Daƙiƙa:Sayyid Jawad Husaini Khamna'i
| Ɗaya daga cikin Mujtahidan Shi'a | |
| Nasaba | Sharifai jikokin Husaini |
|---|---|
| Tarihin haihuwa | 16 Disamba 1895 miladiyya. |
| Mahaifa | Najaf |
| Tarihin rasuwa | Asabar, 5 Yuli 1986M shekarar 1986M/27 Shawwal shekarar 1406ƙ |
| Garin da ya rasu | Mashhad |
| Mahallin kabari | Haramin Imam Rida (A.S) |
| Fitattun dangi | Sayyid Ali Husaini Khamna'i (Ɗansa)•Sayyid Mujtaba Khamna'i(Jikansa)•Sayyid Hashim Mirdamad Najaf Abadi(Mahaifin matarsa)•Muhammad Wa'iz Zade Khurasani (Gida ɗaya suka yi aure) |
| Wurin karatu | Tabriz•Mashhad•Najaf |
| Izinin Ijtihadi daga | Muhammad Husaini Na'ini•Sayyid Abul Hassan Isfahani•Agha Diya'u Iraƙi |
| Sauran abubuwa | Koyarwa•limancin masallacin iyalin Siddiƙi na kasuwar Mashhad•Masallacin Juma'a na Goharshad |
Sayyid Jawad Husaini Khama'i (16 Disamba 1895M– 5 Yuli 1986M) yana daga cikin malamai da mujtahidan Shi'a, kuma shi ne mahaifin Ayatullahii Khamna'i, Jagora na biyu na Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Ya yi karatu a Tabriz, Mashhad, da Najaf. Bayan ya samu matsayin ijtihadi a Najaf, sai ya ƙaura zuwa Mashhad, inda ya zauna a can har zuwa ƙarshen rayuwarsa.
Haihuwa Da Asali
Sayyid Jawad Khamna'i an haife shi a Najaf, kuma tun yana ƙarami ya zo Tabriz tare da iyalinsa.
Asalinsa yana komawa ga sharifai jikokin Husaini, kuma zuriyarsa ta haɗu da Sulɗan Sayyid Muhammad, wanda ta hanyar tsakani huɗu yake daga cikin ƴaƴan Imam Sajjad (A.S).[1]
Saboda zalunci da tsanantawar da gwamnatin Abbasiyawa ta yi, Sayyid Muhammad ya yi hijira zuwa yankunan tsakiyar Iran kamar Tafrish, Ashtiyan, da Farahan. Mutanen waɗannan yankuna sun tarbe shi da girmamawa, amma daga baya jami'an Abbasiyawa sun kama shi a Tafrish suka shahadantar da shi. Kabarinsa yana garin Miƙan, a Arak.
Sayyid Muhammad, ɗan Sayyid Muhammad Taƙiyyu, ɗan Sayyid Mirza Ali, ɗan Sayyid Mirza Akbar, ɗan Sayyid Fakhrud-din , yana daga cikin zuriyar Sultan Sayyid Muhammad. Ya yi hijira daga Tafrish zuwa Azerbaijan, inda ya zauna a garin Khameneh, wanda yake kusan kilomita 80 arewa maso yammacin Tabriz.
Bayan sa, Sayyid Husain, ɗan Sayyid Muhammad, ya ci gaba da zama a Khamene yana wa'azin tare da shiryar da mutane. Daga baya ya tafi Najaf, inda ya shagaltu da karatu da muhawarar ilimi (darasi da bahasi).
Shi ne kakan Ayatullahii Khamna'i, Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Mata Da Ƴaƴa
A kusan shekarunsa na arba'in, matar Sayyid Jawad Khamna'i ta farko, wadda ta haifa masa ƴaƴa mata uku, bayan nan ta rasu.
Bayan rasuwar matar tasa ta farko, ya auri Khadije Mirdamadi, ƴar Ayatullahii Sayyid Hashim Mirdamadi Najaf Abadi.
