Jump to content

Daƙiƙa:Ummu Farwa Mahaifiyar Imam Sadiƙ (A.S)

Daga wikishia

Kada a rikita ta da Ummu Farwa Ƴar Imam Sadiƙ (A.S).

Ummu Farwa Mahaifiyar Imam Sadiƙ (A.S)
Cikakken SunaFaɗima ko Ƙariba Ƴar Ƙasim Bin Muhammad Bin Abubakar
AlkunyaUmmu Farwa• Ummu Ƙasim
Fitattun dangiImam Baƙir (A.S) (Mata)• Imam Sadiƙ (A.S) (Ɗa)
Waɗanda suka ruwaito daga gare shiAn rawaito daga Imam Sadiƙ (A.S)


Ummu Farwa, matar Imam Baƙir (A.S) kuma mahaifiyar Imam Sadiƙ (A.S) ce. Ita ƴar Ƙasim Bin Muhammad bin Abubakar ne, daga cikin fitattun malaman fiƙihu a Hijaz, kuma mahaifiyarta Asma'u Ƴar Abdur-Rahman Bin Abubakar ce.[1] Saboda haka, nasabarta daga ɓangarori biyu yana komawa ga Abubakar. Wannan alaƙa ce ta sa aka jingina wa Imam Sadiƙ (A.S) maganar: Waladani Abubakar marrataini, wato: Abubakar ya haife ni sau biyu.[2]

Ummu Farwa ta kasance daga cikin masu riwayar hadisi; ta riwaito daga Imam Sajjad (A.S)[3] da kuma Imam Sadiƙ (A.S).[4] Abdullahi Mamaƙani, masanin rijal na Shi'a, ya ɗauke ta a matsayin amintacciya (Siƙa).[5] Haka nan, Imam Sadiƙ (A.S) ya riwaito wani hadisi daga gare ta, wanda a cikinsa aka ce Imam Baƙir (A.S) yana yin addu'ar neman gafarar zunuban Shi'arsa sau dubu a kowane dare da yini; domin yana ganin cewa Ahlul-Baiti (A.S) suna yin haƙuri ne tare da sanin lada, amma Shi'arsu suna yin haƙuri ba tare da wannan cikakkiyar masaniya ba.[6] Mas'udi marubucin tarihi na ƙarni na huɗu hijira, ya bayyana ta a matsayin ɗaya daga cikin mata mafi tsoron Allah a zamaninta.[7]

An binne Ummu Farwa a makabartar Baƙi'a',[8] kuma tana da matsayi mai girma a wajen Shi'a; har ma ana kiran Imam Sadiƙ (A.S) da Ibn al-Mukarrama wato: ɗan baiwar Allah mai karamci.[9]

An ce sunan mahaifiyar Imam Sadiƙ (A.S) Fatima ko Ƙariba ne, yayin da kunyarta ita ce Umm Farwa ko Ummu Ƙasim.[10] Ummu Farwa tana da baiwa mai suna Sa'ida, wadda ta shahara da falala da ibada.[11]

Bayanin kula

  1. Kulaini, Al-Kafi, juzu’i na 1, shafi na 393.
  2. Irbili, Kashf al-Ghumma, juzu’i na 2, shafi na 160.
  3. Mas'udi, Ithbat al-Wasiyya, Maktabat Radawiyya, shafi na 152.
  4. Barqi, Rijal, shafi na 62.
  5. Mamqani, Tanqih al-Maqal, juzu’i na 3, shafi na 73.
  6. Kulaini, Al-Kafi, juzu’i na 1, shafi na 72; Mas'udi, Ithbat al-Wasiyya, Maktabat Radawiyya, shafi na 153.
  7. Mas'udi, Ithbat al-Wasiyya, Maktabat Radawiyya, shafi na 152.
  8. Kulaini, Al-Kafi, juzu’i na 1, shafi na 472.
  9. Rijal al-Kashshi, shafi na 212; Qummi, Anwar al-Bahiyya, shafi na 229.
  10. Kulaini, Al-Kafi, juzu’i na 1, shafi na 472.
  11. Qummi, Anwar al-Bahiyya, shafi na 230,

Nassoshi

  • Barqi, Ahmad bin Muhammad, Rijal al-Barqi, rubutun hannu, lamba 18/6955, Dakin Karatu na Tsakiya na Jami'ar Tehran, sashe na 49; da Wallafe-wallafen Jami'ar Tehran, lamba 857, tare da Rijal Ibn Dawud, 1342Sh.
  • Irbili, Ali bin Isa, Kashf al-Gumma, Tabriz, Ofishin Bani Hashimi, 1381H.
  • Kashshi, Muhammad bin Umar, Rijal al-Kashshi (Ikhtiyar Ma'rifat al-Rijal), Mashhad, Jami'ar Mashhad, 1348Sh.
  • Kulaini, Muhammad bin Ya'qub, Usulul Kafi, mai gyarawa: Ali Akbar al-Ghaffari; Shaik Najm al-Din Amili ya duba kuma ya kwatanta, Tehran, Dakin Karatu na Musulunci, 1388H.
  • Mamqani, Abdullah bin Muhammad, Tanqih al-Maqal fi 'Ilm al-Rijal, Najaf, Madaɗɗa'ar Murtadawiyya, 1352H.
  • Mas'udi, Ali bin Husain, Ithbat al-Wasiyya lil-Imam Ali bin Abi Talib, Najaf, Maɗɗaba'ar Murtadawiyyaa, babu tarihi.
  • Ƙummi, Shaik Abbas, Anwar al-Bahiyya fi Tawarikh al-Hujaj al-Ilahiyya, mai fassara: Muhammad Muhammadi Ishtihardi, Qum, Mawallafar Nasir, bugu na uku, 1380Sh.