Jump to content

Daƙiƙa:Hankali

Daga wikishia

Hankali (Larabci: العقل) ɗaya ne daga cikin ƙarfin basira na ɗan Adam kuma ana lissafa shi daga dalliali huɗu da ake amfani da su lokacin fitar da hukunce-hukuncen shari'a a fiƙihun Shi'a. A koyarwar Muslunci hankali yana da muhimmanci na musamman, ana ɗaukarsa matsayin hujja kan mutum kamar Annabawa. Cikin ba'arin riwayoyi an lissafa shi matsayin farkon abin da Allah ya fara halitta.

Masana ilimin yadda ake samun sani (Epistemologists), suna la'akari da hankali matsayin ƙarfi da ake amfani da shi don fahimtar ma'anoni na gama-gamari, kuma suna ganin yana da ayyuka biyu, shuhudi (Fahimtar abubuwan da suke bayyane kai tsaye) da kashafi (Gano ilimin nazari da na ƙa'ida), sun karkasa hankali zuwa kashi biyu aƙlul nazari (Hankali na nazari) da aƙlul amali (Hankali na aiki), aƙlul nazari yana fahimtar gaskiyar abubuwa, a daidai lokacin shi kuma hankali amali yake da aiki na ba da shawarwari da umarni.

Hankali a kusa da Kur'ani, sunna da ijma'i, madogarai ne huɗu da ake fitar da hukunce-hukunce shari'a daga cikinsu a mazhabar Shi'a. Malaman Shi'a ta hanyar hankali suna tabbatar da ba'arin ƙa'idojin ilimin fiƙihu da ilimin usul.

Madogarar Sani

Masana ilimin yadda ake samun sani (Epistemologists) suna ɗaukar hankali matsayi ɗaya daga madogaran samun sani kamar dai misalin ji, kuma sun yi imani cewa mutum ta hanyar hankali yana fahimtar gama-garin ma'anoni; akasin ji wanda ta hanyar tsanantuwa da shi ne ake fahimtar ƙananan abubuwa.[1] cikin ilimin yadda ake sani, an yi bayani nau'in ayyuka kala biyu ga hankali: ayyuka na shuhudi wanda mutum ta hanyarsu ne yake fahimtar ilimomi da bayanai na farko, da ayyuka na hujja wanda suke taimakawa mutum zuwa ga samun sabbin ilimomi, daga ayyuka na farko na hankali ake iya fahimtar abubuwan da suke a bayyane da ba sa buƙatar shaidu (Al-Badihiyyatu) ko (Self-evident truths), kuma daga aiki na biyu na wannan ilimi da kuma ma'arifofi na nazari ne ake samun ilimomi da fahimtar tunani (Theorical knowledge) .[2]

Aƙlul Nazari Da Aƙlul Amali

Masana sun kasa hankali zuwa kashi biyu, aƙlul nazari da aƙlul amali, aikin aƙlul nazari shi ne fahimtar gaskiyar abubuwa, aikin aƙlul amali shi ne ba da umarni. Wasu masana sun yi imani da cewa babu batun cewa mutum yana da nau'ukan hankali guda biyu masu zaman kansu; bari dai kaɗai yana tare da wani ƙarfi guda ɗaya rak wanda shi ne hanyar da yake amfani cikin fahimta. Bisa wannan mahanga, bambance-bambance tsakanin aƙlul nazari da amali suna komawa ga abubuwan da ake iya fahimta.[3] A ra'ayin Muhammad Baƙir Sadar aiki aƙlul nazari shi ne fahimtar gaba ɗaya daga nau'in sani da ganewa (sanin Abubuwan da ya kamata a sani) bai da wata alaƙa da muƙamin aiki, manufarsa fahimta da sanin gaskiyar abubuwa, kamar: nau'in ƙa'idojin ilimin manɗiƙ, lissafi, falsafa da kalam (Aƙida) da suka kasance daga maƙalolin sani da imani, kamar ace "Ɗaya rabi ce na biyu" ko kuma "Dauri da tasalsuli ya gurɓata" Ma'ana zagaye da juyawa a guri guda, kamar ace ba zan tashi ba sai Zaidu ya tashi shima ya ce ba zai tashi sai wane ya tashi, haka dai a yi ta miƙewa ba iyaka.[4]

