Daƙiƙa:Hawan Annabi Isa Sama
Hawan Annabi Isa (A.S) (Larabci: عروجُ عيسى عليهِ السلام) na nufin tafiyar Annabi Isa (A.S) zuwa sama wanda aka yi ishara cikin Kur'ani. Mafi shaharar ra'ayi tsakanin Musulmi shi ne cewa ba kashe shi aka yi ba kuma ba gicciye shi ba, kai tsaye Allah ya ɗaukaka shi zuwa sama, duk da cewa wasu suna da ra'ayin cewa ta yiwu bayan tsira daga gicciye ya mutu ne mutuwa ta ɗabi'a da aka saba da ita. Bisa koyarwar kiristanci, an gicciye Annabi Isa sannan bayan sake raya shi ya tafi sama.
Game da yadda ya yi mi'iraji ya hau sama, wasu sun tafi kan cewa ya kasance ne tafiya ta ruhaniya wasu kuma suna da ra'ayin cewa ya kasance cikin tsari na ruhaniya da gangar jiki baki ɗaya. Ba'arin riwayoyi da suke magana game da dawowarsa a lokacin bayyanar Imam Mahadi da ganin Annabi (S.A.W) da ya yi a lokacin da ya je mi'iraji, suna daga cikin dalilai da suke tabbatar da kasancewar hawansa sama cikin tsari na hawa na gangar jiki. Dawowar Annabi Isa (A.S) a zamanin bayyanar Imam Mahadi (A.S) suna daga cikin abubuwan da ake ganin tabbas za su faru kuma a cikin madogaran Shi'a da Ahlus-Sunna an naƙalto riwayoyi masu yawan gaske game da haka.
Wasu ba'arin ɗariƙun kiristoci suna bikin ranar hawan Isa sama, kuma sun tsimayin dawowarsa matsayin wani alƙawari d aya ɗaukarwa almajiransa da mabiyansa.
Bambancin Mahangar Musulunci Da Kiristanci
Hawan Isa sama na nufin tafiya da ya yi zuwa sama da kasancewarsa a raye[1] An yi ishara game da wannan al'amari cikin aya ta 158 suratul nisa'i da aya ta 55 suratul alu Imran.[2] Bisa abin da ya zo a cikin wasu madogarai, wannan al'amari ya faru ne a shekara 585 kafin hijira[3] kuma a daren 21 Ramadan[4] a lokacin Isa yana da shekara 32[5] ko 33[6] da haihuwa. A cikin wata riwaya da aka naƙalto daga Imam Baƙir (A.S) an bayyana cewa daren shahadar Imam Ali (A.S) ya yi daidai da daren hawan Isa (A.S) sama.[7]
Daidai da koyarwar kiristanci, Annabi Isa (A.S) bayan gicciye shi,[8] ya mutu[9] aka binne shi,[10] a rana ta uku almajiransa suka gan shi amma babu gangar jikinsa.[11] Bayan sake raya Annabi Isa (A.S), sai almajiransa suka haɗu da shi[12] bayan nan sai ya tafi sama.[13] An labarta wannan al'amari dalla-dalla a cikin Linjiloli guda huɗu.[14] Kishiyar haka, Kur'ani ya yi bayani ƙarara[15] cewa ba a kashe Annabi Isa (A.S) ba kuma ba a gicciye shi ba;[16] Bari bisa abin da ya zo a riwayoyi[17] maimakonsa bisa kuskure an kashe wani mutum daban, kuma mutane suka yi zaton cewa an shahadantar da Isa (A.S).[18]
Halin Rayuwar Annabi Isa (A.S) Yayin Hawa Sama
Malaman Musulunci sun yi saɓani game da shin kafin hawa sama Isa ya mutu ne mutuwa ta ɗabi'a ko kuma kai tsaye yana raye ne ya tafi sama.[19] Kan asasin Kur'ani da mafi shaharar ra'ayi a wurin Musulmi[20] Isa ba a kashe shi ba, ba a kuma gicciye shi ba[21] Bari dai ya hau sama ne[22] Kuma zai dawo kafin tsayuwar ranar alƙiyama[23] Wasu sun tafi kan ra'ayin cewa mai yiwuwa Isa bayan tsira daga gicciye, ya mutu mutuwa ta ɗabi'a, bayan nan sai ya tafi zuwa sama.[24]
