Jump to content

Daƙiƙa:Mu'ujamu Rijalil Hadis (Littafi)

Daga wikishia
Mu'ujamu Rijalil Hadis
MarubuciSayyid Abul Ƙasim Khuyi
Maudu'iIlmul Rijal
HarsheLarabci
Adadin Jildi24
Wurin da aka buga shiCibiyar wallafa al'adun Musulunci a duniya.
Tarihin bugawa1413H
Kwafin PDFhttp://lib.eshia.ir/14036

Mu'jamu Rijalil Hadis wa Tafsil Ɗabaƙatir Ruwat wani littafi ne da Sayyid Abul Ƙasim Khuyi ya wallafa kan ilimin Rijal (binciken rayuwar masu ruwayar hadisi). Wannan littafi ya gabatar da masu ruwayar hadisai na Shi'a sama da dubu 15, inda aka tsara su bisa jerin haruffan ƙamus Alphabet, tare da bayar da ra'ayi kan amincin (tabbatuwar) kowane mai ruwayar hadisi ko akasin haka.

A cikin gabatarwar littafin, an tattauna batutuwa guda shida game da ilimin Rijal dalla-dalla, kamar: mahimmancin ilimin Rijal, ma'aunin amincewa da mai ruwaya, da kuma ingancin hadisai da ke cikin littattafai huɗu na Shi'a (Al-Kutub al-Arba'a).

Littafin ya kunshi sassa huɗu: Asma' (Sunaye). Kuna (Kunya). Alƙab (Laƙabi) Nisa'u (Mata)

An wallafa "Mu'jamu Rijalil Hadis" cikin juzu'i guda 24. Daga cikin manyan fa'idojin wannan littafi da masana suka ambata har da: tattara sunayen dukkan masu ruwayar da suka zo a sauran littattafan ilimin Rijal a wuri guda, da kuma mai da hankali kan matsalar «Tahrif» (canza sunaye ko kuskuren rubutu) a sunayen masu ruwayar da kuma gyara su.

Marubuci

Sayyid Abul Ƙasim Musawi Khuyi (1278-1371Sh.) ya kasance ɗaya daga cikin manyan maraji'an taƙlidi na Shi'a kuma ɗalibin Mirza Na'ini da Muhaƙƙiƙ Isfahani.[1] Bayan rasuwar Sayyid Muhsin Ɗabaɗaba'i Hakim, ya zama babban marja'i (Shugaban addini) mafi daraja a ƙasar Iraƙi.[2]

Sayyid Abul Ƙasim Khuyi ya rubuta littattafai a fannin fiƙihu (shari'a), usulul fiƙhi, ilimin Rijal, ilimin tauhidi (kalam), da ilimin Alƙur'ani. An tattara dukkan ayyukansa a cikin wani kundi mai juzu'ai hamsin da ake kira "Mausu'atul Imam Khuyi".[3]

Matsayin Littafin

Ana ɗaukar Mu'jamu Rijalil Hadis a matsayin littafi mafi faɗi kuma mafi tsari a fannin ilimin Rijal na Shi'a, inda ake cewa littafin yana da wasu muhimman abubuwa waɗanda ba a same su a sauran littattafan Rijal ba. Daga cikin waɗannan har da: bincikar masu ruwayar hadisi daga fannoni daban-daban, da kuma yin amfani da hanyar bincike mai zurfi kan ra'ayoyin magabata musamman littattafan farko na Rijal da kuma sake nazarin waɗannan ra'ayoyin.[4]

Haka nan, ana lissafa wannan littafi a matsayin ɗaya daga cikin manyan littattafan Rijal, saboda yadda ya binciki masu ruwayar ta kowane fanni kuma ya bayar da bayanai masu fa'ida waɗanda ba a same su a wani wuri ba, ko kuma ba kasafai ake ganin su ba.[5]

Dalili Da Hanyar Wallafawa

Bisa ga abin da marubucin littafin ya faɗa a cikin gabatarwarsa, ilimin Rijal ya daɗe yana samun kulawa daga masana da fuƙaha (Masu ilimin shari'a); amma a wannan zamani, ana nuna rashin kulawa da shi, alhali kuwa ijtihadi da ciro hukunce-hukuncen shari'a ya dogara ne a kan sa. Saboda haka, ya yanke shawarar rubuta wani littafi mai faɗi kuma cikakke a wannan fanni, wanda zai ƙunshi dukkan darajoji da sifofin wannan ilimi.[6]

Sayyid Khuyi ya samu taimakon mataimaka wajen wallafa Mu'jamu Rijalil Hadis, waɗanda suka taimaka masa wajen tsarawa, kwafa, gyarawa, kwatantawa da kuma duba nassoshin littafin.[7] Wannan ƙungiya ta ƙunshi: Muhammad Muzaffari, Haidar Ali Hashimiyan, Yahaya Araki, Sayyid Murtada Nakhjawani, Sayyid Abdul-Aziz Ɗabaɗaba'i Yazdi, Sayyid Jawad Golfaigani, Muhammad Kazim Khunsari, Fakhrud-Din Zanjani, Muhammad Tabrizi, Gholamreza Rahmani, da kuma Sayyid Murtada Hakami.[8]