Jawadi Amoli masanin falsafa da aƙida ya tafi kan cewa ilimi da tunanin mutum yana kasancewa daga aƙlul nazari, amma aiki da motsin zuciyar mutum aƙlul amali yake konturol ɗinsu da jagoranci kansu, saboda haka shawo kan ɗagawar ilimi kamar wahami, (Tsinkaye mara tushe), hiyali, ƙiyasi da zato suna ƙarƙashin aƙlul nazari, amma daidaito da sarrafa bore da kurakuren sha'awa da fushi aiki ne na aƙlul amali. Saboda haka baki ɗayan al'amura na fahimtar mutum da suke daga launin ilimi da tunani, suna ƙarƙashin jagoranci da ikon aƙlul nazari, amma aiwatar da hukunce-hukuncen Allah da al'amura na motsin mutum da suke daga launin aiki, to suna ƙarƙashin iko da jagorancin aƙlul amali. malamin yana ganin cewa iyakokin ayyukan aƙlul nazari da aƙlul amali gaba ɗaya suna da bambanci. Duk da cewa dukkansu suna daga sha'ani da ayyukan ran na mutum, a wani bayanin daban "Aƙlul nazari ƙarfin doka ne mai tsara abubuwa, shi aƙlul amali yana matsayin ƙarfin aiwatarwa, amma a gaskiya asalin shugaba shi ne aƙlul nazari, saboda shi aƙlul amali yana karɓar umarni daga aƙlul nazari, aƙlul nazari yake bayar da fatawa mene ne halal mene ne haram, mene ne mummuna mene ne kyakkyawa, mene ne gaskiya mene ne ƙarya".[5]

Matsayin Hankali A Mahangar Gazali

Gazali cikin littafin "Mi'iyarul Ilmi" bayan ya kawo ra'ayoyi masana falsafa na ƙasar tsohuwar Girka da malaman Muslunci yace abin nufi daga hankula sune: 1 hankali wanda a wurin baki ɗayan gama-garin mutane. 2 hankali a gurin malaman aƙida. 3 hankali a gurin malaman falsafa, Gazali ya bayyana cewa hankali a gurin gama-garin jama'a shi ne ingancin da lafiyar asalin halittar ɗan Adam (Fiɗra ta farko) wanda yake iya bambance kyau da muni, ko kuma wanda yake iya samun gamammun ƙa'idoji na gaba ɗaya ta hanyar tajriba (Gwaji) kuma yake iya fahimtar muradunsa da manufofinsa ta hanyar amfani da wasu ma'noni da tunani. A wasu lokutan yana la'akari da shi da ma'ana wadda take da alaƙa ta kusa-kusa da mutunci, nutsuwa, da zaɓi da ikon yanke hukunci. A gurin Gazali hankali da malaman aƙida sukai la'akari da shi a hankali, shi ne hankali da ma'ana Aristo a cikin littafinsa mai suna Al-Burhan, ma'ana tunani da kuma tabbace-tabbace na halitta, waɗanda daga su ne ilimi yake samuwa a cikin rai ta hanyar koyo, tunani da kuma neman sani, haka kuma yana cewa hankalin da ake nufi a ma'anar malaman falsafa shi ne wasu ma'anoni da al'amura daban-daban, wasunsu suna da alaƙa da ilimin da ya shallake halitta (Metapyhsic) kamar hankula masu rabuwa da jiki (Material) yayin da wasu suke fassara hankali matsayin wani ƙarfi daga rai.[6]

Haka kuma, Gazali a cikin littafinsa mai suna Ihya'ul Ulumi cikin wata rarrabawa ta daban ya rarraba hankali zuwa hankali na ɗabi'a wanda da shi ne mutum yake bambantuwa daga dabbobi da hankali a ma'anar ilimi da sanin abubuwan da suka zama larura a san su, wanda ta hanyar ilimi da ma'arifa da suka zama na larura da yake bayyana cikin yaro mumayyazi (Wanda yake iya bambance abubuwa) haka nan hankali yana nufin ilimi da ma'arifa da yake samuwa ta hanyar gwaji da sharuɗɗa da halin da mutum yake rayuwa a ciki, sannan daga cikin sauran rabe-raben Gazali na hankali akwai hankali na ɗabi'a da hankali da ake samu ta hanyar ji, na farko shi ne dai wannan ilimi na larura wanda ya kasance tare da ɗan Adam tun farkon zuwansa duniya, amma na biyu ma'ana hankali da ake samu ta hanyar ji da koyon abubuwa da gogewa shi ne wanda yake a matsayin ilimin da ake samu ta hanyar ƙoƙari da koyo.[7]