A ƙasar Amurka kiristoci suna shirya taron addu'a domin tunawa da ranar hawan Yesu (Isa) sama, kuma suna la'akari da wannan rana matsayin wata rana mai matuƙar muhimmancin a koyarwar kiristanci.[25]
Fahimtoci Da Aka Ciro Daga Kalmar Mutawaffika
A cikin aya ta 55 suratul alu imran an yi amfani da kalmar "Mutawaffika" wace aka fitar da mabambantan fahimtoci daga cikinta:
- Mutuwa ta ɗabi'a: Ma'ana Isa ya mutu ne tun kafin hawa sama, kuma kan asasin wannan fahimta, ya hau sama ne bayan mutuwa da ya yi.[26]
- Karɓar rai ko kuma karɓe rai: Wannan jumla kai tsaye bata ishara zuwa ga cikakkiyar mutuwa, ana ganin tana ishara ne zuwa ga ciratar Isa daga ƙasa zuwa sama.[27]
- Kamanta hawan zuwa sama: Kalmar an yi amfani da ita a matsayin misali na (kwatance) domin bayyana hawan sa zuwa sama, kuma hakan yana nuni da cewa yanzu baya rayuwa a ƙasa.[28]
Kasancewar Hawan Na Gangar Jiki Ko Dai Na Ruhaniya
Malaman tafsiri sun yi saɓani game da yadda hawan Isa (A.S) ya kasance;[29] Ba'ari kan asasin aya ta 158 suratul nisa'i, suna ganin hawan ya kasance na ruhaniya[30] Akasin wannan magana, wasu suna ganin cewa ya kasance na ruhaniya da gangar jiki.[31] Wasu masana sun tafi kan cewa hawan Isa (A.S) sama an bijiro da shi matsayin yabo gare shi, shi kuma yabo yana nuni ga kasancewar hawan na ruhaniya da gangar jiki; saboda hawa na ruhaniya bai keɓantu da Isa ba shi kaɗai.[32] Haka kuma, ba'arin riwayoyi da aka kawo da suke magana kan dawowar Isa a zamanin bayyanar Imam Mahadi (A.S)[33] da kuma ganin Annabi (S.AW) da ya yi a lokacin mi'iraji, sun kasance matsayin dalili da suke nuni kan kasancewar hawan nasa hawa ne da gangar jiki.[34] Bisa abin da ya zo cikin wasu riwayoyi, hawan Isa sama ya kasance da wani yanayi lokaci guda na jiki da ruhaniya tare da juna.[35] An naƙalto daga Imam Rida (A.S) cewa bayan hawan Isa sama, a lokacin da yake tsakanin sama da ƙasa ne aka karɓi ransa, sannan aka tafi da shi sama, a can ne aka dawo da ransa cikin gangar jikinsa.[36]
Dawowar Isa (A.S) a zamanin bayyanar Imam Mahadi (A.S) ana ɗaukarsa matsayin tabbataccen al'amari da zai faru[37] wanda Musulmi suka yi ittifaki kansa.[38] Wasu malaman tafsiri, aya ta 46 suratul alu imran[39] da aya ta 159 suratul nisa'i[40] suna ganin suna alaƙa da wannan maudu'i. A cikin madogaran Ahlus-Sunna an kawo riwayoyi 28[41] cikin madogaran Shi'a kuma an kawo riwayoyi 30 mustafiza[42] game da dawowar Isa (A.S).
Bayanin kula
- ↑ Fakhr Razi, al-Tafsir al-Kabir, 1420 Q., Jild 11, Safa 262; Qira'ati, Tafsir Noor, 1388 Sh., Jild 2, Safa 207.
- ↑ Reza'i, “Barras-i Tatbiqi Mi'raj al-Nabi (S.A.W.) wa ‘Uruj Isa (A.S.),” Safa 157.
- ↑ Tabari, Tarikh al-Tabari, 1387 Q., Jild 1, Safa 585.
- ↑ Qomi, Waqa'i' al-Ayyam, Nashir Noor Mataf, Safa 79.
- ↑ Tabari, Tarikh al-Tabari, 1387 Q., Jild 1, Safa 585.
- ↑ Ibn Kathir, al-Bidaya wa al-Nihaya, 1407 Q., Jild 2, Safa 95.
- ↑ Kulayni, al-Kafi, 1407 Q., Jild 1, Safa 457.
- ↑ Injil Luka, Bab 23, Aya 32–34.
- ↑ Injil Matiyu, Bab 27, Aya 50.
- ↑ Injil Luka, Bab 23, Aya 50–54.
- ↑ Injil Luka, Bab 24, Ayat 1–3.
- ↑ Injil Matiyu, Bab 28, Ayat 16–20.
- ↑ Injil Markos, Bab 16, Aya 19.