Abubuwan Da Ke Cikin Littafin Da Tsarin Sa

Littafin ya ƙunshi wata gabatarwa mai faɗi da kuma sassa huɗu. A cikin gabatarwar, an tattauna batutuwa guda shida na farko-farko game da ilimin Rijal. A cikin sassa huɗu na asali kuma, an ambaci sunayen masu ruwayar hadisi tare da bincikar ingancin kowane ɗayansu:

Gabatarwa

Batutuwa guda shida da aka tattauna a cikin gabatarwar su ne kamar haka:

  1. Mahimmancin ilimin Rijal, tare da mayar da martani ga waɗanda suka musanta buƙatar ilimin Rijal, da kuma tattauna ra'ayin waɗanda suke ganin cewa duk hadisan da ke cikin "Littattafai Huɗu" (Al-Kutub Al-Arba'a) ingantattu ne (ba tare da wani shakka ba).[9]
  2. Ma'aunin gane amincin (tabbatuwar) mai ruwaya ko kuma kyawun halinsa.[10]
  3. Ingancin "Tausiƙud Dimni" (tabbatar da amincin mai ruwaya ta fuskar fage/a kaikaice).[11]
  4. Rashin amincewa da Tausiƙatul Amma (Tabbatar da amincin masu ruwaya baki ɗaya), kamar kasancewa cikin "Ashabul Ijma" (Malaman da aka amince da ruwayarsu), kasancewa cikin Mashayikhul Ijaza(Malaman da suka ba da izinin watsa hadisi), riƙe mukamin wakilci daga Imam (A.S), ko kuma kasancewa tare da Imam (A.S).[12]
  5. Bincikar hadisan da ke cikin Littattafai Huɗu da kuma ƙaryata hujjojin da ake amfani da su wajen tabbatar da ingancin dukkan ruwayoyin da ke cikinsu.[13]
  6. Gabatar da muhimman littattafan Rijal na Shi'a, tare da nuna shakku kan ingancin littafin Rijal na Ibn Gada'iri.[14]

Sassan Littafin

Littafin Mu'jamu Rijalil Hadis ya ƙunshi sassa guda huɗu: Asma' (Sunaye), Kuna (Alkunya), Alƙab (Laƙabi), da Nisa'u (Mata). A cikin waɗannan sassan, an ambata kuma an binciki sunaye guda 15,676 gaba ɗaya; kodayake wasu daga cikinsu sun haɗu, wato suna nuni ne ga mutum ɗaya. A kowane ɗaya daga cikin sassa ukun farko, an binciki waɗanda sunayensu, kunyoyinsu, ko laƙabinsu ya zo a cikin littattafan Rijal ko a cikin silsilar ruwayoyin hadisi. Sashe na huɗu kuma ya keɓanta ne ga matan da aka ambata a cikin littattafan Rijal ko a cikin silsilar ruwayar hadisi.[15]

Siffofin Littafin

An ambaci wasu siffofi da darajoji na musamman ga littafin Mu'jamu Rijalil Hadis waɗanda suka bambanta shi da sauran littattafan Rijal, waɗanda suka haɗa da:

  • An ambaci sunayen dukkan masu ruwayar da suka zo a cikin silsilar ruwayoyin Littattafai Huɗu (Al-Kutub al-Arba'a); har ma da waɗanda sunayensu bai zo a sauran littattafan Rijal ba.
  • An tattara sunayen dukkan masu ruwaya da suka zo a cikin sanannun littattafan Rijal da kuma waɗanda ba a san su ba, a wuri guda a cikin wannan aikin.
  • A cikin wannan littafi, abu ne mai sauƙi a gane «Ɗabaƙatur Ruwat» (Matsayin masu ruwaya a ƙarni ko zamani), domin lokacin da ake gabatar da kowane mai ruwaya, an ambaci sunayen dukkan waɗanda suka ruwaito daga gare shi, ko kuma waɗanda shi ya ruwaito daga gare su.
  • An ba da cikakken tarihin rayuwar mai ruwayar.
  • Baya ga ambaton ra'ayoyin sauran masana Rijal, marubucin ya bayyana ra'ayinsa kan mai ruwayar bisa wasu ma'auni na kansa; wato, ya yi "Jarhi wa Ta'adil" (bincikar inganci ko rashin ingancin) mai ruwayar.
  • Ɗaya daga cikin matsalolin da ke shafar silsilar ruwaya (isnad) shi ne «Tas'hif» (Kuskuren rubutu) da «Tahrif» (Canza sunaye) a cikin sunayen masu ruwaya. Misali, mayar da Hassan zuwa Husain ko akasin haka, Ahmad zuwa Muhammad ko akasin haka, ko «An» zuwa «Bin» ko akasin haka. Wannan littafi ya ba da muhimmanci sosai ga wannan batu, kuma an gyara sunaye.[16]

