Daƙiƙa:Tawarruk

Tawarruk, (Larabci: التورك) yana daga cikin ladubban sallah a fiƙihun Shi'a, wanda yake nuni ga wani tsari da hanya ta musamman na zama wanda cikinsa mai sallah yake zama kan cinyar hagunsa, sannan ya ɗora ƙafar damansa a kan tafin ƙafar hagunsa[1] Malaman fiƙihu suna ɗaukar yin wanan aiki cikin tashahhud (Tahiyya)[2] da tsakanin sujjada biyu,[3] a matsayin mustahabbi. Na'am a ra'ayin Sahibul Jawahir wannan mustahabbi ya keɓantu ne da maza kawai ba ya haɗawa da mata.[4]
Bisa wata riwaya, wannan tsari na zama da ake yinsa a cikin sallah Imam Sadiƙ (A.S) ya aikata shi, yayin da Hammad Bin Isa ya tambaye shi game da ƙyamar (Makaruhanci) yin haka, ya danganta ƙyamar yin hakan ga Banu Isra'il.[5]
Abdullahi Jawad Amoli, daga malaman fiƙihu na Shi'a, tare da jingina da riwaya "Ya Allah ka kashe ƙarya ka raya gaskiya",[6] ya fassara Tawarruk matsayin wata alama ta galabar gaskiya kan ƙarya. A fahimtar malamin ƙafar dama alama ce ta gaskiya, ita kuma ƙafar hagu alama ce ta ƙarya.[7]
Wasu daga malaman Ahlus-Sunna a cikin zaman tahiya. Suna ɗaukar Iftirash (Zama kan cinyar ƙafar hagu a lanƙwashe a naɗe, sannan ita kuma ƙafar dama da kasance a miƙe tsaye) a matsayin Mustahabbi.[8] Wasu daban kuma suna ganin ya kamata cikin zaman tahiya na farko a yi Iftirash zaman tahiya na biyu kuma a yi Tawarruk.[9]
Tawarruk a cikin tsayuwa na cikin sallah yana nufin jingina ko ɗora nauyin jiki tsakanin ƙafar hagu da dama[10] haka kuma yana da ma'anar Jingina hannaye kan cinyoyi wanda a fiƙihu ake lissafa shi a matsayin abin ƙyama (Makaruhi).[11]
Bayanin kula
- ↑ Tabatabai Yazdi, Al-Urwat Al-Wuthqa, 1999 AD, J. 2, Shafi na 574.
- ↑ Muhaqqiq Al-Hilli, Al-Mu'tabar fi Sharh Al-Mukhtasar, 1986 AD, J. 2, Shafuffuka na 214 da 228; Khu'i, Sharh Urwat Al-Wuthqa, 1998 AD, Shafuffuka na 177 da 343.
- ↑ Allamah Al-Hilli, Tadhkirat Al-Fuqaha', 1993 AD, J. 3, Shafi na 197.
- ↑ Najafi, Jawahir Al-Kalam, 1983 AD, J. 10, Shafi na 182.
- ↑ Hurr Al-Amili, Wasa'il Al-Shi'a, Mu'assasat Aal Al-Bayt (A.S.) Li Ihya' At-Turath, J. 12, Shafi na 107.
- ↑ Sheikh Saduq, Man La Yahduruhu Al-Faqih, 1992 AD, J. 1, Shafi na 320.
- ↑ Javadi Amoli, Asrar-e Namaz (Sirrin Salla), 2010 AD, Shafi na 143.
- ↑ Nawawi, Al-Majmu' Sharh Al-Muhadhdhab, Dar Al-Fikr, J. 3, Shafi na 450; Muhaqqiq Al-Hilli, Al-Mu'tabar fi Sharh Al-Mukhtasar, 1986 AD, J. 2, Shafi na 228.
- ↑ Muhaqqiq Al-Hilli, Al-Mu'tabar fi Sharh Al-Mukhtasar, 1986 AD, J. 2, Shafi na 228.
- ↑ Najafi, Jawahir Al-Kalam, 1983 AD, J. 11, Shafi na 91; Shahid Al-Awwal, Al-Alfiyya wa An-Nafliyya, 1987 AD, Shafi na 114; Tabatabai Yazdi, Al-Urwat Al-Wuthqa, 1999 AD, J. 3, Shafi na 38.
- ↑ Allamah Al-Hilli, Tadhkirat Al-Fuqaha', 1993 AD, J. 3, Shafuffuka na 298 da 299.
Nassoshi
- Allamah Al-Hilli, Hasan bin Yusuf, Tadhkirat Al-Fuqaha', Qom, Mu'assasat Aal Al-Bayt (A.S.), 1414 AH, 1993 AD.
- Hurr Al-Amili, Muhammad bin Hasan, Wasa'il Al-Shi'a, Qom, Mu'assasat Aal Al-Bayt (A.S.) Li Ihya' At-Turath, babu kwanan wata.
- Javadi Amoli, Abdullah, Asrar-e Namaz (Sirrin Salla), Mai bincike: Husayn Shafi'i, Qom, Isra', Bugu na sha shida, 1389 SH, 2010 AD.
- Khu'i, Sayyid Abulqasim, Sharh Urwat Al-Wuthqa, Mai bincike: Muhammad Reza Musawi Khalkhali, Qom, Nashr Tawhid, 1418 AH, 1998 AD.
- Muhaqqiq Al-Hilli, Ja'far bin Hasan, Al-Mu'tabar fi Sharh Al-Mukhtasar, Qom, Mu'assasat Sayyid Al-Shuhada' (A.S.), Bugu na farko, 1407 AH, 1986 AD.
- Najafi, Muhammad Hasan, Jawahir Al-Kalam, Beirut, Dar Ihya' Al-Turath Al-Arabi, Bugu na bakwai, 1362 SH, 1983 AD.
- Nawawi, Yahya bin Sharaf, Al-Majmu' Sharh Al-Muhadhdhab, Beirut, Dar Al-Fikr, babu kwanan wata
- Shahid Al-Awwal, Muhammad bin Makki, Al-Alfiyya wa An-Nafliyya, Qom, Maktab Al-I'lam Al-Islami, 1408 AH 1987 AD.
- Sheikh Saduq, Muhammad bin Ali, Man La Yahduruhu Al-Faqih, Qom, Daftar-e Intisharat-e Islami, 1413 AH, 1992 AD.
- Tabatabai Yazdi, Sayyid Muhammad Kazim, Al-Urwat Al-Wuthqa, Masu bincike: Mu'assasat Al-Nashr Al-Islami, Jami'at Al-Mudarrisin, Bugu na farko, 1420 AH, 1999 AD.