- ↑ Bigdeli, “Muqayasa Didgah ‘Uruj wa Raj'at Hazrat Isa (A.S.) dar Islam wa Masihiyat,” Safa 34.
- ↑ Ma'refat, Shubuhat wa Rudud hawl al-Qur'an al-Karim, 1423 Q., Safa 102.
- ↑ Surah An-Nisa, Aya 157.
- ↑ Tabatabai, al-Mizan, 1417 Q., Jild 5, Safa 132.
- ↑ Modarresi, Man Hadi al-Qur'an, 1419 Q., Jild 2, Safa 248.
- ↑ Tabrisi, Majma' al-Bayan, 1372 Sh., Jild 2, Safa 759.
- ↑ Makarem Shirazi, Tafsir Namune, 1374 Sh., Jild 2, Safa 569.
- ↑ Ma'refat, Shubuhat wa Rudud hawl al-Qur'an al-Karim, 1423 Q., Safa 106.
- ↑ Bigdeli, “Muqayasa Didgah ‘Uruj wa Raj'at Hazrat Isa (A.S.) dar Islam wa Masihiyat,” Safa 37.
- ↑ Tabrisi, Majma' al-Bayan, 1372 Sh., Jild 2, Safa 759.
- ↑ Mughniyah, al-Tafsir al-Kashif, 1424 Q., Jild 2, Safa 72.
- ↑ https://www.preciousbloodsistersdayton.org/ha/2021/05/10/may-16-ascension-a-sunday-scriptures-blog/
- ↑ Mughniyah, al-Tafsir al-Kashif, 1424 Q., Jild 2, Safa 71; Zamakhshari, al-Kashshaf, Jild 1, Safa 366.
- ↑ Bigdeli, “Muqayasa Didgah ‘Uruj wa Raj'at Hazrat Isa (A.S.) dar Islam wa Masihiyat,” Safa 37.
- ↑ Mughniyah, al-Tafsir al-Kashif, 1424 Q., Jild 2, Safa 71.
- ↑ Sayyid Qutb, Fi Zilal al-Qur'an, 1412 Q., Jild 2, Safa 802.
- ↑ Maraghi, Tafsir al-Maraghi, Beirut, Jild 6, Safa 15.
- ↑ Ma'refat, Shubuhat wa Rudud hawl al-Qur'an al-Karim, 1423 Q., Safa 106; Maraghi, Tafsir al-Maraghi, Beirut, Jild 6, Safa 15.
- ↑ Sa'di, Sharh al-Nasfiya, 1380 Sh., Safa 322.
- ↑ Sa'di, Sharh al-Nasfiya, 1380 Sh., Safa 322.
- ↑ Maraghi, Tafsir al-Maraghi, Beirut, Jild 6, Safa 15.
- ↑ Reza'i, “Barras-i Tatbiqi Mi'raj al-Nabi (S.A.W.) wa ‘Uruj Isa (A.S.),” Safa 159.
- ↑ Shaykh Saduq, ‘Uyoon Akhbar al-Ridha, 1378 Q., Jild 1, Safa 215.
- ↑ Qazvini, Imam Mahdi (A.J.) az Wiladat ta Zuwa Zuhur, 1387 Sh., Safa 678.
- ↑ Kurani, Asr al-Zuhur, 1430 Q., Safa 245.
- ↑ Makarem Shirazi, Tafsir Namune, 1374 Sh., Jild 2, Safa 550.
- ↑ Tabatabai, al-Mizan, 1417 Q., Jild 5, Safa 134–135; Sadeqi Tehrani, al-Furqan, 1365 Sh., Jild 7, Safa 439.
- ↑ Kurani wa digaran, Mu'jam al-Ahadith al-Imam Mahdi (A.J.), 1428 Q., Jild 2, Safa 399–493.
- ↑ Bakhshi, “Barras wa Tabyin Naqsh Hazrat Isa (A.S.) dar Dauran Pas az Zuhur Imam Zaman (A.J.),” Safa 116.
Nassoshi
- Bigdeli, Hasan, “Muqayasa Didgah Uruj wa Raj'at Hazrat Isa (A.S.) dar Islam wa Masihiyat,” Mujalla Ma'arif al-Qur'an wa ‘Itrah, Shekara ta 2, Lamba 5, Payiz 1395.
- Fakhr Razi, Muhammad bin Umar, Mafatih al-Ghayb, Beirut, Dar Ihya' al-Turath al-Arabi, Chap Sahu, 1420 Q.