Daga Khadija Mirdamadi, Ayatullahi Sayyid Jawad Khamna'i ya samu ƴaƴa biyar:
- Sayyid Muhammad
- Sayyid Ali
- Badr al‑Sadat
- Sayyid Hadi
- Sayyid Muhammad Hassan
Khadija Mirdamadi ta rasu a ranar 6 Agusta 1989M (15 Mordad 1368Sh) sakamakon bugun zuciya, kuma an binne ta a harabar Haramin Imam Rida (A.S) a Mashhad, a gefen kabarin mijinta.
Karatu
Sayyid Jawad Khamna'i ya yi karatunsa na farko (Matakin sharar fage) a makarantun Tabriz. Daga baya ya zauna a Mashhad na kusan watanni tara, sannan ya koma Tabriz.

An ce a wancan lokacin hanyar Tehran–Mashhad ba ta da tsaro. Saboda haka Sayyid Jawad ya tafi Badkube, daga nan ya bi Tekun Caspian zuwa Ishƙe'abad, sannan daga can ya isa Khurasan.[2]
A Mashhad ya ci gaba da karatunsa, sannan a shekarar 1345H, ya tafi Najaf domin ƙarin karatu.
Malamansa
Sayyid Jawad Khamna'i ya yi karatun fiƙihu da usulul fiƙhi a Mashhad a wajen manyan malamai kamar:
- Agha Husaini Ƙummi
- Mirza Muhammad Agha Zade Khurasani (Kafa'ī)
- Mirza Mahadi Isfahani
- Fadil Khurasani
A fannin falsafa kuma ya yi karatu a wajen:
- Agha Buzurge Hakim Shahidi
- Asadullah Yazdi.[3]
Daga baya a Najaf, ya yi karatu a wajen manyan malamai irin su:
Kuma daga gare su ne ya samu izinin ijtihadi.[4]
Zama A Mashhad

Bayan ya kammala karatunsa a Najaf kuma ya samu matsayin Ijtihadi, ya koma Iran sannan ya tafi Mashhad. A can ya fara koyarwa, kuma ya zama limamin masallacin Siddiƙi na kasuwar Mashhad (wanda ake kira Masallacin mutanen Azerbaijan).[5]Haka kuma yana daga cikin limaman jam'i na Masallacin Jami'i na Goharshad.[6]
Ya kasance mai matuƙar son karatu da bincike. mhauwarar ilimi da yake yi a kullum da takwarorins, ciki har da Mirza Husain Aba'i, Sayyid Ali Akbar Khuyi (Mahaifin Ayatullahi Khuyi), Mirza Habib Maliki da saurans, ta ci gaba na tsawon shekaru masu yawa.
Halayensa Na Ƙashin Kai
Ya kasance mutum mai tsoron Allah, kuma ba ya damuwa da abubuwan duniya, yana rayuwa mai sauƙi da zuhudu.[7] Bayan nasarar juyin juya halin Musulunci a Iran, duk da cewa ƴaƴansa sun kai manyan muƙaman siyasa da gudanarwa, ya ci gaba da rayuwarsa ta sauƙi da zuhudu kamar da.
Saboda kyawawan halaye da kamalolin ɗan Adam da yake da su, mutane suna yarda da shi kuma suna girmama shi sosai.
Rasuwa
Sayyid Jawad Khamna'i ya rasu a ranar 14 Tir 1365Sh, wanda ya yi daidai da 27 Shawwal 1406H. 1986M.[8] Ayatullahi Abul Hassan Shirazi, limamin Juma'ar Mashhad, ne ya yi masa sallar jana'iza. Daga nan aka binne shi a farrfajiyar da ke bayan kabarin Imam Rida (A.S), a kusa da Darul al‑Faizi.[9]
Imam Khomaini ma ya aike da saƙon ta'aziyya ga Ayatullahii Khamna'i kan rasuwar mahaifinsa. A cikin saƙon, ya bayyana Ayatullahii Sayyid Jawad Khamna'i a matsayin malami mai tsoron Allah kuma mai sadaukarwa.[10]
Ƙaddamar Da Littafin "Zindagi Injast"
A daidai lokacin Ranar Alƙalami (Ruze Ƙalam), a cikin wani biki na musamman, an ƙaddamar da littafin Zindagi Injast (Rayuwa Tana Nan) wanda Mahadi Ƙazli ya rubuta.