Matsayin Da Hankale Yake Da Shi A Muslunci

A cewar Murtada Muɗahhari, babu wani addini da ya muhimmantar da hankali kamar yadda Muslunci ya yi.[8] Cikin wata riwaya da aka naƙalto ta daga Annabi Muhammad (S.A.W) ya zo cewa ana fahimta baki ɗayan kyawawan ayyuka ta hanyar hankali, babu addini ga wanda ba shi da hankali.[9] Imam Kazim (A.S) yana la'akari da hankali kamar Annabawa da Imamai da suke matsayin hujjar Allah ta zahiri kuma hujjarsa a kan bayinsa.[10] Cikin adadin wasu riwayoyi da suka zo ta hanyar Shi'a da Ahlus-Sunna an yi ishara dangane da hankali da kuma kasancewarsa farkon halittar Allah. Cikin wata riwaya a cikin wata gaɓa da Annabi (S.A.W) yake magana da Imam Ali (A.S) ya yi bayani yana cewa : ya Ali kamar yadda hankali ya kasance farkon halittar Allah ta'ala kuma bayan halittarsa ya ce masa : ka matso gaba sai ya matsa gaba, ya ce masa ka juya baya, sai ya juya baya, ya ce ina rantsuwa da izzata da girmana ban halicci wani abu da nafi so fiye da kai ba kuma da kai ne zan ba da lada kuma da kai ne zan yi uƙuba[11] [Tsokaci 1] Haka nan Gazali a cikin Ihya'ul Ulumi ya naƙalto daga Annabi da wannan ma'ana cewa hankali shi ne farkon abin da Allah ya fara halitta. «أوّل ما خلق اللّه العقل» (Farkon abin da Allah ya fara halitta shi ne hankali).[12] Cikin mazhabar Shi'a ƙari kan asalan aƙida da ake tabbatar da su ta hanyar hankali,[13] Ba'arin ƙa'idojin fiƙihu da hukunce-hukunce fiƙihu suma ana tabbatar da su ne ta hanyar hankali.[14] Jawadi Amoli malamin falsafa da aƙida a Shi'a tare da ishara ga layin ƙarshen huɗuba mai tarin albarka ta Kulaini a gabatawar Usulul Al-Kafi: ya rubuta : «إِذْ كَانَ الْعَقْلُ هُوَ الْقُطْبَ الَّذِي عَلَيْهِ الْمَدَارُ وَ بِهِ يُحْتَجُّ وَ لَهُ الثَّوَابُ وَ عَليْهِ الْعِقَابُ» (Idan hankali shi ne ginshiƙin da a kansa komai yake zagayawa, kuma a kansa ake kafa hujja da shi ne ake ba da lada da shi ne ake yin uƙuba) tare da amfani da wannan jumla ya bayyana cewa hankali shi ne ginshiƙin al'adun Muslunci, kuma ginshiƙi na mai tunani da ilimi a Muslunci. Haka kuma ya ce wannan huɗuba Mir Damad a cikin littafin Arrawashihus Samawiyya ya yi sharhi kuma sirri da dalilin sharhin Mulla Sadra kan littafin Al-Kafi shi ne dai wannan huɗuba ta Kulaini.[15]

Matsayin Da Hankali Yake

A cewar Muhammad Rida Muzaffar daga malaman fiƙihu na ƙarni na 14 hijira ƙamari, hankali tare da Kur'ani da sunna da ijma'i ya kasance daga madogarai huɗu da ake fitar da hukunce-hukuncen shari'a.[16] Malaman fiƙihu na Shi'a cikin ijtihadi, suna yawan amfani da hankali. Ba'ari daga wurare da aka yi amfani da hankali, akwai cikin rubuta ilimin Usulul fiƙhi, wani ba'arin ayyuka na hankali cikin tsarin fitar da hukuncin na shari'i sun kasance kamar haka:

  • Madogara ta hukuncin shari'a tare da Kur'ani da sunna: Hankali a wani lokaci cikin sura cin gashin kai kai tsaye yana ba da wasu hukunce-hukuncen shari'a, kamar hukunce-hukuncen da suke zuwa ta hanyar fahimtar Husnu da Ƙubhu aƙli (Kyawu da sharri na hankali)[Tsokaci 2] wani lokaci kuma cikin kasancewa jikin wani hukunci na shari'a yana tabbatar da wani hukuncin shari'a na daban, misalin idan muka tabbatar da cewa akwai dangantaka tsakanin wani hukunci na shari'a da wani hukunci na hankali zamu kai ga fitar da wani hukunci daban.
  • Tabbatar da ingancin matanan addini: Daga cikin sharuɗɗan ingancin riwaya da aiki da abin da yake cikinta, shi ne kada riwayar ta saɓawa tabbataccen hukunci na hankali, alal misali kasantuwar isma da rashin aikata lefin Annabi (S.A.W) ya tabbatu ne da yankakken dalili na hankali, duk wata riwaya da take kore ismarsa da rashin aikata lefinsa ana la'akari da ita matsayin riwaya mara inganci.
  • Taimakawa cikin fitar da hukunci daga Kur'ani da sunna: Ba'ari daga ƙa'idojin fiƙihu wanda tare da amfani da su ana fitar da hukunce-hukunce daga Kur'ani da sunna, ana gano su ne da taimakon hankali.[17]

Matsayin Da Hankali Yake Da Shi A Falsafa

Akasin masu karkata kan abubuwa na zahiri kawai (Materialist) waɗanda aka san su da ƙaryata duk wani abu da ba na zahiri ba[18] haƙiƙa a cikin falsafa da ililimin aƙida na Muslunci an tabbatar da abubuwa da ake kiransu da halittu da ba su da samuwa ta zahiri da jiki. Misalin Allah, hankali, mala'iku, halittu na misali da rai. Masana falsafa sun karkasa halittu zuwa ga cikakkun halittu marasa jiki da tauyayyu, kuma suna la'akari da cikakkun halittu matsayin wasu halittu wanda a cikin zatinsu da aikinsu babu wata alama da zata iya kasancewa a cikinsu nan gaba (Potentiality) a cikin asali ko a aikinsu, kaɗai su cikakken aiki ne kawai (Pure Actuality).[19] Masana falsafa kan asasin ƙa'idar wahid (Abu guda) sun yi imani cewa farkon halitta da yake fitowa daga Allah yana da matuƙa sauƙi da sauƙaƙar kasancewa, wannan halitta bai da mada (Jiki) ko siffofin halitta mai jiki. Haka kuma kan asasin ƙa'idar Imkanul Al-ashraf (Yiwuwar mafi girma) akwai wasu halittu bayan farkon halitta wanda sam ba su da ko wace irin siffofin jiki. Ana kiran waɗannan halittu da hankali, abin nufi daga alamul aƙli (Duniyar hankali) ko jabrut shi ne matsayin da waɗannan halittu suke da shi a duniyar halitta.[20]