- Kulayni, Muhammad bin Ya'qub, al-Kafi, Muhhaqq wa Musahhah: Ali-Akbar Ghafari, Muhammad Akhundi, Tehran, Dar al-Kutub al-Islamiyah, Chap Chaharum, 1407 Q.
- Kurani Amili, Ali, Asr al-Zuhur, 1408 Q., Bi-ja, Bi-na.
- Kurani, Ali wa digaran, Mu'jam al-Ahadith al-Imam Mahdi (A.S.), Qom, Intisharat Masjid Muqaddas Jamkaran, 1428 Q.
- Maraghi, Ahmad bin Mustafa, Tafsir al-Maraghi, Dar Ihya' al-Turath al-Arabi, Beirut, Bi-ta.
- Ma'refat, Muhammad Hadi, Shubuhat wa Rudud hawl al-Qur'an al-Karim, Qom, Moassasa Farhangi Intisharati al-Tamhid, 1423 Q.
- Modarresi, Sayyid Muhammad Taqi, Man Hadi al-Qur'an, Tehran, Dar Mohibi al-Husayn, Chap Awwal, 1419 Q.
- Mughniyah, Muhammad Jawad, Tafsir al-Kashif, Tehran, Dar al-Kutub al-Islamiyah, Chap Awwal, 1424 Q.
- Preciosbloodsisters
- Qazvini, Muhammad Kazim, Imam Mahdi (A.S.) az Wiladat ta Zuwa Zuhur, Qom, Nashr al-Hadi, 1387 Sh.
- Qazvini, Muhammad Kazim, Imam Mahdi (A.S.) az Wiladat ta Zuwa Zuhur, Qom, Nashr al-Hadi, 1387 Sh.
- Qira'ati, Mohsen, Tafsir Noor, Tehran, Markaz Farhangi Dars-hayi az Qur'an, 1388 Sh.
- Qira'ati, Mohsen, Tafsiri Noor, Tehran, Markaz Farhangi Dars-hayi az Qur'an, 1388 Sh.
- Qomi, Abbas, Waqa'i' al-Ayyam, Nashir Noor Mataf, Qom, Bi Ta.
- Qomi, Abbas, Waqa'i' al-Ayyam, Nashir Noor Mataf, Qom, Bi Ta.
- Reza'i, Amina, “Barras-i Tatbiqi Mi'raj al-Nabi (S.A.W.) wa ‘Uruj Isa (A.S.),” Majalla Hadith wa Andishe, Lamba 13, Bazara da Hafsun 1391 Sh.
- Sadeqi Tehrani, Muhammad, al-Furqan fi Tafsir al-Qur'an bil-Qur'an, Qom, Intisharat Farhang Islami, Chap Duwum, 1365 Sh.
- Sayyid Qutb, Fi Zilal al-Qur'an, Beirut, Qahira, Dar al-Shorouq, Chap 17, 1412 Q.
- Sa'di, Abdulmalik Abdulrahman, Sharh al-Nasfiya fi al-‘Aqidah al-Islamiyah, Sanandaj, 1380 Sh.
- Shaykh Saduq, ‘Uyoon Akhbar al-Ridha (A.S.), Muhhaqq wa Musahhah: Mahdi Lajvardi, Tehran, Nashr Jahan, Chap Awwal, 1378 Q.
- Tabari, Muhammad bin Jarir, Tarikh al-Tabari (Tarikh al-Umam wa al-Muluk), Tahaqiq: Muhammad Abul-Fazl Ibrahim, Beirut, Dar al-Turath, Chap Duwum, 1387 Sh.
- Tabatabai, Sayyid Muhammad Husayn, al-Mizan fi Tafsir al-Qur'an, Qom, Daftar Intisharat Islami, Chap Panjum, 1417 Q.
- Tabrisi, Fazl bin Hasan, Majma' al-Bayan fi Tafsir al-Qur'an, Muqaddimah: Muhammad Jawad Balaghi, Tehran, Nasir Khosrow, Chap Sahu, 1372 Sh.
- https://www.preciousbloodsistersdayton.org/ha/2021/05/10/may-16-ascension-a-sunday-scriptures-blog/
- Ibn Kathir Dimashqi, Isma'il bin Umar, al-Bidaya wa al-Nihaya, Beirut, Dar al-Fikr, 1407 Q.
- Sa'id Bakhshi، «بررسی و تبیین نقش حضرت عیسی(ع) در دوران پس از ظهور امام زمان(ع)»،Jaridar Mashriq Maw'ud, Shekara ta 14, Lamba 53, Bazara 1399 Sh.