Littafin yana magana ne game da rayuwar Ayatullahi Sayyid Jawad Khamna'i. An gudanar da wannan bikin ƙaddamarwar a Masallacin Juma'a na Tabriz.[11]
Bayanin kula
- ↑ «نگاهی گذرا به زندگینامهی حضرت آیتاللهالعظمی شهید سیدعلی حسینی خامنهای»، Ofishin Hifze Wa Nashre Asare Hazrat Ayatullahi Al-Uzma Sayyid Ali Khamna'i.
- ↑ Behbudi, Sharhe Ismi,
- ↑ Sharif, Ganjineh‑ye Daneshmandan, Tehran: Islamiyeh, juzu'i 7, shafi127–129; Zangeneh, Mashahire Madfun dar Harame Ridawi, juzu'i 1, shafi 132.
- ↑ Sharif, Ganjineh‑ye Daneshmandan, Tehran: Islamiyeh, juzu'i 7, shafi 127.
- ↑ Behbudi, Sharhe Ismi, shafi 15.
- ↑ Zangeneh, Mashahire Madfun dar Harame Ridawi, juzu'i 1, shafi 77.
- ↑ Golshane Abarar, juzu'i 2, shafi 971.
- ↑ Ha'eri, Ruzshomare Shamsi, shafi 254.
- ↑ Zangeneh, Mashahire Madfun dar Harame Ridawi, juzu'i 1, shafi 77.
- ↑ Sahifeye Imam, juzu'i 20, shafi 71.
- ↑ رونمایی از کتاب زندگی اینجاست
Nassoshi
- «نگاهی گذرا به زندگینامهی حضرت آیتاللهالعظمی شهید سیدعلی حسینی خامنهای»، Ofishin Hifze Wa Nashre Asare Hazrat Ayatullahi Al-Uzma Sayyid Ali Khamna'i. Ranar ziyara: 19 Satumba 2026M.
- Ruzshomare Tarikh, Markaze Pazhuhesh‑haye Islami‑ye Seda Wa Sima.
- Ha'eri, Ali, Ruzshomare Shamsi, mai shiryawa: Cibiyar Markaze Pazhuhesh‑haye Islami‑ye Seda Wa Sima, Qom, Daftare Aƙl, 1386Sh.
- Imam Khomaini, Sayyid Ruhullah, Sahifeye Imam, Tehran, Cibiyar Tanzim Wa Nashre Asare Imam Khomaini, 1378Sh.
- Behbudi, Hedayatullah, Sharhe Ismi, Tehran: Cibiyar Pazhuhesh‑haye Siyasasi, 1391Sh.
- Golshane Abrar, Tattara daga masu bincike na Cibiyar Ilimin Addini ta Qom, Pajooheshkadeh‑ye Baƙer al‑Ulum (A.S)
- Zangeneh, Qasimabadi, Mashahire Madfun dar Harame Ridawi, Kitabekhune Digital, 1314Sh.
- Sharif Razi, Muhammad, Ganjineh‑ye Daneshmandan, Tehran: Kitabekhune Digital Noor, babu kwanan wata.
- Mutanen Da Aka Binne A Haramin Imam Rida
- Malaman Shi'a A Ƙarni Na 15 (Hijira)
- Limaman Jama'a Na Masallacin Goharshad
- Almajiran Sayyid Abul Hassan Isfahani
- Almajiran Agha Diya'u Iraƙi
- Almajiran Mirzayi Na'ini
- Almajiran Sayyid Husaini Ɗabaɗaba'i Ƙummi
- Mutanen Da Suka Yi Karatu A Hauzar Mashad (Daga Zamanin Kundin Mulki Zuwa Gaba
- Mutanen Da Suka Yi Karatu A Hauzar Najaf Bayan 1200 (Hijira)
- Almajiran Mirza Mahadi Isfahani