AH, Mujalladi na 1, shafi na 196-197.
  62. Ibn Hisham, Al-Sirah al-Nabawiyyah, Dar al-Marifa, juzu'i na 2, shafi na 65.
  63. Waƙidi, al-Magazi, 1409 AH, juzu'i na 1, shafi na 204.
  64. Ibn Hisham, Al-Sirah al-Nabawiyyah, Darul Marafa, juzu'i na 2, shafi na 60.
  65. Waƙidi, al-Magazi, 1409 AH, juzu'i na 1, shafi na 325.
  66. Ibn Kathir, Al-Bidaiya wa Al-Nihaya, 1407H, juzu'i na 4, shafi na 50.
  67. Balazari, Ansab Al-Ashraf, 1959, juzu'i na 1, shafi na 338.
  68. Ibn Saad, Thabaƙat Al-Kubra, 1414H, juzu'i na 2, shafi na 38.
  69. Waƙidi, al-Magazi, 1409 AH, juzu'i na 1, shafi na 334.
  70. Waƙidi, al-Magazi, 1409 AH, juzu'i na 1, shafi na 340.
  71. Waƙidi, al-Magazi, 1409 AH, juzu'i na 1, shafi na 364.
  72. Yaƙut Hamawi, Mujam Al-Buldan, 1995, juzu'i na 5, shafi.290.
  73. Waƙidi, al-Magazi, 1409 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 363.
  74. Waƙidi, al-Magazi, 1409 AH, juzu'i na 1, shafi na 374.
  75. Waƙidi, al-Magazi, 1409 AH, juzu'i na 1, shafi na 396.
  76. Ibn Hisham, Al-Sira Al-Nabawiyyah, Dar al-Marifa, juzu'i na 2, shafi na 203.
  77. Yaƙut Hamawi, Mujam Al-Buldan, 1995, juzu'i na 5, shafi na 276.
  78. Ibn Hisham, Al-Sira Al-Nabawiyyah, Dar al-Marifa, juzu'i na 2, shafi na 203.
  79. Balazari, Ansab Al-Ashraf, 1959, juzu'i na 1, shafi na 340
  80. Waƙidi, al-Magazi, 1409 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 387.
  81. Masoudi, Al-Tanbihu wa Al-Ashraf, Dar al-Sawi, shafi na 214.
  82. Yaƙut Hamawi, Majam Al-Buldan, 1995, juzu'i na 1, shafi.358.
  83. Yaƙoubi, Tarikh Al-Yaƙoubi, Dar Sadir, juzu'i na 1, shafi na 67.
  84. Yaƙoubi, Tarikh Al-Yaƙoubi, Dar Sadir, juzu'i na 1, shafi na 67.
  85. Waƙidi, al-Magazi, 1409 Hijira, juzu'i na 1, shafi na 403.
  86. Ibn Hisham, Al-Sirah al-Nabawiyyah, Dar al-Marifah, juzu'i na 2, shafi na 213.
  87. Ameli, Sahih Min Sirat Al-Nabi Al-Azam, Dar al-Hadith, juzu'i na 10, shafi na 105.
  88. Waƙidi, al-Magazi, 1409 AH, juzu'i na 1, shafi na 402.
  89. Waƙidi, al-Maghazi, 1409 AH, juzu'i na 1, shafi 402.
  90. Ibn Hisham, Al-Sirah al-Nabawiyyah, Dar al-Marifah, juzu'i na 2, shafi na 220.
  91. Waƙidi, al-Magazi, 1409 Hijira, juzu'i na 2, shafi:444.
  92. Ibn Hisham, Al-Sirah al-Nabiwiyah, Daral al-Marifah, juzu'i na 2, shafi na 214.
  93. Yaƙoubi, Tarikh Ali Yaƙoubi, Dar Sadir, juzu'i na 1, shafi na 50.
  94. Ibn Saad, Thabaƙat Al-Kubra, 1414H, juzu'i na 2, shafi na 57.
  95. Ibn Saad, Thabaƙat Al-Kubra, 1414 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 57.
  96. Ameli, Sahih Min Sirat Al-Nabi Al-Azam, Dar al-Hadith, juzu'i na 9, shafi na 130.
  97. Waƙidi, al-Magazi, 1409 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 496.
  98. Waƙidi, al-Magazi, 1409 AH, juzu'i na 2, shafi na 501.
  99. Ibn Hisham, Al-Sirah al-Nabawiyyah, Dar al-Marifa, juzu'i na 2, shafi na 280.
  100. Ibn Hisham, Al-Sirah al-Nabawiyyah, Darul Marafa, juzu'i na 2, shafi na 279.
  101. Ibn Hisham, Al-Sirah al-Nabawiyyah, Dar al-Marifa, juzu'i na 2, shafi na 280.