Bayanin kula

  1. Piri Sabzewari, «Ayatullahi al-Uzma Sayyid Abul Ƙasim Khuyi; Qur'an-shinase Buzorge Mo'aser,» shafi na 30; Ansari Ƙummi, «Nujume Ummat Hazrate Ayatullahi al-Uzma Haj Sayyid Abul Ƙasim Khuyi,» shafi na 57.
  2. Sharif Razi, Ganjineh-ye Daneshmandan, jildi na 2, shafuffuka na 3–5; Ra'iszadeh, «Khuyi, Abul Ƙasim,» shafi na 515.
  3. Ra'iszadeh, «Khuyi, Abul Ƙasim,» shafi na 522.
  4. Wanki da sauran su, «Rawashe Ayatullah Khuyi dar Ta'amul ba Usule Awwaliyeh-ye Rejali,» shafi na 120.
  5. Ali-Nejad, «Mu'arrifi-ye Yeki az Muhimmatarin asare Rejaliye Shieh,» shafi na 167.
  6. Duba: Khuyi, Mu'jamu Rijalil Hadis, jildi na 1, shafuffuka na 11–12.
  7. Mukhtari, «Nokteha,» shafuffuka na 222–223
  8. Mukhtari, «Nokteha,» shafi na 223; duba: Khuyi, Mu'jamu Rijalil Hadis, jildi na 1, shafi na L (ko Lam).
  9. Khuyi, Mu'jamu Rijalil Hadis, jildi na 1, shafi na 17.
  10. Khuyi, Mu'jamu Rijalil Hadis, jildi na 1, shafi na 37.
  11. Khuyi, Mu'jamu Rijalil Hadis, jildi na 1, shafi na 47.
  12. Khuyi, Mu'jamu Rijalil Hadis, jildi na 1, shafi na 53-73.
  13. Khuyi, Mu'jamu Rijalil Hadis, jildi na 1, shafi na 79.
  14. Duba: Khuyi, Mu'jamu Rijalil Hadis, jildi na 1, shafi na 93.
  15. Ali-Nejad, «Mu'arrifi-ye Yeki az Muhimmatarin asare Rejaliye Shieh,» shafi na 164.
  16. Ali-Nejad, «Mu'arrifi-ye Yeki az Muhimmatarin asare Rejaliye Shieh,» shafi na 167–177.

Nassoshi

  • Ali-Nejad, Abu Ɗalib, «Mu'arrifi-ye Yeki az Muhimmatarin asare Rejaliye Shieh,» (Gabatar da Ɗaya daga cikin Muhimman Ayyukan Ilimin Rijal na Shi’a), a cikin Sanin Shi'a, kaka 1386Sh/2007M, lamba 19.
  • Ansari Ƙummi, Nasirid-Din, «Nujume Ummat Hazrate Ayatullahi al-Uzma Haj Sayyid Abul Ƙasim Khuyi,» (Taurarin Al'umma: Hazrat Ayatullah al-Uzma Khuyi.) a cikin Majallar Nur-e 'Ilm, juzu'i na 4, lamba 11, kaka 1371Sh/1992–1993M.
  • Mukhtari, Rida, «Nokteha,» (Muhimman bayanai) a cikin Kitabe Shieh, bazara da rani 1389Sh/1389ShM, lamba 1.
  • Piri Sabzawari, Husain, «Ayatullahi al-Uzma Sayyid Abul Ƙasim Khuyi; Qur'an-shinase Buzorge Mo'aser,» (Ayatullah al-Uzma Sayyid Abul Ƙasim Khu’i; Babban Masanin Alƙur’ani na Zamani.), a cikin Mujallar wata uku-uku ta Bostane Qur’an, lamba 126, Oktoba–Nuwamba 2002M.
  • Ra'iszadeh, Muhammad, «Khuyi, Abul Ƙasim,» (Khuyi Abul Ƙasim) a cikin Danisnamah-ye Jahane Islam, Tehran: Cibiyar Bunyade Da'iratil Ma'arif Islami, 1375Sh/1996M.
  • Rabbani-khawah, Ahmad, Ashnayi Ba Daneshe Wa Manabi Rijale Shi'a.
  • Sharif Razi, Muhammad, Ganjineh-ye Daneshmandan, Tehran: Kitabe Furushi Islamiyye, 1352–1354Sh.
  • Wanaki, Fatima da Muhammad Kazim Rahman-Satayes da Fathiyya Fatahi-zadeh, «Rawashe Ayatullah Khuyi dar Ta'amul ba Usule Awwaliyeh-ye Rejali,» (Ra'ayin Ayatullahi Khuyi kan mu'amala da ƙa'idojin farko na ilimin rijal), a cikin Hanyoyi a Ilimomin Alƙur'ani da Hadisi, lamba 97, kaka da hunturu 1395Sh/2016.
  • Khuyi, Sayyid Abul Ƙasim, Mu'jamu Rijalil Hadis wa Tafsil Ɗabaƙatir Ruwat, Qum: Cibiyar Nashr al-Thaqafa al-Islamiyya fi al-'alam, 1413 AH.