Bayanin kula

  1. Husain-zada, Mabani Ma’rifat Dini, 1393 Sh, shafi 38.
  2. Malikiyan, Rahi be Rahayi, 1381 Sh, shafi 253.
  3. Sadiqi, Aqlaniyyat Iman, 1386 Sh, shafi 43.
  4. Sadr, Muhammad Baqir, Durus fi Ilm al-Usul, 1406 Q, juzu’i na 2, shafi 256.
  5. Jawadi Amuli, Tafsir Tasnim, juzu’i na 20, shafi 414.
  6. Ghazali, Mi’yar al-Ilm, 1993 M, shafi 25.
  7. Ghazali, Ihya’ Ulum al-Din, an-nashir Dar al-Kitab al-‘Arabi, juzu’i na 1, shafi 146.
  8. Mutahhari, Majmu’at Asar, 1383 Sh, juzu’i na 23, shafi 184 da 185.
  9. Ibn Shu’uba Harani, Tuhaf al-‘Uqul, 1404 Q, shafi 54.
  10. Kulaini, al-Kafi, 1407 Q, juzu’i na 1, shafi 16, hadisi na 12.
  11. Tabarsi, Makarim al-Akhlaq, an-nashir Mu’assasat al-A’lami lil-Matbu’at, shafi 442.
  12. Ghazali, Ihya’ Ulum al-Din, an-nashir Dar al-Kitab al-‘Arabi, juzu’i na 8, shafi 8.
  13. Rabbani Golpaygani, Daramadi be Shi’a-shenasi, 1392 Sh, shafi 139.
  14. Rabbani Golpaygani, Daramadi be Shi’a-shenasi, 1392 Sh, shafi 144 da 145.
  15. https://javadi.esra.ir/fa/w/پیام-آیت-الله-العظمی-جوادی-آملی-به-مناسبت-روز-بزرگداشت Mulla Sadra
  16. Muzaffar, Usul al-Fiqh, 1430 Q, juzu’i na 1, shafi 51.
  17. Diya’i-Far, “Jaigah-e Aql dar Ijtihad”, shafi 230–234.
  18. Fayyadi, Ilm an-Nafs Falsafi, 1393 Sh, shafi 199.
  19. Tabataba’i, Nihayat al-Hikma, 1434 Q, juzu’i na 1, shafi 170–171.
  20. Tabataba’i, Nihayat al-Hikma, 1434 Q, juzu’i na 2, shafi 290–298.

Tsokaci

  1. يا علي : إن أول خلق خلقه الله عزوجل العقل ، فقال له : أقبل فأقبل ، ثم قال له : أدبر فأدبر ، فقال : وعزتي وجلالي ما خلقت خلقا هو أحب إلي منك ، بك آخذ وبك أعطي وبك أثيب وبك أعاقب.
  2. Mustaƙillatul Aƙliya: su ne abubuwan da hankalin mutum kaɗai zai fahimci cewa suna da kyau ko kuma ba su da kyau, ko wajibi ne ko haramun ne, ko da ba a samu umarni ko hani daga Alƙur’ani ko Hadisi ba.

Nassoshi

  • Diya’i-Far, Sa’id, “Jaigah-e Aql dar Ijtihad”, Naqd wa Nazar, shafi 31 da 32, 1382 Sh.
  • Ibn Shu’uba Harani, Hasan bin Ali, Tuhaf al-ʿUqul, tahkik da tashihi Ali-Akbar Gaffari, Qum, Jami’ar Mudarrisina, bugun na biyu, 1404 Q / 1363 Sh.
  • Jawadi Amuli, Abdullah, Tafsir Tasnim, Markaz al-Bainal-Milali li-Nashr Isra, juzu’i na 20.
  • Kulaini, Muhammad bin Ya’qub, al-Kafi, Tehran, Dar al-Kutub al-Islamiyya, bugun na huɗu, 1407 Q.
  • Malikiyan, Mustafa, Rahi be Rahayi, Tehran, Negah Mu’asir, bugun na biyu, 1381 Sh.
  • Mutahhari, Murtada, Majmu’at Asar, Tehran, Intisharat Sadra, bugun farko, 1383 Sh.
  • Muzaffar, Muhammad Rida, Usul al-Fiqh, Qum, Intisharat Islami, bugun na biyar, 1430 Q.
  • Nasir Khusraw, Diwan Nasir Khusraw, 1385 Sh, Nashr Ilm, Tehran.
  • Rabbani Golpaygani, Ali, Daramadi be Shi’a-shenasi, Qum, Markaz al-Bainal-Milali li-Tarjama wa Nashr al-Mustafa, bugun na huɗu, 1392 Sh.
  • Sadiqi, Hadi, Aqlaniyyat Iman, Qum, Kitab Taha, bugun farko, 1386 Sh.
  • Sadr, Muhammad Baqir, Durus fi Ilm al-Usul, Beirut, Dar al-Kutub al-Lubnaniyya, bugun na biyu, 1406 Q.
  • Tabarsi, Hasan bin Fadl, Makarim al-Akhlaq, an-Nashir Mu’assasat al-A’lami lil-Matbu’at, Beirut, ba tare da shekara ba.