  102. Baihaƙi, Dala'ilul Al-Nubuwa, 1405 Hijira, juzu'i na 3, shafi na 364
  103. Waƙidi, Al-Magazi, 1409 Hijira, Juzu'i na 2, shafi na 536-537.
  104. Jafarian, Sireh Rasool Khoda (SAW), 2003, shafi na 573.
  105. Baihaƙi, Dala'lul Al-Nubuwa, 1405 Hijira, juzu'i na 4, shafi na 180.
  106. Balazri, Ansab al-Ashraf, 1959, juzu'i na 1, shafi na 349.
  107. waƙidi, Almagazi, 1409 h shamnsi, j 2 shafi na 537
  108. Baihaƙi, Dala'ilul Al-Nubuwa, 1405 Hijira, juzu'i na 4, shafi na 188.
  109. Waƙidi, Al-Magazi, 1409 Hijira, Mujalladi na 1, shafi na 405.
  110. Waƙidi, al-Magazi, 1409 AH, juzu'i na 1, shafi na 404.
  111. Yaƙut Hamawi, Mujam Al-Buldan, 1995, juzu'i na 5, shafi na 118.
  112. Ibn Hisham, Al-Sirah Al-Nabawiyya, Dar Al-Marifah, j 2 shafi na 289.
  113. Balazri, Ansab al-Ashraf, 1959, juzu'i na 1, shafi na 341.
  114. Waƙidi, al-Magazi, 1409 AH, juzu'i na 1, shafi na 407.
  115. Waƙidi, al-Magazi, 1409 AH, juzu'i na 2, shafi na 574.
  116. Ibn Hisham, Al-Sira Al-Nabawiyyah, Dar al-Marifa, juzu'i na 2, shafi na 310.
  117. Ibn Khaldun, Tarikh Ibn Khaldun, 1408H, juzu'i na 2, shafi na 447.
  118. Ibn Hisham Al-Sirah Al-Nabawiyyah, Dar Al-Marafa, Mujalladi na 2, shafi na 308
  119. Ibn Hisham, Al-Sirah al-Nabawiyyah, Darul Marifa, juzu'i na 2, shafi na 316.
  120. Waƙidi, al-Magazi, 1409 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 689.
  121. Waƙidi, al-Maghazi, 1409 Hijira, juzu'i na 2, shafi na 634.
  122. Waƙidi, al-Magazi, 1409 AH, juzu'i na 2, shafi na 655.
  123. Ibn Khaldun, Tarikh Ibn Khaldun, 1408H, juzu'i na 2, shafi na 458.
  124. Baihaƙi, Dala'ilul Al-Nubuwa, 1405 AH, juzu'i na 5, shafi na 5.
  125. Ibn Hisham, Al-Sira Al-Nabawiyyah, Darul Marifa, juzu'i na 2, shafi na 389.
  126. Ibn Khaldun, Tarikh Ibn Khaldun, 1408H, juzu'i na 2, shafi na 460.
  127. Yaƙoubi, Tarikh Al-Yaƙoubi, Dar Sadir, juzu'i na 2, shafi na 62.
  128. Waƙidi, al-Magazi, 1409 AH, juzu'i na 3, shafi na 885.
  129. Waƙidi, al-Magazi, 1409 AH, juzu'i na 3, shafi na 892.
  130. Waƙidi, al-Magazi, 1409 AH, juzu'i na 3, shafi na 912.
  131. Hosni, Tarikh Tahlili Sadre Islam, Payam Noor Publications, shafi na 94.
  132. Ibn Sa’ad, Thabaƙat Al-Kubra, 1414H, juzu’i na 2, shafi na 120.
  133. Ibn Sayyid al-Nas, Ayoun al-Athar, 1414H, juzu'i na 2, shafi na 250..
  134. ɗabarsi,Elamul Alwara, 1417 AH, juzu'i na 1, shafi na 233.
  135. Ibn Sa’ad, Thabaƙat Al-Kubra, 1414H, juzu’i na 2, shafi na 120.
  136. Moghdisi, Al-Bad'u wa Al-Tarikh, Maktabat Al-Saƙafatil Al-Diniyeh, juzu'i na 5, shafi.70.
  137. Balazri, Fatuh al-Baldan, 1988, shafi na 67.
  138. Baihaƙi, Dala'ilul Al-Nubuwa, 1405 Hijira, juzu'i na 5, shafi na 469.
  139. Ibn Hisham, Al-Sira Al-Nabawiyyah, Darul Marifa, juzu'i na 2, shafi na 516.
  140. Balazri, Fatuh Al-Buldan, 1988, shafi na 67.
  141. Sobhani, Forough Ebedit, 2005, shafi na 873.

Nassoshi

  • Aiti, Mohammad Ibrahim, Tarikh Payabare Islam, Tehran, Jami'ar Tehran, 1369H.
  • Ibn Khaldun, Abd al-Rahman bin Muhammad, Tarikh Ibn Khaldun, Beirut, Darul Fikr, 1408H.
  • Ibn Khayat, Halifa, Tarikh Khalifa, Beirut, Darul Katb al-Alamiya, 1415H.
  • Ibn Rasteh, Ahmad bin Omar, Al-Alag al-Nafisa, Beirut, Dar Sadr, 1892.
  • Ibn Saad, Muhammad bn Saad, Tabaƙat Al-Kubari, Taif, Mazhabar Sadik, 1414H.
  • Ibn Sayyid al-Nas, Muhammad, Ayoun al-Athar fi Fanon al-Maghazi wa al-Shamail wa al-Sir, Dar al-ƙalam, Beirut, bugun farko, 1414H.
  • Ibn Kathir, Ismail bin Omar, al-Bidaya wa Al-Nihaya, Beirut, Darul Fikr, 1407H.
  • Ibn Hisham, Abd Al-Malik, Al-Sirah Al-Nabawieh, Beirut, Dar al-Marafah, Bita.
  • Balazari, Ahmad bin Yahya, Ansab Al-Ashraf, Alkahira, Dar al-Maarif, 1959.
  • Balazari, Ahmed bin Yahya, Fatuh al-Baldan, Beirut, Dar and al-Hilal School, 1988.
  • Baihaƙi, Abu Bakr Ahmad bin Hossein, Dala'ilul Al-Nubuwa wa Marifah Ahwaal Sahib Al-Shari'a, Research: ƙalaji, Abd al-Mu'ati, Dar al-Katb al-Alamiya, Beirut, bugu na farko, 1405H.
  • Jafarian, Rasul, Seerah Rasool Khoda (S.A.W), ƙum, Dalil Ma Publications, 2003.
  • Hosni, Ali Akbar, Tarikh Tahlil Sadre Islam, Tehran, Payam Noor Publications, Beta.
  • Sobhani, Jafar, Farazhaye az Tarikh Payambare Islam, Tehran, Mashaar, 2006.
  • Sobhani, Jafar, Forough Abdit, ƙom, Bostan Kitab, 2005.
  • Salehi Shami, Muhammad bin Yusuf, Subulul Al-Huda wa Al-Rashad fi Sira Khair Al-Ibad, Beirut, Dar al-Katb al-Amliyah, 1414H.
  • ɗabarsi, Fazl bin Hasan, Elamul Al-Wara bil Alamul Al-Huda, Cibiyar Al-Baiti (A.S.), ƙum, bugun farko, 1417H.
  • ɗabari, Muhammad bin Jarir, Tarikh Al-ɗabari, Beirut, Darul-Tarath, 1387H.
  • Ameli, Sayyid Jafar Morteza, Sahih Min Sirah Al-Nabi Al-Azam, ƙom, Dar al-Hadith, 1426H.
  • قائدان، اصغر، «سازماندهی جنگی در غزوات عصر پیامبر»، در مجله مطالعات تاریخی جنگ، شماره ۳، بهار ۱۳۹۷ش.
  • ƙazi Abarƙawah, Ishaƙ bin Mohammad, Sirat Rasul khoda (a.s), Tehran, Khwarazmi, 1377.
  • Masoudi, Ali bin Hossein, al-Tanbihu wa Al-Ashraf, Alkahira, Dar al-Sawi, Bita, ƙum Offset Printing, al-Manaba Al-Tulfaƙa al-Islamiya Publishing House.
  • Masoudi, Ali bin Hossein, Moruj Al-Dahab da Al-Jawhar ma'adinai, ƙum, Darul Hijrah, 1409H.
  • Moghadsi, Motaher bin Taher, Albad'u wa Al-Tarikh, Port Saeed, Al-Taƙfa al-Diniyeh School, Bita.
  • Waƙidi, Muhammad bin Omar, Kitab al-Magazi, Al-Alami Foundation, Beirut, bugu na uku, 1409H.
  • Yaƙut Hamawi, Shahabuddin Abu Abdallah, Ma'jam Al-Baldan, Dar Sadir, Beirut, bugu na biyu, 1995.
  • Yaƙoubi, Ahmed bin Abi Yaƙoob, Tarikh AliYaƙoubi, Dar Sadir, Beirut, B.T.A.